[Advertisements⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 21 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA
CHAPTER 21
Washe gari kaman yanda rahma tace hakan koh ya faru ta tafi ganin mutumin a garin Kano, bata wani sha wahala ba wajan gane company dinshi tunda sananne ne, tana tafiya tana kallon girman company din, tace mutum Mai wannan dukiyar maiya bashi sha’awa wajan yin wani hotel da plaza a kauye, office dinshi ta tambaya inda aka nuna mata, koda ta bud’e kofar taji a rufe, wajan wasu ma’aikatan wajan ta nufa, tace dan Allah Ina son ganin alh Mahmud, matar dake zaune tace ya baki appointment ne? Tace a’a, matar tace toh zaki iya zama a can, zama tayi tana jira har wajan awa d’aya taji shuru, tashi tayi ta kuma nufa wajan matar tace naji har yanzu shuru, matar tace ina zuwa, waya tayi ban San mai ake fad’a mata ba naji tace OK tare da kashe wayan, kallon rahma tayi tace baiwar Allah kiyi hakuri yau bazai zo office ba rahma tace dan Allah ki taimaka Ina son ganinshi cikin gaggawa, nazo mishi da magana Mai muhimmanci ne, shuru matar tayi ganin yanda rahma ke ro’kanta yasa ta fad’a mata address din gidan gonanshi, amma saida matar ta gargad’eta akan Karta ce itace ta bata address din, rahma taita Mata godiya sannan ta wuce, direct inda aka fad’a mata yahau tace Mai mota ya kaita, koda ta karasa dakyar suka barta ta shiga, bayan ta shiga katon gidan gonar da yake da gefe daban daban, can ta hango mutane a tsaye wani kuma yana can yana buga ball akan doki, tare da y’ar sanda, wajan ta nufa amma wani yayi saurin tsayar da ita, tace nazo ganin alh Mahmud ne, yace kunyi dashi zaki zo ne? Tace a’a amma ina son magana dashi Mai muhimmanci, yace OK saiki jira ya gama, tana nan tsaye awa d’aya biyu uku, shuru ta kalli mutumin tace dan Allah ka mishi magana ina bukatar ganinshi, mutumin yace Idan yana Abu ba’a tsayar dashi dan haka ki jira, haka taita tsayuwa ga rana ga gajiya, sauka taga yayi akan dokin a tunaninta ya gama kenan amma sai taga ya shiga wata karamar mota ana zagayawa dashi, a wani waje taga sun tsaya ta faki idon mutumin ta ruga da gudu tare da nufa wajan mutumin Shima binta ya bita tare da fad’in ta tsaya amma ina gudu take jin ihun da mutumin yake yasa ya janyo hankalin alh Mahmud, wajanshi ta nufa ta tsaya tana haki tare da fad’in dan Allah ka saurare ni tun dazu nake nan, waigowa yayi ya kalleta dukansu zare ido sukayi alaman sun San juna, shiya Fara magana yace maiya kawo ki? Mai kika zoyi nan? Ko yau ma maulan kika zo,? K0 kin biyoni har inda nake kici min mutunci ne? Maza ki f ……. Dakatar dashi tayi tare da fad’in dafarko ban San kaine alh Mahmud ba, saida na ganka amma Nayi takaicin daya kasance kaine, mutane suna ta fad’in kyawawan Abu a kanka Toh amma da nazo naga kaine saina shiga rud’u ,Mai yasa ka bige mata ka wuce ba tare daka tsaya ba? Amma kuma ta wani gefen saina Lura kai d’an kasuwa ne, komai kakeyi kanayi ne dan kaci riba haka mutanen da kake taimako Suma sai sunma Abu kake mu ….. Dakatar da ita yayi tare da fad’in tunda kin fahimci haka tafi kibar nan, bana bukatarjin komai daka gareki, koda yake Mai ya kawo ki mai kike nema? Tace nazo tun daka Jigawa in ganka domin akwai wata makaranta da kake son rushewa nazo akan makarantar ne, in kana son gina hotel ka nemi wani waje, karka rushe ma yara karatun su, ko sau d’aya ne kayi abun kirki ba tare daka samu riba ba, dan Allah na ro’keka ….. D’aga mata hannu yayi tare da fadin wannan hotel din da zan bude a nan Nayi niya kuma a nan zan budeshi, tace munada takardan cewa fllin namu ne, murmushi yayi tare da fad’in gwara ku ‘kona takardan domin kuwa fili a wajan gwamnati na siya kunga baku da takardan da zaku nuna kuce naku ne, infact ma ba zaku iyaja da gwamnati ba, yana fad’in haka yace ma security dinshi muje,tareshi tayi tare da fad’in hakane bazamu iyaja da gwamnati ba, amma muna da shaida kuma muna da gaskiya dan haka mu zuba saina nuna maka Mai gaskiya baya fad’i, Tana fad’in haka tayi gaba abunta da ido ya bita ranshi na mishi zan 
Magajiya duk wani labe tayi danta gane koh zarah munafurci takeyi amma bata ganoba, su zainab na kasa suna aiki, Aneesa na zaune tana yanke kumba tana tsaki, zarah ta fito tace Aneesa lafiya kuwa? Aneesa tace zarah kumba na nake son gyarawa amma ina tsoro Kar in yanke, k0 zaki min? Su zainab suna kallon suji Mai zarah zata cema aneesa domin dai Sun san itace babba ta girmi mijinta amma ga mamakinsu sai sukaji tace 0K kawo in miki, dukansu cikin takaici sukaci gaba da aiki, zarah kam ta gyarama Aneesa kafa da hannu, Aneesa Tana kallon yanda su aysha sukeyi ita kam sai murmushi takeyi dan dama da biyu tayi ta nuna musu ko yayarsu bata isa ba, bayan ta gama ta kalli Aneesa tace wow kafar tayi kyau gaskiya, yau faruk zai rud’e, dariya Aneesa tayi Sosai domin farida na wajan dan dai kawai taba farida haushi, bayan ta gama dariya tace zarah kawai saboda nayi gyaran kafa shine zan rud‘a faruk? Zarah tace kwarai kuwa, Aneesa ai kina da kyau Wanda duk Wanda ya kalleki zaki rud’a shi, aneesa dariya ta kuma saki, dai dai lokacin magajiya tazo tana fad’in lafiya kuwa Aneesa? Aneesa tace ina flra nida zarah ne kin San zarah akwai fad’in gaskiya, magajiya tace hakane kin San tana da hankali, Aneesa tace hakane, tace magajiya ki bud’e ma zarah d’akinta ta koma tunda ita Tana kauna ta, zarah cikin fara’a tace Kai Aneesa nagode Daka ke babu Kari faruk naki ne ke d’aya, dariya Ta kuma saki cikin jin dad’i, su zainab kam babu komai a ransu sai tsanar zarah yanzu domin. Rahma ta koma Gida ta fad’ama Haulat yanda sukayi, Haulat tace rahma kaman yanda Ya fad’a miki babu yanda za muyi dole mu basu wannan wajan dan bazamu iya Jada gwamnati ba, rahma shuru tayi ba tare data ce komai ba, Haulat tace rahma Ina takaicin wannan abun wannan filin mahaiflna da kudinsa ya siya ya gina gidan shi da mahaifiyarmu tana bashi kasa yana daurawa, yau gashi za’a rushe, bazan iya juran hakan ba’
MIYE ILLAR Y’AY’A MATA‘ 
 rahma tace 
Haulat Nayi miki alkawarin bazan bari a rushe ba duk yanda zanyi sai Nayi dan abar wajan nan a inda yake, domin Kar a rushe ma yara karatu, dan shuru tayi sannan tace alh Mahmud baka da tausayi kai neman kud’i kawai kasa a gaba, amma zan nuna maka. 
Aneesa ce zaune a d’aki, zarah ta shigo mata da snack da drinks ta ajiye mata shi, Aneesa cikin murmushi tace sannu zarah, zarah itama murmushin tayi tare da fad’in in zuba miki drinks dinne? Aneesa tace eh zubamin amma kad’an, zuba mata tayi tare da mi’ka mata, Aneesa sha tayi tare da ajiyewa, zarah cikin murmushi tace Aneesa nikam in baki shawara mana, aneesa tace inaji zarah fad’amin, Zarah tace Aneesa ya kamata ki nutsu ki duba abunda zan fad’a miki, aneesa gaba d’aya hankalinta ya nutsu wajan zarah, tace Kinga yanzu farida nada ciki Idan ta haiyu dukiyar da faruk ya mallaka Kinga da sunanshi ne inaga ya kamata kisa ya dawo da dukiyar ta d’anki ko kuma naki, Aneesa shuru tayi tana nazari, ganin haka yasa zarah tace kiyi tunani a Kai, suna cikin haka magajiya ta shigo ganin magajiya ta shigo yasa zarah tabar d’akin tare da labewa jikin window dan taji Mai zasu ce, magajiya tace ya naga zarah na shige miki ne? Aneesa tace ai tafi min ke, tunda baki bani shawaran da take bani, magajiya tace Aneesa kina nufin zarah ta fini yanzu a Wajanki? Aneesa tace eh kusan haka ne, magajiya tace ok babu damuwa, fita tayi fuuuu zarah dake labe ganin zata fito yasa tabar wajan,cikin murna,. Aneesa da magajiya yanzu fad’a suke Sosai zarah da Amina sun had‘e kai, suke had‘asu fad’a, akwai wani sarka da Aneesa ta siya magajiya ce kadai tasan da sarkan, Aneesa ta nemi sarkan ta rasa, ta kira kowa dake gidan tace su fito mata da sarka, kowa yana ta fad’in bashi ya dauka ba, zarah da Amina suka matsa kusa da Aneesa Amina tace haba Aneesa miye kike wani tada hankali? Aneesa tace mama Amina sarkan diamond ce fah, Amina tace karki damu aje a duba kayan kowa, aneesa tace hakane kowa ya tsaya inda yake ta kalli zarah tace zarah muje mu fara dubawa, an duba kayan kowa babu dawowa falo sukayi, Aneesa sai huci take, kallon magajiya tayi lokaci d’aya Aneesa tace zarah zo muje d‘akin magajiya domin ita d’aya tasan na siya sarkan, magajiya tace Aneesa mai kike nufi? Aneesa bata kulata ba sai haurawa da sukayi, d’akin magajiya suka shiga inda suka fara dubawa, aiko Aneesa tana bud’e wardrobe din magajiya sai gashi taga sarkan dai dai lokacin magajiya tashigo d’akin, aneesa tace magajiya yaushe kika Fara sata? Dama ke kikemin Kananan dauke dauke, nan Aneesa ta rufe ido taci ma magajiya mutunci a gaban kowa, magajiya harda kwalla dan ba‘kin ciki, koda daddare da akazo wajan cin abinci magajiya ta fito Aneesa ko kallonta batayi ba Bayan magajiya ta zauna tace a zuba mata abinci, ummi ta Fara zuba mata magajiya tace mai yasa kuke dafa taliya Bayan bana so? Aneesa tace ni nace su dafa domin gida nane nan bana wata ba, ran magajiya ya kuma baci zarah na zaune tana dan murmushi, tashi magajiya tayi tabar d’akin, zarah itama Bayan ta gama d’akin magajiya ta nufa Bayan ta shiga taga magajiya nata surutai, zarah tace sannu magajiya, magajiya tace yauwa, zarah tace gaskiya banji dad’in abunda Aneesa ta miki ba Wlh, ko kad’an, duk wani abu da take takama dashi duk da taimakonki take samu, Kece kika taimaketa shi yasa yanzu take da komai amma gashi yanzu Tana son juya miki baya ta tozartaki cikin mutane ta zubar miki da Kima, magajiya cikin fushi tace kyaleta zan rama nan bada dad’ewa ba, duk wani sirrinta yana wajena harda kisan alh I ……. Shuru magajiya tayi zarah tace me kika ce? Magajiya tace babu komai, zarah fita tayi amma gaba d’aya kanta ya kulle, kissan alh I.. To wa suka kashe, zarah zama tayi tana ta tunani lokaci d’aya tace kodai Abba suka kashe Kai ba haka bane, Toh Waye magajiya naga Tana turama kud’i duk wata? Kai koma Waye dole inyi bincike, Washe gari da safe zarah ta nufi police station, akan tana son a taso da bincike akan mutuwar mahaifinsu, amma tana son ayi Abun cikin sirri, tayi signing sannan police din yace kasheshi akayi amma za muyi bincike mu gano ko 
Waye, zarah gida ta dawo ranta a jagule. 
Su rahma na zaune, suna aiki saiga mutanan alh Mahmud Sun zo suna duba gidan, rahma da gudu ta tashi ta nufesu tare da taresu tace maiya kawo ku? Wani daka cikinsu yace Munzo duba wajan ne sannan mu baku takardan notice nan da wata uku Kubar wajan nan dan za’a fara aiki, mikama rahma takardan akayi ta amsa tare da fad’in kuje ku fadama Mai gidanku bazamu tashi ba karya sake ya kara turoku nan, tafiya sukayi koda suka koma suka fad‘ama Alh Mahmud yanda sukai da rahma, ranshi a bace yace wacece ita? Babu wanda ya isa ya hanani wannan ginin dan haka gobe ku koma kuce mata na basu nan da sati d’aya subar wajan, suka amsa da Toh, kaman yanda ya fad’a hakan sukayi suka koma, suka fad’a mata abunda yace suka wuce, Washe gari da safe rahma ta nufi Kano direct office dinshi ta shiga budewa tayi taga suna meeting amma bai hanata ta koma ba shiga tayi cikin masifa tace Mahmud karaye dan kasuwa na Africa yaro dan shekara 33, nunashi tayi da yatsa tace Mai kakeji dashi kud’i iko, baka tausayin yara, Mai yasa kake son rushe musu karatu? Anya kana da imani kuwa, kauyen da makaranta biyu ne na primary babu ko secondary school a nan ne kake son bud’e hotel da Plaza, Mai makon kayi abun kirki da kud’in da Allah ya baka ka bude secondary school a kauyen yanda yara zasu sami karatun boko amma kai kana burin bud’e hotel kai Anya Kai mutum ne mai tunani, ko sau d’aya Kayi tunani akan ilimin yaran da suke zuwa makarantar, dan Allah kayi tunani duk da Nasan ba lallai bane kayi tunanin dan baka da lokacin tunani akan abunda kake gani kaman shirme ne a wajanka kai d’an kasuwa ne kullum tunaninka akan yanda zaka samu riba kakeyi, kallon wanda suke zaune tayi tace dan Allah ku dinga bashi shawaran kwarai tana gama fad’in haka tabar office din, bayan ta fita ya lumshe ido meeting din aka fara amma baya jin komai sai maganan rahma yake ta mishi yawo daka karshe dai d’aga meeting din akayi, Washe gari alh Mahmud da kanshi ya nufi kauyen da safe shida masu bashi tsaro, koda yaje yaga yara na karatu basu fi mutum ishirin ba, Haulat jin tsayuwan motoci yasa ta fito itama rahma fitowa tayi kanta k0 dankwali babu dan yanda taga Haulat ta fita ganin alh Mahmud da mutanan shi yasa ta koma da sauri ta yafo Gyale, nufanshi tayi tare da fad’in maiya kawo kanan? Murmushi yayi yace nida Fili na in Zanzo sai an tambaye ni maiya kawo ni, kallon yaran yayi yace yaran da basu fl Goma shaba kike fad’in ana koyar dasu, har kike fad’in za’a rushe musu gurbin karatu, maganan ki gaskiya ne ni d’an kasuwa ne ban San komai ba sai yanda zanci riba, dan haka za muyi wani yarjejeni Wanda shine na farko da zanyi abun, na baki nan da wata d’aya ki tara yara sukai d’ari Indai suka Kai d’ari zan bar muku wajan in kuma basu Kai ba zaku tashi, d’an shuru rahma tayi tana tunani can tace shikenan mun yarda, yace good Ina miki fatan Sa’a yana fad’in haka ya wuce, Haulat tace rahma mai yasa kika yarda Bayan kin San kauyen nan ba kowa yake kai yaranshi makaranta ba? Rahma 
tace karki damu Haulat insha Allah zamu bashi mamaki …… Hmmm muje zuwa 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]