[Advertisements⬇️]

YAR SHUGABA CHAPTER 2 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

YAR SHUGABA

CHAPTER 2

Su Basma suna isa club, suka wuce cikin hall d’in, mutane ne sosai a ciki maza da mata, daka gansu kaga ‘ya’yan manya, tsautsayi ne zai kai d’an talaka wurin, kid‘a da sauti ke tashi kowa na zaune, kamar yanda suka saba zuwa suna da nasu wurin zama na musamman, duk suka zauna, aka cike musu wurin da kayan motsa baki, wani kyakkyawan Guy ne yazo kusa dasu suka gaisa Amma banda Basma domin bata shiga harkan Maza. Leema ce ta mik’e saurayin mai suna Jalal ya rik’ota ta kugunta suka wuce tare da hiransu na masoya, fita sukayi a wurin suka wuce cikin hotel da club d’in ke ciki. D’akinsa ya bud’e suka shiga, kamar suna jirace da juna suka fara kaiwa juna sak’onni, nan da nan suka rikice suka lula duniyar shashanci, Allah ya shirya Ameen, nan na fito na basu guri.
Ita kuma Meena ta mik’e ta wuce group d’insu na mashaya, wurin mata ne da maza a had’e, suna ganinta suka fara ihu, wuri suka bata ta zauna ta fara aikawa da syrup. Queen itama Abokan rawanta suka matso kusa da ita nan suka d’unguma zuwa saman dandamali, nan fa kowa hankalinsa ya ‘ashi ganin Basma ta hau, hayaniya ya k’aru suka fara ihu domin sunyi missing ganin rawan Basma, aka d’aura mata best wak’arta na music d’in labarawa, Queen Basma ta soma rawa mai ban mamaki tamkar ba jikinta take k’aryawa ba, sai wuri ya kuma hautsinewa da ihu, dama abinda Basma keso kenan, mutane suka fara mata yayyafin kud’i masu taya ta rawa suka k‘ara dagewa farin ciki ne ya rufe su domin sunsan yau zasu kwashi kud’i. Dan in sun gama Basma cewa take a basu kud’in su raba.
Sai da taci rawa mai isarta kana ta sauka ta samu guri ta zauna tana maida numfashi, sauran ‘yan rawar suma suka sauka, aka kwashe kud’in su tas aka basu, farin ciki ya gama rufesu domin yau sun samu kud’i sosai, suna alfahari da Queen data zama star d’insu. Sai misalin k’arfe ukun dare suka dawo gida, ko wacce ta nufl d’aki ta kwanta, nima saina tayasu rufe k’ofa nace saida safe. ‘Washe gari‘
Da misalin k’arfe takwas na safe Aryan yayiwa Umma sallama ya wuce kasuwa kamar kullun, yana isa rumfansa hawaye ya ciko fal idonsa, girgiza kai yayi saiya bud’e k’aton buhu da yake kasa kayan miya, haka ya karkasa tumatur, tarugu, sai tattasai, samun wuri yayi ya zauna daga inda rufin shagonsa ya kifa ya rab’e, sai ya rafka tagumi ya fara tuno rayuwansu. ‘ASALIN ARYAN? “’
Sunan mahaifinsu Aliyu, Asalinsu fulanin Gombe ne, mahaifinsa ya rasa lyayensa tun yana k’arami, a wurin k’anin Baffansa ya tashi Malam Mu’azu, ya had’ashi da yaransa su biyu Aisha da Ibrahim ya rik’e. Matarsa Inna Amina suna kiranta da Inna Lami ta rik’e Aliyu Amana tamkar ita ta haifeshi, duk inda Aliyu yake Khalil na wurin, sun shaku sosai makaranta tare suke zuwa, ga k‘anwarsu Aisha sunaji da ita. Wata rana Inna Lami ta aiki Khalil kasuwa shuru-shuru bai dawo ba har aka d’auki tsawon lokaci, abu kamar wasa Khalil ya b’ace anyi niman duniya amma ba amo ba labari, Malam Mu’azu da Inna Lami sun shiga tsananin damuwa, tun ana kwana d’aya da b’atan Khalil har
ya d’auki tsawon wata ba’a ganshi ba balle aji labarinsa. Haka su Inna suka runguma Aliyu da Aisha suka barwa Allah lamarin da Addu’an Allah ya bayyana musu Khalil ko a mace ko a raye. Aliyu kuwa har rashin lafiya yayi saboda rashin d’an uwansa. ’Bayan shekaru’ Aliyu ya gama diploman sa a b’angaren kasuwanci, yana da shekaru 26. Aisha kuma tana da shekara sha takwas Malam Mu‘az ya had’a Aliyu da Aisha auren zumunci, basu damu ba dama suna son junansu saboda akwai shakuwa mai k’arfl a tsakaninsu, Ana d’aura musu
Aure sai suka tare a wani gefe daga cikin gidansu. Bayan wata biyar da aurensu wani abokin Malam Mu‘azu yazo Gombe mai suna Alhaji Sani, Malam yayi masa kyakkyawan tarba, d’aya tashi lafiya ya rok’i Malam akan ya bashi Aliyu ya tafi dashi Abuja tunda yayi karatu, ya d’auke shi aiki a companyn sa, da farko Malam bai yarda ba, amma daga baya saiya amince bisa sharad’in sai dai Aliyu ya tafi da matarsa, Alhaji Sani ya amince, cikin kwana biyu suka shirya sai garin Abuja.
Alhaji Sani mutum ne mai kirki, ya siyawa Aliyu k’aramin gida mai d’aki ciki uku da kicin da ban d‘aki, sai kuma filin tsakar gida k’arami madaidaici a unguwar suleja, ya kuma siyan masa mashin da zai rik’a zuwa aiki. Farin cikin wurin Aisha da Aliyu baya misaltuwa, Aliyu ya fara aiki a company Alhaji Sani a matsayin Massinger. Sukan ziyarci Gombe duk bayan watanni biyu ko uku tare da alkhairai masu yawa. ‘Bayan wani lokaci’
Aisha ta haifo d’anta Namiji suka sanya masa suna Aryan, Aryan ya tashi cikin kulawa da gata na iyaye, sun sanya shi makaranta mai kyau da tsada, Aryan yaro ne mai hazak’a b’angaren boko da islamiya, ga kuma natsuwa, gashi da kyau sosai, da ka ganshi gaka Asalin bafula tani, hakan yasa yayi farin jini sosai a makarantansu. Aryan yana da shekara takwas Aisha wanda Aryan yake kiranta da Umma ta haifo ‘Yarta kyakkyawa khajida, tun tana k’arama Aryan yake matukar son k’anwarsa duk abinda ya samu tofa na Khadija ce daya sanya mata suna Deeja.
Arya ya kammala secondary school Khadija na primary 5, mahaiflnsa ya nima masa makaranta a kadpoly Kaduna ya tafi ya fara karatun computer science, cikin ikon Allah da mai da hankali ya kammala, shekarunsa uku a makaranta ya dawo da certificate d‘insa na diploma, ya koma Abuja lokacin Deeja ta shiga jss3 a secondary.
Wata rana mahaifin Aliyu ya wayi gan da matsanancm cnwon Clkl Abu kamar wasa, zuwa yamma yace ga garinku, wannan family sun shiga tashin hankali sosai da rashin Mahaifinsu, karma ace maka Aryan da yayi mugun sabo da mahaifinsa, mutanan Gombe suka zo saida akayi arba’in sannan Inna ta tafi, sun so su Umma su tattara su koma Gombe amma Alhaji Sani yace su barsu anan, yana so Aryan ya cigaba da aikin Mahaifinsa, haka suka amince badan ransu yaso ba.
Aryan ya fara zuwa aiki a company Alhaji Sani, tunda ya fara zuwa ya fara samun matsaloli, wasu daga wurin aikin suka sanya masa ido saboda sunga yanda Alhaji sani ke nan-nan dashi. Daga karshe suka yi masa sharri bayan shekaransa guda da fara aiki Alhaji Sani ya koreshi.
Aryan yayi kuka sosai rayuwa tayi musu k’unci abinda za suci wuya yake musu cikin k’ank’anin lokaci duk suka rame suka lalace, Khadija ta daina zuwa makaranta domin ba kud’in school fees, Allah yasa ba haya suke ba domin da gidan su kawai suka tsira. Dole yasa Aryan ya fara bige~bige, Umma kuma ta soma wankau a gida da haka ne suke samun abincin da zasuci, Aryan yayi yawon niman aiki Amma bai samu ba, wani wurin inya je sai suce mai Digree suke nima, ba suda kud’in da zai koma karatu dole yasa ya soma dako a kasuwa. Allah ya taimakeshi ya samu baro yana amfani dashi wajen dakon. Da wannan kud’in baron ne ya samu ya kafa runfa a cikin kasuwa yana biyan kud’in hayan wurin, ya fara saida kayan miya, abu kamar wasa sai sana‘arya amshe shi, da haka Deeja ta koma makaranta ya cigaba da biya mata school fees, Umma kuma ta daina wankau saboda sanyi ya fara mata illa, sai ta samu jari ta fara dafawa Deeja kwai tana saidawa, in ta dawo makarantan boko saita fita tallan kwai, da yake duk sunyi saukar Al’Qur‘ani, boko kawai take zuwa. A daddafe Khadija ta kammala secondary school, tunda ta gama Aryan yaso nima mata school of health ta cigaba amma ba kud’i, burin Khadija ta zama babban likitan mata amma ba hali. Samari sosai take da su amma Yaya Aryan ya hanata hira, saida Umma ta sanya baki ya fara barinta tana fitan ma wani malaminsu na ialamiyan da ta gama mai suna Musa. Soyayya sosai suke yi, sun fara zancen Aure Iyayen Musa suka hana shi aurenta saboda akwai yarinyar da suka zab’an masa, wannan dalilin ne ya kawo k’arshen soyayyan Dija da Musa. Tun daga nan Dija ta tsani soyayya burinta yanzu bai wuce ta samu ta cigaba da karatuba. Aryan yazame mata uba duk abinda ‘ya budurwa take buk’ata Aryan ya tsare mata shi, ta maida hankali sosai wajen tallan kwai.
Aryan runfansa ya rufta tun daga wannan ranar komai ya dagule masa cinikinsa yaja baya, wata biyu kenan da rushewan rumfansa. Ana cikin hakane mak‘ocinsu Malam Lawal yaje ya
kafa tashi rumfan kusa dana Aryan da hakane Malam Lawal ya kwashewa Aryan customers, Aryan saurayi ne matashi mai cikar kamala, yanada tsayi amma dai-dai misali, yanada kauri, kuma fatarsa mai haske ne, yanada dogon hanci da dara-daran ido, bakinsa dai-dai da fuskansa, Namiji ne mai cike da kwarjini ga faffad’an k’irji, suman kansa luf-lufyake tamkar d’an India, in ya d’auki lokaci baiyi aski ba gashinta yana taruwa wanda zai iya kamawa da ribom, gashi da santsi sosai. Hakane kesa kullun Kansa da Hula baya son sumansa na fitowa. ba kowa yasan sumarsa haka take ba saboda baya flta ba hula. sai dai
in yaje masallaci wurin yin Alwala sai mutane su gani. ‘yan Matan unguwansu Aryan sun rud’e sosai akansa, suna haukan sonsa, shi kuma bai san ma suna yi ba. Shekarunsa Talatin (30yrs) a duniya haryanzu baida budurwa, baima kallon mata balle ma su birgeshi, shiyasa ranar da sukayi ido hud’u da Basma gabansa ya fad’i domin shi Sam baya kallon mata, amma fuskan Basma ya kasa b’ace masa a ido saboda wulak’ancin da tayi masa. A yanzu kullun burinsa bai wuce ya samu kud’i ya farantawa Ummansa rai da k’anwarsa abin sonsa.ba ‘Cigaban Labari…‘
Malam lawal ne ya kwad’a ma Aryan sallama, firgigit ya farka daga dogon tunanin da ya shiga, cikin sark’ewan murya yace “Naam Malam Lawal ashe harka iso” cikin dariya Malam Lawal yace
“tun d’azu nazo, nayi maka magana naga gaba d’aya hankalinka ya yi nisa ince dai lafiya?” murmushi yayi yace “lafiya lau Malam Lawal, ya kwanan iyalin?”
“Laflya lau, d’azun nan naga Deeja zata aiken Ummanku, sai na tambayeta ko ka wuce? sai tace aika flta da wuri”
“eh wallahi na flto da wuri, da yake na biya wajen saro kayan miya”
“0k, Allah ya bamu sa’a da kasuwa mai Albarka”
“Ameen Malam Lawal”. Nan suka cigaba da tattaunawa akan maganar kasuwan.
B’angaren su Queen Basma sai goma na safe suka farka, ko wacce ta fito cikin shigan mu ta Hausawa, Leema ta sanya leshi riga da zani rafa, Meena ta sanya shadda doguwar Riga, Basma kuma ta sanya atamfa super, d’inkin Riga da siket, ba k’aramin kyau sukayi ba, ko wacce da gyale a kanta, hakan da suka yi sai suka bani mamaki, gaba d’aya kamar ba sune
jiya suka yi shigan dogayen riga sai kace ba ‘ya’yan Musulmai ba, suka tafi zuwa club. Queen ce tace
“Ni zan tafi gida domin a yanzu haka anajirana domin yin breakfast, in kuma za kuje tom sai mu tafi tare” Leema ta yatsine fuska tace “Ni bazani ba saboda Momynki akwai takura gwara-gwara Ammi, dan haka hotel d’in da muka sauka ni da Meena zan wuce” Meena tace kai Leema kiyi hak’uri muje kawai kinga fa sunsan muna garin nan bai kamata muje wani guri ba tunda duk Family ne mu ba bare ba” Queen ta yi hanyar fita tace “ban takurawa kowa ba, in kun so ku flto mu tafi in kuma kun k’i ko wacce ta kama hanyar inda zata,yau dai ba mai kwana min a wannan gidan, nima gidan Ubana zani na kwana” tana gama fad’an haka tasa kai ta fice,tsaki Meena tayi tace “In kina tak’ama da mulki muma fa gidanta muka fito, kinga Leema mu wuce gidan President d’in inya so in munyi two days sai ki koma Kano ni kuma na wuce Kaduna, domin wallahi ina missing Family na” Murmushi Leema tayi tace
“hmmm wallahi nima hankalina ya koma gida fa, yanzu fa iyayenmu sun d’auka yau ne zamu dawo daga Dubai da muka tafi, bacin yau satinmu d’aya da dawowa, muna biyewa Queen bayan ita iyayenta sun ga dawowarta a ranar, muko munyi k’arya sai yawo muke bamu nan bamu can” Dariya Meena ta kwashe dashi tace
“kefa saboda Jalal kika tsaya anan” hararan wasa Leema tayi mata tace “Ke kuma saboda mashayarku kika tsaya, saboda kinsan in kika koma gida Yaya Jamal zai takura miki ba shiga ba flta” duka Meena ta kaiwa Leema saita goce ta fice da sauri tana dariya. Haka su dukansu suka d’unguma zuwa babban gidan Shugaban k’asa.

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

‘WACECE QUEEN BASMA?…‘ 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]