[Advertisements⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA THEND - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA 
CHAPTER 24 THEND
Amina tace rahma mai kike fad’a haka? Tace mum abunda na fad’a Shl nake nufl, zarah tace rahma miye haka kin san abunda kike fad’a kuwa shin ….. Tace zarah dan Allah ya isa haka bana son wannan auren plz Kar Wanda ya takura min akai tana fad’in haka ta haura Sama da sauri, kowa shiru yayi dan mamaki alh Mahmud ne ya Katse musu shirun da fad’in plz zan iya ganinta muyi magana, zarah tace eh muje in raka ka, tashi yayi suka haura sama a falon sama suka ganta zaune zarah fita tayi ta koma, matsawa yayi kusa da ita tare da kiran sunanta, d’ago dakai tayi ta kalleshi ido suka had’a sunyi wajan minti biyu suna kallon juna Kafin ta kawar da idonta, murmushi yayi tare da fad’in naga sona a cikin idonki, amma rahma mai yasa kika ce kin fasa auren bayan Nasan kina so na? Kuka ta saki mai sauti zama yayi kusa da ita tare da rarrashinta, yace haba my princess ki daina Yimin asaran wannan hawayen naki plz, dan tsagaita kukan tayi yaci gaba da fad’in Rahma din dana sani bata boye abunda ke ranta dan haka fad’amin miye dalilinki?tace Mahmud bazan iya aure ba har sai naga khairat tayi, ta girmeni nice kanwarta, mutane za suyi ta Mata surutu, wannan shine dalili na, murmushi yayi tare da fadin hakane rahma, inaso ki sani ina sonki sannan duk wani abu da Kike so zan miki, zan jira har khairat tayi aure sai muyi namu, wani irin murmushi ta saki cikin jin dad’i, tace amma dan Allah kamin alkawari kar kowa ya Sani, yace na miki my love, tace nagode fita sukayi tare alh Mahmud yace mama munyi magana da rahma Nima banso Ayi auren yanzu har sai ta yarda yana fad’in haka yayi musu sallama tare da tafiya, dukansu an barsu cikin duhu Toh Mai rahma take nufi? Amina ce ta kama hannun rahma sukai ciki, tace mai kike nufi rahma? Rahma tace mum bazanyi aure ba har sai Khairat tayi aure sannan nima zanyi, Amina tace what? Kina da hankali kuwa? Yanzu saboda khairat kika ‘ki yarda da aurenki? So kike kiyi ta zama a gida, har yanzu babu wanda ya taba cewa yana son khairat koh yazo da Sunan zance, dan haka sam ban amince da wannan maganan naki ba, rahma tace mum nariga na yanke hukunci bana tunanin zan canza, marinta Amina tayi tas tare da fad’in har yaushe zaki ta jira?waye yazo yace yana son khairat fad’amin? Rahma tace bazan iya Sani ba amma mum koda zan mutu bazanyi aure ba har sai Khairat tayi tana fad’in haka ta fita fuuuu ganin khairat tayi ta wajan kofar d’akin da alama taji komai, rahma tace khairat, ganin Rahma zata karaso inda take yasa khairat ta ruga da gudu tana kuka ta shige d’akinta tare da rufewa, rahma buga mata kofar tai tayi tana fad’in khairat dan Allah ki bud’e jin haka yasa su Ummi dasu zarah suka zo, suna tambaya laflya? Rahma tace mu fara fito da ita tukunna, sunyi bugun duniya amma taki bud’ewa saida Abubakar da driver suka zo suka balla kofar, a kwance suka ganta a kasa farin kumfa na fita a bakinta, da sauri suka kira Dr, ba’ayi minti biyar ba saiga Dr din, nan aka fara bata taimakon gaggawa sannan aka sata 3 mata ambulance akai asibiti da ita, koda suka karasa emergency akai da ita cikin ikon Allah aka ceto rayuwan ta, amma bata riga ta farka ba, sai dai duk wani guban da ‘taci ya fita, Koda Dr tama su ummi bayanin ciwon y’ar tasu, ran Ummi ya baci Sosai akan Mai zata sha guba? Rahma kam babu abunda take sai kuka, dan tana ganin kaman saboda ita khairat take son kashe kanta, sunyi wajan awa d’aya suna jira Kafin ta tashi, dishi dishi ta Fara gani sannan ta Fara ganin kowa dakyau, ummi rungume y’ar tata tayi, lokaci d’aya kuma ta saketa tare da fad’in khairat Ashe baki da hankali? Kinsha guba so kike ki kashe kanki kin San makoman Wanda ya kashe kanshi kuwa? Cikin kuka tace ummi kiyi hakuri banda wani zabi ne, shi yasa Nayi hakan, rahma tazo da sauri ta rungume khairat tana kuka tare da fad’in kiyi hakuri khairat Wlh b…… Khairat tace ya isa haka naso in mutu dan na baki daman yin aure ne rahma kika sani ko Ina cikin wanda har su mutu ba zasu taba yin aure ba. shi yasa haryanzu babu wanda yace yana sona, duk da kullum burina Nima in sami Wanda zaice yana sona amma hakan bamai faruwa bane, rahma tace ki daina fad’in haka insha Allah zakiyi aure nan bada dadewa ba sanna karki kara aikata wannan abunda kikayi a rayuwa, tace nayi alkawari, kara rungume junansu sukayi suma su zarah suka rungume su, suna cikin haka farida tayi kasa tare da ri’ke cikinta tana nishi, da sauri suka kira Dr, nan akace haiyuwa ne, labour room akai da ita akace suje su d‘auko kayan haiyuwa, Abubakar da zarah ne suka tafi daukowa, batai wani doguwar na‘kuda ba farida ta sullubo y’arta mace kyakyawa sak babanta faruk, kowa yana ta fad’in Kai yarinyar kyakyawa ita kam Amina k’in amsan yarinyar tayi, ummi ta Lura da hakan ta amshi yarinyar a hannun khairat dake zaune ta mi’ka ma Amina, Amina ja baya tayi tare da fad’in barta kawai, ummi tace jikarki cefa ,Amina tace bajikata bace domin bazan amshi d’iya mace a matsayin jika ba,jiba halin da muka fad’a damma Allah yasa yaranmu suna da basira, bazan so hakan ta kara faruwa ba har abada, ummi tace y’ay’a mata rahma miye illar y’ay’a mata? Haba Amina baki ga abunda son d’a namiji yaja ma mijinmu ba? Jikin Amina ya fara sanyi ganin haka ummi taci gaba da fad’in kalli babyn sak kaman faruk,jin haka yasa kwallan da take makewa ya fito tare da amsan yarinyar tana murmushi, lokaci d’aya tace sak faruk Allah sarki inama yana nan, kowa shuru yayi yana kallonta, kwanan su biyu aka sallamesu, sukai gida. Anata hidiman suna amma Amina kwata kwata taki sakewa, yau suna zaune a falo, Amina tazo ta dur’kusa wajan mama tana kuka hankalin kowa ya tashi nan mama tahau tambayan Amina lafiya kuwa? Amina tace dan Allah mama kisa baki su zarah su saka a sake faruk tunda bashi bane yayi laifin ba dan Allah, aneesa amfani dashi tayi dan Allah mama, mama cikin bacin rai tace bazai taba yihuwa ba, Amina tace mama ki taimaka bashi ya kashe mijin mu ba, ki tausaya Mai kodan darajan yarshi, mama shuru tayi can tace shikenan zarah kusa a sako shi, rahma tace mama shinef ….. Mama tace umarni na baku, duka yaran shuru sukayi amma ransu a bace, mama tace su tashi suje su ciro faruk, haka suka tashi su duka harda amina da take ta murna suka nufl station, inda aka basu faruk duk yayi ba’ki ya rame, Amina rungumeshi tayi tana kuka, matsawa yayi kusa da y’an uwanshi dan yayi musu godiya, yace nago ….. Zarah tace dakata karka d’auka danka fito kasha ko mun manta abunda kayi sam ko d’aya bamu manta ba sannan sai munsa kaima an hukunta ka, daka yau babu mu babu kai ka d’auka baka sammu ba a rayuwa, Amina ta kamo hannun faruk dake hawaye tace muje, rahma tayi tsaki sannan Suma suka wuce, koda suka je gida faruk hakuri yaita bama mama tace babu komai ya gefen ummi ma babu yabo babu fallasa, sai dai yaransu da sukeji kaman su tsige faruk, farida kam k0 kallanshi batayi ba yaga yarinyar shi ba karamin dad’i yaji ba tare da son yarinyar Sosai duk da yana son yima farida magana amma bata bashi fuska ba dan tana tare dasu Rahma.Anyi suna yarinya taci suna Amina, yayi ma Amina takwara suna kiran yarinyar da suna Afra. 
BAYAN WATA U KU ‘ 
Haryanzu Anata case dinsu Aneesah a kotu, inda a zama na karshe ake sa ran yanke 
hukunci, abubuwa da dama sun faru ciki harda komawan aysha d’akinta domin Maman mijinta tazo da kanta ta bada hakuri tare da fad’in shairin shaidan ne, zainab kuma an raba gado an bata nata kason ita da y’arta, sannan akwai wani guy Da yake Sonta Mai suna Muhammad, abokin alh Mahmud ne da suka zo tare yaga zainab ya mutu a kanta da farko bata amince ba saida kyarta amince domin irin kyautata mata da yakeyi da nuna yana son y’arta, shine yasa ta yarda gasu ummi da zarah dake ta bata shawara, ta gefen faruk kam har yanzu y’an uwanshi mata basu sake Mai ba domin Sun tsaneshi Sosai, khairat ita kuma ta sami aiki a wani babban company inda kwazonta yasa kowa ke yabanta, oganta a offlce sunanshi Muktar yana da son Mata Sosai gashi yaro Muktar shine d’a d’aya wajan mum dinshi, shi yasa yake she‘ke ayarsa babu ruwanshi tunda yaga mum dinshi na sonshi tun yana dan shekara Goma sha biyu dad dinshi ya rasu mum dinshi ita ta ri’ke Business dinsu har Mukhtar ya girma ya kammala karatu ya amsheta, Muktar kyakyawa ne ajin Farko, Mata na sonshi Sosai dan yana da kyauta, akwai wata yarinya mai suna hauwa da yaso ya aura mum dinshi ta gano y’ar iska ce ta hana auran, duk da burinta kullum shine d’anta yayi aure, akwai sanda khairat takai mai wasu takardu office taga yana kissing din wata yarinya, tace mishi kaji tsoran Allah komai kakeyi Allah yana kallonka mum dinka mutuniyar kirki ce Banyi zaton jininta zaiyi haka ba, tana gama fad’in haka ta fita, tun daka ranan yake ta neman hanyar da zaiyi maganin khairat, yau yana office yana duba file ya tashi tsaye cikin fad’a ya nufi waje wajan staff bai tsaya wajan kowa ba sai wajan khairat yace no wander shi yasa har yanzu kika kasa samun mijin aure saboda wannan idon naki Mai ido hudu ke wace irin wawiya ce haka nace kiyi watsa mata yayi a fuska yace maza ki gyara yana fad’in haka ya koma ciki, khairat kuka tasa Mai taba zuciya, lallai itama rashin jin magananta yaja mata suda suke da nasu company din amma tazo wani waje tana aiki ai dole taga ba dai dai ba amma daka yau zan ajiye aikin, rubuta resignation letter tayi takardan barin aiki, yana zaune a office sai gata ta shigo kallonta yayi cikin fad’a kin gyara? Jefa Mai takardan tayi a fuska tace gashi takardan barin aiki,nane bazanci gaba da aiki a karkashin dabba irinka ba, tana fad’in haka ta fita gashi da karfi take maganan duk staff suna ji, Muktar tunda yake yau itace rana ta farko da akaci zarafin shi, iska Mai zafi ya furzar tare da fad’in saina aureki nasa kinyi dana sanin wannan abunda kikayi saina lalata miki rayuwa nayi alkawari. 
Khairat gida ta koma rai a bace, tana shiga taga Mahmud da rahma a falo, wanda yasa dole ta saki fuska, dan karsu fahimci halinda take ciki, rahma taga shigowanta tace a’ah yana ganki yanzu Nasan lokacin tashi baiyi ba, khairat tace rahma na ajiye aiki, rahma tace mene? Khairat tace eh na gaji gwara in huta, rahma zata kuma magana khairat tayi sauri ta rigata tare da gaida Mahmud tace saukan yaushe? Yace dazu nazo dan inga gimbiyar, dariya khairat tayi tace oh I can’t wait to see your weeding, alh Mahmud murmushi yayi cikin jin dad’i domin shidai bashi da burin daya wuce ya auri rahma, Khairat shiga ciki tayi inda ta fad’ama y’an uwanta tabar aiki tare da fad’a musu dalili koda rahma tazo itama Sun fad’a mata ransu ya baci Sosai sukace gwara ma data bari. Iyalan marigayi alh Ibrahim ne zaune suna cin abincin dare akan dinning, suka ji karan nocking, khairat ce ta tashi danta bude kofar Tana bud’ewa ta zare ido domin ganin oganta Muktar, cikin mamaki ko magana ta kasa, rahma jinta shuru yasa taje itama, tace sannu shigo, shigowa yayi tare da kallon khairat yace Wajanki nazo, sannan ya karasa cikin falon, inda yagaida su Ummi, suka amsa cikin fara’a dan basu San ko Waye ba, yace nine ogan khairat, nazo in bata hakuri akan abunda ya faru ne, khairat kallon mamaki take mai, yace dan Allah Ina neman izinin magana da ita, ummi tace babu damuwa tashi khairat tayi yabi bayanta har zuwa falon ba’ki, zama yayi akan kujera sannan ya kalli khairat yace nazo in baki hakuri akan abunda ya faru, dazu sanda nazo Ina miki fad’a mum dina tazo office din duk taji abunda Nayi miki ranta ya baci Sosai dan Allah kiyi hakuri, tace babu komai sir, murmushi yayi tare da fad’in Banyi signing a takardan barinki aiki ba dan haka saiki dawo aikin ki, tace kayi hakuri sir bazan dawo aiki ba domin na riga Na yanke hukunci, yace baki hakura ba kenan? Tace koh d’aya na hakura, murmushi yayi tare da fad’in Indai kin hakura Toh ki koma aiki, tace sir am so sorry bazan iya komawa aiki ba, dan shuru yayi sannan yace koda na aureki? Da sauri ta kalleshi ya d’aga mata kai alaman eh dagaske nake, tace sir ….. Yace Nasan Kin taba ganina da hauwa dan shuru yayi can yace ko wace mace dole tayi zargin wani abu, hauwa ita naso na aura amma tunda tamin wannan abun na fasa danna gane bata da kamun kai, khairat gaba d’aya ta yarda da abunda ya fad’a mata tun daka ranan suka fara soyayya har manya suka shiga wanda za’a had’a bikinsu su uku, Zainab rahma, khairat, sai hidiman biki akeyi. Faruk ne zaune yana cin abinci cikin wani gidan cin abinci sai yaga Muktar shida wata suna magana yana ta bayansu ne shi yana ganinsu amma su basa ganinsa, yaji yana fad’in ma yarinyar kiyi hakuri hauwa zan auri yarinyar nan ne saboda wani dalili, hauwa tace miye dalilin,? Labarin abunda khairat tayi mai yayi yaci gaba da fad’in saina wulakanta ta na mayar da ita abun tausayi, Idan na rama abunda tamin saina saketa in shawo kan mum muyi aure, faruk cikin Tashin hankali ya fita daka wajan rasa abunyi yayi can ya dawo ya daukesu hoto shida yarinyar sannan ya fita, Muktar yazo wajan khairat suna zaune a falo harda su Ummi domin a kullum yazo sai ya shigo ya gaidasu Kafin su tashi suje falon ba’ki, faruk ne ya shigo ya kalli muktar yace asirinki yau zai taunu, munafuki Allah bazai baka Nasaran auran yayata ba, zarah ta tashi ta wanka Mai Mari tace karka manta kaiba kowa bane a gidan nan, harka sami bakin fad’ama Wanda zai zama siriki a nan gidan magana, yace zarah abunda zan fad’a yanzu saiya baku 
mamaki Labarin abunda ya faru ya basu tare da nuna musu hoto, zarah ta kalli muktar tace wannan fah, muktaryace itace da zan aura rabona da ganinta wajan wata biyu kenan, khairat amsan hotan tayi sannan ta kalli faruk tace Kai Waye? Mai yasa kke son batamin aure? Na ro’keka ka fita daka harkan mu, bazamu kara yarda dakai ba dan kaci amanan mu, faruk cikin kuka yace khairat Dan Allah ki yarda da abunda zan fad’a miki Wlh wannan mutumin cutanki zaiyi marinshi zarah ta karayi tare da fad’in bar nan, Amina ce taja hannun faruk sukai sama, zarah bama muktar hakuri sukayl’, yace babu komai, koda faruk da Amina suka haura Amina tace faruk na yarda da abunda ka fad’a Nasan gaskiya ka fad’a amma ina ro’kan ka karka kara magana akan komai zai faru, tunda basu yarda dakai ba,yace Nayi miki alkawari mum. 
Rana bata karya yau aka d’aura auren Zainab, khairat, rahma, daurin auren daya tara dubban mutane, Anata taya angwaye murna tare da fatan alkairi, faruk shima ya tayasu murna koda yaje yima muktar murna murmushi muktar yayi tare da fad’in daga yau zan fara azabtar da y’ar uwarka kuma babu abunda zai faru maci amana, faruk baice komai ba ya wuce cikin takaici tare da tausayin khairat, karfe biyar aka Kai ko wacce gidanta rahma Suma a kaduna zasu zauna, haka zainab, khairat gidan sirikarta aka kaita katon gida mum din muktar nada kirki Sosai ta tarbi y’an kawo amarya cikin mutunci da kulawa, kowa ya watse anbar amare suna jiran angwayensu, zainab Tana zaune saiga nata angwan yazo inda ya bukaci tayi alwala suyi sallah hakan ko sukayi sannan ya ciyar da ita da kaza da drinks nan suka shiga farantawa rai. Gefen rahma ma haka Mahmud yazo ya sameta cikin farin ciki ya cire mata gyalen dake fuskanta sakar mishi murmushi tayi yaja Hancinta tare da fad’in Alhmdlh Allah na godema daka nunamin wannan rana, murmushi tayi yajanyota jikinshi tare da fad’in muje muci abinci Nasan kina jin yunwa, falo suka fita har wajan dinning sukaci abinci suka koshi sannan suka dawo sukai sallah raka’a biyu daka nan kuma aka fad’a duniyar ma’aurata. Ta gefen khairat kam muktar bai shigo da wuri ba har bacci ya fara daukanta taji an budo kofar Wanda yasa tayi firgit ta tashi ganin muktar ne yasa ta dan rufe fuska da gyalenta, janyota yayi kasa tare da fad’in Banan ya kamata ki zauna ba can ne wajan kwananki ya nuna mata kujera, yace Kina tunanin zan iya zama dake a matsayin mata ne? Never ni muktar Mai zanyi dake na aureki ne dan in wulakanta ki kaman yanda kikamin, wani irin hawaye Mai zafl ya fara zubo mata, ashe gaskiyan faruk ne, daka mata tsawa muktar yayi yace tafi kiban waje, da sauri ta matsa wajan kujera ta kwanta shi kuma ya d’are gado, kuka khairat tai tayi cikin Tashin hankali yau itace ranan dako wace mace take buri amma ita gashi ranan tazo, amma yazo mata cikin kunci, ranan kasa bacci tayi ga muktar yana ta waya da y’an mata haka dai ta kwana tana kuka har gari ya Waye, Washe gari da safe mahaifiyar muktar ta had’a musu breakfast da kanta, suna ci muktar najan khairat da fira mum dinshi taji dad’in yanda taga yana mata, mum dinshi ta bashi ticket tace gashi yau karfe hudu jirginku zai d’aga zuwa kasar London Don zuwa honey moon, muktar yace mum Aida kin bari ba yanzu ba, mum din tace Nop yau zaku wuce, yace 0K 
amma ranshi baiso ba, haka kuwa akayi karfe hudu Nayi suka tafi, koda suka isa kasar Londo, da yake suna da gida a kasartunda ya kaita yabar gidan , hotel ya kama inda yake jiran zuwan hauwa gobe, mum dinshi ta kira a telephone din gidan khairat ta d’auka mum din tace kun sauka lafiya, tace lafiya mum, tace ina muktar? Tace ya dan fita amma Nasan yanzu zai dawo mum tace 0k, suna gama waya ta kira Layin muktar na kasan tace kana Ina yace mum Ina gida, tace muktar banson karya bayan tafiyanku Kanin khairat yazo ya ro‘keni akan dan Allah Kar in Bari ka cutar da ita ya fad’amin komai muktar dama har yanzu kana tare da hauwa, wlh Idan baka fita hanyarta ba saina saba maka mara tunani kuma Wlh duk inda kake ka koma Gida yanzu yanzu sannan ka kai matarka yawo taga gari, yace Toh mum tare da kashe wayan cikin bacin rai, gidan ya koma inda ya sami khairat a falo tayi kwalliya cikin riga da wando kallonta yayi cikin mamaki dama Tana da wannan suran haka mai kyau, ganin irin kallon da yake mata yasa ta tashi daka falon ta koma d’aki tare da kwanciya, dan tsaki yayi tare da kawar da tunanin da yakeyi, d’akinshi shima ya nufa ya kwanta. Washe gari hauwa tazo shida kanshi yaje airport ya d’auko ta, khairat ta fito dan taje kitchen ta dafa abunda zata ci taganshi shida hauwa hannunsu ri‘ke dana juna, wani irin kishi taji yana dibanta amma babu yanda ta iya, komawa d’aki tayi niyan yi, kiranta yayi da fad’in ke, tsayawa tayi yace zoki bamu abunda zamu ci yunwa mukeji, bata musa ba tayi kitchen ta had’a musu abinci ta dawo dinningtace gashi na gama, komawa d’aki tayi tana ta kuka ko abincin ma bata ciba, tana zaune sai gashi yazo yace ke tashi mu fita, yana fad’in haka ya fita riga da wando tasa saita d’aura boyfriend jacket akai tare da Dan karamin Gyale duk da haka saida suran jikinta ya bayyana, muktar kallo d’aya yayi mata ya kauda kai baya khairat ta shiga hauwa kuma gaba, wani super market sukaje, khairat ce ke tura basket din zuba kaya yayin da muktar da hauwa suke zaban abunda suke so, haka suka gama d’auka khairat kam babu abunda ya bari ta d’auka, tunda suka koma Gida ta shiga d’aki bata flto ba, kullum sai sun fita hauwa da muktar suyi ta soyayya a gaban khairat, mum dinshi inta kira taji suna tare ba karamin dad’i takejiba, yau wani shagon saida sarka suka nufa inda yasai ma hauwa sarkan diamond Mai shegen kyau da tsada, mai saida sarkan yace ba zaka saima wannan ba ita? Muktar yace no ba tare muke ba, tana jin ya fad’i haka ta fita da sauri Jim kad’an sai gasu Sun fito shida hauwa kiranshi akayi a waya ya dan saki hauwa yaje yana amsa wayan, wata mota ce ta rugo da gudu khairat tazo da gudu ta tureshi gefe motar ta bugeta sama tayi sannan ta fad’o kasa, cikin firgici da shock yake kallon khairat da sauri ya nufeta yana fad’in khairat ki tashi plz Khairat plz ki tashi ambulance ne yazo shida kanshi ya dauketa ya daurata akan gadon aka sata a mota dan zuwa asibiti, emergency akayi da ita ko numfashi batayi oxygen aka sa mata, muktar ya shiga cikin Tashin hankali Sosai tare dayin dana sanin abunda yayi mata saboda ta ceci nashi rayuwan tasa nata cikin hatsari kuka yake Sosai a haka hauwa tazo hspt din ganinshi haka yasa ta Fara fad’a Wai ya tafl ya barta sannan yazo nan yana kuka, ni Mlm ka tashi mu tafi ni Allah yasa ma ta mutu mayi aurenmu cikin kwanciyan hankali, marinta muktar yayi tare da fad’in baki da hankali baki da tunani hauwa ki tafl kibar nan saboda ke na wulakanta matata ki tafi banson in karayin wani abu da zan bata Mata rai, hauwa tace baka isa ba matar taka da kace baka Sonta lafiyan ka kuwa muktar, yace lafiya na kalau kuma matata daka yau zan fara nuna mata so da kauna, zaginshi hauwa ta farayi ta tara mutane 
Sosai tana ta dura Mai ashar muktar yayi dana sanin sanin hauwa a rayuwa, security din asibitin suka zo sukayi waje da ita, khairat sai wajan 5 na yamma ta farka tare dayin salati lokaci d’aya kuma tace muktar sai kuma ta saki kuka, domin a tunaninta motar ta bigeshi jin magananta yasa yazo da sauri ya ri’keta ganinshi a gabanta yasa ta rungumeshi tana kuka tace ashe bai bigeka ba Alhmdlh, kara rungume ta yayi yana kuka shima yace khairat ki yafe min abunda nayi miki Wlh Nayi nadama, inda motar ta bigeni na mutu a lokacin ban San mai zance ma Allah ba, dan Allah kiyimin afuwa badan niba na…. Toshe Mai baki tayi cikin kuka tace na yafe maka duniya da lahira, yace ngd ngd, Kwananta uku aka sallameta, suna zuwa Gida suka diba kayansu ya kama musu hotel inda sukaci amarcinsu a can yaji dad’in yanda ya sami matarshi a matsayin budurwa, soyayya yake nuna mata Sosai, kwanansu 8 suka wuce saudiya daka nan suka dawo gida, mum dinshi taji dad‘in yanda taga khairat tana wani walkiya ga muktar yana nan nan da ita Koba ta tambaya ba tasan komai yayi dai dai yanzu, kwanansu uku da dawowa suka je gidansu khairat inda sauran y’an uwanta mata suma sukazo tare da maza jansu, faruk ne yazo zai fita inda khairat ta kira sunanshi kallon mamaki su zarah suke mata bama muktar hannu yayi dan tun tuni ya gaisa dasu mazajan su rahma, khairat tace zarah dan Allah kuyi hakuri ku yafe ma faruk wlh yana sonmu shairin Aneesah ne yasa yajuya mana baya, nan ta basu Labarin akan abunda muktar ya fad’a Wanda faruk yaji, Sosai suka tausaya ma faruk tare da fad’in sun yafe Mai inda suka roki farida itama ta yafe Mai, tace komai ya wuce faruk yace yana son ya fad’i wani abu, sukace name, yace Ina son in dawo da matata inta yarda, zarah tace faruk amma ai saki uku kayi Mata, yace a’a saki d’aya Nayi Mata, farida tace Wlh ni tunda Yaban takardan bamma duba ba, nan muktar ya ciro kud’i yace ga sadaki ya biya, a ranan aka mayar musu da aure. 
‘BAYAN SHEKARA BIYU’ 
Abubuwa da dama sun faru harda haihuwan su khairat ta haifi y’an biyu Mata, Zainab kuma namiji, rahma ta haifl mace, an yanke ma Aneesa hukuncin kisa, magajiya kuma zaman gidan yari na shekara ishirin da aiki Mai tsanani, saleh shima Allah ya mishi rasuwa, faruk bai wani Ji mutuwar mahaifin nashi ba, sai dai yana mishi addu’an neman gafara wajan uban giji, mama ta kara tsufa Sosai hindu itama ta sami wani bazawari tayi aure su Ummi kam sunce sun gama aure har abada, Abubakar da faruk suke juya kasuwanci yanda suke samun riba Sosai arziki kam yanzu sai dai muce Alhmdlh, su Ummi kullum dasu mama maganansu shine y’ay’a mata rahma dan sunce basu ga ILLAR Y’AY’A MATA BA, sai dai alkhairinsu, k0 wacce Tana zaune ita da mijinta laflya ga tarin dukiya Abun dai sai san barka 
Toh nima a nan zan ajiye alkalamina ince ALHAMDULLILAH. 
Mu hadu cikin sabon littafinmu mai suna MUSAYAR ZUCIYA

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]