[Advertisements⬇️]

MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 7 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MUSAYAR ZUCIYA 
CHAPTER 7
Da gudu suke bin ta suna cewa ta basu bokitan su na talla amma tamkar iska gudu kawai take har se da ta shige cikin gida sannan ta dire bokitan ta zauna tana maida numfashin wahala. Inna ta kalleta tana jimamin hali irin na ‘yarta ta ganin babu ranar da zata fito ta fad’i INdo bata yi wani abun na zagi ba, wannan dalilin ne yasa tayi niyarzuwa gidan me salati ko zata samu wani temakon da za‘ayi mata akan fltinar ta amma baban su ya hana yace shi ‘yarsa lafiyar ta sumul. Kad’a kai kawai Inna tayi ta cigaba da mark‘ad’an ta akan irin dutsen nan, INdo na gefe su kuma su Idi sai faman kumbura suke ta bud’i bokitan Ubale me d’auke da awara ta d’ibi guda biyu sannan ta tura mai bokitin nasa, ta janyo na idi shima ta d’ibi wainar rogo ta mik’a mai sauran tana ce musu. 
“Naci lada kuma wabillahillazi kuka sake ganina kuka fad’i wata kalmar sai najamuku asara kuce ba suna na A‘isha ba.” Suka d’auki bukitan su sukayi waje kowanne da irin kalar wulak’ancin da zai mata a zuciyarsa, Nafeesa k’anwarta ta shigo gidan tana ganinta tayi saurin Goye kwanon awarar dan karta d’aukar mata. 
“INdo rowarjaraba.” Cewar Nafeesa tare da k’arasawa wajan INdon ta zauna harda su 
tankwasa k’afafuwa ta mik’a mata hannu alamar ta sammata. Mtww “idan ni marowa ciya ce dalla malama kekuma mecece? Ungoni ki matsa ki bani guri.” Ta juya tana kallon Inna tace “Inna ga awara idan zaki ci.” Inna ta k’araso gurin tana cewa “Ni wallahi ‘yar nan bana son wannan mitar taki, inda Allah ya temaka ma kun koma makaranta zaku shiga ajin gaba ni banaci na k’oshi da abin fltina.” INdo ta fara sosa kai tana kanne ido d’aya sabidajin zafin yajin bakinta tace “Inna wallahi bazan koma makarantar nan ba wata zaku sakemin, wai d’azu harni malam Sadeeq zai cewa tinkiya! Wallahi toh bazan koma ba yaje yacinye makaranta.” ‘ 
“Yanzu kin dena zuwa ‘yar nan? Toh wacce kike so!!?  ke ba tsayayyan saurayi 
ba bare ayi miki aure yau na shigesu ni Maryama.” “Inna wallahi bazan koma tsefawa ba na fasa zama likitar dama temako zan dinga yi toh yanzu kuma nafasa suje sunemi wata.” Inna ta kad’a kai babu abinda zata iya cewa akai koda baban su ya shigo ma bata gaya maiba bare su d’auki wani mataki haka suka barta kullum bata nan unguwar bata waccen har aka d’iba sati biyu ko hanyar makarantar bata biba bare asakaran zata shiga, tsab Sadeeq ya manta da ita domin ya toshe duk wata hanya daya san suna had’uwa. 
A Gangaran Abubakar kuwa yana matuk’ar son Mareeya har hakan ya fito fili ragowar nurses suka fuskanta, wasu suka hakura dashi yayinda wasu kuma suka d’auki tsana da takura suka d’orasa akan ita Mareeyan suna ganin itace tayi wani kulla-kullan harya karkata wajanta ya barsu. Sosai suka shaku Abubakar har ya had’a su da Sadeeq awaya suna gaisawa hakan ya sake narkar da sonta a cikin zuciyar Abubakar d‘in. 
Wata ranar juma’a ne Sadeeq dayaje makaranta dama duk juma’a yakewa ‘yan ajinsa duban tsabta, yana duba farcensu, hak’oransu, mata ya duba kitso maza kuma aski da kuma uniform duk wanda yafi kowa tsafta zai bashi kyauta. Ashe INdo ta samu labari yau 
yana cikin dudduba su sai gata ta shigo asukwane cikin ajin malam Sadeeq ya kalleta cikin tsananin mamaki kamar aljana uniform d’in nata sharkaf da ruwa a haka tasa su gashi tayi wata mahaukaciyar kwalliya kamar wata iflrituwa ta fara tafiya zuwa bencin su Uwani halilu suka matsa mata har ta kusa kai duwawunta k’asa yayi saurin dakatar da ita ta hanyar yi mata wata razananniyar tsawa ya had’a da cewa. 
“Ke meya kawoki wannan ajin? Wacece ke haka? Daga wane sahun aka zakuloki..?!” 
lNdo ta kalli kan teburinsa taga kayan kyaututtukan da zai bayar sai ta dashare mai jawur d’in hak’oranta domin tunda ta siyi brush da makilin d’in nan bata taba yi ba zuwa tayi ta zubesu a gida toh dama ba’a sababa ta k’arasa zama tukunna tace masa. “Haba malam Sadeeq nicefa INdo malam Hamza.” “Will you shut up…Nonsence, zoki Fltar min daga aji wawuya waya kawoki jss 3? Keda har yanzu kina jss 1 shine yau zaki wani shigo min zoki fita inba hakaba na lahira ya fikijin dad’i.” Yayi maganar yana nuna mata k’ofar data shigo ransa a matuk’ar had’e, sai ta fara kallon ‘yan ajin d’aya bayan d’aya tare da mutsittsike idanuwa taga dai still sune dai ‘yan ajin nasu nada amma ya za’ayi yace wai nan ba ajinta bane dan shi munafukine, tokuwa babu inda zata dan nan gwamnati ta tsaga mata dan haka tayi kicin-kicin da fuska wai taga ko zai kuma 
cewa tafita. “Ke Aisha ba magana nake yi miki ba?” Ya fad’a yana k’arasowa bencin da take, INdo tayi saurin mik’ewa tana kallonsa tace “Yo toh malam duk fa k’awayena ne kuma ‘yan ajinmu ne ya zakace na fita ina zanje ni.” Yace “Tallah, koba ita kika fiso ba? And bakin ce bazaki sake zuwa tsefawa ba yau kuma wane munafuncin ne ya shigo dake da wasu jik’akk’un kayanki kila ma fitsarin kwance kika yi, oya zokiyi out kina b’ata mana lokaci.” Duk cikin maganarsa babu wacce take k’ona mata rai irin yace tazo ta Flta, kuma kallon kayan kyautar tayi kawai sai ta rushe da kuka tana fad’in “Kai malam.. Kai malam, sai da kaga nazo na kusa cinye kyautar nan shine zaka ce natafi ba ajina bane. Toh malam wane ajin zan koma kuma?.” Tsananin mamaki ya cika Sadeeq ganin tana kuka, tunda yake be taGa ganin hawayenta ba sai yanzu haka kurum kuma sai yaji duk ya tsani kansa domin yasan ita d’in mahaukaciya ce ya kamata ya dinga bata kulawa ta wani bangaran ko Allah zaisa ta gyara wani abun 
hakan yasa shi juyawa yanaci gaba da duba ‘yan ajin harya zabo mutum shidan da zai bawa kyautar . Yana zuwa kan INdo tundaga kan uniform ya fara rankwashin ta domin haka yake yiwa duk wanda yake da gyara, INdo tayi saurin dafe gurin tana fadin “Kai…kakai…kakai..! Malam da zafifa.” Yace “ha.bude.bakin muga teeth naki.” INdo da taji yace ha bakin yasa ta bud’e mai tamkar zata cinyeshi yayi saurin matsawa sabida wani hamami dayake tasowa daga ciki yana toshe hanci yace. “Such a stupid hak’oranki zaki nuna min bawai cewa nayi ki hangame min ba.” 
Hannu tasa ta toshe bakin tunawa da tayi lokacin da sukace bakinta yayi,,,,,,, ya kalleta yace. “Bazaki bud’e ba saina mareki..?!” 
Ta d’aga maikai bakinta a toshe da hannunta tace “Malam gara ka marenin da na bud’e ma ballahillazi.” Mtwww yaja tsaki dan yasan babu abinda za’a zaba a gurinta, ya kuma matsawa ta baje hancinta tana shak‘ar k’amshin turaren jikinsa yace “muga farcenki.” Tana jin haka tayi saurin zame hannunta daga baki ta cukwaikuye hannuwan acikin hijjabi tana zaro mai ido ya kuma kuluwa yace “muga kanki..? 
A hankali ta bud’e shi ya kalla tare da tabe baki ya bar gurin, akwai kitso saidai ya tsofa sosai dan ko tsagar ba’a gani gashi gashin nata jah ne kamar gashin akuya sai dai da ka ganshi kasan zaiyi laushi domin irin me yalai-yalai d’in nan ne, ta kalli Uwani halilu tana sosa hanci tace. ‘ 
“Uwani kin taba cin gasar kuwa?!” Uwani ta harareta tare da k’in bata amsa ganin haka yasa tayi mata kallon sama da k’asa tana fad’in “ji banza kina jima ina tambayarki.” Malam Sadeeq ya d’akko wani yadi na maza ya mik’awa D’ahiru Miko ya durkusa har k’asa ya karba sannan yayi godiya malam Sadeeq yace. “Ku tafawa D’ahiru miko ya samu wannan kyautar ne saka makon d’inkin uniform d’insa sabo ne, yayi aski sannan baya barin farce zak’o-zak’o gashi yana k’amshi babu wari a jikinsa hak’oransa ma sun fara haske..” Aka fara tafawa raf-raf-raf INdo sai k’arayi take da k’arfl har aka gama yi sau biyar yadda ya koya musu INdo bata denayi ba sai da yace “ke naji..!, ya isa haka baki ji yadda suka had’u suka yi nasu ba ne a tare?” Sai a lokacin ta dena amma fa bakin nan a wangale tamkar ita aka bawa yadin. 
Mace kuma Murja Ashiru ce ta samu ya bata fallen atamfa biyu itama aka tafa mata still INdo sai da ta zarce har wani dak’irewa tayi sai da Atika bawa ta bige mata hannun sannan ta denayi yace musu “Yau Atika bawa tafi ko wace mace tayi kitso harda kunshi, kayan makarantar ta harda guga babu farce ta yanke itama tayi brush.” Aka sake tafawa sam INdo bata iya ba da kowa zai denayi amma ita sai ta k’ara. har ya kammala bama ragowar suka koma suka zauna yayi musu nasiha akan tsabta sannan ya kwashi littattafansa zai fita INdo tayi saurin cewa. 
“Malam…!” Ya tsaya cak ba tare daya juya ba tace, “nima wata juma’ar zanyi duka amma ni hadda (shadda) nakeso ruwan bula kaji ko…?!” Juyawa yayi ya kalleta sannan yace “Toh kiyo amma bake zaki gaya min abinda kike so ba 
sai abinda nayi niyar bayarwa kinjiko..?!” Tayi shiru bata amsa mai ba yayi tafiyarsa ta zauna tana cewa “kajishi fa, salan kawai a baka abinda bakaso mtww.” Babu wanda ya kulata ta mik’e ta koma wajan Atika ta k’arbi atamfar tana gani ji take inama ta tace har ta hango irin d’inkin da zatayi dan taga wani style a jikin Rukayya amarya. Duk wanda aka bawa kyauta sai da taje ta ansa ta gani har ta fara Allah-Allah wata juma’ar tazo itama taci 
Hmmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]