[Advertisements⬇️]

ZEENAT YAR JARIDAH CHAPTER 14 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

ZEENAT YAR JARIDAH
CHAPTER 14
Ahmad ne tsaye a kofar gidan su Zeenat shida Kabir, Suna tsaye Yana karkada key din motarsa Sega Zeenat ta flto 
Gaisheshu tayi, Kabir yace amaryanmu, uhm tace” Ahmad kuwa tsare ta da ldo yayi kamar zai cinyeta 
Harararshi tayi ta murgudamai baki wai kallon ya isa haka, Kara kashe mata ldo yayi Da Kabir yaga cikin shaukin Soyayya yake se ya Basu waje, Matsowa kusa da shi tayi tace haba my Man! Smiling yayi yace” karkiga laiflna duk lokacin Dana ganki wani yanayi nake shiga, itadai tace uhm wannan Ahmad din zaiyi rigima da alama Ciro kudi yayi ya Bata yace” gashinan duk abun da take bukata gashinan, Mamakin kudin tayi tace” wannan ai yayi yawa! Ce mata yayi karki damu, Nan dai suka Dan taba Hira kadan sukai sallama Washe gari’ Ahmad da Kabir ne Zaune Suna Shirin zuwa company Dan yin ordan kayan da za’a saka a dakin, 
Kabir yace” but ya kamata tun yanzu mu hada kawancen ta wajena da Zeenat, Kabir yace hakane Kam Dan I think Bata da kowa, Kuma dama ni banason matata ta kasance masu yawan kawaye, Kabir murmushi yayi yace” da gaskiyanka Dan yanzu kana Zaune da matarka lfy sai kawaye su chanzata ta Fara maka wasu abubuwa daban, Ahmad yace” wlhi kuwa, 
Nan Kabir yai dialing numbern girlfriend dinshi me Suna Asma’u yake sanarda ita ta shirya idan Bata komai Zasu kaita gidan matar da Ahmad zai aura Asma’u Irin wayayyun Nan ne tafi Zeenat bude ldo sosai, tace” ai dama zuru nai maku inasha Rowan amaryan ake Mana! Kabir yace” wane mu gamunan zuwa tace” Ok 
Ta shirya Tana Zaune phone dinta yai ringing dama already ta sanar da mum dinta tace” to ba komai sai kundawo adai kula tace” 0k sannan ta flce 
Direct gidan su Zeenat suka wuce da Ahmad da Kabir da ita asma’un, Nan sukai Introducing Asma’u ga Zeenat, itama Zeenat taga asm’u, Zeenat taji Dadi sosai Dan at least tasama abokiyar shawara, 
Bayan sun shiga gidan ne, dama Maman Zeenat Batanan Asma’u tajanyo hannun 
Zeenat tace” ya shirye shirye? Zeenat tace” Wani shirye shirye bana komai 
Asma‘u tai warr da ldo alamun Bata Gane ba tace” Yan shirye shiryen da amarya ake mata ko Takeyi kafin aure mana 
Zeenat tace” uhm nasan bazaki rasa Jin labarina agun Kabir ba, duka duka haduwan mu da Ahmad befi one month ba auren ne yazo a bazata, Asma’u tace nasani Amma duk da haka ba Zama zamuyi ba, it’s not too late, yanzu muje 
akwai gidan wata mata me gyaran amare muje muyu mata magana Gaban Zeenat ne ya Fadi tace to faa abun yazo, Nan ta shirya tace mu tafi to, Asma’u ta Kara da cewa fannin night gown da turaruka duk kingama siya ko? Zeenat tace” nifa bansan komai ba, Asma’u tace” Wayyo Allah! Zeenat let’s go to market yanzu idan mundawo sai muje wajen me gyaran amaryan Nan suka fito da sauri suka shiga adaidaita suka nufa kasuwa, wani shago naga sun nufa me uban night gown masu kyau hadaddu, Suna shiga yan shagon suka ce ma’ouh customer, aran Zeenat tace wato har sun Saba, Nan se zagaye suke a shagon, Asma’u Kam ta zabo ma Zeenat night gown ubansu masu kyau ga shagon turaruka da suka shiga Nan ma aka hadu mata masu kamshin gaske, ga kananan kaya Riga da wando ba’a magana Dan saida suka hada akwatuna biyu na kayan bacci Dana gayu sannan suka fito, 
Zeenat ne ta kalla kayan tace” gaskiya bazan iya zuwa gida da kayan Nan ba, Asma’u ki tafi mun Dashi gidanku, idan anyi auren sai ki kawomun Asma’u tai dariya tace” Amarya bakya laifi, angama ba matsala, Nan suka wuce gidan suka 
ajiye kayan sannan suka dawo gidan Gyaran Amarya Nan Asma’u tai mata magana tace” batashan komai gashi this Friday ne bikin so ki mata dilka Kuma ki hadata sosai yanda ya kamata ko nawane zamu baki, sannan ahada mata turarukan jiki na maiduguri Wanda zata Dade Tana anfani Dashi, Hajiya mairo me gyaran jiki tace” karki damu kudinku 50k ne da komai da komai, Nan aka ciro aka Bata, tace” idan ana Saura kwana uku bikin tazo Nan sukai sallama bayan sun fito kowa ya kama hanyar gidansu Bangaren Su Ahmad kuwa anje kasuwa an siyo duk Wani Abu da ake bukata a gidan, tunda gidan ko shekara beyi da ginawaba, fenti kadai aka sake sannan aka sake decorating gidan kamar ba shiba, komai Yaji a dakin Amarya kawai akejira akawo 
ooooo
Bayan kwana biyu, Yaune alkawarin da sukai na Zeenat zataje gidan Gyara,,,,
 gashi bataso mamanta ta Gane Dan kartace tayi Rashin kunya, Dan haka tai hikima tace” Umma Kinga Yan’uwanki sun Fara zuwa Kuma ni banason aita kallona, dama shine nace zanje gidan su Asma’u na zauna tunda a chan zamuyi taron mu na kawaye, Umma Batace komai ba Dan ta yarda da Zinatun ta dari bisa dari tace” to bakomai adai kula, Allah yai Miki albarka, kinga dama yau za’a kawo akwatunarki 
Basu Gama magana ba sega Asma’u nan ta shugo ta gaida umma, Nan tai musu nasiha ‘tace’ kudai kula sosai ku rike amanar junanku, zasu tafine Zeenat ta ciwo kudi kusan 20K taba mamanta tace koda ana bukatarwani abu, duk da ansai komai da komai Mamanta tace” zinatu ai kudin Nan sunyi yawa, tunda mun ajiye komai, itadai ‘tace” umma ki rike sannan suka fice Zeenat da asma’u fitowa daga gidan sukai, Asmau ta kalla Zeenat tace amaryanmu, Zeenat tai smiling tafiya suke Basu tsaya ko Ina ba se gidan me gyaran amare Suna shiga sukaga mutane cike da gidan, Ko wacce da bukatar da tazo nema,wasu jikasu za’ai da kayan ni’ima wasu dilka etc dai Hajiya me gyaran ta kallesu tace” Sannunku da zuwa sukace yauwa, Nan sukai mata bayanin komai yanda sukeso, tace bakomai angama cikin kankanin lokaci Ta fara gyarata, Yamma nayi Asmau tai gida tace gobe Zata dawo 
Bangaren Ango kuwa ba zama se zirga zirga suke Dan su tabbatar abun da suka tsara yayi, Dakin da amarya Zata zauna kuwa Baku gani ba kamar ba a unguwar yake ba dan wasu tsadaddun Kaya da akasa Bayan kwana biyu 
Ahmad duk ya matsu yaga amaryanshi, 2days da be gantaba harwani Rama yayi, Ga phone dinta be shiga, Zuwa gidan su Asmau yayi yace” Wai Ina saheebanshi ne? Asmau tace Kai sarkin zalama Kai da ga ganta se gobe ai, Kai da gidanka za’a kaita saima ka Gaji da ganinta shine zakazo wani nemanta Dan Sosa keya yayi dan yasan asma’u akwai mayyance yace”  Sorry bafa wani Abu bane, Ciro kudi yayi ya Bata yace ta kaimata k0 zatai wani abun dashi, Hannu tasa ta amsa ta kirga taga 50K tace” ok zan Bata Har ya tafi ya juyu yace” please tell her I miss her sosai, Murmushi tayi tace” to Romeo zan fada mata, Shima smiling yayi ya shiga motarshi ya nufa gida Yana taflya Asmau takai mata sakon tace kawai kisa a account tunda bama bukatar komai for now zeenat tace yeah ki ajiye a wajenki by Monday Sai kije ki samun Washe Gari ran daurin aure_
,,,,,,,,,,,,,
An daura auren Zeenat da Ahmad Alhamdulillah, kowa yayi murna Yan Uwa da abokan arziki sun Suna musu Soyayya 
Yan uwan baban Zeenat kuwa da sukaga yanda tai kyau se gulmace gulmace sukeyi Wai an bar yarinya ta zama yar bariki Dan sunga tayi kyau su Kuma Yan kauyema 
Ba wasu frnds gareta ba a can Dan haka ba gayya tayi ba Amma Asma’u ta gayyato nata Friends Din din Dan za’ai wani event a 3 Millennium Hall by 4 PM Nan abokan Ango suka fara daukan kawayen amarya har hall Kabir kuwa shi ya dauka Ahmad da Zeenat se Asma’u kawai a cikin motar, 
Ba Ahmad kadai ba kowa da yaga Zeenat ya yaba da kyan da tayi,Ahmad kuwa da ya zura mata Ido kamarzai cinyeta, kasa hakura yayi a cikin motor yajanyota jikinshi yai mata kiss Yace” wow you look so beautiful, Kokarin kwace kanta tai Dan tasan Basu kadai bane, Hmm yace sannan ya saketa Amma Hannunshi rike da nata gam Se wani kallon I wanna be with you yake mata Itadai sedai tace uhm k0 ta kauda idonta Sun Isa hall din iya haduwa yayi ga decoration da akai lrin kayan kawayen amarya red and Ash wajen ya hadu sosai Nan aka fara gudanar da program, Kawayen asmau se gulma suke Wai lalle wannan yarinyar tayi Dace Ji yanda ya kashe mata kudi Kuma da alama Sonta yakeyi sosai, Suma sukai fatan Allah ya kawo Masu Mr Right me sonsu Wanda zai kashe Masu kudi Nan MC yace” yanason ganin Amarya da Ango a saman stage din hall din, Dur kusawa tayi Asmau wlhi banason zuwa, Asmau tace ai baki isaba wlhi Nan ta rike mata hannu takaita saman, Ango kuwa shi already har yahau 
Nan MC yace” to ga amarya dai ga Ango yanzu zaman amana da hakuri za’ai duk wani Soyayya ya biyo bayan wannan Ahmad wani kashe mata Ido yayi tai sauri ta juyar dakanta, Yana Bata mamaki sosai yanda be boye soyayyarshi ko a inane 
MC ya kara da cewa to yanzu su gwada majunansu Irin Soyayyan da suke ma junansu, Nan aka sa wani Wakar ‘Umar M Shariff‘ _na duk Wanda be murna yayi baya, Amarya kyakkyawace Amarya.._ 
Sautin na tafiya ahankali, Ga hall din yadau speakers kota ina sauti na tashi, Nan ya janyo hannunta Wai suyi rawa tace” a a ya langwabe mata Kai ya rike hannunta Gam suka fara Dan juyawa Nan hall din ya rikice da ihu Wai Angon beda kunya lol…sunsha rawa itakam Zeenat se nokewa Takeyi Dan  kunya.. Anyi biki Alhamdulillah Dan komai daidai abinci Kam sedai bakaje ba, AHMAD kuwa duk ya kosa a kawomai amaryanshi Family dinshi ma Suna gan’ln Zeenat sukaji ta kwanta musu arai, Suna Sonta sosai Angana an dawo gida Nan aka fara Shiryea Shiryen Kai amarya, asma’u ta Miko mata wasu kaya tace ta chanza, Tasa atamfa sun amsa jikinta tsaf, Nan aka kaita manyanta sukai mata fada, Tayi kuka sosai sosaiMamanta ma tayi kuka Dan dai aure ne ba bazataso ta rabu da Yar tilon yarta ba, Nan aka mata fada yanda ya Dace Sannan aka dauketa sai gidan Mijinta Ahmad Suna shiga Kawayen Asma’u da Yan Uwa da sukaga gidan Sunyi mamaki, Dan ya tsaru sosai, dangin babanta Kuma basuso haka ba, Masu dai farin ciki nayi Yan bakin ciki nayi Nan fa Yan mata ganin gidan ya hadu kowa ya fara allaumma arzuquni gida me kyau wa miji me bada kudi, wa tankameman gida…etc Lol 
Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]