[Advertisements⬇️]

ZEENAT YAR JARIDAH CHAPTER 12 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

ZEENAT YAR JARIDAH
CHAPTER 12
Bushewa da dariya sukai sannan sukaja motar Sukai cikin daji da ita Wani gida Naga sun Shiga dasu sun dakko su sun jefar a wani daki kamar mutattu 
Bayan Sun ajiyesu ne daya daga cikinsu ya Kira Mudansir yace” Kana inane? Yace” on my way to court, Wanda ya kirashi yace” ranka ya Dade munyi abun da kace 
Mudansir wani farin ciki yaji yace” make sure Kun chajesu ko ina Kun dauke camera din please 
Jan wuya yace” don’t worry from head to toe ba inda bazamu chajesuba har cikin motarsu, Mudansir yace” good job 
,,,,,,,,, 
Maman zeenat kuwa Tana hospital gabanta se fadi yakeyi Nan ta karanto wasu addu’oi tasan faduwan gaban Nan duk akan Zeenat ne Nan ma ta Kara cewa Allah ya baku Sa’a 
An shugo court kowa ya zauna Anajiran yanke hukunci, 
Barrister Lawal yai Kiran number Ahmad shuru a kashe, ya Kira yafi sau goma but still switch off 
Hakanan ya fito daga office dinshi yazo main inda ake gudanar da shari’a Me shari’a yace” ina Wanda suka kawo karar Barr Lawal yace” Suna hanya 
Kararaf Mudassir yace” me girma me shari’a wannan fa karar da aka kawo karya da kazafi 
akemun, ya za’ai kamar ni nai ma yarinya karama fyade’ Mahaifiyar Aisha wacce akai ma fyaden tace” Wallahi da gaske ne Kaine ai har daukan ka hoto anyi 
Mudansir yai wata murmushi Dan yasan Already an chapke su zeenat ba yanda za’ai suzo su kawo wata shaidar da za’ace yayi Dan haka yace” shifa bashi bane idan da gaske ne me yasa har yanzu Basu iso ba, ya me girma me shari’a nifa haryanzu ban yarda ba ni na aikata ba, kazafi ne kawai Nan court din ya hargitse da maganganu kowa na fadan Son ranshi Barrister Lawal yace” Kai ka gyara maganar ka be carefull fa Nan Mudansir ya sunkuyar dakai Court dai ta dauka shuru na wasu Yan mintina 
Kusan One hour ba Iabarin su Zeenat hankalin barrister Lawal ya tashi sosai, kallon Mudansir yayi yaga hankalinshi kwance a zuciyarshi yace” Kai Akwai alamar tambaya a tare da wannan yaron 
Har me shari’a yace” an daga karar se wata sati me zuwa tunda masu bada shaidar basanan kawai se ga Friend din Ahmad wato Kabir ya Shugo Dama yasan Barr Lawal wajenshi ya nufa yace” inasu Ahmad? Hankalin kowa ya karkata wajensu Dan Kar su hada wata munafurci 
Mudansir kuwa yanaji ance inasu zeenata ranshi yace” tab ku da ku gansu se a lahira Barr Lawal yace” inata Kiran number Shi a kashe Me shari’a ne yace” me kuke cewa Barr lawal kunsan ba‘a Son magana sosai a Court Kabir yace” ya me shari’a I think wani Abu ne ya faru dasu a hanya, 
Dan sun fito yace” inyi hakuri inje gidanshi na duba sun bar (camera) shaidar karar da suka kawo na dakko na kawo mai 
Me shari’a yace” in da gaske kke ina camera din Nan Kabir ya Ciro ya mik’a mai 
Barr Lawal yace” Alhamdulillah 
Mudassir najin haka idonshi ya chanza yaija, Nan danan yaji fitsari da zawo sun taho mai, Masu goyon bayanshi Basu ji dadi ba Sam, cos ciki akwai yaranshi da suka zo Nan wasu harda Kuka sunsan he’s dead sedai mamanshi ta haifo wani badai Mudansir ba Maman Aisha wacce akai ma fyaden, da Wanda dama sukeso karshen Mudansir yazo, Alhamdulillah suke ta cewa a mind dinsu Dan dama ya Dade Yana aikata abubuwa da dama Maman Mudansir kuwa itama idontane ya ciko da kwalla tace” wannan abun kunyar har ina 
Bayan me shari’a ya ga camera din ya kalla Mudansir tsaf yace” tabbas shine, aka Kira 
Aisha da yai mata aika aika itama akaga itace Nan me shari’a yace” akaishi gidan yari yai shekara 30 Kuma sannan a mai bulala guda 100 Kuma asamai Shocking a bananarShi Nan Mudansir ya fara Kuka wiwi kamar karamin yaro Barrister lawal da yake babba ne yace” dama daga ganinka baka da gaskiya Kenan kanada hannu wajen sace su Zeenat, Nan yai wiki wiki da ido, Acikin yaranshi da sukazo Ana gama shari’ar suna kallo aka tafi dashi, Habawa suka arce Ana Kare Dan Kar suma a hada dasu Ansa Mudansir a cikin mota Nan phone dinshi Tai ringing aka ce ya daga Kuma yasa handsfree Kawai sukaji ance” Oga mun duba ko ina bamuga camera din ba, har cikin motarsu, Yanzu 
sun farfado yazamuyi dasu kenan Wani a cikinsu ne ya kwace wayarya kashe Barrister lawal da Kabir sukai mai wani mugun kallo, Ga police da suka cika motar 
Barrister yace” magana ta ta futo Dan haka yanzu kafin mu wuce dakai muje ka kaimu gidan da aka Kai su Zeenat Ba musu yace” 0k Dan yasan karshenshi yazo Kabir yace” laifi kan laifi
Nan Mudansir ya Fara Basu hakuri akan abun daya aikata, _Iolz mukace da sauri haka har ka saduda kasan komai na karewa Amma Banda ikon Allah, and idan ka tsare gaskl’ya bakajin kunya_ Wani police ne ya kwala mai bindiga yace” zakai Mana shuru ko a’a Nan yaja bakinshi yayi 
shuru Tafiya me tsaho sukai se gasu a bakin gate din gidan Nan suka bashi wayan Sukace ya kirasu su bude kofar Ringing daya suna ganin numbern Mudansir Sukace Oga namu baka wasa Kawai cewa yayi ku bude, Sukace 0k 
Suna budewa Sukaga taron mutane ‘GHAM’ _kowa yaji a kirjinshi
Suna budewa sukaga taron mutane 
Kabir ne yai musu wani mugun kallo seda suka tsorata, yace” Ina kuka ajiye su? Wuri Wuri da ido sukai sannan suka nuna musu wani daki Dakin suka wuce daya daga ciki yasa key ya bude Sega Ahmad a tsaye ranshi a bace sosai, Zeenat kuwa Tana Zaune gefe daya duk abun duniya ya isheta Ahmad ne ya balle kofar ganin su Kabir yasa yadan sake fuska yayo waje Zeenat ta biyoshi a baya 
Mudansir kam kamar tsohon kwarto yai wiki wiki da idanu Dan yasan yau jikin maza zaiyi tsami Ahmad suna ido hudu da Mudansir, Yaji ya Kara tsanarshi, zuwa yai ya wanke shi da Mari Sau uku then Kabir yace” don’t suffer your self yau ai kashinshi ya bushe, wani nunfashi 
Ahmad yaja sannan ya kalla yaran gidan yace” wato ku kananan yan iska ko? Yau kun mutu, dukansu hanjinsu ya kada 
Barr Lawal ne yace” me akejira duk ku kwashesu mukaisu gidan maza achan zasu tantance acid no be ice cream 
Nan Aka kwashesu Zeenat kuwa ta kalli mudansir ta kyalkyale da dariya tace” iskanci beyi ba, sannan ta hada Mai ga gwalo, Wani bakin ciki Yaji sosai ba yanda zaiyi Suna cikin tafiya ne Zeenat ta tino ba gidan da aka kaita na farko bane, Nan Tai ma Ahmad magana tace” akwai ma wani gidan Da yake ajiye yan iskan yara suna gallaza ma yaran mutane azaba, 
Ahmad yace really? Tace” yeah Nan aka umurcesu da su nuna gidan tafiya kadan akai Sega wani babban gida, Nan suka shiga Suka ga dakuna ya kusan Goma 
Ko wanne da mutane a ciki, Yan mata kyawawa da maza, kana ganinsu kasan butters ne, Ahmad girgiza kai yayi yace” Wannan tantirine ya Dade Yana iskanci 
Zeenat tace” Wallahi kuwa Kabir Kam Yace” kalleshi fa, he is young amma se iskanci da mugunta a cikinsa Zeenat tace” dama ninety nine days for the thief one day for the owner, 
Kabir yace” hakane, Nan aka bude duka dakunan Sega Yan mata da samari sun fIto Dama a jakar Zeenat akwai abun daukar magana Nan ta fito dashi 
Ahmad yace” me zakiyi tace” zansa a radio ne in shaa Allah kowa yaji muguntarda Mudansir yakewa mutane, Aiko Nan suka Bata goyon baya 
Ta Fara da wata tace baiwar Allah ko me ya kawo ki Nan gidan? Tace Ina tafiya a hanya ogan cikinsu yace” Yana Sona nace” akwai Wanda nakeso shikkenan ya sa aka kawoni Nan gidan 
wai se randa na yarda dashi ze barni, akaje kan na biyu duk kusan daya ne 
Maza Kuma da yaga yaro babanshi nada kudi sesuyi kidnapping dinshi wai sa an kawo kudi tukunna zasu kyaleni 
Zeenat tace” Tir da Wannan halin mutumin, yanzu dubunshi ya cika Kabir da Ahmad sukace wannan k0 a Yan iskan babba neh!!! Nan aka sake duka Yan gidan akace kowa yai ta kanshi, Ma’aikatan gidan Kuma Wanda Basu da laifi aka sakesu Suma, masu laifin Kuma aka tarkatasu se gidan yari Acikin Wanda aka saka har da Wanda yake kawo wa Zeenat abinci lokacin da aka saceta na farko Dama tamai alkawarin insha Allah zata temakeshi Nan yai mata godiya sosai sannan ya kama hanyar garinsu An kaisu dukansu aka sasu daki daya banda Mudansir, Shi wani daki aka kaishi anata gallazamai azaba 
Cikin mintuna kadan kamanninshi ya chanza, banana kuwa har laushi tayi saboda azaba Kuma akace a gidan ze karace rayuwarsa saboda muguntar da yai Allah kadai ya Sani, Oh Mudansir kaga ta kanka da ace haka za’a dinga ma mutane da Nigeria ta sama zaman laflya
,,,,,,,,,,
Ahmad da Kabir Nan sukai ma Barr Lawal godiya sosai yace” bakomai 
AHMAD ma yai ma kabir godiya yace” haba ai ana tare Bari naje gida zuwa anjuma zamu hadu Ahmad yai godiya sosai sannan Zeenat Da Ahmad suka kama hanyar hospital 
Suna tafe suna Hira Zeenat ta kalle Ahmad tace” amma nagode sosai da tsayamun da Kai har asirin mutumin Nan ya tuno 
Ahmad yace” don’t thank me please you deserve more than this, Wani smiling tayi tace” uhm 
Ahmad yace” nasan kinajin yunwa muje ostrich mu siyo abinci daganan mu siyo ma mama tace 0k 
Tana Zaune a cikin mota ya shiga ya siyo musu sannan ya Mika mata, Nan ta Ciro nata ta Fara ci ya kalleta yace” chop chop wani murmushi tamai da seda Yaji tsikar jikinshi ya tashi Kasa daurewa yayi yace” baby wai yaushene auranmu? 
Kunya taji tai shuru, ganin tayi shuru ya sama wani waje yai parking yace” idan kin fada sai mu tafl ko? 
Kara rufe fuskarta tayi Dan Tana tsaninin son Ahmad Kuma da shine takeson kasancewa har karshen rayuwarta 
Shiko Binta da kallo yayi yaga Bata da Shirin magana gashi ta rufe fuskarta, 
Wani dabara yayi yace” Baby kafarki wani abu da sauri ta bude fuskar Tana kallon wajen kafarta taga Bata ga komai ba kallonshi tayi ya sake mata wani murmushin I Love you hade da kashe ido, ji tai itama duk jikinta yai sanyi ta Kara rufe ido tace“ Dan Allah ya Ahmad muje 
Smiling yayi sannan yaja motar daganan Bata sake magana ba seda suka sauka a hospital din Yana parking kamar Tana jira da sauri ta flto tayi ward din da aka kwantar da mamanta Binta da kallo ta baya yayi yace” gaskiya Ina son yarinyar Nan komai nata na burgeneni, rufe kofar yayi Shima ya biyota 
Zeenat na shiga taga mamanta a Zaune ta gaisheta da jiki tace” Alhamdulillah jiki da sauki Zatace Ina Ahmad din se gashi ya shugo 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]