[Advertisements⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 8 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA
CHAPTER 8
Washe gari da safe su zarah suka had’a breakfast Bayan sun kammala suka jera akan dinning wajan karfe 8 duka iyalan gidan suka hallara akan 
dinning din, kaman dai kullum ummi Alh Ibrahim ta Fara saka mawa, sannan tasa ma mama sauran kuma suka saka nasu, kowa abinci yake ci cikin kwanciyan hankali, Bayan sun gama Alh Ibrahim ya tafi office shida Abubakar da faruk, su zarah Suma fita sukayi Bayan sunce ma ummi zasu kasuwa, kai tsaye maraban jos sukace driver ya kaisu, Bayan sun tafi driver ya kaisu suka ce ya faka a gefen wani layi inda suka ga maza da mata a kofarwani Gida, daka ganin gidan kasan na karuwai ne, dan haka fita sukayi wani dake zaune a gefe yana zugar sigari wajanshi suka nufa, zainab tace sannu kallonta yayi tun daka sama har kasa sannan yace Kai kina da kyau, d’an bata fuska tayi sannan ta Ciro hotan yasmin tace mishi dan Allah ko ka taba ganin wannan a nan? Kallon hotan yayi kaman zaiyi magana sai yayi shuru tare da girgiza kai alaman a’a, tafiya sukai gaba suka ga wata yarinya taci uban makeup ga attachment da kanta yasha, zainab ce ta isa gareta tare da fadin sannu, bata amsa ba sai kallon tara saura kwata da tayi ma zainab din tare da fadin miye? Zainab ta nuna mata hotan tare da fadin dan Allah kin Santa? Kallon hotan tayi tare da fadin ban taba ganin mai kama da ita bama, haka sukai ta nunama mutane 
hotan amma babu wanda yace musu ya Santa haka suka dawo gida cikin takaici, Bayan sun isa Gida zainab tace gobe Ya kamata mu kara komawa zarah tace hakane amma nifa sai naga kaman basa son fad’a mana ne amma taya zasu ce basu Santa ba Bayan a nan take da, khairat tace hakane Amma ai mu bamu da tabbacin dagaske abunda mukaji, zainab tace koma dai miye gobe mu koma. 
Washe gari kaman yanda sukai alkawarin komawa hakan suka koma, yau dinma yawo sukai tayi amma shuru kakeji babu Labarin yasmin, zarah tace mubar wannan abun kuzo kawai mu koma, zainab tace no bazamu koma yanzu ba koma miye akwai wani abu suna cikin haka saiga mutumin da suka fara tambaya jiya matsowa kusa da zainab yayi tare da fadin nawa zaku biya? Zainab tace mene? Yace eh nawa zaku biya domin in zaku shekara kuna zagaye nan babu Mai fad’a muku, zainab ta bude jakarta ta Ciro duba biyar ta bashi yace yayi kadan lndai kunji na fad’a muku wani abu a kanta sai kun ban dubu d’ari, kallon juna sukai su duka zarah tace haba mlm Ina laifi dubu 
hamsin? D’an shuru yayi sannan yace ok ku bani 
zarah ce ta budejaka ta kirgo dubu arba’in da biyar Suka had’a dana zainab suka bashi kusa da motarsu sukaje, yace wannan sunanta Aneesa sannan tayi aure ta auri wani yaron mai kudi suna can ita da magajiya binta, wacce sukai Karya suka ce itace mamanta, wannan kenan, kallon juna sukai tare da fadin ko zaka iya bin mu? Yace Kai gaskiya ba zani ba, aysha tace zamu kara maka 10k dan Allah ka bimu taimako za kayi, dakyar ya yarda Bayan ya amshi 10k din ya shiga motar ya zauna gidan gaba suka koma. 
Gaba daya family Alh Ibrahim suna zaune suna cin abincin dare, aka danna bell, khairat ce ta tashi ta nufi kofar budewa tayi mutumin ya shigo cikin gidan kowa dake kan dinning idonshi na kanshi domin basu San shiba, ita kam yasmin da binta da faruk tsuman tsaye sukai, gaida Alh Ibrahim mutumin yayi sannan ya kalli binta yace sannu magajiya, yasmin da take ta zufa, ya kalleta yace sannu Aneesa, an bar maraba an dawo anguwan rimi anzo ana cin daula, Alh Ibrahim yace Waye Kai? Yace Alh nazo ne in fad’a maka gaskiya akan wannan matar d’an naka, ba sunanta yasmin ba sunanta Aneesa sannan ri‘kakkiyan karuwa ce, 
sannan wannan matar ba mamanta bace magajiyan karuwai ce, Alh Ibrahim yace mai kake fad’a, yace Alh in baka yarda ba ga d’anka nan ka tambayeshi zai fad’a maka gaskiya, Alh Ibrahim ya kalli faruk wanda zufa ta wanke mai jiki, yace faruk maganan nan gaskiya ne? Yace Abba Karya ne ni ban taba ganinsa bama, mutumin yayi dariya yasmin itama ta Fara fadin Karya yake Wlh ni ban sanshi bama ban taba ganinsa ba, hoto ya ciro Ya mi’ka ma Alh Ibrahim yace gashi Alh kalla ka gani, bude hotan yayi yana kallo Aneesa ce ga tanan tasa kaya kaman tsirara nononta a waje daka gani rawa take ana mata liki, ci gaba yayi da kallon hotan harda Wanda akwai faruk din idon Alh Ibrahim ya kad’a yayi ja, d’agowa yayi ya Kalli faruk cikin bacin rai ya nufeshi ji kake tas tas, ya sakar mishi Mari har biyu, mutumin na ganin haka yabar gidan, kowa dake falon ya tsorata da Marin da yayi ma faruk abunda bai taba yiba, cikin fad’a yace ban taba tunanin zaka min haka ba, na yarda dakai na baka kulawa Wanda bana bama sauran yan uwanka domin Ina tunanin kaine zaka gajeni, ko Bayan raina Ina tunanin kaine zaka ri’ke gidan nan ashe tunani na ba haka bane, ka rasa wacce zaka auro sai karuwa amma ba lafinka bane laifi nane, inaso kaida matarka ku tattara Kubar min Gida nan da 30min ban bukatar in sake ganinka a rayuwa 
yana fadin haka Ya haura sama …… 
Gaba d’aya kowa dake falon shuru yayi, su zarah da sauri sukabi mahaifinsu domin basu San wannan hukuncin zai yanke akan faruk ba, duk da yayi laifi babba amma basu taba kawo wa zai koreshi ba, alh Ibrahim yana zaune a d’aki ya zabga tagumi kallo daya zaka masa kasan yana cikin fushi Sosai su zarah ne suka karaso koda suka isa d’akin kasa magana sukai sai aysha ce tayi karfin halin fad’in Abba, bai d’ago ya kalleta ba amma yana jinta bata damu da hakan ba dan tasan dole yana jinta, tace kayi hakuri Abba Ina faruk zashi shifa d’anka ne, yanzu Idan yabar gidan nan yaje ya fad’a cikin wani hali Abba ba zaka ji dad’i ba 
dan …… Ya d’aga mata hannu alaman ya isa haka, zainab tace dan Allah Abba kayi hakuri cikin fad’a yace ku fita kuban waje bazan zauna da wannan fasikan matar tashi ba maz ……. Bai ‘karasa ba suka ji muryan amina tana fadin ya saketa yanzu yace tabar gidan, da sauri ya kalli Amina d’aga mishi Kai tayi alaman eh ya saketa, shuru yayi can yace Ina faruk din? Kafin ta bashi amsa saiga faruk din nan ya shigo cikin kuka tare da dur’kusawa a gaban Abba yana mai bashi hakuri tare da ro’kanshi akan ya yafe mishi bazai kara ba ya tuba, ganin irin kukan da faruk yake ga magiyan dasu zarah kemai yasa yaji zuciyarshi ta sauko amma da yayi mugun fushi da d’an nasa Wanda yake matukarso, d’ago shi yayi tare da fadin na yafe maka amma duk 
ranan da naji koda wasa wani abu ya had’aka da wannan yarinyar sai nayi mugun Saba maka,jin abban nasu Ya sauko yasa su zainab suka nufi d’akin Aneesa da binta inda suka samesu suna had’a kaya, zainab tace inaso in baki shawara daga yanzu sai ki koyi hankali duk abunda kayi shi badon Allah ba Toh ba zaka taba ganin albarkan Abun ba, kin auri faruk Nasan saboda kudin Abba dan Nasan ba wani sonshi kike ba, amma Allah ba azzalumin kowa bane sai gashi ya tona miki asiri cikin ‘kankanin lokaci, dan haka maza a tattara zarah ta kalli magajiya dake had’a kaya tace toh magajiya sai a koma gidan jiya suna fadin haka suka fita suna dariya, aneesa Bayan fitan su ta kalli binta tace sunyi kuskure saki d’aya faruk yayi min amma kota wani hali sai ya dawo dani sannan ldan na dawo saina tarwatsa wannan family din sai Nayi abunda zanyi dan in mallaki komai na gidan nan inko ban aikata hakan bah Toh ba sunana Aneesa ba, magajiya tace toh ni yanzu Ina zamu dosa? Aneesa tace magajiya dan Allah kibar Yimin wannan tambayar kawai ki dauki akwati mu tafi 
duk inda zamu in mun fita zamu tattauna. 
Bayan kowa Ya nufi d’akinshi faruk ya silale yabar gidan inda ya tafi neman Ina Aneesa suka nufa tafiya yake a hanya can ya hangosu a gefen titi daka gani sun rasa mafita ne suka tsaya a wajan, magajiya tace Kai nifa Wlh na gaji tun dazu sai yawo muke, Aneesa shuru tayi kanta na faman juya mata, faruk ne ya faka matarshi daidai inda suke, Aneesa na ganinsa ta saki kuka, cikin damuwa ya fito yana bata hakuri, tace dan Allah ka kyaleni inje in mutu ka rabu dani, hakuri yaita bata yace su shiga yaje ya kaisu inda zasu kwanta Kafin gobe saiya kama musu Gida tunda wancan gidan an siyar, Aneesa tace babu inda zan bika, magajiya ta zungureta, amma Aneesa tace babu inda zata dakyarta yarda suka shiga motar, hotel yaje ya kama musu tare da basu kudi ko zasu bukaci abu, sallama ya musu akan gobe zai dawo, Bayan fitanshi magajiya tace Kai Aneesa da kinso ki mana tsiya zaki sa mu kwana a titi, Aneesa tace ai tunda yazo bazai Bari mu kwana a titi ba wannan abun da kika ga Nayi duk cikin plan dina ne, dariya magajiya tayi tare da fadin mai kike shirin kullawa yanzu? Aneesa tace karki damu magajiya koma miye zaki gani kawai kisa min ido, saina nuna musu babu wanda ya isa ya d’aga min yatsa dariya magajiya ta saki tare da fadawa kan lafiyayyan gadon d’akin tace wow ji gado kaman ina cikin gidan da aka koromu,tsaki ta saki ni Wlh Ina 
takaicin barin mu gidan nan, Aneesa tace zamu koma bada dadewa ba, wayan dake manne ajikin d’akin Aneesa ta kira tace a kawo musu abinci Bayan ta fadi abunda take so, saida yayi wajan 40min sannan aka kawo, ana ajiyewa magajiya ta Fara ci, ita kam Aneesa warin abincin taji Ya bugar mata hanci da gudu tayi toilet ta Fara kwarara amai, Bayan ta fito magajiya tace aneesa amai? Kodai ciki gareki? Aneesa tace abincin ne ya sani Tashin zuciya magajiya ta saki wata Uwar guda tace Wlh ciki ne gareki gobe da safe dole muje asibiti a gwadaki, Aneesa tace inko ciki ne shine zai ban dama aikata Abun da nayi niya cikin sauki shafa cikin tayi tana murmushi tare da sa’ka abubuwa da dama cikin ranta ….. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]