[Advertisements⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 5 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA 
CHAPTER 5
Alhaji Ibrahim ne zaune a office yana duba wasu file saiga wani guy Ya shigo kallo daya zaka mishi ka gane Dan gidan masu hannu da shuni ne domin fatan nan tashi gwanin sha’awa, Alh Ibrahim dake duba file ya kalleshi cikin murmushi tare da fadin faruk ga wannan file din akai office din manager amsa yayi da fadin Toh Abba tare da flta, direct office din manager yakai inda ya amsa file din zama faruk dinyayi tare da fadin yaushe zaka Gida? Manager yace anjima kadan zan tafi ya akayi? Faruk yace lafiya kawai na tambaya ne in yanzu zaka mu wuce tare, shuru manager yayi can yace OK jirani in duba file din nan saimu tafi, faruk yace OK manager na dubawa yace su tafl, fita sukayi suka nfi Gida koda suka karasa sun Tarar da Alh Ibrahim harya rigasu dawowa yana zaune akan dinning gefe ga hjj Amina da hindu da mama sai ummi dake tsaye tana zuba musu abinci da sauri zarah ta fito ta tari manager tare da zuba mishi abinci Waye manager? Manager shine mijin zarah sunanshi Abubakar sun hadu ne a skul inda suka fara soyayya shiba masu kudi bane talakawa ne amma son da take mishi yasa Alh Ibrahim ya yarda sukai aure tare da kafa mai sharadi akan zasu zauna a gidansa sannan a company dinshi zaiyi aiki haka ya yarda ya amince akai auren Alh Ibrahim ya bashi mikamin manager Bayan shekara daya suka haifi y’a mace suka saka mata suna afra, Alh Ibrahim lokacin data haifi mace haka yaita mita tare da goranta mata Wai sun biyo uwarsu, zarah mace ce kyakyawa ga saurin gano abu haka aysha da zainab Suma suna da kyau amma duk khairat ta fisu kyau sai dai ita kawai matsalan idonta shine ya kwafsa mata, Alh Ibrahim yanzu Ya dan sake ma ummi da y’ay’anta amma ba Sosai ba abunda yasa ya Dan sake mata shine tunda yarta tayi aure kuma mijin y’ar nata yana mishi aiki wannan yasa yaji dadi tare da burin Idan sauran ma sukai aure haka nasu mazan zasu dinga mishi aiki wannan kenan. Faruk tunda ya taso bai taba neman abu ya rasa ba tun yana yaro wannan Abun yasa ya fara neman mata Wanda iyayenshi basu San da hakan ba, garin yawon neman matan nashi ne harYa kaishi maraban jos inda ya hadu da wata yarinya mai suna Aneesa suka kulla soyayya gashi kaman ta girmeshi Dan kana kallonta zaka gane babba ce, Aneesa Lura da irin kudin da yake kashe mata yasa taji tana son aurenshi dan tasan Labarin gidansu tana ganin Idan ta aureshi dukiyar gidan zata zama tasu tunda shine namiji, haka ta dinga tusa mishi ra’ayin aure tare da taimakon magajiya sunyi nasara inda yace ya amince zai aureta amma dole subar gidan karuwai zai kama musu wani Gida sai su zauna, Aneesa tace bata da iyaye magajiya zata zauna a matsayin mamanta sannan zata canza suna Kar Ayi saurin ganeta haka ya yarda inda ta koma yasmin magajiya kuma da sunanta ake kiranta  faruk ya kama musu wani Gida mai kyau duk da ba wani girma gareshi ba dan yace Idan akai auren tare da magajiya za’a koma gidansu. 
Faruk yama mamanshi maganan yana son yin aure taji dadi Sosai tare dayin na’am da batun dan babu abunda zai nema Wanda ba zata iya mishi ba, domin shine farin cikinta tunda ta haifeshi itama rayuwanta ya canza Sosai, hjj Amina tayi ma Alh Ibrahim magana akan auren da d’anta yace yana so da Farko ya danyi musu amma ta shawo kanshi yace babu damuwa, za’a tura haka aka shirya aka nufi gidansu binta neman auren yasmin Wanda suka sami dattawa guda biyu da Sunan sune kannen mahaifln yasmin Wanda ya rasu nan take aka biya sadaki dattawan basu bata lokaci ba suka ce bikin basaso yayi nisa nan da sati biyu sukeso Ayi tunda sun amshi sadaki Alh Ibrahim da abokinshi suka ce babu damuwa Allah ya Sanya ma auren albarka suka amsa da Ameen tare dayin sallama, suna fita magajiya da Aneesa suka fito tare da amshe kudin magajiya ta kirga taba dattawan tace sauran Idan aka daura aure zan cika muku suka amsa suna dariya 
magajiya ta kalli Aneesa tace kin kusa zama attajira dariya Aneesa tayi tare da fadin a hankali zan maida komai na gidan ya zama nawa Indai akai auren gaba daya saina maida iyayenshi kaman bayi musamman mamanshi da yakeji da ita kaman kwai dariya magajiya tayi tare da fadin duk abunda kika ce zaki aikata Toh Nasan zaki iya, itama dariya Aneesa tayi tare da fadin sannan haka yake. 
Yau Friday aka daura auren Umar faruk da yasmin inda aka tafi da amarya gidanta wato gidan Alh Ibrahim, tare da magajiya aka tawo dan dama faruk ya fadama mamanshi kuma ta yarda da zaman binta a gidan duk da dakyar mijin nata ya yarda ganin Amina tayi fushi yasa ya yarda, tunda yasmin tazo gidan ta Fara Lura da mutanan gidan, ta Lura sai abunda Amina tace shi akeyi dan haka duk wata hanya da zata ga tabi dan komai ya dawo wajanta shi takeyi, yasmin Na zaune a falo saiga Amina ta fito kallo daya tama yasmin tace bani juice insha kishi nakeji, yasmin ta tashi tare da fadin Toh, kitchen ta nufa tana gunguni tare da fadin nan gaba kadan nice zan dinga ai kyanki, bayan yasmin ta kawo mata juice din ta nufi kujera zata zauna Amina tace yasmin zo ki min gyaran kafa kafata tayi datti, cikin takaici ta amsa da Toh tare da dauko Abun yanke kumba ta Fara mata tana yanke mata Kumba tana ji kaman ya yanke ta, haka ta gama, tana gamawa ta nufi dakin binta inda ta sameta tana kwance yasmin tace ni Ina can wancan matar zata kashe ni da aiki amma ke kina nan kina jin dadi abunki, binta tace ai dole inji dadi komai ina zaune ake min mai tasa ki? Labari yasmin ta bata binta tace Idan mukaci gaba da zama a haka Toh matar nan babu abunda zata dinga baki sai wahala ya kamata mu nemi mama, yasmin tace karki damu binta Nasan yanda zanyi maganinta. 
Zainab da aysha ne suke tayi ma ummi mita akan ta yarda suje kano wajan limam su ganshi, ummi tace su tambayi babansu inya barsu. bata fuska sukayi tare da fadin ita tayi mishi magana tace ashe baso kuke kuje ba, ganin ummi ta dage akan ba zata mishi magana ba yasa suka tashi suka nufi dakinshi suka tambayeshi yace babu damuwa sai su shirya gobe suje cikinjin dadi suke ta mishi godiya. 
Washe gari suka shirya khairat taso taje amma tana final exam dole yasa ta hakura suka tafi, tun a cikin mota wani yake ta kallon zainab ganin irin kallon da yake mata yasa ta daure fuska suna sauka a tasha wani ya fisge mata waya Wanda yake ta kallonta ya bishi da gudu harya kamashi ya amshi wayan tare da mi’ka ma wani police dake wajan mutumin zainab na zaune tana hawaye tare da fadin address din gidan da zamu yana cikin wayan yanzu miye Abun yi? Sai ganin mutum tayi yana mi’ka mata waya tare da fadin ki dinga kula yana fadin haka Ya wuce wani irin dadi taji tana kokarin tayi magana tana son yi mishi godiya tare da tare da tambayan sunanshi amma yayi nisa tsaki tayi tare da fadin Allah Ya kara hadamu aysha dake gefe tace har kin kamu ne dariya tayi tare da fadin haba dai sai kace wata mara wayau kawai dai ina son yi mishi godiya ne Kinga mu tafl muje mu nemi gidan da zamu ……
Tafiya suke akan titi aysha tace nifa na gaji Kinga duba mana address din sai mu tambaya, zainab tace toh tare da duba wayan amma Abun takaici babu chaji tana kokarin shiga message inda ta ajiye address din a draft din wayan ta mutu tsaki tayi tare da fadin wayan tayi shutdown, aysha tace Kai mudai yau munga ta kanmu dama babu caji a ciki ne? Zainab tace eh Wlh babu caji Sosai gashi battery dinma baya ri’ke caji kwata kwata, aysha tace toh yanzu ya za muyi gashi naga yamma ta farayi zo muje mu dinga tafiya ko ma sami wani waje musa caji, tafiya suke duk sun gaji ga yunwa na damunsu suna ta tafiya ko za suga wajan da zasu sa caji aysha ce tace tsaya ciro sim din Asa a tawa wayar, zainab tace k0 amsa ai message din ba’akan sim yake ba a draft nace miki na ajiye Kinga yana kan wayan kenan, aysha tace toh nidai Wlh na gaji gaskiya zainab tace Hmmm ni baki ga dakyar ma nake magana ba alaman na fiki gajiya, aysha tace uhm bari Ki gani zama tayi akan wani dan dakali dake gefen titi tare da fadin bari in huta Dan Wlh kafata zafi yake, karan wayan aysha dinne yasa zainab ta bita da kallo tare da fadin Waye ke kira? Aysha bata ce ma zainab komai ba ta dauki wayan tare da fadin ummi gamu mun lso tun dazu muna nan muna neman gidan gashi…. Kai zainab ta girgiza mata alaman Karta fadama ummi dan haka ta canza maganan da fadin ga zainab, mi’ka ma zainab wayan tayi tace ummi bari in munje gidan ma kiraki ta kashe wayan, aysha tace mai yasa kika hanani fad’a ma ummi? Zainab tace zamu tada mata da hankali ki bari zamu sami inda zamu sa caji nida kin daure kin tashi Wlh mun taf ….. Sannunku sukaji ana musu magana zainab ta waigo tare da mishi kallon mamaki domin mutumin dazu ne daya amso mata waya, aysha ce ta iya amsawa tare da fadin yauwa, yace yana ganku a nan? Ko baku gane inda zaku bane? Aysha ta kalli zainab sannan tace Wlh address din wajan da zamu yana cikin wayanta gashi kuma ya mutu babu caji, Dan shuru yayi sannan ya ciro wayanshi irin tata ya cire battery din ya mi’ka mata tare da fadin gashi kisa kin karba tayi kanta na kasa sai aysha ce ta amsa tare da dan dungurinta ta mi’ka mata sannan ta amsa tasa, kunna wayan tayi ta duba address din sannan ta dago tace kofar wambai zamu murmushi yayi tare da fadin ok muje ku sami mota sai ya kaiku mai a daidaita ya Samar musu aka mishi kwatancen inda zai ajiye su ya ciro kudin ya biya aysha tayi mishi godiya zainab ta mi‘ka mishi battery dinshi yace Nop ki ajiye a Wajanki, har ku gane gidan, tace toh a Ina zan ganka in baka? Yace karki damu zamu sake haduwa yana fadin haka Ya wuce mai mota kuma yaja, zainab tunanin mutumin da batasan Sunanshi ba take tayi tare da mamakin kirki irin nashi daga haduwa yau amma yana ta musu kirki ido ta lumshe har suka isa inda mai motor zai kaisu flta sukayi tare da daukan akwatinsu wasu maza dake zaune suka tambaya dan Allah inane gidan limam? Nuna musu gidan sukayi Godiya sukai musu tare da nufar gidan, sallama sukayi aka amsa tare da basu izinin shigowa, Bayan sun shiga wata mata ce fara tace Sannunku ta shimfida musu tabarma tare da kawo musu ruwa suka sha sannan matar tace sai dai ban shaidaku ba? Aysha tace daga kaduna muka zo wajan Malam, matar tace kodai yaran kubra ne ku? Zainab tace eh matar tace a’ah Sannunku Ya hanya? Suka amsa da Lafiya tashi matar tayi ta dauko musu abinci tare da fadin limam din bai dade da fita ba amma Nasan bazai dade ba kuci abinci bari insa muku ruwan wanka dan Nasan Kun gaji zaman mota babu dadi tashi tayi ta Fara kokarin hada murhu. 
,,,,,,,,
Amina ce zaune a falo tana shan fruit tana wani kashe ido da alama tana jin dadin yanayin da take ciki, yasmin ce ta fito zata kitchen kiranta amina tayi tare da fadin kai plate din nan kitchen sannan kizo muje shopping, yasmin tace toh amsan plate din tayi cikinjin haushin yanda sirikar tata take son maidata yar aikin karfi da yaji Bayan duk yawan masu aikin gidan, dan murmushi tayi tare da fadin bari inyi sauri in shirya hala ni zata siyan ma kaya, da sauri ta fita ta shirya ta fadama binta zasu shopping ita da Amina binta tace itama a siyo mata nata tsaraban yasmin tace mai kike so? Binta tayi murmushi cikin jin dadi tace sarkan zinari, dariya yasmin tayi tare da fadin karki damu zan siyo miki yau sai nasata kashe kudi Sosai, binta tace wow yasmin Nasan komai kika fada sai kin cika shi, sai dai ni nafl son musan Abun yi Wlh so nake naga komai na gidannan ya dawo gareki amma Nayi wani nazari hakan bazai faru ba sai mun aikata wani abu amma karki damu jeki dawo daka rakiyar kiji maina shirya dariya yasmin tayi tare da fadin binta Idan komai na gidan nan ya 
zama nawa zan juya mutane yanda naso dariya sukayi sannan ta fita. 
Wani dangareren super market suka shiga kaya ne na mata dinkakku da kuma kayan dankunne da sarka Kala Kala komai dai da kuka sani na Ado na mata ana samu a wajan, kujera aka basu yayin da suka je wajan sarka, Amina ta nuna wani tace a dauko mata karashi tayi a wuyan yasmin tace wow yayi kyau Kinga yanda Ya miki kyau, yasmin cikin jin dadi tace sarkan yayi kyau Amina tace tunda yayi kyau a wuyanki Nima zai min tace ma mutumin ya bata, ta kalli yasmin tace da bikin yarinyar kawata zan sa, yasmin wani kululun bakin ciki taji wato ba ita tasai mawa ba, haka Amina taita daukan kaya ko tsinke bata saima yasmin ba saida suka koma Gida tace au Kinga yasmin na manta baki dauki komai ba, dan murmushi tayi tare da fadin babu komai sannan ta wuce dakin binta, binta dake zaune yasmin ta budo kofa cikin zafln rai tana huci, binta tace lafiya kuwa? Labarin abunda Ya faru ta bata tare da fadin lokaci yayi da zan nuna mata Waye yasmin binta bari faruk yazo zansa yasa a maida komai da sunanshi Idan hakan ta faru Kinga mallakan komai bazai min wuya ba, binta tayi dan murmushi I’rin na tsofaffin bariki tace waya gaya miki wannan abu mai sauki ne? Bari kiji abu daya za kiyi ki mallaki komai shine ki haiyu in kin tashi haiyuwan ma ki haifi d’a namiji yanda sirikin ki keson namiji yana ganin haka zaiba mijinki komai ke kuma daka nan sai kice a maida da Sunan d’anki dariya yasmin tayi tare da fadin wow binta Banyi niyan haiyuwa ba yanzu amma dole yanzu in sami ciki dan in mallaki komai dake gidan nan. 
,,,,,,
Su zainab sunyi wanka tare dayin sallah, limam bai shigo gidan ba sai Bayan sallah isha ‘I ya shigo suna zaune akan tabarma suna flra da matar limam din dan an dauke wuta, limam yace baki mukayi a gidan namu yau,? Matarshi mai suna larai tace eh kishiyoyina ne suka zo daga kaduna, yace badai yan wajan kubra ba? Tace eh sune yace ah ikon Allah lokaci na gudu kune kuka girma haka,? rayuwa kenan gaidashi sukayi ya amsa tare da tambayan kunzo lafiya? Sukace lafiya yace ya kubra din da Baban naku? Suka amsa da lafiya limam yace Nima Ina tason inzo in duba ku amma Abun yaki yau lafiya gobe ciwo haka nake ta fama ga tsufa, cikin tausayin tsohon suka ce insha Allah zaka samu lafiya da yardan Allah, dan murmushi yayi tare da fadin wani lafiya ai lafiya daya shine yau Idan akace Na mutu shine zan huta insha Allah, dukansu hawaye ne ya zubo musu na tausayinshi zainab tace cuta Aiba mutuwa bace yace hakane amma Aina tsufa Allah dai yasa mu dace Ya canza maganan dan yaga hankalinsu Ya tashi, sunyi fira Sosai inda suka tashi dan kwanciya. 
Washe gari su zainab Kafin matar limam ta tashi sun gyara ko Ina tare da hada murhu suka saka ruwan zafi dan sunzo da kayan su tea zainab ta dauki kudi tace ma aysha bari in siyo bread aysha tace toh ki siyo harda kwai, ta amsa da Toh tare da flta, tayi dan tafiya kadan ta Sami shago ta siya bread amma babu kwai Dan haka ta kara gaba, a wani katon shago ta tsaya ta siya Kwan waigawan da za tayi taga wannan guy din nan daya bata batir murmushi ya sakar mata tare da fadin Kinga mun sake haduwa, tace Anya ba bina kake ba,? Tayi maganan ne cikin tsiwa tare da ciro batir dinshi tace gashi inna baka Nasan bazaka sake ganina ba, nasan danshi kake bina, kallonta yake cikin mamaki ganin tana bashi batir din dan murmushi yayi tare da fadin bani ke binki ba zuciyarmu kebin juna ido ta bude tare da sakin baki, yaci gaba da fadin tunda na ganki naji Ina sonki amma tunda kinmin wani fahimta daban daga yau bazan sake bari mu hadu ba tunda Na fada miki abunda ke zuciyata ni Nasan Kema taki zuciyar tana sona Idan har kika bari muka sake haduwa Toh Nasan kina so na, ledan dake hannunshi Ya kamo hannunta ya mi’ka mata tare da barin wajan, gaba daya ta kasa wani motsi mai karfi magananshi ne keta mata yawo a kunne. 
Zarah ce zaune ita da ummi suna tattaunawa akan mutumin da yazo nema ma danshi auren aysha Wanda Alh Ibrahim ya amince Ya bashi tare da fadin a gidanshi zasu zauna in anyi aure amma mutumin yace a’a yana bukatar ya zauna shima da danshi da kuma sirikar shi, domin yana son y’a mace amma Allah bai bashi ba saiya bashi d’a guda daya namiji, Alh Ibrahim yayi mamakin jin haka da yaji Wai shi wannan mace yake bukata ba namiji ba, haka sukai sallama Alh Ibrahim nata tunanin maganan shine ummi da zarah suke tattaunawa akan maganan zarah tace toh Kinji ummi shi duniya abunda kake ‘ki toshi wani yake nema ido rufe, ummi tace hakane a kullum Ina alfahiri da kasancewata Uwar mata ban taba dana sanin haiyuwarku ba, dan Ina ji a jikinta wata rana zaku zama Abun alfahari 
sannan insha Allah mahaifinku nan gaba zai gane irin albarkar y’ay’a mata. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]