[Advertisements⬇️]

YAR SHUGABA CHAPTER 14 - Bankinhausanovels
Thu. Mar 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

YAR SHUGABA
 CHAPTER 14
Yace “Ahmad kasan inda ka kawo mu kuwa?” Ahmad murmushi kawai yayi, sai yayi parking mota, ya fito tare da cewa 
“Umma mun kawo Ku futo” a sanyaye suka fito suna k’arewa gidan kallo, cikin kulawa Yaya Ahmad yace kumu je” Umma tace 
“Kai Ahmad wai ina ne nan, gaskiya a tsorace nake” murmushi yayi yace 
“Umma Ku kwantar da hankalinku bakomai fa” a tsorace suka bi bayansa, direct part d’in president ya kaisu, suna shiga duk mutanan falon suka zuba musu ido,jikin su Deeja sai ya d’au rawa, ido suka saki suna kallon kayan alatu da aka zuba a falon, har suka isa tsakiyan falon, Basma ne ta rugo da gudu ta rungume Umma, ai sai ta fashe da kuka, Umma ta rik’eta gam tana lallashinta, a haka suka k’arasa cikin falon suka zauna a kan kafet, Ahmad yace su zauna a kujera amma suka k’i hawa, Su Ammi da Momy suka bisu da kallo, su Meena ma dasu Yaya Naufal kallonsu suke yi da mamaki, sun gaisa gaba d’aya sai falon ya d’auki shuru, baifi minti goma da zuwansu ba President ya fito, cikin shiga na manya kaya, yana tafiya cike da izza
Su Aryan suna arba dashi sai cikinsu ya d’uru ruwa, kamma ace Umma da tayi mutuwar zaune, Deeja ko kamar ace mata ket ta ruga a guje dan tsoro. 
Zama yayi a kan kujeransa na alfarma, Ahmad ne yace “Abba gasunan nazo dasu” Abba ne ya kalli inda suka zauna yace “barkanku da zuwa” baki na rawa suka amsa gami da gaisheshi, Abba yace “Nine mahaifin su Basma, Ahmad shine Babban Yaro na, nasan za kuyi mamaki da haka, Ahmad ya sanar dani labarinku, sai dai Ku bakusan nine Mahaifinsu ba sai a yau” a razane Aryan yake kallon Abba yana magana, ya juya kallonsa ga Yaya Ahmad da Basma, murmushi Yaya Ahmad yayi masa ya gyad’a masa kai alaman eh, Basma Kuma ta sunkuyar da kai k’asa, tunda tayi tozali da Yaya Aryan hankalinta ya tashi, taga ya rame sosai tausayinsu ya kamata tasan lallai an yiwa rayuwansu gib’i. Nan Abba ya cigaba da bayani yace 
“Aryan nasan komai dake tsakanin ka da Basma, kayi hak’uri da abinda ya faru, ba zan iya hana Auren ta da Shureym ba, domin ina martaba zumunci, dan haka ne na amince da Auren Ahmad da ‘yar Uwanka saboda in sanya muku farin ciki, ku tabbatar da bama kyamar talaka, sannan yanzu nayi maka alkhawarin ka kawo duk yarinyar da tayi maka, insha Allah zan zame maka Uba na jagoranci lamarinka, sannan nasan a company na kake aiki, yanzu na baka MD na company, sannan zaka Zab’i k’asar da kake so domin kaje ka k’aro karatunka a can” Aryan kuka ya fara yi, yace cikin ladabi, “Yallabai nagode kwarai da karamci, ban tab’a kawowa a rayuwata zanga Shugaban k’asa da idona ba, sai gashi a sanadin soyayyan Basma na ganka, Basma ke haske ce a rayuwanmu, Yallab’ai nagode da duk abinda ka bani, amma ina so ku sani, ba kudi ko mukami ba zai iya siyan soyayyan Basma ba a zuciyana, domin an riga an halittamin shi ne a zuciya, na hak’ura da 
soyayarta dan nariga na sadak’ar Basma tafi k‘arfi na, mun gode sosai da karamci” yana gama magana sai yayi shuru. 
Shasshek’an kukan Basma ke tashi a falon, kowanne yayi shuru suna zancen zuci. Umma itama tayi godiya tace “lallai Basma da Ahmad kunyi gadon halaye na kwarai wurin mahaifinku, nayi mamaki sosai da yanda kuka shigo cikinmu kuka zauna damu duk girman matsayinku, kun rungume mu tamkar jininku” saita k’arasa maganar da kuka, Deeja ma kuka ta soma yi, falon ne yayi shuru na ‘yan dak’ik’a, sai Abba yace “Hajiya kuyi hak’uri ai wannan ba abin kuka bane, kai Aryan ba wai na maka wannan kyauta bane domin ka fansar min da soyayyarka ba, nayi maka ne saboda Allah a matsayin d’an cikina, taso ka amshi wannan takardun, na gidan Hutun Basma ce da kuma takardun motanta guda uku, ni na baka su halak malak, ina so kafin lokacin Biki Ku tare a gidan” Yaya Ahmad ne ya matsa danya Amsa takardun, sai Abba yace 
“shi nake so ya amsa da kansa, domin shima d’ana ne” jikin Aryan ne yayi sanyi, haka ya mik’e yaje ya amsa tare dayi masa godiya. Momy itama tayi masa Addu’a da Allah ya bashi mata tagari, har a zuciyarta taji tana son Aryan, taso ace ya zama sirikinta. Ammi kuwa ta gama k’ulewa kamarzata fashe dan haushi, Meena da Leema sun shaida Aryan kuma sun yaba da kyawunsa lallai sun dace da Basma, Yaya Naufal da yake yasan Aryan ya tayashi murna, amma har a azuciyansa baya son ya auri Basma domin tafi k’arfinsa.
Nan Umma tayita godiya, Abba yace 
“Hajiya ya isa haka Allah ne ya baku, ina ‘yata Khadija?” Kanta a sunkuye tace gani, Abba yace “Masha Allah, Allah ya muku Albarka yasa Albarka a aurenku” ya kai dubansa ga Momy yace “Hajiya Maryam gafa surukarku nan, matar Ahmad” ai sai Momy ta fad’ad’a murmushinta tace”Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi, ai tunda tazo ma ba zasu tafi da ita ba, zata zauna anan domin ayi mata gyaran jiki dasu Leema gaba d’aya” Abba yace 
“To shikenan, Abu yayi kyau, bari na tafi ana jira na” nan yayi musu sallama ya fice, Ammi ce ta mik’e da sauri tace 
“Ahmad yanzu ka rasa matar aure sai wannan yarinyan, to ka sani ba da yawuna ba, dan bataimin ba” tana gama fad’an haka ta fice, da mamaki duk suka bita da kallon, Ahmad cike da tashin hankali yace ma Momy, “Momy kinji abinda Ammi tace k0, dan Allah ki shawomin kanta” Momy tayi murmushi tace “karkaji komai zata sakko ne” ta kai dubanta gasu Umma tace 
“Hajiya kuyi hak’uri rashin fahimta ne” Murmushin yak’e Umma tayi domin abin ya bata haushi tace “ba komai ai” nan Yaya Ahmad yace su tashi ya rakasu gidan da Abba ya basu, Basma ta mik‘e tace “Yaya Ahmad zani” hararan wasa yayi mata yace 
“kinsan dai yanzu bakwa flta, kiyi hak’uri kiyi zamanki a gida” marairaice fuska tayi tace “tom zanyi magana da Yaya Aryan” da sauri Aryan ya juyo yace “a’a Basma magana a tsakaninmu ya k’are” yana gama fad’an haka yayi waje da sauri, ai da gudu Basma ta bi bayansa tana kwala masa kira. Ya kusa kaiwa gate, sai ya tsaya tsak amma bai juyo ba,ta cimmasa ta tsaya a gabansa tana haki, kallonta yayi ya kauda kai, hawaye ke sauka bisa kuncinta tace cikin sark’ewan murya “Yaya Aryan guduna kakeyi na zama abin gudu ko, ko ka daina sona ne?” Runtse idonsa yayi ya bud’e su, sun rine sunyi ja yace “Basma dole na gujeki domin ke yanzu ba tawa bace, Basma kin haramta a gareni, magana a tsakaninmu bai dace ba, domin zai tado min da mikin dake zuciyana wanda bai gama warkewa ba,  Sonki Basma baya musaltuwa, amma ki sani soyayyan da mukayi dake kisa aranki tamkar mafarki ne, ki cireni a zuciyarki kiyiwa iyayenki biyayya” yana gama fad’an haka ya matsa ya cigaba da tafiyansa Basma durkushewa tayi a gurin ta saki wani kuka mai tsuma zuciya, Aryan shima da kuka ya fita gidan, yana fita ya tsaya gefen wani dakali ya durkusa agun ya shiga rera kuka tamkar k’aramin Yaro. Leema, Meena da Deeja ne suka zo suka d’aga Basma, suka wuce da ita part d’in Momy. Umma suka fita itama tana kwalla, a haka suka cimma Yaya Aryan ita da Yaya Ahmad da kuma Yaya Naufal, dafashi Yaya Ahmad yayi, ya d’agoshi ya shiga share masa hawaye tare da gaya masa kalamai masu sanyaye rai. A haka ya sanyashi a mota ya wuce dasu gidan da Abba ya basu. 
B’angaren Shureym kuwa Mami ta aika Sarkin Gida da wasu mutane garin Yola, an basu auren Safeena, sun kai musu akwati da komai da Shureym ya siya, anyi shagulgulan Biki lafiya an d’auko Amarya. sun sauka a gidanta dake garin Kano wanda Shureym ya gyara shi sosai, komai najin dad’i akwai a gidan. Sun gama bikin auren sirri, wanda daga Mami sai Shureym sai wanda suka je nema masa aure sune kawai suka sani. An bar Amarya da Ango 
suna cin Amarci. Momy ta samu Ammi akan batun Auren Yaya Ahmad da Deeja, tayi mata bayani mai gamsarwa, Ammi ta sauko, tace ta hak’uri amma tana son Ahmad ya zauna da matar anan cikin gidan President,  da sanyawa Auren Albarka, Momy taji dad’in haka sosai, tace zata Sanar ma President domin a gyara part d’in da Ahmad zai zauna. Biki saura mako guda’ Anata shirin biki ta ko ina, mutanan Kano sun tattaro sun wuce Abuja, mutanan Kaduna ma haka, gidan president ya cika da dangi da abokan arziki, kowa kagan shi yana cikin farin ciki.Amare kuwa sunsha gyara sai kyalli suke, a zuwa yanzu su Yaya Naufal da Yaya Jamal sun sauko da k’in da sukewa su Meena, yanzu burinsu bai wuce a d’aura aure ba susha amarci, sai dai a Kasan zuciyan Yaya Jamal yayi alkawarin sake aure da sabuwar budurwa domin shima ya mori aure, dan yasan Leema saura zai samu agunta. Basma ta saduda sosai tayi sanyi, tana tsayawa tayi hira da Yaya Shureym amma a k’asar zuciyanta Aryan yana nan, kullun dare saita yi kuka na rashinsa, Shureym sai rawan jiki yake yi, yana nunawa Basma kuwala ta musamman, dan burinshi bai wuce yaga an d’aura 
Auren ba, domin yana cike da tsananin sha’awarta, yasan duk k’insa da take yi da an d’aura zata bada kai bori ya hau. 
B‘angaren Safeena, Yaya Shureym ya sanar mata da komai na aurensa da Basma, ta nuna rashin damuwa akan haka, sun tawo Abuja a tare, ya kama mata d’aki a hotel har a gama bikin su wuce America, Safeena burinta bai wuce ana gama shagalin biki ba su wuce America, tajuya Basma yanda ranta keso, domin Shureym ta gama dashi a tafln hannunta yake, sannan tayi alkhawarin Shureym bazai tab’a tarawa da Basma ba in dai tana raye. 
Amarya Deeja tayi kyau tamkar ba ita ba, hatta Ammi da take k’inta ta yaba da yanda ta sauya, fatarta tayi kyau, kamannin ta ya flto sosai, a hankali taji ta kwanta mata arai saboda yanda Deeja take mata biyayya da kuma nuna kunya a gareta a matayinta na mahaifiyan mijinta, cikin k’ank’anin lokacin ta nima k’iyayyar da take mata ta rasa, har wautan kanta take gani akan meyasa ta nunawa Yarinya tsana haka. Deeja ka koma gida, ta 
samu su umma a sabon gidansu, domin a nan ne za’a d’aukota a kawo‘ta gidan president. ’Ana gobe biki’ Mutane sun gama hallara, ta wajen su Umma mutanan Gombe sunzo, sai dai mahaifinta Malam ba shida lafiya, dan haka Innarta basu samu zuwa ba sai danginsu, sunata shirye
shirye cikin kwanciyar hankali. 
Yaya Aryan ya bar K’asan ana saura kwana uku biki, ya wuce K‘asar Manaco domin yaji ba zai iya tsayawa bikin ba, koda ya isa k’asar ya kashe duk wayoyinsa ya soma Harkan karatunsa, Basma tana ransa, shi kad’ai yasan irin k‘unan da zuciyansa yake ciki, kullun saiya kalla hotunanta da wanda take ita kad’ai da wanda suka d’auka tare a cikin system 
d’inshi, wani yayi murmushi wani yayi kuka, ya saba da haka, harya zame masajiki. ‘Ranar daurin aure’ Angwaye sun fito sunyi fas sai shek’i suke yi, ta b’angaren amare kuwa tsayawa fad’an kyawunsu ma b’ata lokaci ne, Basma koda tana cikin damuwa tayi kyau, tasha kwalliya amma bai hana zuban hawaye a fuskanta ba, duk wanda ya ganta saiya tausaya mata, ta k’ara tsukewa ta rame, ko tayi dariya yake tayi, sam bata farin ciki da wannan auren, Addu’a take Allah ya bata hak’uri da juriya akan auren. Bayan sun idar da Sallah Juma’a limamin masallaci ya sanar da d’aurin Auren yaran 
President da Gomnan Kaduna, da kuma Sarkin Kano. Biki na ‘yayan gata. 
An d’aura auren 
Yaya Ahmad da Khadija 
Yaya Shureym da Basma 
Yaya Jamal da Haleema 
Yaya Naufal da Ameena 
Yaya Adam da Munaya ‘yar wazirin Sarkin Kano. Anyi addu’o’i kana aka wuce taron walima a babban hall dake fadar Shugaban k’asa, anci ansha kowa ya shaida wannan aure, na ‘yayan manya ne kuma masu gata. Basma tanajin an d’aura ta shiga d’akinta ta kulle kanta, kwantawa tayi a gadonta ta fara kuka mara sauti, hoton Aryan a wayanta take kallo tace 
“shikenan an rabamu, Yaya Aryan ina sonka , Allah kasamin juriya da hak’uri azuciyata, Aryan na aje soyayyarka a zuciyata, zan yi kok’arin yin biyayyar aure ga mijina, Allah ya had’a fuskokinmu yasa na zama matarka a aljanna” saita b’alle da sabon kuka. A haka barci mai nauyi ya d’auketa, ba ita ta farka ba sai bayan sallan La’asar. Wanka ta tayi, ta canza wasu kayan zuwa leshi marun mai fulawa fari, tayi makeup tamkar ba Basma ba, ta b’ata lokaci sosai wajen kwalliya, kana ta aza gwagwaro Fari, ta sanya takalmi mai tsini, turaruka kuwa kamarwanka tayi dasu. Kallon kanta tayi a madubi, ita kanta ta yaba da Kyan da tayi. Ta fito a Queen Basma.dint A can kuwa cikin gidan hankalin kowa ya tashi ba’a ga Basma ba, an duba duk inda ya kama ta amma ba’a ganta ba, gaba d’aya gidan ya hautsine cikin tashin hankali, a cikin wannan yanayi ne Basma ta fito cikin taku na k’asaita, yau Queen Basma ta fito a sunanta, ai sai kallo ya koma gunta cike suke da mamakin ganinta a rinin wannan shiga, nan take suka fara murna, Basma tayi kyau sosai, masu d’aukan hoto suka fara d’aukanta, Ammi ce ta taho da gudu ta rungemata tace “Basma ina kika shige ne haka?” dariya tayi tace ina d’akina, nayi bankwana da Yaya Aryan shine barci ya d’aukeni, yanzu na kimsha nace bari na fito a cigaba da shagalin Biki dani” ai baki bud’e Ammi ta bita da kallo tana mamakinta tare da tausayinta. 
Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]