[Advertisements⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 3 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA 
CHAPTER 3
Lokaci daya ta saki wani irin kuka mai ban tausayi, saida tayi mai isarta sannan ta tashi tayi toilet ta gyara yar Tata tare dasa mata kaya, Bayan itama ta kimtsa jikinta ta gyara dakin kaman bashi ba, sai wajan asuba Alh Ibrahim Ya nufi dakin Dan dubata Kafin ya tafi masallaci, yana shiga yaga baby akan gado ita kuma bata nan amma yaji motsinta a toilet, da sauri ya karasa kan gadon duk da kayan mata ne a jikin baby din bai hanashi cire mata wando da pampers ba dan yaga mai aka samu, yana gani’ Ya saki tare da tashi ya flta cikin fushi, dakin mama ya shiga inda ya sameta tana zaune akan dadduma, tana ganinshi tace Ibrahim lafiya kuwa? Kai ya girgiza mata alaman a’a sannan ya fashe da kuka kaman wani karamin yaro mama cikin damuwa tace Ibrahim lafiya kuwa? Yace mama ta kara haiyuwar mace, mama shuru tayi tana tunani Dan itama harga Allah Abun ya isheta tana bukatar abunda d’anta keso wannan karan ba zatayi shuru ha dole ma ya kara aure tunda ita kubra kwanta na mata ne, shafa kan Dan nata tayi tare da fadin kayi hakuri karka damu abunda za’ayi shine ka kara aure tunda ita mata take haifa tayiwu wacce zaka aura ta haifo maka d’a namiji alh Ibrahim yaji dadin shawaran mama Dan haka yace hakan zaiyi a dakin mama yayi sallah. 
Bayan gari Ya gama wayewa Ummi ta nufi dakin mama danta fada mata ta haiyu, Bayan ta shiga ta Tarar da mama ita da d’anta Alh Ibrahim kenan Bayan ta shiga duka suka 
tamke fuska, ummi fuskanta dauke da fara’a ta gaida mama, amsawa mama tayi ciki ciki, hakan bai dami ummi ba dan Koba a fada ba yanzu tasan sun San ta haiyu tunda basu ga cikin ba kuma gashi sun canza fuska, shiko mijin nata kin amsa mata gaisuwa yayi, cikin murya irin na mai son yin kuka tace mama na sauka lafiya an sami ma …… Alh Ibrahim ya Katseta mace koh ai dama ke baki da rabon haiyuwan d’a namiji dan haka zan kara aure zan kawo mai haifar min d’a namiji, kukan da take kokarin Karya fito shine ya fito mata, ba tare da tace komai ha, ta tashi tayi dakinta tana kukanta,jin kukan jaririyan yasa ta tsagaita da nata kukan daukanta tayi ta bata nono tasha, haka ummi taci gaba da kula da yaranta wannan karan ma k0 rago bai siya ba dan kunnenta ta siyar ta siya rago amma yayi ma y’ar huduba da zainab, batai taron suna ba dan tasan ma babu halin yi, gaba daya ya daina kula ummi ya fita harkanta ko magana bata hadasu yanzu sai kace itace take bashi y’ay’a matan ba Allah ba. 
Ummi tayi arba’in tana kula da y’ay’anta Sosai yanda ya kamata duk da ba komai take iya musu ba dan bata da mai bata tallafi amma dai yana biya ma zarah da aysha kudin makaranta, yau ummi na kwance a dakinta ita daya dan dama ita daya take kwana sai zainab dake gefe itama akan nata gadon, saiga Alh Ibrahim ya shigo kaman daka sama, zama yayi kusa da ita tare dayin gyaran murya ya fara magana kaman haka kubra tashi tayi dan tasan magana ne mai muhimmanci tunda har Ya kira sunanta, yace zan sake baki dama amma a wannan Karon in ban sami abunda nake soba Toh Kar kiga laifi na, hawaye neya zubo mata tana son magana amma ta kasayi dan takaici jin tayi shuru yasa ya dauka ta yarda ne wanda hakan ya bashi daman damuwa da ita, tun daka ranan ya Dan sake mata amma yaranta Sam baya wasa dasu yanda kukasan yan riqo wanda baya son riqonsu haka yake shida yaran nashi babu wani kulawa kullum fuskanshi a daure Indai yaran na wajan ganin yanda yake hantaransu yasa in yana gidan zarah da yake tayi wayau sai ta dinga jan kannenta daki suna wasa dan dai kawai ta dauke musu hankali dan Kar su shiga falo ya dinga hantarar su. Ummi gaba daya tana jin canje canje a jikinta ga yawan kasala da amai hakan yasa ta gane tana dauke da ciki ne amma kuma Abun mamaki duk cikin da tayi baya bata laulayi irin haka ganin haka yasa take ta roqan Allah akan yasa namiji zata haifa dan tana jin canji Sosai ba kaman cikin da tayi baya ba, shima Alh Ibrahim ya Lura da hakan wanda yake ganin wannan Karon namiji zata haifa tunda yaga ta canza Sosai ba irin sauran cikin ba, gashi wannan Karon ta rame tayi baki kaman wacce tayi shekara da shekaru tana ciwo haka ta koma, Alh Ibrahim yana tausaya mata domin Ya riga ya gama yarda namiji zata haifar mai wannan Karon wani irin kulawa yake bata 
na musamman wannan Karon harda yaranta yake kulawa ummi najin dadi har cikin ranta  wanda kullum tana roqan Allah akan yasa ta haifi namiji dan farin cikin da take ciki a yanzu ya dauwama, a kwana a tashi babu wuya a wajan Allah cikin ummi ya shiga watan haiyuwa wanda wannan karan cikin baiyi wani girma ba kaman sauran cikin da tayi a baya ba, suna zaune suna hira ita da mama a falo ummi ta saki kara mai karfi wanda yasa mama ta nufeta da sauri dan bata taimakon gaggawa, kamata tayi dakyar dan mama jiki ba kwari haka suka karasa mota inda driver yaja sukai asibiti, suna zuwa akai labour room da ita wannan karan tayi doguwar na’kuda jin shuru yasa mama ta ari wayar driver ta kira danta ta fada mishi suna asibiti bai bata lokaci ba yazo, koda yazo shuru kake ji Dr ne Ya fito yace su sameshi oflice binshi sukai a baya Bayan sun shiga Alh Ibrahim yace Dr maike faruwa? Dr yace gskiya akwai matsala operation za muyi mata sannan dole zamu cire mata mahaifa dan Idan ta kara daukan ciki zata iya rasa ranta, Dan haka muna bukatar signing dinka Kafin muyi mata aikin, Alh Ibrahim da zufa yake ta keto mai bai San sanda yace a bashi takardan ba, Dr Ya bashi yayi sighing sannan ya fita dan ayi mata aikin …….. 
Toh masu karatu muje zuwa muga ya aikin zai kasance sannan wannan Karon Alh Ibrahim zai samu abunda yake bukata 
Post yayi kadan 🙏 haquri zamu Kara gobe

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]