NAYI GUDUN GARA NEW BOOK CHAPTER 1

Advertisements

_____

NAYI GUDUN GARA
NEW BOOK
SABON LITTAFI
CHAPTER 1
Hall din cike ya ke da tsadaddun ‘yan mata masuji da haduwa kota ina, yayinda kida ke tashi sai kwasar rawa suke kowacce najuya irin kalar jikinta. 
Tsakiya amaryace ke murmushi ta na takawa ahankali, can kujerun da aka tanadar dan zama, samari ne da sauran ‘yan biki ke ta bawa idanuwansu abinci ganin yanda ‘yan matan ke cin uban rawa. 
Tun sanda yarinyar ta fara juya jikinta cikin salon tata rawar ya daskare a wajen, danji ya yi duk wasu ma’adanan jikinsa sun tsaya da aiki, cikin ‘yan mintuna ya bawa kowacce yarinya mark a zuciyarsa daidai iya haduwarta, amma ya hak’ik’ance babu kamar yarinyar,dan duk ta kere wa ilahirin ‘yan matan wajen, yanayinjikinta shi ya fi rudarsa,duk wani kallo da zai mata sai ya ga babu makusa atattare da ita. 
Gajiya da rawar ce ta sanya ‘yan matan su ka koma su ka zauna, Laila kuwa tunda ta zauna take kallon shashin da mazan nan ke zaune,sai wani yauk’i take tana satar kallonsu, duk wannan tana yi ne dan ta birge, kuma dan ta samu a taya ta,tamkar an tsikareta ta mik’e tsaye har tana neman faduwa, kayan jikinta ya matseta tsam nan ta fara tafiya sautin takun tafiyarta yana ba da k’was-k’was, sai juya k’ugu ta ke hade da gantsara k’irji gaba, hannunta rik’e yake da iphone 7 tana dannawa alamar tana son tai waya Ta gaban samarin nan ta wuce, duk sai suka zuba mata ido saboda yanda ta rudesu da surarta. 
Tun da ta taso ya mik’e tamkar wani wawa ya bita a baya yana k’arema halittarta ido, ganin yanda jikin nata ke kadawa, ya sanya sai hadiyar yawu ya ke, wayar da ke hannunsa ce tai k’ara ya tsaya ya daga. 
Gama wayarsa ke da wuya, sai ya shiga dubata bai ganta ba, nan ya koma wajensa ya zauna yana waige -waige. lta kuwa, bayan gama faretin nata ta dawo ta can bayan kujerun ta wuce, ta koma mazauninta, ko babu komai ta ba da show. 
10:PM Ramadan yana tafe acikin motarsa bayan fitowarsa daga wajen dinner din sakamakon gamawa da akai, babu tunnninda ya ke sai tunanin yarinyar da ya gani a wurin dinner, ta tafi da shi iya tafIya, da shi sai yace ya dade baiga yarinyar da ta ko’ina ta yi ba irinta, gashi bai samu damar koda lambarta ba, amma yana ji aransa tabbas zai sake haduwa da ita. Ita
Adaidai lokacin ya k’arasa wadataccen gidansa yayi horn maigadi ya bude masa, nan ya kunna kan motarsa cikin harabar parking lot, cike da mutuwar jiki ya flto daga motarya shiga gidan. 
Tana zaune a falonta, sai tashin k’amshi take tana kallon tasharArewa 24 ta sha wanka cikin wasu k’ana nan kaya riga da wando, bakin nan sai k‘yallin man lebe yake. Kallonta yayi hade da yin yak’e yana mata kallon rako mata duniya da tai.”Sannu da zuwa zauji”. D’aga mata hannu yayi Alamar bai san damuwa, ko dar bataji ba sakamakon ta saba da hakan. 
“Bari na kawo maka abinci, ko za kai wanka kafln nan?.” Ta fada tana kallonsa da manyan idanunta
Kallonta ya yi sama da k’asa ya tabe baki, ko kadan ba ta birgeshi a yanzu, saima wani haushin da ta ke bashi aduk sa’ilin da ya ganta, ya rasa ma mai ya sa ya aureta ne, banda kyan fuska da take da shi, sai yace ba ta da wani mamora ko’ina fayau!, runtse ido yayi. Ya bude su akanta, ya sauke kallonsa akan labbanta, abinda ke burgeshi da ita kenan,tana da kyan lebe me daukan hankali, musamman inta shafa man lebe, tabbas yasan kyawun fuskarta ne ya dimautashi ya aureta, dan idonsa ya rufe alokacin.Bai gano makusarta ba sai 
yanzun. “Baka bani amsa ba?.” “Ba na ci,” ya fada yana mai zama akan kujerar. “Ni kam sai na kawo dan na k’arasa ladana, ko ba zaka ci ba donna fita hak’k’inka.” 
Nan ta yi hanyar kitchen ta dauko try na abincin ta ajje, da ya ke dining table din na kicthen kuma ta san ba zaije can ya ci ba. 
Ga shi ta fada tana mai tura mai ido. 
Hannunsa ya sanya ya Janyota jikinsa, ganin yanda ta yi raurau za tai kuka. “Fuskarki ta yi kyau.” Ya fada mata, nan ya shiga maida kwadayinsa akan lebunanta, ya dade yana sarrafa bakin nata sannan ya saketa ya kalleta na wasu ‘yan mintuna . 
lta kuwa sai maida numfashi take, tana kallonsa hawaye na san zubowa, dan inda sabo ta saba da yanda ya ke mata, muddin tai kwalliya to bai yabawa in banda lebenta da zai kasa hak’ura da shi.Kuma a wulak’ance zaina yi mata komai. “Dan ALLAH ki daina saka irin kayan nan, Sam! basa miki kyau, bakya kallon kanki a mudubi ne? dama kina da kumari ne sai kiyi kyau, da manyan kaya ma kike sakawa da kinfi kyau, wannan ka dai ke kwatarki a wajena.” Ya fada yana mai shafar fuskarta zuwa labbanta. Hawayenta ta share ta ce ” ka yi hak’uri, bara na canja dama kwanciya ma zan”, da sauri ta yi hanyar step na bene tana kuka. Binta da kallo yayi ya saki tsaki “Yarinya sai shegen ci amma jiya iyau, duk abinda nasan zai k’ara miki armashi ina sayowa, amma kullum kamar maburgi.” Tsaki ya kuma yi, tare da yin hanyar dakinsa ko kallon abincin nata baiba. 
Watsa ruwa yayi ya shirya cikin shirin baccci ya kwanta, sai kuma ga tunanin laila ya dawo mai, nan da nan ya shiga darawa, ba abinda ke rudashi sai kyawunta, tuno yandajikinta ke kadawa yayi tamkar ana kadashi yayinda take tafiya, nan ya kuma runtse ido, yana ayyanawa aransa dama ace yanzu haka mallakinsa ce, juye -juye kawai yake har bacci barawo ya sace shi. 
Can ita kuwa Lad’ifa kuka ta sha sosai har kanta na neman ciwo, ta rasa mai yasa yake mata wulakanci kan yanayin jikinta, sai kace shi ya halicceta, in banda Iabbanta ba abinda ya ke wa mazari akanta, nan ta shiga tunanin anya ma yana sonta kuwa? domin da yana sonta ba zai na kushe ta ba, aduk yanda take to zai sota a hakan, mafita kawai take son samowa amma duk ta rasa mafita k’arshe bacci barawo yayi gaba da ita. 

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

NAYI GUDUN GARA CHAPTER 40NAY

Advertisements _____ NAYI GUDUN GARA CHAPTER 40 Yau ramadan yasan girkin safna ne yaki dawowa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *