[Advertisements⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 7 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA
CHAPTER 7
Alh Ibrahim yayi gyaran murya sannan yace naji maganarku karku manta k0 ku su Waye, ku mata ne ba zaman office bane ya dace daku zaman Gida shi yafi dacewa daku dan haka kubar maza suyi aiki, faruk yace Abba Idan ka basu dama Suma babu abunda ba zasu iya ba, amma zarah inaso kuyi hakuri Nima da kaina kaninku duk wani abu zanyi karku damu, shuru sukai su duka,zainab ce ta tashi tabar wajan zarah da khairat suka bi bayanta, aysha na kokarin tashi Alh Ibrahim ya kira sunanta da Aysha amsawa tayi da na’am yace gobe kina da ba’ko zaizo da yamma, tace toh tare da barin wajan, koda ta shiga d’aki taga yan uwan nata sai faman zurga zurga suke alaman miye mafita, zainab ta kalli aysha tace wannan shawaran batai aiki ba dama nace har abada Abba bazai taba bamu muhimmanci, inda yasan haka zai ajiye mu mai yasa ya barmu mukai karatu? Daya barmu cikin jahilci ta yanda za muji dadin zama matan Gida masu bauta, zarah ta dafa zainab tace kiyi hakuri zamu nemi wata hanyar, zainab tace zarah bana tunanin komai za muyi zaisa Abba ya dauke mu akan Muma y’ay’a ne ba ….. Shigowan yasmin d’akin yasa sukai shuru dan murmushi tayi tare da kallon zainab tace zainab zaki Raka ni hspt gobe, zainab tace OK Allah ya kaimu, ta amsa da Ameen tare da fita, khairat tace mai za tayi a hspt? 
Zainab tace taya zamu sani, canza maganan sukai inda aysha take fad’a musu Abba yace gobe tana da ba’ko, tsokananta sukai tayi tare da fadin an kusa zama matar aure tashi tayi tabar d’akin ta wuce nata, dariya suka bita dashi, sannan ko wacce itama tayi dakinta. 
Washe gari da safe wajan karfe 9 komai ya kammala akan dinning na breakfast, gaba daya iyalan gidan sun hallara, domin cin abincin, kowa abinci yake ci ba tare dayin magana ba, wayan Alh Ibrahim aka kira ya dauka da hello, ban San mai aka fad’a mishi ba Ya tashi rai a bace ya kalli amina yace lna saleh? Tace baya nan ko ka manta ne? Yace ki fada mishi inya dawo Karya sauka a gida na inko ya sauka zansa a rufeshi da Farko ma dai koda ban sa an kamashi ba police nemanshi suke, amina cikin damuwa da Tashin hankali tace mai yayi? Alh Ibrahim cikin fad’a yace sata yayi musu a office na kudi wani ma’aikacinmu ya ganshi, sannan yama wata yarinya fyade, kowa dake wajan salati ya rafka, ita kam Amina kuka takeyi tare da fadin shairi aka ma saleh, Alh Ibrahim baibi ko ta kanta ba Ya fita rai bace ganin haka faruk d’a 
Abubakar suka bishi, d’aki amina tayi tana shiga ta 
doka ma saleh kira bugu biyu ya dauka tare da fadin my kanwa ya akayi cikin fad’a take cewa Wai mai yasa kai ba Zaka taba canza hali bane tur da halinka Wlh, yace ke miye ne Wai abunda mijinta ya fad’a ta gaya mai tare da fadin yace karka kara shigo mai Gida, saleh cikin fushi yace sai me gidanshi din banza kashe wayan yayi cikin bacin rai, Amina shuru tayi tana tunani ya kamata su hadu da saleh gaskiya amma dole in bari ya d’an huce, 
Zainab da yasmin sun fita zuwa asibiti driver ya kaisu, koda suka je yasmin ita d’aya ta shiga, tayi wajan 40min sannan ta fito tace suje, Bayan ta fito suka hadu da wani yana ta fadin Aneesa Aneesa, yasmin ta kalli zainab tace lah nayi mantuwa Ina zuwa, ciki ta koma da sauri, labewa tayi ganin mutumin dake ta kiranta da Aneesa  a gabanta zare ido tayi, yace wow kin kara kyau yau nazo garin gashi na ganki muje inda na sauka mana, cikin tsiwa tace dakata muje Ina? Bari kaji in fad’a maka ni yanzu matar aure ce, waigawan da zatayi taga zainab a bayanta ido ta bude alaman tsoro mutumin na ganin haka Ya wuce, zainab tayi 
murmushi tare da fadin faruk ne yake ta kira yace ya kira wayanki ba’a dauka ba gashi yana kan layi, amsan wayan tayi da sauri magana ta farayi tana kallon zainab amma daka ganin yanda zainab keyi bata ji komai ba wannan yasa hankalin yasmin ya d’an kwanta, koda suka koma Gida d’akin binta yasmin tayi inda ta sameta tana gyaran kumba, yasmin tace binta yau naga Ak, binta tace a ina? Tace a hspt yana ta kirana da Aneesa Labarin abunda Ya faru ta bata, binta tace zainab din kin tabbata bata jiba? Yasmin tace eh gaskiya dakyar in taji Kai bata majiba, binta tace Kai amma wannan ko d’an iska ya kamata ki fad’a ma faruk, yasmin tace yana dawowa kuwa. 
Koda zainab taje d’aki ta Sami zarah da khairat suna taya aysha kwalliya bata ce musu komai ba ta Sami waje ta zauna, zarah tace Yadai zainab kikai shuru lafiya kuwa? Tace zarah Anya yasmin babu wani Abun da suke boyewa kuwa? Zarah tace name fah? Labarin abunda Ya faru ta basu, khairat tace kina nufin yasmin tana da wani suna, sannan kuma tana bin maza da? Zainab tace toh nidai abunda naji kenan, zarah tace ldan kika ga 
mutumin zaki gane shi? Zainab tace eh, zarah tace 
shikenan koma miye zamu gano bada dadewa ba yanzu abunda ya rage shine ba’kon aysha yazo muga ko zasu daidaita, suna cikin haka ummi ta shigo tace toh khairat maza jeki rakata falon baki ba’kon yazo, tsokananta suka farayi tashi tayi wanda tayi kwalliya cikin leshi dinkin riga da skirt kayan Ya amsheta ta yafa Gayle ba karamin kyau tayi ba, aysha Fara ce Sosai gata tana da tsawo ga idonta Manya, fita sukayi ita da khairat har falon baki aysha na dauke da turen juice da snack khairat kuma tana dauke da cooler a tray, tunda suka shigo idonshi nakan aysha, yana dan murmushi khairat tace siriki Barka da zuwa d’an murmushi yayi tare da fadin yauwa kanwata, khairat fita tayi dan ta basu waje tace Ina zuwa, tana fita yayi gyaran murya yace aysha d’agowa tayi suka had’a ido wani irin murmushi yake sakar mata gaba daya sun kasa dauke idon nasu akan na juna, aysha tana tunanin irin haduwanshi domin kallo daya zaka mishi ka gane cewa namiji ne iya namiji, su zarah kam da khairat suna window sun labe suna kallonsu sai dariya suke ta musu tare dajin dadi dan ko ba’a tambaya ba suna son juna dan irin kallon da suke ma juna, aysha ce ta Fara yin ‘kasa da Kai, murmushi yayi tare da fadin sunana jamil sannan ni d’an kasuwa ne yau Ina wancan ‘kasa gobe Ina wancan ‘kasa ban cika zama ba, na taba ganinki a wani super market 
keda wata kaman mum dinki ce, aysha cikin ranta tace tasan Amina yake magana dan in zata super market suna yawan zuwa tare, Katse mata tunani yayi da fadin tunda na ganki Allah yasa min sonki, toh sai nabi yanda addini yace na turo magaba na akan su nema min izini in kin amince mun fahimci juna sai Ayi aure, rufe fuska tayi alaman jin kunya, dariya yayi, tashi tayi ta zuba mai juice tare da kokarin bude cooler yace Kar kisa min komai Alhmdlh, tace toh ga juice din bashi tayi garin amsa hannunsa ya d’an hade wani irin shock taji, da sauri tayi baya, shiko murmushi yayi tare da fadin an amince dani,? Kai ta d’aga tare da rufe fuska Alhmdlh Ya furta tare da fadin Allah na gode ma, su zarah dake waje Suma murnan suke, shan juice din yayi sannan yace mata zai tafi Bayan ya amshi number dinta, fita sukayi tare inda Ya bata katuwar Leda dakyar ta amsa sukai sallama akan sai sunyi waya driver yaja suka bar gidan, su zainab na ganin fitanshi suka rugo da gudu suka rungumeta, khairat ledan ta amsa ta bude wani yar takarda ta dauko da sauri aysha ta kwace tayi ciki da gudu binta sukai Suma khairat kam ledan ta dauka ta bisu a baya, key aysha tasa ma d’akinta ta fad’a kan gado tana sauke ajiyar zuciya bude takardan tayi dake ta faman kamshi 
……. 
Bude takardan tayi taga rubutu kaman haka ….. *_my love nayi rubuta Kala biyu na farko Idan kin amince dani shi zan baki wanda gashi yanzu kina karantawa, ina sonki dagaske bada wasa ba ban taba jin son wata mace ba kaman ki, Nima Ina fatan zaki soni kaman haka, koda ban sami haka ba a dan nema min waje cikin zuciyarki koda kad’an ne, I really love you Ki kulan min da kanki_* ido ta lumshe tana wani jin dadi lallai ta sami irin namijin da take buri a rayuwa,jin karan ana buga mata kofa yasa ta tashi da sauri ta boye letter din sannan ta bude kofar su khairat ne suka shigo, khairat ta Fara ciro kayan dake cikin ledan, su chocolate ne dasu biscuits masu tsada sai turaruka masu dadin kamshi, zarah ce ta dauki chocolate daya ta bude takai wajan bakin aysha da sauri ta kawar dakai tare da rufe fuska tana dariya, ummi ce ta shigo ta samesu suna ta dariya tace miye kuka wani sata a gaba? 
Dariya suka kuma yi zarah tace ummi ki fadama Abba tace bata sonshi, da sauri aysha tace ni nace miki haka? Jin ummi tayi dariya yasa ta tuna tana d’akin da sauri ta tashi ta fita suko in banda dariya babu abunda suke, ummi fita tayi ta sami Alh Ibrahim a falo dasu mama, Bayan ta zauna yace ya kinyi mata magana? Ummi tace eh ta amince, Abba yace Toh Alhmdlh Allah ya tabbatar mana da 
alkhairi suka amsa da Ameen, Amina ce ta fito 
domin tunda akayi magana akan saleh bata fito ba sai yanzu, kallo daya zaka mata ka gane tana cikin damuwa, Alh Ibrahim yace amina baki da lafiya ne? Tace lafiya na ‘Kalau, zama tayi tana d’an shan kamshi hindu tace Amina kin fadama saleh sa’kon kuwa? Wani irin kallo ta wurgama hindu sannan tace eh. 
Zainab da aysha ne cikin shiri zasu raka khairat ganin Dr domin glass dinta Ya fadi ya d’an tsage gashi guda d’aya gareta, Bayan sun gama shiri 
suka fita kama khairat din sukayi har mota, driver yaja suka nufi hspt din, Bayan driver ya faka motar suka kamo khairat din suka fito domin in bata sa glass din ba dishi dishi take gani, suna cikin tafiya wayan zainab yayi kara dauka tayi tare da fadin aysha kuje zan amsa waya, dauka tayi tare da fadin zarah ya akayi? Zarah tace Kun Kai taga Dr din? Zainab tace eh yanzu suka shiga ita da aysha, zarah tace OK sai kun dawo, kashe wayan zainab tayi d’ago kan da zatayi suka had’a ido da yazeed gabanta taji yana dukan uku uku, matsowa yayi kusa da ita tare da fadin mun sake haduwa ko baki fad’a ba nasan kina so na, kasa magana tayi sai kallonshi da takeyi ta gefen ido, yazeed yakai 
namijin da duk wata mace zata soshi …… Katseta yayi da fadin kin gudu daga kano kin dawo nan gashi mun hadu, zainab plz ki bani lokacinki, cikin rawar murya tace taya akayi kasan sunana? Yace Aiba Abun mamaki bane dan Nasan sunanki zainab tun ranan dana ganki Allah yasa min sonki, dan Allah ki bani dama, ……. Jin maganan su aysha sukayi suna fadin sannu, yazeed yace sis yakike har kun dawo ashe? Aysha tace eh Wlh, yace gani ga mutuniyar inata ro’kan a bani dama inzo Gida, khairat da aka bata sabon glass tasa da kuma wani extra, ta Fara mishi kwatance yace a’ah gidan Alh Ibrahim? Khairat tace eh yace muna kusa ma ashe, kallon zainab yayi yace sai kin ganni, yayi masu khairat sallama ya wuce, sun fito zasu tafi zainab ta hango mutumin daya ma yasmin magana rannan da sauri ta bishi tana son ta isa gareshi, waigowa yayi yaga zainab wanda ya ganeta sarai ganin shi take nufowa yasa yayi saurin tsaida mashin yahau, mota ta koma da sauri tare da cema su khairat su shiga da sauri, Bayan sun shiga tace driver yabi mai machine din can, aysha tace zainab Waye ne shi? Zainab tace shine wanda yama yasmin magana rannan, zainab tace driver kayi sauri mana, mutumin ganin suna bin shi yace ma mai machine subi ta wani lungu Wanda mota bata shiga hakan k0 sukayi suka bace musu, tsaki 
zainab taja haka dole suka koma Gida, koda suka 
koma sun fadama zarah abunda Ya faru tace subi a hankali koma miye zasu gano bada dadewa ba. 
Magabatan yazeed sun zo neman auren zainab Alh Ibrahim yayi na’am, koda yasa ummi ta tambayeta ta amince Dan haka aka saka rana ita da aysha za’a had’a bikin amma Alh Ibrahim saida yayi maganan a gidansa su yazeed zasu zauna, yace babu damuwa duk da bawai yana so bane Amma son da yake ma zainab zai iya yarda da komai dan ya mallaketa, zainab ce kwance tana tunani tunda suka had’u da yazeed a hspt bata sake ganinsa ba, harya turo gidansu kuma ta amince gashi ko kiranta a waya bai taba yiba, tana cikin tunanin zarah ta shigo tace zainab tashi ki shirya zaki raka ni, amma fah kici gayu sannan kiyi sauri dan Allah, tace zarah ban son fita Wlh wani iri nake ji, zarah tace plz my little sister ba dadewa za muyi ba, zainab tace toh, zarah tace yauwa my little kiyi sauri, Bayan fitan zarah zainab ta tashi tayi dan normal makeup sannan ta fito, a falo taga zarah tace yauwa danje falon ba’ki ki kaimin drinks din nan Nayi baki, amsa tayi ta fita tana shiga sukai ido biyu ido ta zare alamun mamaki shiko murmushi 
yayi tare da fadin Barka da shigowa my hrt, cikin jin kunya ta ajiye tray din tare da zama a gefe tace sannu da zuwa amma baka kyauta min ba, yace mai Nayi? Tace bana son surprise visit, dariya yayi tare da fadin dan Zanzo wajan wife dina saina fad’a mata? ltama d’an murmushin tayi tare da zuba mai drinks din tace bismillah, kallonta yayi tare da fadin nifa nayi alkawarin matata zata dinga bani abinci, cikin jin kunya tace ai matarka kace Dan haka saika bari a d’aura koh? Murmushi yayi tare da fadin my luv baki da dama sunyi fira Sosai wanda dukyawancin firan akan yanda bikin nasu zai kasance ne, koda zai tafi ledan waya Ya bata tace waya kuma Bayan Wanda ka bani, yace wancan dana baki na nagani Ina so ne wannan kuma Na amsan soyayyata da akayi ne dariya tayi tare dayi mishi godiya tace na aure kuma fah tana fadin haka ta shige Gida da gudu, dariya yayi tare da fadin komai kikai yana miki kyau zainab motarshi ya shiga yaja yabar gidan, zainab koda ta shiga d’akin zarah tayi dan tasan suna ciki, aiko tana shiga ta gansu khairat ta amshi wayan tace wow iPhone, aysha ce ta shigo da sauri tace zarah naji binta da yasmin suna magana Wai duk da sun bar maraba faruk ya canza musu Gida amma wani d’an iska nason tauna musu asiri, zaman gidan karuwai ai bain ba ko wani shege ya gaya maka magana amma nan gidan komai yi mana ake kai 
zaman gidan masu kudi akwai dadi, aysha tace ina jin iya nan nabar wajan, zainab tace kenan yasmin karuwa ce Anya binta mamanta ce kuwa? Tace zarah nayi alkawari Kafin auren mu nida aysha saina gano ko miye kenan faruk yasan komai, 
zarah tace bake d’aya ba har damu koma miye daka gobe zamu fara 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]