[Advertisements⬇️]

MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 6 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MUSAYAR ZUCIYA
CHAPTER 6
Zaune suke a cikin d’akin su, babban d’aki ne domin a da a matsayin sitting room yake lokacin da suka taso suka zama samari yasa abban su ya bar musu shi suka gyara shi aka sanya musu katifu guda biyu d’aya na gefen hagu d’aya na dama sai durowar kayan su ko wanne ya d’auki gefe d‘aya domin kayan nasu ya bambanta. Abubakar shine yake son sanya k’ananun kaya sabanin Sadeeq daya fi son manya kamar su shadda boyal da sauran su. Shiru Sadeeq yayi idanunsa a sama kai da ka ganshi kasan ya fad’a cikin zurfaffan tunani, kallan sa Abubakar yayi cikin tabe baki yace. “Twinnie ya aka yi ne kake wannan zurfaffan tunanin?” 
Sadeeq ya numfasa tare da tashi zaune ya janyo kofin zobon da Maman su ta aiko musu dashi ya d’iba yasha sannan ya zuba wani ya mik’awa Abubakaryana cewa. “Twinnie ina tuna nin maganar Mama ne ta jiya, kaga tace Abba zura mana ido kawai yake yaga dame zamu fara. Gaskiya ni yanzu na fara tunanin gara na fara yin gini na tunda ya riga ya bamu filayen kuma yace duk inda muka ga ya kakare mana toh muyi mai magana gara kawai nazo na fara dan ina son lokacin da zan fara neman aure toh ya zamto koda ban k’arasa ginin ba to ya zamana sauran k’arashe shi yasa kaji nayi shiru ina tunani.” Kai kurum Abubakar ya jin-jina sannan ya mik’e tsaye, shirin taflya asibiti yayi ganin be ce komai ba yasa Sadeeq cewa. “Toh kai naji baka ce komai ba ka kuma tashi zaka tafi meke nan hakan da kayi..?!” Shafa gashin kansa yayi tare da d’aukar turare ya fesa. “Karka damu twinnie da rashin maganata, kasan dole idan naga ka fara nima na fara har addu’a nake mana Allah yasa mu samu matan aure ‘yan biyu kawai mu aure su, dan haka karka damu kai dai ka fara samo 
matar tukun na.” Sadeeq yayi dariya tare da komawa ya kishin gid’a, yana murmushi yake cewa. “Lallai kuma a ce mun had’a gida kuma kamar su d’aya like me n you, tab ai sai mu kasa ganewa haka kurum wata rana in dirfafi matar ka ko kai ka shigar min gona toh a’a..” Abubakar ya kyal-kyale da dariya irin wadda be taba yi ba ya kalli Saddeq yana nuna shi da yatsa yace. “Amma dai my twinnie muguwar fassara gareka, babu abin da zai faru kai dai kayi mana fatan alkairi..” “Toh ai gaskiya na fad’a ko kuma matar ka ta fito ta ganni tayi tunanin kaine tazo ta mak’ale min ni bazan hanata ba tunda jiki dajini, ko kuma tawa matar ta ganka tayi tunanin nine gaskiya twinnie ka dena yi mana fatan auran twins dan ni gaskiya ka san bani 
da kauda kai, shi yasa ma da Abba yace baxai bamu gida kusa da juna ba banji haushi ba.” “Hahaha twinnie ai ina tausayawa duk wadda zata aure ka wallahi domin zata sha wahala, kana gani a yanzu ma baka da auran sai kayi dreaming sau uku hud’u bare kana ganin ta.”Murmushi Sadeeq yayi tare da gyara kwanciyar sa yace “twinnie kayi tafiyar ka kana yin 
late ga marasa lafia can na jiranka ni bacci ma zanyi dan ban gama ba ka tashe ni bye.” “Hmmm ka dai kore ni toh Allah ya baka mata a kauyan daka baro tun da baka son muyi iri d’aya.” “Wallahi ba amin ba, duk basu da hankali musamman ma iNdo kai! wannan yarinya ba hauka ne yake damunta ba harda jahilci kasan shi yafi hauka. Gasu k’azamai tunda naje garin banga wayayye ko wayyayi ya ba wallahi, ba amin ba dan kamar yadda kake son 
nutsattsiyar mata haka nima nake so kuma ‘yar gayu mai ilimin zamani da na addini..” “Twinnie kad’auki zafi da yawa so sorry dan Allah, bari naje na dawo bye..” “0k sai ka dawo.” Da haka suka rabu sai da Abubakar ya shiga cikin gidan yayi sallama dasu Maman sa sannan ya fita, yayin da Sadeeq ya kwanta duk da cewar maganar da d’an uwan nasa ya fad’a tasa baccin ya gudu sabida takaici hakan yasa ya tuno da lNdo yaja tsaki tare da mik’ewa ya koma cikin gida ko zaiji dad’in ranshi a gurin su Maman su.
 ‘IHSAN MEDICAL CENTER‘ 
Ahankali yake karasawa asibitin na ihsan medical center dake unguwar sultan road nassarawa gra agarin na kano,sanye yake cikin kananun kaya kirar suit blue tacikin kuma fara ce hannunsa rike da jakar laptop d’insa fuskarsa sakale da farin glass se bulbula kamshi yake haka yashiga harabar asibitin,yana shiga ya hango nurse hidaya k’ok’arin juyawa yake ta cinmashi da sauri, “Wlcm Doctor,lna kwana..?!” “Fine Alhamdulillah nurse hidaya..” Yana gama fada yai gaba ya barta wajen Office d’insa ya nufa inda sunansa ke rubuce boldly ajikin k’ofar office din ‘Dr Abubakhr’ kamar kullum Mani Cleaner ne aciki yana tsaftace office din se mopping terrazzo din yake dake ta shekin kyalli,da sauri Mani ya tsugunna yana kwasar gaisuwa “Sannu da xuwa yallabai Barka da safiya” “Barka dai Mani.” 
Kan kujera dr Abubakar ya xauna yana dudduba files din kan tebur din one by one,har Mani yakarasa ya feshe office din da freshener, “Yallabai na kammala” “Yawwa Mani godia nake xaka iya tafiya” 
Har Mani yakai kofa yadawo yana sosa keya, yqce yallabai an bani sako wajenka amman wlh na sha,afa da sunan nurse dinnan ce dai ta tayi transfer daga Cotonou” Sarai abu abubakr ya gano wacece naccaciyar yarinyar data nace masa ce, To Mani ba damuwa tunda kamanta sunan kaje kawai” Shiru Mani yai da alama ya zurfafa tunani bejima ba ya dago yana murmushi, “Yallabai natuno nurse natasha ce da sassafe xuwana kenan tabani sako nabaka nikuma hartamin alkhairin Naira dubu yallabai” “Toh madallah”cewar Abubkhr tareda shan kunu Kyakkyawar farar takarda datasha xanen heart Mani ya ajiye akan tebur se faman sosa keya yake don wannan bashine karo na farko ba da nurses suka sabayiwa ogan nasa haka,cikin dakakkiyar murya Abubkhr yace “Jeka Mani sena neme ka..” “To Yallabai Nagode ahuta lapia..” Mani naflta abubkhr yaja tsaki k0 duban takardr beyiba ya mike don yin round na patients fltarsa kenan suka kusan yin gware da nurse Deexah uniform dinnan sun matse ta koina na 
jikinta ya bayyana se wani rausaya take tana karkada jiki, “Dr..Pls”tace hakan cikin wata irin siga “Please what ?linada patients daxan duba pls..”yakarasa hade da kaucewa ta gefanta xe wuce tai hanxarin shan gabansa bayan tahada tafukan hannayenta biyu sama alamar roko, “Dan Allah dr ka saurareni minti d’aya pls” Allah data ambata yasanya shi tsayawa ba tare daya karasa tafiya ba amma bejiyo ba fuskarsa kan agogon dake daure a hannunsa yanajiran minti dayan ta cika, “Ki magana kafln minti dayan ki tacika pls” ‘ “Dr Meyasa kake mun haka? Kaso me sonka,ka agaxawa xuciyata kaceto ta daga fadawa kogin halaka,duk asibitin nan babu wanda na xaba amatsayin wanda zuciata take muradi sekai” ‘
Karasa maganar ta yayi dede da cikar minti dayan data ambata don haka yai gaba abinsa Yashiga bin round na patients sedaya kammala tsaf sannan yashiza office din abokinsa wato dr luqman, Sun dan taba hira sunayi suna tafawa sannan luqman yashigo da wata hirar, “Nikwa Abokina nagaji da kawo korarrafinan da ake kawomun akanka wlhy,yanxunnan nurse deexah taflta hawaye kwance shabe shabe kan fuskarta dukde akan ka,dama yanxun nake maganar koba ka shigo ba xanxo na sameka don nikam nagaji” Murmushin takaici Abubkhr yayi cikin nutsuwa yace, Toh Aboki bani shawara shin mexanyi akai?” “Ni Ina ganin kaxabi d’aya kawai ka aura kaga ai dole sauran su kyale ka k0?!” Ajiyar zuciya Abubakhr yai kafln yace, “Gaskia Aboki kabani mamaki wallahi domin bantaba sakaka a sahun mutanen daxasu bani shawarar naxabi d’aya daga cikin nurses dinnan na aura ba,karka manta dukwani namiji yana sone ya auro yarinya yar mutunci me dattako da sanin yakamata wadda ‘yayan daxata haifa ma xasuyi alfahari da kasancewarta uwa tagari, To axahirin gaskia de magana d’aya ce xanyi wallahi duk cikin nurses dinnan babu wadda xan iya xaba a matsayin wacce xan dauka nakai ta gidana wai amatsayin matata ta aure,Kowa Allah ya hadashi da rabonsa kawai ko ya kagani?!“ 
Shiru dr luqman yai yana cin faratansa da alama yarasa tacewa,knocking akai a kofa har sau uku hakan yasanya abubkhr bada izinin shigowa bayan yace,“Yess” Shigowa tai sanye cikin abaya baka bakinta dauke da sallama hannuwanta rike da files cikin siririyar muryarta kamar anbusa sarewa tace, Gashi Doctor,duk nagama komai har room 13 dakace nayi mata inducing ruwan..” “Okay nurse Mareeyah thank you..Xaki iya taflya” Dama abinda Mareeya kejira kenan tai hanxarin ficewa abinta,baki galala abubkhr yabude yanabin k’ofardata rufe da kallo kafin yadawo da kallonsa kan Doctor luqman cikin sauri yace, “Dr ai naxatan nurses d’innan sun gama aikinsu sun koma ya kuma Naga wannan?!” “0h mareeyah riketa mukai wallahi yarinyar ta iya aikinta ga hankali da nutsuwa wallahi ba ruwanta da shiga harkar mutane kullum ita kad’ai xakaga tana aikinta”“Mareeyah..”Dr abubkhr ya maimata sunan “Kwarai sunanta mareeyah..A’a kode kafada’a da…”ai luqman ne k’arasa ba abubkhar yai hanxarin ficewa Cikin sa’a ya hangota tsaye a corridor tana shimfida sallaya xatai sallah, “Salam alykm..”cewar Abubkhr daga bayanta.. “Wa alykm Salam”tabashi amsa tana k’ok’arin gyara mayafin data yafa Ya salam,,abubkhr yafurta azuciyarsa Dakyar da lalubo salati yasamu ya saisaita kansa kamar bashi ba yace, 
Dama uhm..idan baxaki damu ba magana nakeso nayi dake” “Babu damuwa amma xanyi sallah de tukun..” “Tohm shikenan take ur time xanjira”cewar abubkhr 
Ya jima azaune sedata idar tai addu’ointa tukun sannan ta nannade praying mat dinta ta mayar cikinjaka, “Ina jinka dr..” 
“Okay.. Sunana Dr Abubkhr..” Allah sarki..Ni sunana mareeyatul qibdiyya.” “Nice name qibdiyyah,” Nande abubkhr yashiga gaya mata meke tafe dashi da abunda ke cikin zuciyarsa,itade mareeyah kawai kallonsa take tana mamakin dama yana magana haka?!Abubkhr be bar maareryah ba har seda ya tabbatar ya dana mata tarkon son sa tukun sannan sukai exchanging numbers zuciyarsa fes yakoma gidah, 
Kullum de abinda ke faruwa kenan abubkhr har gidah yake xuwa xance wajen mareeyah ashema basuda nisa su su abubkhr suna unguwar Court Road ita kuma Mareeyah tana Hausawa,Sosai suke gwangwaje soyayya abun su shikuwa sadeeq har yanzu be samu wadda ta kwanta masa ba duk ya gwada amma babu sa’a ga cuku cukun transfer dayake nema amma yakasa samu haka ya hak’ura yafara shirin komawa makarantar tsefawa dake kauyen Sani a k’aramar hukumar sumaila.. 
Ranar asabar da safe sadeeq yatasamma titin sumaila bayan yasha adduoi daga mahaifansa da kuma dan uwansa abubkhr wanda sam be so komawar d’an uwan nasa kauyan kayayau d’inba, 
Yana shiga cikin unguwar kuka sunan unguwar tasu kenan ya farajiyo hayaniya sama sama be tabbatar da muryar ba seda yaxo daf da dandaxon jama’ar da suka taru suna kallon fadan da ake tayi muryarta yagane kowacece siririn tsaki yasaki jin muryar lNdo ce dan turmutsawa taron yai ya hangota sanye cikin kodadd’un kayanta se jurwayen fltsari riga daban xani daban d”ankwali kuwa ba’a xancensa se tumurmusar fad’a suke da wasu yara maza kuma duk itace me karfin ciki,wani daga cikin taron ne yace “Ke y’ar nan kome sukai miki ki hak’ura ki kyalesu tunda ke macace dan Allah” Cikin turo baki had’e da k’ank”ace idanuwa tana girgixa kugunta data d’aure da shamilallan hijabinta tace, “Ta kwarankwasa baxan hakura ba,Babban bala’in can,se in xauna gani sokuwa sumin lefi sannan na hakura wallahi babu xancen hak’uri a dishenari (dictionary)na ramuwa ta da ta taxama dole..” Tana gama fada tacigaba da kokawar da take yi cikin xafin nama sadeeq ya k’arasa cikin su 
ya wanke mata fuska da mari hade da hankadata gefe yatsan sa yasa yashiga nuna ta, “Ke wai wacce irin kidahuma ce ne eh?! Kina mace kike fad’a? fad’anma da maxa dandaxon mutane akanki ko kunya bakyaji? Tukun nama me akai miki da kika kamasu kina duka kaman wata tinkiya..” 
Rike baki Indo tai tana kada Kai 
“Kai ka Kai Kai Kai wacece tinkiyar?!” “Kece tinkiyar” “To wallahi ka bude kunnuwanka kaji niba tinkiya bace kuma kwarankwatsa ka kara cemin tinkiya seka gani. Haba nifa kana shiga rayuwata da yawa makaranta ce de nace ni INdo Malam hamxa nadena xuwa tsefawa unifam d’ina ma na yadashi amma saboda tsabar shisshigi da neman sani seka tsoma wannnan bakin naka a xancen da ba naka ba” Tana gama fada ta shuri bokitan su ubale da idi na talla da suke fad’a tai gaba dasu tana sharara uban gudu,ganin haka yasanya su ubale binta a d’ari suna rokonta da tabasu bokin tallansu da ta kwashe, 
Karkad’a kai kawai sadeeq yai wani b’angare na zuciyarsa na tabbatar masa da lallai yarinyar nan ba aljanu bane kad’ai da itaba Lallai babu shakku acikin kwakwalwarta ta tabu, da haka ya k’arasa gidansa yashiga bakinsa d’auke da sallama tamkar da mutane a ciki. 
Hmmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]