[Advertisements⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 9 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA
CHAPTER 9
Magajiya ce ta cinye abincin ita kam Aneesa sai Maltina tasha, shima tana gama sha ta Fara amai kaman zata fitar da hanjin cikinta, magajiya sai faman sannu take mata, ganin yanda tayi amai din Sosai gashi ta kasa cin komai yasa magajiya tace kota kira faruk ne? Kai ta girgiza alaman a’a tace bari sai munje mun tabbatar da ciki gareni sai inyi magana dashi, magajiya tace toh kodai zamu yanzu ne? Aneesa tace gobe da safe zamu ranan dai bacci rabi da rabi Aneesa tayi na farko ga daukin taga gari ya Waye taje asibiti na biyu jikinta baya mata dadi haka dai har gari Ya Waye suka nufi asibiti, koda tayi ma Dr bayani ya tambayeta taci wani abu? Tace a’a scan yayi mata saida ya gama yace madam congratulations kina da cikin wata d’aya da sati biyu, wani irin ihu ta saki na murna Dr yanda yaji tayi ihun saita bashi dariya, DrYa bata magani tare da fada mata saita dinga kula, godiya suka mai sannan suka wuce, suna tafiya Aneesa na fadin magajiya yau nafi kowa murna nice da ciki Kai Alhmdlh wannan cikin nawa shine jarina shine silan samun arzikin mu, dariya magajiya tayi tare da fadin wannan haka yake, suna tafiya taga mai waina saida ta tsaya suka siya ita sai magajiya tace baza taci ba abincin hotel za taci Alh Ibrahim ne zaune da iyalan gidanshi suna cin breakfast, Bayan an kammala ya kalli ummi yace ya kamata ku Fara siyayya,ummi tace hakane naji dama bakai magana ba, yace anjima inna fita office zan turo faruk da kudi Ya kawo sai kusan abunda zaku fara siya sannan in zaku kuje da Yaran Su zabi abunda suke so, Amina tace ni kam wani siyayya za’ayi tunda naga ita zainab a nan zasu zauna sai dai ita aysha din, Abba yace hakane amma ai a canza ma zainab din kayan d’akinta koh? Amina ta tabe baki tare daci gaba da cin abincin ta, tashi Alh Ibrahim yayi suka fita shida Abubakar da faruk dan tafiya office, koda su ka fita faruk yaso ya zarce wajan Aneesa amma babu dama haka ya hakura dole akan in sun tashi daka office, Bayan sunje office baiyi k0 awa biyu ba Alh Ibrahim ya bashi check yace yaje bank ya ciro saiya kaima ummi, hakan ko yayi saida ya fara zuwa bank sannan ya wuce hotel din daya sauke su magajiya, koda yaje magajiya ce ta bude mishi kofa, a kwance ya sami gimbiyar tana wani kashe ido irin nasu Na yan duniya, kallonta yayi yace baki da lafiya ne? Mai makon ta bashi amsa sai ta kanne mai ido d’aya lokaci daya jikinshi ya fara amsawa amma saiya dake tunda magajiya na wajan, yace Aneesa kiyi magana mana maike damunki? Kuka ta saki ta Fara fadin yanzu faruk duk da nayi aure Allah ya shirya ni sai Ayi ta bina da shairi, ban taba tunanin 
mahaifinka zai min haka ba, ldan da nayi rayuwa mai muni yanzu ai na shiryu tunda na daina, amma saida yasa ka sakeni, gashi yanzu Ina da ciki dole zubarwa zanyi tun ……. Yace ciki Aneesa kina nufin kina da ciki ciki na? Kai ta d’aga tare da fadin hakane amma zan zubar dashi Dan zan koma rayuwa ta tabaya tunda mahaifinka baya bukata ta Kaga kam bazai so had’a zuri ‘a dani ba, faruk yace haba Aneesa har gobe Ina sonki sannan karki kuskura ki zubar min da ciki kiyi hakuri kiban lokaci kad’an komai zai daidaita, sannan zan siya muku Gida koda karami ne Kafin musan Abun yi, cikin kukanta na makirci tace a’a ka barshi kawai zamu nema da kanmu, yace Aneesa plz kibar wannan maganan zuwa gobe ko jibi insha Allah zamu sami Gida koda haya ne Kafin Abba ya sauko, tace toh shikenan, kudi Ya dauka ya kara basu tare da fadin zai kara biyan kudin d’akin sannan yace mata in zai dawo mai zai kawo mata, tace ice cream yace shi kawai? tace eh sallama ya musu ya fita saida Ya biya kudin d‘aki na sati daya sannan ya nufi Gida inda yakai ma ummi kudin ya koma office cike da farin ciki zai zama uba shima. 
gyara Sosai duk inda suka gifta sai kaji kamshi domin wata mata hindu ta dauko musu daka borno take musu gyaran jiki ciki da waje, zainab na kwance wayanta yayi kara dauka tayi dan tasan mai kiran domin ringing dinshi daban ta ware mai, dauka tayi tare da sawa a kunne tayi shuru, cikin muryansa mai dadinji yace baby yakike? Bata amsa ba sai dariya da take kunshewa, yace hello, uhm tace murmushi yayi tare da fadin yau sarautan ya tashi kenan? Murmushi tayi tare da fadin ka tabajin dan Talaka da sarauta ai sarauta sai wanda ya gada, yace aike a cikin zuciya ta kinfi mai sarauta mulki ni bawanki ne Kece sarauniya ta, zainab na rasa mai yasa nake sonki da yawa, da zan iya nuna miki irin son da nake miki da Kinji tausayi na koda sau daya kince min I love you yazeed, dariya tayi Sosai yace eh mana baki taba cemin I love you ba fah, tace Kai haba? Yace dagaske mana, dariya tayi sannan tace uhm, yace plz say it, tace a’a yace shikenan nan da kwana biyar zan saka ki kice min ai, uhm tace sannan tace taya zan ce maka? Yace sanda akace an daura min ke kin zama matata a ranan zan saka ki kice, bama sai nace kice ba da kanki zaki cemin, tace ni kam bazan ceba, dariya yayi yace ni kam Nayi alkawari sai kin fad’a min haka, canza maganan yayi da 
fadin an dai hanani ganin matata koh ance Kar in 
kara zuwa sai ranan da aka kawo ki, Wai miye sirrin Abun ne? Nifa a matse nake ina bukatarganin ki, tace ba yanzu ba dole hakurin za kayi, yace Anya zan iya kuwa? Murmushi tayi tare da fadin saura kwana nawa Ya rage ka ganni in kayi hakuri kaman yanzu ne fah, yace hakane, tare da fadin anjima zan aiko a kawo miki sa’ko sai Ayi min Lalle da kitso mai kyau, kashe wayan tayi tana dariya, saida tayi mai isarta sannan ta fita zuwa d’akin khairat Dan daka yau can zata koma kwana dan za’a kawo kayan d’aki yau, cikin d’akin khairat ta sami yan uwan nata suna ta tattaunawa akan yanda bikin zai kasance, sun dade suna ta tsara yanda za suyi hidiman bikin, wayan zainab yayi kara dauka tayi dan tasan ko Waye, yace kisa aje waje a anso miki sa’kon Kar kije da kanki Dan ban yarda a ganki ba, dariya tayi tare da fadin Toh, kashe wayan tayi sannan ta kalli khairat tace danje waje ki amso min sa’ko, khairat ta amsa da Toh sannan ta fita, bata dade ba sai gata ta dawo da akwati trolley ajiye ma zainab din tayi, Bayan ta ajiye zainab ta bude kudi ne masu yawa da d’an kunne da sarka Na zinari sai kaya Kala biyu masu tsadan gaske duka dinkunan gown ne kayan kana gani kasan na event ne, wanda bridal zata saka, kiranta yayi ta dauka tare da barin d’akin dan yan uwan nata suna ta magana akan haduwan kayan, Bayan ta fita suna magana yace kayan shi zata saka in za suyi mothers day 
dayan kuma ranan bridal shower, yace plz tasa 
kayan Dan yasan may be anyi mata Wanda zata saka a gidansu, mum dinshi ce ta bada a kawo mata kayan, dan tace baza a sasu a akwati ba wannan kyautar tace ta musamman, zainab tace Allah sarki mum dina plz ka tayani godiya Sosai a wajanta, yace zan fad’a mata sunyi d’an fira kadan sannan sukai sallama, koda ummi taga kayan tace su zata saka da event, ummi tace kudin naira million uku ne tace sai Asa a account domin wata rana zaiyi amfani hakan k0 akayi. 
An fara hidiman biki an kawo akwati ko wacce guda 6, an cika su da kaya makil, yau za Ayi mothers day, amare anyi musu kwalliya na Kece raini Kalan kayan da yazeed Ya kawo ma zainab shi jamil ya kaima aysha Dan haka anko sukayi sai dai colour din daya banbanta, mother day din ya hadu an kashe naira Alh Ibrahim yayi bazata domin ya bada kudi Sosai a bikin, Washe gari kuma akai bridal shower, shi wannan kawayen amare ne kawai sukayi, Anci ansha taro ya watse, yau Friday aka daura auren jamil da aysha sai yazeed da zainab akan sadaki naira dubu d’ari d’ari, Anci taron biki wajan 7 aka tafi da aysha malali amma 
ba’a nan zata zauna ba gidan mijinta na katsina inda iyayenshi ke zaune amma sukan zo jefi jefi kaduna, za su danci amarci ne anan Kafin su tafi can, yazeed kam abokananshi ne suka kawo shi inda suka musu yar nasiha sannan suka fita, ya rage daka zainab sai yazeed …..
Yazeed matsowa yayi kusa da gimbiyar tashi da fuskanta ke rufe da gyale a hankali Ya fara kokarin cire mata gyalen tunda ya fara cire mata gyalen gabanta keta fad’i dan tasan yau mai kwatanta sai Allah, gashi kuma cikin gidansu suke, ido ta lumshe tare dayin takaicin amincewan mijin nata akan zai zauna a gidan nasu, tana cikin tunanin taji ya matseta cikin jikinshi bakajin karan komai saina bugun zuciyarta domin a tsorace take, magananshi taji cikin kunnenta yace muje muyi alwala muyi sallah, bata musa ba ta tashi shiya Fara shiga toilet yayi sannan itama ta shiga, sallah raka ‘a biyu sukayi sannan ya daura hannu akanta ya fara addu’a, bayan ya gama ne ya kwanta ta bayanta tare da janyota jikinshi ya matseta Sosai, kissing din wuyanta ya farayi tare da wasa da kitson kanta yana dan ja, bata an kara ba taji hannunshi akan kirjinta da sauri ta Fara kokarin tashi amma ta kasa dan ya ri’keta da kyau, a hankali tace I love you, murmushi yayi tace plz nace maka abunda kake so amma dan Allah Kar kamin komai ina jin tsoro, a hankali yace babu abunda zan miki sai mun tafi honeymoon yanda zanji ihun babyna ni d’aya hannu tasa a fuska ta rufe alaman kunya shi kam babu abunda yake in banda dariya. 
lta kam aysha Bayan an kaita gidan mijinta dake malali, bai shigo ba sai wajan 9 shida abokananshi shima, sunyi raha daka karshe suka musu nasiha suma, sunyi sallah raka’a biyu dan nuna godiya ga uban giji, da yawa maza kan manta wannan sallah na nuna godiya tare da addu‘an neman tsari daka shaidan Kafin a sadu da mace, matasa yanzu a matse suke sau da yawa wasu na auren ne a muguwar bu’kace ya kamata dukyanda namiji yakai da bukata ya daure yayi sallah na nuna farin ciki da wannan rana sannan Ayi addu’an neman tsari daka shaidan ldan shi namiji ya manta ke amarya saiki tuna mishi, bayan sun gama komai jamil ya fara nuna ma aysha irin son da yake mata babu komai da kakeji sai karan AC dana bugun zuciyar aysha Dan a tsorace take, wani irin ihu ta saki mai karfi wanda yasa na tsorata nabar dakin da gudu ban koma ba saida asuba inda naga aysha nata kuka jamil nata rarrashinta amma ina kukanta takeyi kaman bama tajin abunda yake ce mata, ganin kukan bana karewa bane yasa ya dauketa cak yai bayi da ita shi ya mata wanka sannan ya kara taimaka mata tayi wankan tsarki tare dayin alwala dan sallah asuba, Bayan ta gama ya fito da ita tare da dauko mata riga da hijab tasa ya shimfida mata dadduma, Shima toilet din ya koma dan ya tsarkakejikinsa, bai dade ba Ya fito 
yasa riga ya kalleta tare da fadin swty na tafi masallaci, a zaune tayi sallah tana gamawa bacci ya dauketa a nan, koda ya dawo yaga tana bacci murmushi yayi tare da kara Sonta domin ya sami matarshi a budurwa, canza bed sheets din yayi sannan ya kamata ya kaita kan gadon d’akin ya kwantar da ita shima kwanciya yayi kusa da ita tare da matsota jikinsa. 
Washe gari da safe kowa nakan dinning ciki harda amarya da ango, sai faman ji da yazeed ake, ana ta tura mai abinci gabanshi, ita kam zainab kunya takeji dan tana ganin kaman kowa yana zargin sunyi wani abu ne, ummi ce ta kira sunanta da fadin zainab ci abincin mana, da sauri ta Fara ci harta gama, yazeed ya kalli Abba yace Abba mum dina tace ya kamata a kawo mata amarya tayi mata sati daya sannan za mubar kasar na sati biyu zamu tafi Dubai, alh Ibrahim yace babu damuwa Allah ya taimaka ya kuma tsare, yaushe zaku tafi? Yazeed yace yau dan tafiyan jibi ne, Abba yace shikenan, ya kalli zainab yace zainab Ina son ki sani da mum din yazeed da ummi duk d’aya suke a Wajanki sannan ki kasance mai bin umarnin mijinki a duk inda kike, tace toh Abba ngd, tashi 
Alh Ibrahim yayi dasu Abubakar da faruk dan tafiya office, Suma su zainab d’aki suka koma suna shiga yazeed ya janyota jikinshi tare da kara matseta yana shakar kamshin jikinta,jin nocking din da sukayi yasa ya saketa tare da bude kofar zarah ce da khairat, khairat tace baku Fara had’a kayan ba Bari mu had’a muku, murmushi yazeed yayi nan suka fara had’a kayan suna yi suna fira har suka gama, saida yamma suka tafi gidan su yazeed, inda ta sami tarba Sosai wajan mum dinshi mai kirki gidan su yazeed katoto ne kana ganin gidan kasan sun tara Abun duniya, mum din yazeed nata kula da zainab har ranan wuce warsu Dubai yayi suka d’aga,. 
Sun sauka a Dubai a wani babban hotel, zainab taji dadin kasar Sosai, koda suka sauka a masaukinsu wanka zainab ta fad’a tayi Bayan ta fito yazeed ya manneta a jikinsa yace da kin bari ai kinyi mai dalili amma tunda kinyi wankan yanzu zaki sake wani ido ta rufe alaman kunya, shi kam dariya yayi tare da sakinta ya shiga toilet dan shima yayi wanka, Bayan yayi wanka ya Tarar da hartasa riga, shima 
kayan yasa tare da fadin muje muci abinci, tashi 
tayi suka fita a restaurant din hotel din suka ci sannan suka koma ciki, saida sukai sallah isha’i sannan suka kwanta janyota yayi jikinsa tare da juyo da ita ta gefenshi idonta a kulle bakinshi yasa cikin nata ya fara kissing dinta tun bata mayar mishi da martani harta Fara, duk da tana jin tsoro ya dade yana kissing dinta Kafin ya fara shafata tako Ina saida ya gigitar da ita Ya fitar da ita daka hayyacinta Kafin yayi mai gaba dayan tun tana kuka tare da kokarin tureshi harta kasa motsi, ranan dai su zainab an zama babban mace wato cikakkiyar mace, yanda yazeed yayi mata yayi mugun tausaya mata Sosai, ko motsi ta kasa dan haka ya sata cikin ruwan zafi sai a sannan ta d’anji dama dama, yazeed basa fita ko Ina yana zaune yanajinyar matarshi. 
Faruk ya Samar masu Aneesa Gida ya saka musu kaya amma ba wasu masu yawa ba,domin gidan ma ciki da falo ne ba wani babba bane, magajiya ce zaune tana wanke wanke tana faman banka tsaki Aneesa tace Wai miye ne magajiya haka? Magajiya tace yanzu dan Allah kalla yanda muka dawo Wai mu da kanmu muke ma kanmu komai amma gidan mijinki muna zaune ake mana Wlh na gaji da 
wannan wanke wanken da goge goge, aneesa tsaki ta saki tare da fadin kiyi hakuri lokaci kad’an ya rage zamu koma 
Alh Ibrahim yana ta shirye shiryen yima faruk aure ba tare da sanin kowa ba, wata yar abokinshi Wanda suka rasu yar tana zaune wajan yan uwan babanta ita Alh Ibrahim yake son aura ma faruk …… Hmmm muje zuwa 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]