[Advertisements⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 6 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA
CHAPTER 6
Koda zainab ta Koma kasa aikin komai tayi dan haka ta shige dakin da suka kwana, yar ledan daya bata ta bude taga waya ne sabuwa FIL a kwalinta kiran w4 kallon wayartai tayi tana mamaki mai yasa zai bata waya? 
Mai yake nufi dani haka taita tunani har aysha ta shigo dakin taga wayan a hannunta amsa tayi tare da fadin wow wayan Waye wannan? 
Zainab tace “wannan mutumin ya bani, Aysha tace wa kenan? Zainab tace mutumin da muka hadu dashi jiya, Aysha tace kai amma yana da kirki dama wayarki ta Zama sai a hankali gashi kin sami wata, wani irin kallo zainab tayi mata tare da fadin wannan wani irin magana ne? Taya mutumin da ban sani ba zai ban abu daka haduwa jiya sannan ki nuna Abun ya birgeki karki manta da irin tarbiyan da aka mana, Aysha tace amma koma dai miye so yasa ya miki domin nasan sonki yake, wani irin kallo zainab ta kuma yi mata tare da fadin yana da aiki danko ni baiyi min ba sannan wannan kyautar da yayi min dole in mayar mishi, Aysha tayi shuru tana kallonta can tace toh taya akai kika amsa? Shuru zainab tayi tana tuna lokacin daya kamo hannunta ya bata ledan tare da tunanin kalamanshi Indai muka sake haduwa Toh Kema kina sona, ido ta lumshe tare da fadin no no bazan ganshi ba, bazan bari mu hadu ba, dariya Aysha ta 
saki tare da ja mata kunne tace har kin Fara 
tunaninshi haka? Tashi tayi ta Fita da sauri ta shige cikin soron gidan tana mai sauke ajiyan zuciya. 
Alh Ibrahim ne zaune da iyalan gidanshi suke yin breakfast, kallon ummi yayi tare da fadin kunyi waya dasu aysha kuwa? Mamaki tambayarya bata yaushe ya fara kula da al’amarin yaran da harzai tambaya ….. Katseta mata tunani yayi tare da fadin gaskiya ne ba mutuwa akema kuka ba sabo akema kuka naji kawai Ina kewarsu ne, ummi wani irin dadi taji Koba komai ya nuna kulawanshi akansu…. Karan telephone din gidan yasa zarah ta tashi ta dauka tare da fadin hello, tace aysha ya kuke Ina zainab? Ummi ce ta taso da wuri ta amshi wayan tare da gaisawa da Yaran nata, zainab ce tace Ina khairat? Ummi tace kin San tana exam da wuri take fita, zainab tace hakane ina mama dasu Anty hindu da inlow dinmu yasmin? Ummi tace mama tana lafiya Anty hindu itama tana lafiya sannan yasmin itama tana lafiya, zainab tace toh ki gaidasu, tana kokarin kashe wayan ummi tace baki tambayi abbanku ba? Alh Ibrahim wanda idonshi da kunnenshi yake wajan Dan tunda ta Fara fadin 
kowa na lafiya yaji bata kirashi ba, yaji wani iri Koba komai ai shine mahaifinsu basu isa su canza shiba, zainab kam tunda taji ummi tace haka ta kashe wayan ba tare da tayi magana ba, aysha dake kusa da ita tace zainab Yadai? Tace ummi ce take min magana Wai ban tambayi abba ba, shine na kashe wayan dan bani da ra’ayinjin koya yake, aysha tace zainab wannan kiyayyar ta isa haka shine fah mahaifinmu karki manta, zainab tace aysha hakane shine ya haifemu amma baya bamu kulawa na uba bama muba harta mahaifiyarmu saboda ta haifemu yasa ya tsaneta yake horar da ita tsawon shekara ishirin, ina alfahari kasancewa y’ar ummi mace mai jarumta juriya hakuri boye bakin ciki dan kuma fahimta   aysha nasha ganin ummi tana kuka a d’aki ita daya ko kin San kukan mai takeyi? Kukan ba’kin ciki takeyi mijinta daya zama shine uwa uba a wajanta ya juya mata baya saboda bata haifi d‘a namiji ba, MIYE ILLAR Y’AY’A MATA? fad’a min MIYE ILLAR Mu da yasa Abba baya son mu ya tsanemu ya manta da Allah shine yake badawa, har yanzu bazan manta da Abun da Abba yamin ba ina karama, lokacin daya siyo ma faruk motor wasa naje nahau Nima Ina wasa dashi motor ta fadi taya d’aya ya fita har naji ciwo a kafa ranan Abba Ya mareni saboda taya d‘aya Ya fita Wanda bada 
gangan nayi hakan ba, aysha kin San mai Nayi 
tunani lokacin muba yaran Abba bane aysha tace zainab ki dawo cikin hankalinki ki daina fadin wannan maganan mu yafe ma Abba Dan Allah, zainab tace aysha taya zan iya manta komai in mu mun manta ummi fah wacce take ta ‘kunsan ba’kin ciki tsawon shekaru da dama? Aysha shuru tayi can tace zainab mu shirya gobe mubar garin nan inaso muyi wani abu in munje abba baya son Y’ay’a mata saboda yana ganin bamu da wani amfani da za muyi mishi, inaso mu nuna ma Abba Muma y’ay’a mata zamu iya mishi abunda d’a namiji zai iya koma fiye da abunda d’a namijin zaiyi what man can do a woman can do it better, zainab shuru tayi tana nazari …… Suna cikin haka matar limam ta shigo tare da fadin dan Allah kuyi hakuri yau na tashi da zazzabi gashi limam tunda ya fita da asuba bai dawo ba, kuyi hakuri na barku da yunwa bari in daura mana abinci, aysha tace lah ai munyi ma sannu Ya jikin naki? Matar limam ta amsa da lafiya, tare da fadin kai amma dai banji dadi ba taya baki zasu daura abinci da kansu harda dawainiya, zainab tace haba aimu ba baki bane sannan ku ka kanninmu ne dole muyi muku abunda zamu faranta muku rai, matar Limam tace Allah ya muku albarka suka amsa da Ameen, aysha ta zuba mata tea da bread tare da kwai ta bata, Bayan ta gama zainab ta bata paracetamol tasha 
lokaci daya zazzabin Ya saketa Suna ta fira har 
lokacin daura abincin rana yayi suka fara hidiman daurawa, aysha ce ta fita dan yin cefane wannan karan bata dade ba ta dawo suka daura dambu Wanda yaji zogale da kayan hadi, koda limam ya dawo suka fada mishi gobe zasu tafi cewa yayi bai yarda ba su bari jibi Dan sai sunje sunga danginshi haka suka hakura akan gobe zasu ganin dangin nasu
Washe gari kaman yanda limam yace Bayan sun Karya, suka shirya yace matarshi ta kaisu gidan yan uwanshi su gaisa, ya bata kudin mota aysha tace ya bari zasu biya limam yace gidanku karki sake kuce zaku biya, maza kuje ku dawo da wuri fita sukayi suna dariya, keke napep suka hau, Ya kaisu kofar mata, wanda yawancin dangin limam a nan suke sunga dangin limam suna da kirki sun kuma karramasu Sosai tare da basu tsaraban gurasa da sauransu, sai wajan karfe biyar suka fito dan nufa gidan, tunda zainab ta fita take ta boye boye kaman wata mai laifi kaman ance ta daga kanta ta hangoshi zaune a saman mota yana daga mata hannu da sauri tajuyar da kanta gefe Wanda yayi dai dai da samun keke napep din Dan haka ta shige da sauri dan kallon gefen data ganshi tayi taga Ya 
sakar mata murmushi Wai Waye wannan guy din? 
Yazeed d’a ne daya tilo ga general usman, general usman soja ne daya riqe mikamai da dama a soja daga karshe yayi ritaya ya fada kasuwanci Sosai yana da kudi Sosai matarshi daya hjj hauwa, tunda ta haifi yazeed bata kara haiyuwa ba, dukansu yan asalin kano ne amma suna zaune a kaduna, general ya rasu a hatsarin jirgin sama daya afka har dashi a ciki, tun daka lokacin daya rasu yazeed yake kula da wani harkoki nashi, yazeed dogo ne sannan shiba fari bane sannan kuma ba baki ba, yana da faffadan kirji namiji ne iya namiji wanda ya amsa sunanshi mata da yawa suna nuna suna sonshi amma shi bata su yake ba, ya taba ganin zainab ne tun a kaduna yaji yana Sonta sai gashi sun hadu a mota lndai zaije kano motor haya yake shiga yaje in yaje a gidansu Na kano yake sauka akwai mota da yake yawo dashi a gidan, tunda yake bai taba jin son abu ba kaman yanda yake son zainab, wannan shine labarin yazeed. 
Zainab da kirjinta yake ta buga mata da sauri, 
domin batai zatan zata kuma ganinshi ba a yanzu, koda suka shiga Gida kasa wani motsin kirki tayi sai kwanciya ba komai take ba sai tunanin yazeed yanda Ya d’aga mata hannu da kuma murmushin daya sakar mata ido ta lumshe tare dayin mamakin jin canjin data fara ji lokaci daya, da sauri tace no hakan bazai faru ba gobe zamu bar garin bazan kara haduwa dashi ba har abada …… 
Abincin dare suka daura matar limam da aysha basu wani dade ba dan taliya ce da miya suka daura Bayan sun gama matar limam tace bari ta shiga ciki yau ta gaji fitan da sukayi, zainab tunda aka saka mata abincin take ta juyawa ta kasa ci, kana kallonta kasan ta fad’a duniyar tunani, zunguranta aysha tayi tare da fadin tunanin mai kike haka? Sai juya abinci kike? Tashi tayi tare da fadin na koshi d’aki tayi da ido aysha ta bita, koda ta shiga d’akin kwanciya tayi tana tunanin yazeed lokacin daya dago mata hannu da sanda ya sakar mata murmushi, ido ta lumshe na wajan minti d’aya sannan ta tashi ta dauko wayar daya bata, ciro wayar tayi a kwali tana kallo tare da jujjuyata jin kaman motsin mutum zai shigo yasa tai saurin boye wayar cikin jakarta, matar limam ce ta shigo dauke da abincin data ki ci, tace haba zainab mai kika ci da zaki ce kin koshi maza amsa kici, amsa tayi dan bazata iya musu da matar limam ba, matar limam tai ta dan janta da fira suna firan tana ci kuma taci da yawa, aysha ita ta shigo suka Dan taba firan matar limam tayi musu saida safe, Bayan fitar matar limam aysha tace uhm nikam zainab naga duk kin canza kodai ….. Da sauri zainab tace kodai me? Dariya aysha tayi tace bazan fad’a ba amma zan zuba ido inga ikon Allah, zainab tace Hmmm tare da juyawa ta kwanta, ita da kanta ta rasa mai yake damunta yanda takeji yanzu bata tabajin irin haka ba. 
Washe gari tun wajan karfe 8 da wani abu suka gama komai dan da wuri suke son tafiya, limam sukejira ya dawo dan ya fita yace su jirashi, suna zaune suna fira har wajan goma saura saiga limam yayi sallama, amsawa sukayi dukansu suka mishi sannu da zuwa, limam yace kuyi hakuri naje siyo muku gurasa ne, gashi anyi Sa’a gashin yau ne, zainab tace lah aiko an bamu gurasa jiya da muka Fita, yace eh na gani bata da yawa, godiya suka mishi, yace Wlh ban so ku tafi d’an zaman nan da mukayi naji mun Saba Sosai, matar limam ta cafke da fadin Wlh koni zanyi kewarsu, zainab tace inye ashe dai ana son wannan amaren, dariya sukayi su duka, tashi sukayi tare da dauko akwatinsu, limam ya rakasu hartasha suka shiga mota saida motarta tashi ya bartashan. 
Amina da mama da yasmin ne zaune a falo hindu ta fito tana nuna ma amina wani riga data siya tace amina kalla ki gani tayi kyau kuwa? Amina tace eh babu laifi, ummi ta fito dauke da meat pie a tray ta 
ajiye akan center table tare da daukan plate tasa ma mama ta mi’ka mata, mama tace sannu da aiki tare da amsa, hindu ta kalli ummi tace ummi kalla ki gani rigan nan tayi kyau kuwa? Ummi tace yayi kyau Sosai ….. Shigowan su zainab yasa ummi yin shuru da sauri aysha ta fad’a jikin ummi tana fadin kai nayi kewarki ummi na, ummi tayi dariya tare da fadin nima haka ya hanya? Aysha ta amsa da lafiya zainab itama ta fad’a jikin ummi tare da fadin ummi na, dariya ummi tayi cikin son yaran nata tace Sannunku da zuwa, gaida mutanan falon sukayi hindu tace ina tsaraba zainab ta mi’ka mata katuwar ledan gurasa, hindu ta amsa tare da budewa tace wow gurasa ta kwadama ‘ khairat kira wacce ta fito da sauri ita da zarah dan sunji hayaniyar yan uwansu, rungume juna sukayi suna dariya, hindu tace khairat in kun gama murnan ki hadamin wannan gurasan yau shi zanci da daddare khairat tace toh, faruk ne ya shigo gidan nufan su zainab yayi yana fadin
 saukar yaushe? Aysha tace yanzu muka dawo yace Kun dawo lafiya? Suka amsa da lafiya, ya kalli zainab yace sis mai kuka kawo min? Dariya zainab tayi tare da kamo hannunshi ta zaunar dashi, ta nufi inda ledan gurasa yake ta dauko guda biyu ta nufeshi tura mishi tayi a baki yana fadin a‘ah Na koshi amma ina tura mai take ganin haka yasa ya tashi ya haura sama da gudu sai dariya suke ta musu, 
duk wannan drama din akan idon Alh Ibrahim ake yinta dan tare da faruk suka dawo, ummi ce ta Lura dashi tace sannu da zuwa, baya duka suka waiga ganin mahaifinsune yasa duka suka tamke fuska tare dayi mishi sannu da zuwa ga mamakinsu saiya amsa tare da fadin kun dawo lfya? Kallon mamaki suke mishi saida ummi tace baku ji ana tambaya bane? Aysha tace lfya Abba, sannan sukai ciki suna mamakin nuna kulawanshi a kansu, suna shiga ciki khairat ta matsa kusa da aysha tace anzo neman aurenki fah Abba ya kuma amince, ido aysha ta zaro tare da fadin ban San wasa, dariya zarah dake gefe tayi tare da fadin dagaske ne, Abba yace ldan kuka dawo saiku hadu keda shi in kun fahimci juna shikenan, uhm kawai tace ita kam zainab sai dariya take tayi alaman jin dadi yar uwarta zatai aure, aysha ce tayi ajiyan zuciya tare da fadin zarah matso kiji duka suka matso sukai magana, zarah tayi dariya tare da fadin zamu gwada hannunta ta ajiye aysha ta daura nata akai zainab ma ta daura khairat tasa nata tare da fadin zamu nuna ma Abba Muma y‘ay’a ne, dariya sukayi tare da rungume junansu. 
Da daddare kowa Ya hallara akan dinning wajan cin abinci, ummi kaman kullum saida tasa ma Abba yayin da su zarah suke zubama junansu, suna cikin cin abinci zainab tace Abba, dagowa yayi ya kalleta tace Abba Muma muna son mu fara zuwa office, kallonta yayi da sauri Kafin yayi magana aysha tace Abba Muma munyi karatu sannan duk abu d’aya ake koyawa sai dai Inba course dinku daya da mutum ba, Muma muna son mu tallafa maka, khairat tace Abba akan zaman gidan da mukeyi gwara muje Muma mu bada Tamu gudun mawar, zarah tayi caraf tace Abba ka bamu dama domin Kaga irin Tamu baiwar 
kowa dake wajan kallonsu yake yana son jin mai Alh |brahim zaice …….. Hmmm ku biyoni muji ko Alh |brahim zai yarda da wannan maganan ta yaran nasa 
mata …… 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]