[Advertisements⬇️]

YAR SHUGABA CHAPTER 9 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

YAR SHUGABA 
CHAPTER 9
‘Washe gari‘ 
Da misalin k’arfe hud’u na yamma, ya Aryan yayi wanka, sai ya d’auki d’aya daga cikin kanyan da Basma ta siya masa ya sanya, yayi kyau sosai da yake k’ananun kaya ne, sai ya d’auki hulan sanyi ya sanya a kansa saboda gashin kansa. Ya fito yace wa Umma sai ya dawo, Deeja tace “Yaya Aryan kayan nan ya maka kyau, amma meyasa ka sanya hulan nan, ai daka cire zaka fi kyau” murmushi yayi yace Deeja banyi aski bane, kinga sumana ya taru shiyasa na sanya” murmushi tayi tace “hakane, to sai ka dawo” kana yasa kai ya fita. Tafiya yake bai san ina zashi ba, ya mik‘e hanya sanb’al saida ya kai k’arshen layin su kana ya karya kwana, tafe yanke yana tunanin Basma da irin hiran da suka yi jiya, bai ankara ba wata mota ta taho a guje, gadan-dagan tawo kansa, ai ba shiri yayi tsalle ya koma jikin bangon wani gini saura kiris ya fad’a kwata, ya razana sosai, Basma dake cikin motan me zata yi inba dariya ba, da yake motan mai bak‘in glass ne, Aryan ya kafa wa motan ido yana jiran wanda yake ciki ya fito, saida ta gama cin dariya sosai, kana ta bud’e ta fito, ido Hud’u suka yi sai ta kwashe da dariya, iya kuluwa yayi sai ya tamke fuska, cikin fushi yace “dama kece kika son bigeni da gan»gan k0? anya Basma ba kida Matsala a kwakwalwa kuwa” yana fad’an haka saita tsaida dariyanta tace cikin tsiwa “haba Yaya Aryan ya zaka kamanta ni da hauka, nifa da wasa nayi maka, tun daga nesa na hango ka nace bari na dan tsokane ka, ashe Yaya Aryan haka kake da tsoro” saita k’ara kwashewa da dariya, a yanzu shima dariyan yayi domin Basma ta kai mak‘ura wurin shak‘iyanci, tace “Yaya Aryan dama fa wurinka zani, ka rakani wani wuri” kallonta yayi tare da tsare gira yace “ni sa‘anki ne, kije ki samu Deeja tana gida ita saita raka ki, amma ba dai ni ba” ai nan da nan Basma tayi fuskan tausayi tace “Yaya Aryan ni kai nake so ka rakani” yayi murmushi yace “to bazani ba” b’ata rai tayi kamar zatayi kuka tace “haba Yaya Aryan kayi hak’uri muje ba zamu dad’e ba” ganin zata fara masa kuka yace “to muje”. 
Nan suka shiga mota suka fara tafiya, ta sanya wak’ar larabawa yana yi a hankali, ta juyo tace “Yaya Aryan kayi kyau amma abu d’aya ya b’ata wankanka” murmushi yayi bai tanka mata ba, ai bai aune ba sai yaje ta janye hulan kansa ta b’oye a dayan gefenta, da sauri ya juyo yace 
“wai ina wasa dake ne?” tuni Basma ta shagaltu da kallon sumansa saura kad’an ta buga motan dake gabansu, da sauri ta gyara tuk’in ta mai da hankali kan hanya, Yaya Aryan ya kwashe da dariya yace 
“Yarinya taga suma ba irin nata ba ta rikice” dariya kawai tayi bata ce komai ba harsuka isa wurin shak’atawa. 
Parking suka yi duk suka fito, suka jera ba tare da sunce ma juna komai ba, shi dai binta kawai yakeyi, sun isa wani wurin da aka zagayeshi da furanni masu k‘amshi, wuri sanyi ga iska mai dad’i, kujerune a ciki da table a tsakiya duk suka zauna, waita ne yazo da sauri ya tambayesu abinda za a kawo musu, Basma tace “ice cream da shawarma da kuma drink” ta kalli Yaya Aryan tace “Yaya me za’a kawo maka” yace “duk abinda zaki ci shi zanci” murmushi tayi ta gaya ma weta ya tafI ya kawo musu. Suna fuskantan juna Yaya Aryan yace “dama nan wurin zaki kawoni” dariya tayi tace “eh, saboda in dan saka ka waye, dan naga kamar baka waye ba” hararanta yayi yace “kece dai baki waye ba da kike sanya kananun kaya ki fIto ko ajikinki wai irin kin had’u ” da sauri ta kalli jikinta tace “Yaya kana nufin banyi kyau ba ne?” “eh bakiyi kyau ba saboda shigan bata dace dake ba” tace “Yaya Aryan, na sanya ne saboda naga a mota nake” riga da wando ta sanya sun kamata sai dai rigan ya sakko har gwiwanta amma duk shape d’in jikinta ya fito sai ta yi rolling da gale a kanta ta rufe gashinta” yace 
“eh, ai ba shiga bane na musulunci mace tayi ta fita” jikinta ne yayi sanyi tace 
“To insha Allah bazan sake yin shigan na fIto ba, amma zan rik’a sanyawa a gida” murmushi yayi yace da dai yafi miki” tace 
“Yaya Aryan sumanka tayi maka kyau, meyasa kake rufewa?” ya kalleta suka had’a ido sai da suka kalli juna na tsayin minti uku, kana ya sauke ajiyan zuciya yace “Basmaaa” sai duk jikinta ya mutu ta sunkuyar da kai k’asa, sai taji ta cigaba da magana, “bana son barin suman, kuma yawan askewa yana k’ara yawansa, shiyasa nake yawo da hula, saboda in mutane suka gani suna yawan min magana akai” murmushi tayi tace “Yaya Aryan dan Allah karka aske, zan siyo maka mayuka na maza, da zaka rik’a gyarawa, wlh har sheki zai rik’ayi, ba kaga yanda mazan India suke yi bane” murmushi yayi yace “ni Basma bana son sumar dan a takure nake” marairaice fuska tayi tace 
“to ko zaka aske, karka aske duka ni ina son ganinka dashi” hararanta yayi, kan yayi 
magana an kawo musu shawarman. 
Sai wayar Basma ce ta d’auki k’ara, da sauri ta d’auka ta kara a kunne, tace “My Shureym” saita shagwab’e fuska ta fara shagwab’a, “bayan kasan ina missing d‘inka, shine duk yau baka kirani ba ka manta dani” ta b’angaren Shureym kuwa ya shiga lallashinta. Aryan zuciyansa ne ke dukan uku-uku hankalinsa ya tashi, amma saiya dake, ya cigaba da cin shawarman, amma abin mamaki kamaryana cin magani sam baya jin dad’in sa, sunkuyar da kai yayi k’asa, zuciyansa nayi masa zugi, numfashinsa yana fita da k’arfi, dakiya kawai yayi. Basma sun d’auki tsawon minti sha Biyar suna wayan, daga bisani suka yi bankwana ta kashe wayar. 
Ta kalli Yaya Aryan tace “Yaya kayi hak’uri na d’auki waya ban nima izini ba” d’agowa yayi idonsa ya kad’a ya d’anyi ja, sai yayi mata murmushin yak’e yace karki damu bakomai” murmushi ta mayar masa, ta mik’a hannu ta d’auko sauran shawarman da ya rage ta soma ci ko ajikinta. Sam bata lura da sauyawan yanayin sa ba, saida ta gama tace “Yaya Aryan” ya d’ago ya kalle, ta tace “bari muyi salfee mana?” murmushi gefen baki yayi yace “ni bana hoto” shagwab’e fuska tayi tace 
ni dai dan Allah muyi” bata jira me zaice ba ta mik’e ta zo bayansa ta tsaya, shi kuma yana zaune, aiko ta kashe musu photo har uku, shi dai fuskansa ba yabo ba fallasa, gaba d’aya zuciyansa a takure yake, tace 
“Kaga kuwa yanda mukayi kyau?” ta nuna masa, ya kalla shima kanshi hoton ya mishi kyau yace “yayi kyau” tace “Yaya muje gida yamma yayi sosai”. Bayan sun kama hanya, ta ciro hulansa ta bashi tace 
“Yaya Aryan, gobe in Allah ya kaimu zanzo mu k’ara fita” murmushi yayi yace “Allah ya kaimu” haka ta sanya wani waka da music na soyayya, sai bin wakar take, shi ko kwantawa yayi a bayansa yana sauraren wak’ar da muryarta ,gaba d’aya ya shiga wani duniya wanda shi kanshi bai san wani irin duniya ya lula ba. Ta sauke shi suka yi sallama, kana ya wuce cike da damuwa a zuciyansa, itama ta wuce cike da farin cikin a zuciyarta mara misaltuwa. Da dare misalin k’arfe goma da rabi, Basma ta kira Yaya Aryan, yana kallon kiran yak’i d’auka, ta kira shi ya kai sau goma amma yak’i d’agawa, haka nan yaji ba zai d’auka ba, domin shak’uwar da zuciyansa yake da Basma, ya fara bashi tsoro kuma ga dukkan alamu ya soma shiga wani hurumi da ba nashi ba, dole ya d’auki matakan kaucewa damuwa. Basma kuka ta shiga yi hawaye wannan na bin wannan, iyaka damuwa ta shiga, da kyar barci ya d’auketa. Haka ma ta b’angaren Yaya Aryan, k’arshe ma tashi yayi ya gabatar da sallan nafila yayi Addu’a akan, Allah ya k’are masa zuciyansa da irin abinda ya soma raya masa game da Basma. 
Washe gari’ Basma da ciwon kai ta tashi, ta samu ta karya tasha magani sannan ta koma barci. Ta wurin Yaya Aryan kuwa ya samu sassauci game da abinda yakeji, ya shirya ya tafi kasuwa kamar yanda ya saba kullun, amma a k’asan zuciyansa yana tuna masa hiran Basma da Shureym sai damuwa ya ziyarce shi. Da misalin k’arfe biyar ya dawo daga kasuwa, da sauri yayi wanka ya shirya ya fita, unguwar ya bari gaba d’aya saboda baya so su had’u da Basma. Ta b’angarenta kuwa ta zo tayi parking in da suka had’u jiya, tayi ta kiran wayan ba’a d’auka ba, kuma ta jira shi bai zoba har kusan k’arfe shida na yamma, abinda bata sani ba Aryan yana hangen motanta ya b‘oye a wani shagon aski, hakanan yaji tausayinta kamarya fito sai kawai ya basar, haka ta hak’ura zuciyarta na mata zafi ta tuka motan a hankali, idonta na zubda hawaye, ta shiga damuwa na rashin zuwan Yaya Aryan, a haka ta isa gida kamar mara lafiya. Shima Aryan cikin damuwa ya wuce gida bayan tafiyarta, koda Umma ta ganshi ta tambaye shi ko lafia? yace mata kansa ke ciwo, sai tayi masa sannu. Yau da wuri ya dawo gida ya kwanta, yau ma yak”i d’auka wayarta, a haka ko wanne ya kwana cikin damuwa. ‘Washe gari Monday‘ Basma da sassafe ta fito tazo gidansu Deeja, ta samu Deeja ta shirya suka gaisa da Umma, Aryan yana d’aki yana jinsu amma yak’i fitowa, dauriya Basma tayi tak’i tambayar ko yana nan, suka yiwa Umna sallama suka wuce University dake cikin Abuja, da yake ansan da zuwansu basu sha wani wahala ba wajen yin registration d’in, kuma dama president yasa hannu, Deeja an d’auke ta ba tare da zana wani exam ba, ta samu Medicine b’angaren mata (gynecology). Zuwa k’arfe biyu sun gama komai, sai suka kama hanyar gida. B’angaren Yaya Aryan, ya tafi companyn su Basma, ya had’u da Yaya Naufal kamar yanda Yaya Ahmad ya gaya ma Naufal d’in, Yaya Naufal yayi masa interview, ga mamakinsa duka Yaya Aryan ya amsa masa, gashi dai ba digree gareshi ba amma ya amsa masa duk tambayoyinsa. Ya duba takardunsa sosai, cikin k’asaita da mulki yace “sunana Naufal, a yanda na gwadaka kuma na duba takardunka gaskiya komai yayi yanda muke so, mun d’auke ka aiki, sannan bayan kamar watanni zamu turaka ka k’aro karatu kayi degree da masters, ga wannan kud’in kuma ka samu ka siya kaya na zuwa office, dole ne ka rik’a shiga mai kyau domin zaka rik’a ganawa da manyan mutane, office d’inka shine na b’angaren computer, kai ne mai shigar da komai in an fitar da kaya ko an shigo da su, da fatan ka fahimta” 
Yaya Aryan cike da farin ciki yace 
“na fahimta, nagode Allah ya saka da alkhairi” duk wannan bayanin cikin harshen turanci suke magana, kana Yaya Naufal ya rakashi katon office d’insa, mai d’auke da kujeru na alfarma da katon table, ga AC, ga fridge, kai har toilet akwai a ciki, komai dai normal, Yaya Naufal ya gama nuna masa komai ya fice, Yaya Aryan ya zauna kan kujeran table d’in ya juya yana kallon kud’in da aka zubama office d’in, sai hawaye ya soma zarya a kuncinsa, farin ciki da begen son ganin Basma ne ya bijiro masa, ba dan Allah yasa sanadin ta ba, da ba zai tsinci kansa a irin nan wurin ba. Suna isa Basma ta fad’a d’akin Yaya Aryan ta kwanta bisa katifansa, cikin kankanin lokacin barci ya d’auke ta. Deeja ce ta shigo taga tana barci, taso tashinta ta koma d’akin su, amma saita kyaleta ta cigaba da barcin, ta koma wurin Umma tace “Umma Basma fa barci takeyi, da zan tasheta ta koma d’akinmu saina barta” Umma tace “kyaleta ta kwanta ta gaji ne, kinsan yaran masu kud’i basu saba da wahala ba, kuma ma ai d’akin Aryan yafi namu gyaruwa zata fi jin dad’in barcin anan”. Khadija tace “hakane kuma” sai suka cigaba da aikin su na girki, Umma na rangad’a musu, tuwon shinkafa miyar kub’ewa d’anya wanda yaji nama. 
Da misalin k’arfe uku da rabi, Yaya Aryan ya dawo gida daga companyn su Basma, ya zauna bisa tabarma a tsakar gida, ya gaisa da Umma, kana yace “Khadija kun gama registration d’in?” tace “eh, Yaya mun gama komai, Monday mai zuwa zan fara zuwa d’aukan lectures” yace “masha Allah, Allah ya taimaka” duk suka amsa da “Ameen”, Umma tace ya kuka yi ne a wurin da kaje?” murmushi tayi yace “Umma komai Alhandulillah, an min interview, kuma na ci, musamman suka bani office nawa ni kad‘ai, nine zan d’inka shigar da komai na company” kud’i ya ciro daga aljihunsa yace “wannan kud’in dubu D’ari biyu ne, suka bani na siya kayan sawa kawai na zuwa office, saboda zan d’inga ganawa da mutane, masu amsan kayan company” baki Umma ta bud’e tace “ikon Allah, wannan Abu haka, gaskiya ba abinda za mucewa Basma da Yayanta sai Allah ya 
saka musu da gidan Aljanna” duk suka amsa da “Amin” Yaya Aryan yace 
‘gobe insha Allah zan fara zuwa aiki, albashi na kuma dubu d’ari biyu duk wata” ai Umma sai kabbara, ta yiwa annabi salati s.a.w, hawayen farin cikin ta soma fIddawa, Deeja tace “Umma ba kuka za kiyi ba, waraka Allah ya kawo mana dan haka saimu gode masa”. Nan ya mik’e ya shiga d’akinsa, ai sai yaci karo da Basma tayi d’ai-d’ai bisa godonsa, gashin kanta ya baje a bayanta, da gani barcin gajiya take yi, murmushi kawai tayi yace a ransa “Basma rigima, wato ba tad’a wurin barci sai d’akina” Wasu kaya ya d’auka, ya fito ya shiga bayi, Basma da tun shigowarsa ta farka tabi bayansa da kallo tana murmushi. Bayan ya fito daga wankan ya wuce d‘akin Umma ya sauya kaya, masallaci ya wuce dan yin sallan La’asar, suma su Umma suka gabatar da nasu sallan. Basma ta flto tayi alwala ta shiga d’akin Umma tayi sallah, anan Deeja ta kawo masu tuwo suka ci tare, bayan sun 
gama ta shirya zuwa gida ta yiwa su Umma sallama ta fito, Deeja ta rakata mota ta wuce. Tafiya take a hankali zuciyarta cike da son ganin Yaya Aryan, aiko tana yin kwana ta hangeshi tsaye inda ta d’auke shi rannan, farin ciki taji a zuciyana kana ta d’aure fuska tamkar ba ita ba, ta k’arasa tayi parking mota, ba tare da ta ce masa uffan ba ya bud’e motan ya shiga, yana shiga ta tada motan suka wuce ba wanda yace wani Abu, ko wanne da abinda zuciyansa ke saka masa. Yaya Aryan ya katse shurun yace Basmaa” juyowa tayi ba tare ta tace komai ba, sai hawaye ya fara zuba a idonta, ta juga ta 
cigaba da tukasu…. 
Hmmmm wannan abu ya fara bani tsoro koya zasu kwashe…®’ 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]