ZEENAT YAR JARIDAH CHAPTER 5

ZEENAT YAR JARIDA
CHAPTER 5
Tana nan Zaune tsuru ta takure jakarta na hannunta 
Bata dawo hayyacin taba ballantana ta fahimci a inda take itadai gatanan ne kamar mutum mutumi jikinta amace ruwan sihirin da aka fesa mata bai sake taba wani dum! Takeji akwanyarta 
Karfe takwas na dare kwamanda yatako dakansa zuwa dakin da aka ajiye zeenatun Sarkin daki yana daga kofar dakin ta waje yana gadinta 
Ya bude masa dakin yashiga 
Ya kunna fitilar dake hannunsa daya shigo da ita Ya hasketa yataka har inda take akuryar dakin Idanunta arufe tamkar me bacci 
Abune akwalba ya tsiyayo ahannunsa ya yarfa mata a fuska 
Aiko dai tayi furgigit ta mike tsaye tana zare idanu 
Dakin ta fara karewa kallo kana ta dawo da ganinta gareshi 
Suffarsa babu kyan gani ya firgitata sosai saida taja da baya
Ta kare mishi kallo bak’i ne sosai kansa sai kyalli yake ba gashi kona kwayar zarra Ga manyan idanunsa kamar sa fito waje 
Hancinsa kato tamkar na boto rami bakinsa wawakeke lebensa kamar ganda Fadin fuskarsa baxata misaltuba 
Gashi kato irin masu fadin nan tamkar wani basamude 
Tayi karfln hali tace dashi ” mallam waye kai ? 
Yayi dariya yace ” kizauna tukunna sai ingaya miki koni waye ” 
Bata yarda dashiba ta sake watso masa wata tambayar ” Dan Allah ka gaya min kai waye 
kuma ina ne nan wayasa ku ku kawo ni nan din. Jin ta watso masa wadannan tambayoyin rututu yasa shima ya mike yace da ita 
” to tunda bazaki zauna ba bari na tafi kawai duk randa na sake dawowa na amsa miki tambayoyinki. 
Da taga da gasken taflyar zaiyl’ tuni ta zauna tana fadin ” shikenan na zauna fadamin. Yajuyo ya zauna shima 
Yace ” kinutsu zeenatu zan miki wasu tambayoyi nima. 
“Kintuna wanda yai miki waya tun biyar kika ki dagawa na kuma turo mk sako kika dawo da 
reply kikace mishi wawa mahaukaci? Ta jima tana tunowa can data tuno tace dashi 
” natuna mana wani ne da zai rainan hankali… ya katseta da cewa ” to ai gashi gabanki. Ta zaro idanu 
Yagyada kansa yace ” kwarai nine naturo mk sakon nan nakuma saka aka dauko min ke domin wannan me dan sahun da kuka hau yaro nane saida muka nemi gidanku ma tukunnan yataho gun aikinki 
Mamaki fal cikinta haba no wonder mana bai zuga mata kudin da wasu ke zugawa ba indare yafara kawo kai don inharyamma tayi sosai masu abin hawa tsada sukeyi sbd go slow Yakatseta da fadin ” kinyi mamaki ko? Ta baki gama mamakin bama har saikinji abinda yasa muka kawo ki nan 
Tambayar daya sake watso mata ta furgitata ce mata yayi ” ina camerar da aka dauki mudansir da yar aiki? Ta furgita ta razana ta kuna fara daukar haske Tace dashi ” wace camera kuma ? Ni bansan da zancen taba. 
Yayi wata shakiyyar ””dariya yace ” karya kikeyi domin tana hannunki ayanxuma nasan tana tare dake kuma baxan miki ta karfiba da hannunki da yardarki dole zaki bada don banayiwa mata ta karfi saidai ina me baki shawara daki mikota cikin lumana don inhar kikai mana gardama to tabbas kome na iya faruwa akanki. 
Tace ” ni babu abinda ke hannuna kawai ku barni na tafi ku nemi camera acan inda kuke ganin zaku samu ato. 
Ya gyada kansa yace ” to tunda haka kika ce zantafi zan barki kiyi tunani akan bayarwarki 
fitarki ko hanawarki zamanki na wasu shekaru ko ince ba ranar fitar ma. Yana gama fada yatashi zai tafi 
Da sauri ta mike tayi gunsa tana kuka tana fadin ” dan Allah kayi hkr kataimakamin 
kabarni inma inkoma gida wallahi babu camera aguna 
Yace da ita ” naki wasa ne ” yammata kima sani wannan dakin yazama naki na din din din gara ma kifara sabo dashi ga toilet can gefenki sarkin girki zai kawo miki abinci yanzun amma kisani sau biyu muke bada abinci inkinci na safe to sai na dare kona rana ba yanda bata yiyuwa inzamu fita aikin dare to na rana zaki samu tunda da dare bamanan inko 
bazamu fitanba to zaki iya samun na daren. Ya juya yafice daya gama mata bayanin 
Ta koma ta zauna ta takure ta kankamejakarta ajikinta domin camera din tana ciki bayarwa ne kawai bazatai ba koda zasu kasheta domin camerar nada matukar muhimmanci agunta sannan kuma ita zata taimaka ayi shari,a cikin sauki 
Sai ayanzu ta gano makasudin dayasa aka kawota nan da alamar ma dasa hannun mudansir aciki 
ltako tasha alwashin duk rintsi duk wahala saita fita a gidan nan kuma da camerar kota halin ka’ka …… 
Bakin cikin Zinatu na yanda wayarta babu service sannan cajinta yakusa karewa tecno ce android ta ringajan tsaki duk layinka nata babu network yasaka no service banda hakan da 
ayau ba sai gobe ba zataiwa jami,an tsaro waya tafada musu tunda wayarta da kudi 
Saidai kuma data tuna a dajin da take sai gabanta ya fadi domin bata ma san sunan dajin ba balle ta kwatanta inda take da alamar gidan yanada tsaro tunda yafurta mata bazata iya 
fitan be to gashi dako ma ansaka masa me tsaro tabbas Allah ne kadai zai iya flddata 
Ta tuno salloli biyu magriba da ishsha,i dake kanta ta kunna tochlight din wayarta taga haske ya bayyana tashige toilet din taganshi fes yasha tayels 
Tayo alwala ta fito tayi sallarta akan kafet din saida tayi sallolinta kana ta kwanta ta kudundune jakarta na katararta 
Bawai bacci zatayi ba kawai dai tana so tayi nazari ta nemo mafita 
Tana kwance cikin duhun taji anshigo dakin ana hasketa 
Atsorace ta tashi tana addu,a cikin ranta 
Sarkin girkine ya ajiye mata taliya jolouf ya fice kawai bece mata uffan ha 
Ta duba agogon wayarta taga tara na dare dan wulakanci sai yanzu za,a baiwa mutum abinci kenan yunwa taci ta cinyeshi aiko baxata ci ba yanda yakawoshi haka zata bar masa yazo da safe yadauke 
Hhhmmm ai da yunwa tace mata bata san hakan ba dole ckn dare ta tashi ta gashi da juyin da take tayi kan kafet cikinta yanata kugi ‘ 
Ai duka ta cinye taliyarwacce taji gishiri yafl magi yawa haka ‘tacinye dai badan taso ba 
girki salam kamar a bursin Da asuba kuwa tabi lokaci tayi sallarta akan lokaci 
Kafln gari yagama wayewa tabi dabarar data samo ta shiga toilet ‘a boye camerar nan acikin wani rubabben kwamin wanka da aka loda masa tayels da duwatsu 
Tananan kwance har wajen karfe goma na saflyar amma ba,a kawo abin kariba Tunanin mahaifiyarta ne kadai yadameta ba abin kariba Ta tabbata tana can tana wani hali tunda ko dare tayi bata iya bacci har sai intashigo 
Hawaye taji ya surnano mata Allah sarki rayuwa dama gwagwgonta ba sonta da irin wannan aikin takeba akullum abinda takejiye mata kenan fadawa irin wannan halin tunda 
tanajin akasarin halin da wasu yanjarida ke fadawa 
Mafarkin data tabayi akwanakin baya ya fado mata wanda wasu kartai sukaita binta a dokar daji akan saita basu plet CD ita kuma taki basu suka nemi su hallakaa ta Wato abinda zai faru da ita kenan shine aka nuna mata makamancin hakan kenan amafarki Tahau addu,ar kariya da kubuta 
Sarkin girki yashigo mata da buredi baifi rabin dan sittin ba da kuma shayi ruwan bunu rabin kofi me murka 
Wato azabtarda ita za,a yi kenan da garau garau lallai dole tanemi mafita yaushe rabon tasha bunu ai tun tana sch 
Yadebi kwanukan taliyar dare yafuta dasu yauma baice da ita komi ba yana dai binta da kallo kawai haryaje kofar fita Ta tsargu da kallon nasa tamkar wanda yasanta awani gurin. 
Ta cinye buredin bata koshiba adole tasha bunun nan don ita da bakin bunu gara ta hakura 
amma ayau kam babu zancen hakuri dole ta zukeshi tunda abincin rana zai iya kaiwa dare Ta dada duba wayarta taga ko network ya dawo 
Sai alokacin ta fahimci bazai taba dawowaba don da alama babushi kwata kwata adakin nata sbd kada tayi waya hakan ta faru To ai dama asalima ba,a fiye samun network adajiba sai in kafita inda kai sa,a ko kan dutse Da rana aka kawo mata shinkafa fara da mai sai gishiri akai ba yaji man baijiba 
Haka tayita kasumar garaurau din ba yanda ta iya harda hawayenta gadai kudi ajakarta amma bazai mata amfaniba harda ATM dinta ajakar amma dole taci kamusu don kudi bazai 
amfana mata komiba Da yamma wajen shida saiga kwamnada yazo mata karbar camera Nanma ta dage akan ita bata gunta Kwamanda yace “ke kada ki rainamin wayo domin munyi waya da oga mudansir ya gaya mana wanda ya baki camera wato me ban ruwan gidansu domin shikadai yake da camerar yin hoto agidansu kuma shima yasa ankamashi hukuncinsa ma yafi naki tsanani don haka 
ki miko ta salin alin ayau amaidaki gidanku. 
Zeenatu tace ” nifa mallam ka kyaleni da zancen camera nace maka bata guna bata guna ko bakajin hausane aikin banza aikin wofi kawai. Taja masa tsaki 
Wuuuuu! Ai abinda kwamanda yatsana kenab garama ka xageshi akan kayi masa tsaki yafl daukartsaki akan raini aikuwa Take ya xabga mata mari saida taga hasken taurari kuwa 
Yanunata da yatsa yace ” ki iya bakinki domin ba.a min tsaki zan kuma miki hukunci me tsauri afarko na kyaleki ne don ina tausaya miki to amma tunda ke bakya tausan kanki zan azabtarki domin kisani ba haka nakewa sauran da muka kamo dake cikin gidan nan ba kima sani bake kadai bace akwai dakuna sunyi goma duk da mutane kuma suma ansa mukamo sune wasu kuma munyi garkuwa dasune kuma arana sau daya suke samun abinci wasunma mun daina basu kema kuma zaki shiga sahunsu domin ogah yace dama kada muiyi miki ta sanyi sbd haka ajibi za.a koma kotu dan haka miko camera! Tana kuka tace ” nifa bata guna. Ya finciki jakarta ahannunta yahau dubawa 
Saida yatabbatar baiga camerar ba kana ya cilla mata jakar 
Yaga kudade da ATM acikin jakar amma batasu yake ba 
Hankalinsa tashe ya mike tsaye yace da ita ” dole kinsan inda kika boyeta ki fada mana a inda take ko ina ne zantura yara suje su dauko min ita 
Tace ” ni bansan inda takeba. Yafl minti talatin yana nacin tafada masa amma takiya Dole yahakura ya fita yabarta 
Tana kuka tana tausan kanta da kuma mukhtar me ban ruwansu mudansir ko wane hali yake? 
Allah sarki mukhtar tasan zai iyayin nadamar bata camerar dayasan zaishiga wani hali dabazai bataba 
Da dare kuwa har goma taji shiru ba,a kawo mata abincin dareba tasan kenan kwamanda ne yahana 
Bata iya zama da yunwa ba yanzu ya zatayi kenan? ina maflta gareta? 
Tabbas dolene tayi wani abun akai baikamata zauna ackn gidan nan ba yakamata tasan 
yanda zatayi tafita agidan nan koo taje ta taimaki masu neman taimakon…. 

About Ismail

Check Also

ZEENAT YAR JARIDAH CHAPTER 13

ZEENAT YAR JARIDA CHAPTER 13 Zatace Ina Ahmad din kenan sai gashi ya shugo da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *