[Advertisements⬇️]

ZEENAT YAR JARIDAH CHAPTER 7 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

ZEENATU YAR JARIDAH
CHAPTER 7
Zeenatu gudu takeyi a cikin dajin, har karfinta ya kare, nan ta fadi kasa still batai kasa a gwiwaba ta mik’e 
Dakyar ta ja kafarta ta kara gaba burinta kawai Tayi nisa da gidan azzaluman chan OO
Bangaren mahaifiyarta kuwa tun randa zinatu ta fita bata dawo ba hankalinta ya kasa kwanciya komai ma be mata dadi Uwa kenan Tayi kuka, har ta gaji har Wajen aikinsu Taje suma sukace sunsan something is wrong but Tayi hakuri insha Allah Zinatu nanan zata dawo, Suma ba zama sukai ba binciken inda take sukeyi 
Se a time din mahaifiyarta tadan sama natsuwa but Kullun cikin addua takeyi Allah ya dawo mata da diyarta lafiya, Dama seda ta Fada mata ita batasan aikin nan Saboda aikin hatsarine, Wani zuciya kuma tace mata ko wani Dan Adam a rayuwa da jarabtan da yake samun shi…wannan kenan 
Mudansir Bayan sun fita ne yaji gabanshi yai mugun faduwa, Nan ya tsaya chak kamar me tino wani Abu! Nan Hankalinshi gaba daya ya Tafi wajen ‘Zeenat Yar jarida’ a cikin su ne wani yake tambayar shi Oga lafiya kuwa? Mudansir murmushi yayi yace wannan babyn ta fado mun arai dan na kosa na mallaketa_ Su kace” Oga kar ka damu ai Yar jarida ta zama taka! Smile yayi, nan dai suka ci gaba da taflya but she kadai yasan what he’s feeling Dan gabanshi bugun Tara Tara ma yakeyi kawai dakewa yayi irin na Mazan nan Yasan he’s sure something terrible Zai sameshi “Zeenat Kuwa Bayan ta tabbata ta Bar bakin dajin, Ga ko Ina na jikinta ciwo yakeyi, Waje ta samu Ta zauna Chan ta hango wani bishiyan mangaro se a time din taji wani yunwa nan ta Dan rarrafa duk da bawani dadi takejiba Dan ba karamar bakar wahala tasha ba ko ince take sha ma Takawa tayi taje ta ballo mangaro guda uku sunyi jajir ta zauna ta fara sha se ta Dan dawo hayyacinta 
Nan wani mugun kishin ruwa taji ta duba Cikin Dajin nan gabas da kudu yamma da arewa ba alaman Ruwa Ta sama waje ta zauna kenan chan ta hango Wasu maza suna taflya, da alamar sun hango ta, 
Dan gudu suke yi burinsu su cimmata 
Nan ta yarda mangoron da ke hannunta Ta kankame Jakarta sosai Ta arta ana kare Gudun fitan rai takeyi Dan batasan inda zata dosa ba, Allah yasa ma tabar dajin Ta fara shugowa kauyuka nan karfinta ya kare gaba daya nan ta fadi _sumammiya_ kusa da wani garken shanaye (Shanu) 
Chan bayan kamar awa daya saiga wani bafulatani yazo duba shanayensa 
Ya ga mutun A kwance da jaka kankame tare da ita, Bafulatinin ya tsaya na yan Mintina ko Zai ga motsinta, shuru shuru ba alama nan dai ya danyi tafiya kadan yaje ya Kira matar shi 
Da farko sun tsorata Dan wannan zamanin ba kowa ne zaka gani ka temakeshi ba, Nan dai sukai shahada ganin jikinta duk ta kakkarce gata da alamar gajiya a tare da ita suka dauketa Suka kai cikin gidansu 
Wuni daya kwana har wuni zeenatu bata farfado ba gashi bama cikin gari ba balle akaita a duba ta Tun da Zeenat ta zo gidan inna wuro taji tana kaunar yarinya 
Kwananta daya da wuni bata farfado ba, A kwana na biyu zeenat ta fara motsi sakamakon Jigatan da Tayi sosai 
Inna wuro tana ganin haka nan suka fara Dan mata jikejike na magani, tana Dan sha Cikin ikon Allah cikin sati daya Zeenat ta dawo normal Batai mamakin ganin ta a gidan ba Dan Tasan insha Allah tana safe hand Nan Inna wuro da Baba haye sunan da suka Fada mata kenan Suka zaunar da ita suna mata sannu, Taji matukar dadi sosai yanda suke kula da ita sun maida ita tamkar Yar cikin su, bata boye masu komai nataba Sun tausaya mata matuka 
Sukace tai zamanta har ta gama gigijewa in shaa Allah zasuyi mata jagora har gida tace toh ba komai, nan ta sakejiki dasu sosai Inna wuro na debe mata kewa sosai, Zeenat ko bata bari inna wuro tai wani aiki komai ita takeyi, A yanzu kam Zeenat ta saba dasu inna wuro Har makwabta tana Zuwa Amma kowa kallo daya ze mata yasan ba a kauyen take ba Dan kalarta daban ne…. Makwabtan Da take zuwa akwai yan yara kanana gidan kowa yana son zeenat Tana zaune dasu tana Dan koya masu ‘A B C D‘ duk da baganewa sukeyi ba Dan Kauye ne sosai Sai ga wata babban mota ta tsaya a kofar gidan Nan Yara suka fito a guje suna ‘Ga mota ga Mota’ abun yadan bata mamaki se kuma tai la’akari da kauye ne ba kowa ke ganin
mota ba itama tadan fito Kallo Dan rabonta da gani tun ran da ta gudu lol
Wani mutun ne Bezai wuce 40years ba ya fitO da ganin shigarsa ita tasan ‘LAWYER NE’ LAUYA ya shiga gidan yara suka bishi da gudu itakam tai gidan Inna wuro 
‘AHMAD‘ kenan Babban lauya da yake birni  Yazo kauyen ne gaishe da ka karshi,Ya hado mata sha Tara da arziki taji dadi sosai Da Lauya Ahmad zai tafi yace” yaga kamar wata Yar budurwa anan dazu
Kakarshi tace” eh anan makwabtan mu take, Yanaso ya tambaya a kirata amma se yai shuru yace” toh Kakas bari na tafi 
Ya fito kenan yara ma sun biyoshi Ya ci karo da Zeenat! Nan ta gaisheshi, Kallo daya shimayai mata Yaga tamai matukar kwarjini, Kamar zai furta wani Abu Kuma seyai shuru Yasa kai ya tafi ya shiga Motarshi, ltama zeenat da zuka hada ido ji tai yamata kwarj’ln’l, 
Lauya Ahmad tada motarshi yayi ya fara Barin kauyen but ji yake kamarya dawo dan Tinanin zeenat kawai yakeyi, Kallo daya yai mata Yaji yarinyar ta kwanta mai arai amma to a garin take? Meyasa be taba ganin ta ba And Kalar fatar ta baiyi kama Dana kauyen ba Dan Skin dinta a goge yake and the way she 
talk kasan ba Yar kauyen bane da wannan tinanin ya Isa gida 
‘WAYE AHMAD’ 
Ahmad wani Dan Tsohon Commi  ne A jahar Kaduna, an kashe iyayanshi a sanadiyyar yan fashi da suka shugo gidansu, Tun yana Dan 25years a gabanshi aka kashe lyayanshi. 
Da doctor yake Shirin zama amma tunda aka kashe mai iyaye ya chanza course ya dawo karanta Law, Saboda yayi alkawarin K0 yayane seya remake wasu, Saboda Irin badalaka da yan fashi suke ma mutane, basu ji basu gani ba azo har gida A kashe ma yan Uwa kana gani kanaji, Shi yasa tuni ya chanza course Ahmad Ba fari Sol bane but Yanada haske, ga natsuwa ga tausayin mutane, Gashi da girmama na sama dashi, yana da kyau sosai Dan mata har ribibi sukeyi akanshi, but basa gabanshi, Saboda a tinaninshi Idan ya biye wa mace bazai sama time din yin aikin shi yanda ya kamata ba 
Ahmad ajin Farko ne Wanda yan mata ke burin samu a zamanin nan Dan komai ya hada Indai fannin daukan wankane ga Iya speaking ga kallo daya yai miki sai Kinsan Shi namiji ne, Be cika magana ba  Kallon shi Yana bayyana abun dake mind dinshi, A takaice He’s damn Handsome ta ko ina!
°°°
Ahmad na dawowa gida wanka ya shiga bayan ya Fito ne ya bude fridge Dan yunwa yakeji coke ya dakko da ruwan faro yazo ya zauna, Wando ne ajikinsa se towel a saman wuyanshi ya d’aga Coke din kenan zaisha Zeenat ta fado mai arai, ajiye wa yayi wata zuciya kuma tace INA ruwanka da ita? Yar karamar ‘saki yayi yaci gaba da shan coke dinshi Dakyar fa cos zuciyarshi ta Riga ta Mutu da tinanin ‘Zeenat’ 
Bangaren su mudansir kuwa Sunje fashi sundawo dama tun a Hanya ya kudirta yau seya bata ma ‘Zeenat’ rayuwa kota halin kaka ne, dama tunda sukaje fashi ahanya gabanshi yaji yanata faduwa 
Suna shugo wa gidan da wani Dan iskan dariya mudansir ya shugo su kuma Se husir sukeyi irin na yan daban nan A chan fashin da sukaje suka Taho da wata kyakkyawar yarinya wai ta musu kyau suna shiga gidan suka jefata Daki, itama sun rabata da iyayanta 
Mudansir ne ya shiga yai Wanka a dakin da yake dashi a cikin gidan daga shi se wani vest da gajeren wando, Wardrobe dinshi ya bude ya dakko key dinshi na musamman ya taho Dakin da aka ajiye zeenat 
Yana sa key Ya bude ya shiga da wani Mugun dariya yana amaryace, Amaryace amaryace!!! Shuru yaji ba alamar mutun Dan bata falon Yar jarida Yar jarida Ina kika shiga? 
Nan ma yaji shuru, direct bayi ya wuce Anan idonshi yai arba da lnda Zeenat ta fita ta cilin Jakar ubanchan ya fadi_Sannan ya fito 
A kofar dakin yai wani irin Kara ‘lnaa Kukeeee’ gaba ki dayansu suka fito suka zube a gabanshi suna gamunan ranka ya Dadel! 
Idon mudansir Ne yayijajir yace” Ta gudu ta gudu! Gaba dayansu suma zare ido sukai ta gudu? Yace kwarai kuwa 
Nan hankalinsu ya tashi Dan Sunsan confirm Zeenat zataje takai Camera dinnan Dan gobe Monday kuma Dole zai Fuskanci hukunci 
A tsaya Mudansir yake Hawaye masu zafi suka buyomai fuska Yace” I‘m dead, Daya daga cikin su ne yace Wannan yarinyar semun nemota a duk inda take bata isa tasa Oganmu ya kare rayuwar sa cikin prison ba Mudansir yace” sai na wulakantaki zeenat Sai na kashe ki 
Wani a cikin su me sunajan Wuya yace” Oga saida nace maka a aikata lahira kace” a barta kana sonta, Kai kasan ba sonka takeyi ba she can do anything Dan ka wulakanta..Tsawa mudansir yai masa yace“ kaimun shuru ko a bakin aikin ka 
SANNAN ya kallesu Yace” Yanzu meye abunyi? Wani daga cikin su yace” wannan yafi karfin Lauyanka, Se Anje wajen Me gabatar da shari’a,yanzu ka kira lauyanka kace mai yarinyar nan fa ta gudu kuma kana ganin komai zata iyayi, In taso me shari’a a cika mai kudi da account yace ya kora karar daga koton 
Mudansir murmushi yayi yace” mai shi yasa nake sonka Saboda akwai ka da shap Brain, nan ko ya kira lauyanshi ya sanar dashi Zeenat ta gudu and zata Iya zuwa takai Camera dinnan Dan shi kadai ya rage, Gashi Gobe Monday, Nan take Lauyanshi yai kasa kasa da murya yace” kasan komai na kudi ne Na tabbata shima yana ganin kudi cike da account dinshi zaiyi burus da maganar, 0K mudansir yace” bari nama transfer Nan take ya aikamai da 1.5m yace mai 1m name shari‘a shi kuma ya dauka 500k Hmmm Kudi masu gidan rana!! 
Lauya na ganin alert, shima take ya tura ma me shari’a kudi dama already yana da acct details dinshi, 
Yana gani alert dama Gashi beda kudi sosai tun kan yasan waye ya turamai yace” tai mako me wannan Kudin ke bukata zan mai tin ba Lauyan mudansirya kira shi yake mai bayani yana so a kashe maganar ne Yace” OK OK angama kar kuji komai kuna tare dani Nan lauyan Shima ya kira mudansirya Sanar dashi yamai Godiya 
‘Washe GARI MONDAY’ 
Tun wuri aka zazzo kowa nason jin karshen mugun nan Mudansir Lauyan Zeenat yazo amma shuru ba ita ba labari, Da me shari’a ya ga haka se yai amfanl’ da damar yace an kora Wannan korafin nasu Zeenat tunda bata zo ba, da alamar rashin gaskiya a wannan lamarin, kan kace meye Koto ta dau yan gulmarmaki da Lalle Masu kudi suna abun da sukeso, kowa yaji ansan kudi aka basu akai shuru amma ba damar magana haka kowa ya tafl jiki a sanyaye se Tsinewa Mudansir ake, 
Maman shi itama najin haka taji dadi Dan dama itama seda ta kara basu kudi 
Hmmm shegiya naira 
Haka Lauyan Zeenat ya koma gida da bakin ciki Gashi number ta be shiga Yasan he’s sure wannan mugun mutumin ne yaje yasa aka boye ta, aranshi yace kome meye Akwai Allah kuma komun Daren Dadewa gaskiya zatai halinta 
Bangaren zeenat kuwa yau monday tasan confirm za’a nemeta Dan ta bada shaida, Haka 
nan ranarta wuni tana kuka dan tsabar bakin cikin a ranta tace Mudansir in shaa Allah seka wulakanta Inna wuro data ga haka tazo kusa da ita tace” yata meye ya sameki? Tun dazu kike kuka? Dariyaryake zeenat Tayi yace” mamana nake tunowa shi yasa, abun da yasa ta boye Mata tasan ko Bayanin me zatai mata bazata gane ba sbd a kauye suke ga Fulani da tsoro Idan taji labarin Hmm
Nan ta bata hakuri, Zeenat tace shikkenan, tana ganin ta flta ta dakko camera din tana kallon Abun dayai ma Aisha, wani bakin ciki taji tai tsaki, tace katon banza seka Yi Dana Sani 
Mudansir kwana biyu da faruwan abun Hankalinshi ya kwanta, amma Saboda banza ne Kullun yana cikin Tinanin zeenat kuma wai ze Aure ta!!!! Hmmmm wani Barin na zuciyarshi na fadamai yaje ya nemota 
oo
Bangaren Ahmad Kuwa tun Lokacin da yaje kauyan Yaga zeenat har yau dai Hankalinshi be kwanta ba 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]