[Advertisements⬇️]

YAR SHUGABA CHAPTER 6 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

YAR SHIGABA 
CHAPTER 6
Ya Ahmad saida ya bari sun kusa gida sai ya samu guri yayi parking, ya kalli Basma yace “Basma ki gaya min me ya faru? dan bazani gida dake a haka ba” share hawayenta tayi ta fara bashi labarin duk abinda ya faru, bata boye masa komai ba tun farkon haduwanta da Aryan, saida ta gama tsaf kana ya gyara zamansa ya fuskanceta da kyau yace Basma gaskiya baki kyauta ba, domin ke kikaja komai ya faru, meyasa idonki zai rufe saboda samun duniya ki wulakanta Mutum, Allah da kanshi ya karrama dan Adam ya fifitamu akan Aljanu, Basma yanzu halittan Allah ya cancanci wulakanci? haba Basma ban san yaushe kika sauya halinki ba, kina takama da mulki da kudi ko, to wallahi Allah zai iya amshesu daga hannun mu ya bama wasu, ki sani wannan duniyar ba matabbata bace munzo cin kasuwa ne, duk kuma abinda muka shuka shi zamu girba a makomarmu, Basma na lura tunda kuka tafi England ke dasu Meena duk kuka sauya hali” Jikin Basma ne yayi sanyi sosai, tabbas maganganun  sun ratsata, cikin mutuwar jiki tace “Yaya Ahmad wallahi yanzu hankalina ya dawo jikina tabbas ban kyauta masa ba, nagode daka tunatar dani da kayi, lallai na shagala da rudin duniya, Yaya Ahmad bansan me ya shiga kaina ba” saita karasa maganar tana kuka, murmushi yayi yace “Ai shi Allah mai gafara ne, inaso duk lokacin da kika kara haduwa dashi, to ki bashi hakuri” tace “to Yaya Ahmad insha Allah zanyi yanda kace” wannan karan dariya yayi har hakoransa na fitowa yace “yauwa kanwata farin cikina, yanzu bani labarin yanda kika karasa a gidansu Khadija” murmushi tayi ta soma bashi labari, masha Allah yace, kana ya tada motan suka wuce gida suna hira cikin nishadi tamkar Basma batayi kuka ba. ‘ Yaya Aryan yana isa gida ya tadda Umma rike da kudi tana juyasu a hannunta, da sauri ya karasa yace 
Umma wannan kudin fa? Khadija ta dawo kuwa? dan na zaga sosai ban ga mai kamarta ba, na tambaya ba wanda ya ganta” murmushi Umma tayi tace 
“Khadija ta dawo yanzu ta shiga bayi, ashe wai wata Yarinya ce ta bigeta a mota suka kaita asibity” nan dai Umma ta labarta masa abinda ta sani, Yaya Aryan yajinjina lamarin yace “to Allah ya kyauta nagaba, yanzu duk wannan kudin su suka bada?” 
“eh su suka bayar, harda siyayya ma suka yi mata na kayan ciye-ciye” kafin yayi magana Khadija ce ta flto daga wanka tace “sannu da zuwa Yaya Aryan” 
“yauwa Khadija” nan suka gaisa itama ta kara bashi labari, Umma ce ta mika masa kudin tace “ga kudin saika gyara runfarka daga nan ka biya kudin haya, sauran kudin ka siya mana kayan abinci” Amsa yayi cikin natsuwa yace “Allah ya saka da alkhairi, bari na flta in duba Muntari kaflnta sai mu fara maganar gyaran” to Aryan saika dawo, Allah ya muku albarka” duk suka amsa da “Ameen” kana ya fice. 
Bayan sallan Magrib jirginsu Prince Shureym ya iso, yana sauka ajirgi motoci najiransa, ya karasa su tafi gidan president. Bayan sun kai ya wuce falon shugaban kasa ya gaisheshi, kana ya wuce part din Ammi ya gaisheta, ya shiga wurin Momy itama ya gaisheta, saiya wuce part dinsu Yaya Ahmad can ne
masaukinsa, yana shiga falon sai ya fada wani daki, wanka yayi ya kimtsa saiya gabatarda sallan Magrib, yana idarwa aka kira sallan isha’i, ya tashi ya gabatar, sai da ya kammala gaba daya, kana ya tashi ya fita falon ya zauna, TV ya kunna sannan ya dauki wayarsa ya kira Safeena hira suka shiga yi na kewar junansu. ‘Bangaren Basma kuwa, ta sanya aka kawo masa abinci aka jera a kan kafet dake tsakiyar falon, wanka tayi ta sanya doguwar riga na leshi, tayi daurin Maryam Babangida, tayi kyau matuka sai kamshi takeyi. 
Basma doguwa ce kadan tanada kiba shima kadan, sai fatarta akwai dan duhu mai hade da haske, ita ba baka ba ita ba fara ba, tsaka tsaki, sai kuma tana da Boobs dai-dai da jikinta maca ce mai hips sosai, mazaunanta yayi dai-dai da jikinta, cikinta a dame yake tamkar bata cin abinci, Basma akwai shape mai kyau da diri. Fuskarta dauke yake da dara daran idanu, bakinta dan karami ne pink color, sai dogon hanci da yayi tsini har baka, in tayi dariya dimple dinta sai ya lotsa, gashin giranta tamkar anyi mata kabin, Basma tanada yalwataccen gashi har gadon baya, mai silbi da baki sosai, Basma ta hadu domin ko ba makeup fuskarta a hade take, Allah ya gama halitta anan. A fili in ka ganta za kayi zaton za tayi nauyi amma ana daukarta shagwal take, kyau dai ta hada na Barebari da kuma Fulani. Masu karatu ya kuka hango kyawun Basma, abin ba acewa komai A hankali take taku, saboda dogon takalmin dake kafarta, a haka ta isa part din su Yaya Ahmad, ta same shi yanata waya ganinta ne ya sashi saurin kashe wayar, galala yayi yana kallon halittar Allah, hadiya miyau yayi a zuciyansa yace “gaskiya Basma kin hadu, dole in fara lasar zumanki kan muyi aure, dan bazan jure ganinki haka ba” a fili kuma yace walcome my Baby” ya bude hannu domin taje tayi hugging dinshi, rungume hannunta yayi ta gyara tsayuwa, domin ba zata iya abinda yake nufi ba, mikewa yayi ya isa gab da ita kamshin turarensu ya gauraye gurin, kama hannunta yayi sai ta runtse ido, kokarin rungumeta ya shiga yi, da sauri ta janye tace “miye haka Yaya Shureym, ka bari kaci abinci mana“ dariya yayi yace “afwan gimbiyata ganinki ne duk ya rudani, muje ki zuba min” suka je suka zauna, ta zuba masa abincin ya soma ci, yana santi duk a haukansa ya dauka ita tayi. Bayan ya kammala ci, saiya mike yaje ya wanke bakinsa ya dayo, ita kuma ta zauna akan kushum tana jiran dawowarsa, daya dawo saiya zauna kusa da ita, hannunta ya kama yace “Basma ina sonki sosai, gobe ina son zamu fita zaki rakani wani guri da yamma” “0k Allah ya kaimu”. 
Wasa ya farayi da yatsun hanunta, yana mata magana rad’a-rad’a,janye hannun tayi tace “haba Prince ka bari mana” sosa k’eya yayi yace “haba my Basma ya kike yi kamar baki waye ba, ina ce a England kika yi karatu, ai nasan duk kin waye da irin wannan ai” gaban tane ya fad’i tana tambayar kanta “shin me wannan yake nufl?” a ranta, bata ankara ba taji ya rungumeta yana kokorin ya had’a bakinsu guri d’aya, ai da sauri ta fara kiciniyar kwatar kanta, shi kuma ya rik‘eta gam, Sallaman da Yaya Ahmad yayi ne ya shigo, shine yasa yayi saurin sakinta, ita kuma ta mik‘e da sauri tayi k’ok’arin barin d’akin da gudu, Shureym ne yake kiranta amma ina ta fece a guje, haka ta isa part d’in Ammi tana haki, Allah yasa bata tadda kowa a falon ba, saita wuce d’akinta ta fad’a kan gado, runtse idonta tayi tana mai ambaton Allah, tsananin damuwa ta shiga, yanda Yaya Ahmad yazo ya gansu shine matsalanta. Acan kuma Yaya Ahmad yace 
“haba Shureym wallahi ba girmanka bane yin haka, iskancin da kake yi a can America sai kace zaka gwada a kan k’anwarka, kuma akan matar da zaka aura?” shafa kansa yayi yace “to meye? ai aurenta zanyi, kuma ma kasan duk abinda zanyi bazan wuce gona da iri ba” tsaki Yaya Ahmad yayi yace “Allah ya shiryeka” bai jira Mai zaice ba ya fice a falon. Bayan Basma yabi, yasan tabbas tana part d’in Amminsa, can ya wuce ya sameta a d’akinta ta kwanta,jin an shigo mata d’aki ne yasa tayi saurin d’agowa ta zauna, Yaya Ahmad ya rufe d’akin, ya jawo wata kujera 
ya zauna ya fuskanceta, sunkuyar da kai tayi k’asa tana wasa da hannunta, kiran sunanta yayi yace “Basma, ban sanki da hali haka ba, ko da yake nasan shaidani ne shi, amma kuma duk da haka da laifinki Basma, kinje har d’akinmu a wannan shigar kuma ba mayafi, sannan kuma daga ke sai shi, kin san cikon na ukun ku shaidan ne, Basma mace da Namiji ba aso suna keb’ewa haka, in dai ba mata da miji bane, ki daina d’aukar Shureym a matsayinmu, domin mu jininki ne, shi kuma aure zai shiga tsakaninku, dole kiyi taka tsan-tsan dashi domin na Fiki sanin waye Shureym”. Dago jajayen idonta tayi tace “Yaya kayi hak’uri ba laifina bane, shine ya matsamin, ina k’ok‘arin kwacewa ne kazo ka samemu a haka” “eh, Nagani ai, ina so in dai zaki sashinmu, tofa ki tafi dasu Na’im da Anwar, karki yarda kina keb’ewa dashi ke kad’ai” tace”to Yaya Ahmad, insha Allah zan kiyaye” 
“yauwa k’anwata” nan yayi ta mata nasiha har ta saki jiki sukayi barkwanci, kana yayi mata saida safe ya wuce. Basma ji tayi duk Shureym d’inma ya sire mata a rai, bata zata haka yake ba, amma ta d’auki alkhawari za tayi maganinsa. Washe gari’ Da misalin k’arfe 4:30pm na yamma Basma ta shirya cikin riga da sket na kanti, ta sanya lafaya, ba k’aramin kyau tayi ba, yau ta fito a ‘yar Maiduguri sosai, futowa tayi su Anwar da Na’im suna biye a bayanta, suma sunyi shigan kananan kaya sunyi kyau, shekarunsu zai kai 16yrs, har motan Prince suka isa, sai ga shi ya taho, tun daga nesa yake washe baki harya k’araso, ganinsu twins ne yasa yace 
“My Basma kin ga yanda kika yi kyau kuwa” murmushi tayi ba tace komai ba,yace “ba dai da su twins zamu tafi ba?” da murmushi a fuskanta tace “tare Zamu tafl, ko akwai Matsala ne?” bata rai yayi yace “amma ai kinsan ba haka mu kai dake ba k0?” Kafin ta bashi amsa twins suka ce 
“Haba Yaya Shureym me mukayi da ba za’a damu ba, mu gaskiya sai munje” Basma ma tace “in ba zamu dasu ba sai dai a fasa taflyan” k’ara tsare gira Shureym yayi, sai ya bud’e mota bai ce komai ba, haka su ka tafl tare badan ransa ya so ba har suka dawo Prince bai saki fuska ba. Siyayyan kayan kwalama yayi musu suka dawo, Basma ko a zuciyarta sai dariya take yi. 
Bayan Sallan Isha‘i, Yaya Ahmad ya shigo falon Ammi, bai sameta a falon ba, saiya wuce wurin Basma ya sameta tana danna system d’inta, rufewa tayi suka gaisa, ya samu guri ya zauna tace “Yaya Ahmad kasan yanda nayi yau da mutuminka kuwa?” cikin dariya yace “wa kenan?” tace 
“Yaya Shureym mana” nan ta kwashe yanda suka yi ta bashi labari, aiko sai ya kwashe da dariya yace “good k’anwata, yanzu ma k0 yace kije side d’inmu karki je, kice yazo falon Ammi kuyi hiran, kinga ai ba zai yi shakiyanci anan ba” dariya itama tayi tace “sosai ma kuwa, ai ba zai yi ba, maganinsa zanyi ai tunda shi shaid’ani ne” dariya yayi yace “Mijinki ne dai ba ruwana, yauwa gobe ne fa zaki kawomin patient d’ina ko?” Tace “eh, insha Allah gobe ne zanje har gida na d’aukota, “to Allah ya kaimu” “Ameen”. Nan suka yi sallama ya wuce. Washe gari’ 
Da misalin k’arfe goma na safe, Basma ta shirya ta flta cikin shigar doguwar riga na atamfa ya kamata daga sama k’asa ya bud’e, babu wani kwalliya a fuskanta, ta shiga motarta sai d’aya daga bodyguard d’inta yazo zai yi magana tace “yau ni ka d’ai nakejin fita ba dad’ewa zanyi ba” daga wannan bata sake magana ba ta tada mota tayi gaba. Yau ak’ofar gidan tayi parking ta shiga a nutse, ta samu Deeja tana wanke-wanke, da sallama ta shiga, Deeja ta mik’e da sauri tace “sannu da zuwa Anty Basma” Basma ta amsa cike da fara‘a, tabarma ta d’auko ta shinfid’a mata ta zauna, tace “Deeja ina Umma” tace 
“Umma ta flta mak’ota dubiya yanzu zata dawo, bari na k’arasa wanke-wanke kan tazo” Basma ta mik’e tace 
“bari na tayaki” da sauri Deeja tace “a’a ki barshi nagode” ai sai ta b’ata rai tace 
“baki so na samu lada ne nima?” 
“a’a inaso ki samu, gani nayi daga nin ki baki saba da wahala ba” dariya tayi tace “haka dai kika gani” haka ta sanya mata hannu tana d’auraye kayan tana kifewa a kwando suna kuma hira. Yaya Aryan ne yayi sallama ya shiga, ai sai gaban Basma ya fad’i, da sauri ta waiga aiko tsaraf suka had’a ido nan take gabansu ya fad’i dukansu, mamaki ne ya kama Aryan, sai da suka yiwa juba kallon tsayin minti uku, kana ya je ya zauna kan wata kujera, Deeja ce tace “Yaya ba kaje kasuwan bane?” yace “naje, wani Abu nazo amsa gun Umma” “ok, aiko ta fita amma bazata dad’e ba” a sanyaye Basma ta k’arasa taya Deeja wanke wankeb, ta koma ta zauna, Deeja ta d’au kayan ta kai kicin ta dawo ta zauna gefen Basma, tace Basma ga Yayana Aryan” “ok” tace, Deeja ta kai dubanta ga Yaya Aryan tace “Yaya Aryan ga Basma nan, wanda na baka labari,yanzu ma tazo muje asibiti ne a k‘ara dubani” murmushi yayi na gefen baki yace “ok na ganta” sai Khadija taji abin yayi mata wani iri yanda Yaya Aryan yace, Basma tace “ina kwana” tayi maganar a sanyaye, amsawa yayi a dak’ile, sai ya mik‘e yace “Deeja zan koma, anjima zan dawo, dan yau ba zan dad’e ba a kasuwan” “To adawo lafiya” Basma ta bi bayansa da kallo. Saita juya tace dama wannan ne Yayan naki?” da murmushi Deeja tace “eh” Umma ce tayi sallama sai duk suka amsa, nan Basma ta gaishe ta, ta kuma mata bayanin komawansu asibity, Umma tayi godiya tace “to sai kun dawo” Deeja ta d’auko hijabi ta sanya suka wuce. Umma da mamaki tace “ikon Allah, Basma sam bata kyamarmu”. 
Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]