[Advertisements⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 16 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA
CHAPTER 16
Faruk tuki yake yana tunanin mai zai fad’ama Abba Idan akaje banki akaga bai sa kud’i ba, haka yaita tunani harya karasa gida, koda ya shiga gidan d’akinshi ya nufa inda Ya sami farida zaune ta zabga uban tagumi, kallo d’aya ya mata yaga ta rame tayi d’an duhu, abunda yake kanshi a halin yanzu yafi karfinshi dan haka ba tare da tambaya ba ya sami waje ya zauna, ganin ya zauna yasa ta nufeshi tare da kiran sunanshi tace faruk na maka wani laifi ne? Dan Allah Idan Nayi maka laifl kayi hakuri Wlh rashin bani lokacinka yana sakani shiga cikin wani hali, faruk ko dan ban haihu bane har yanzu yasa kake canza min? Kallonta yayi sannan yace farida plz ina bukatar hutu yanzu bana son damuwa, jin haka yasa wani hawaye Mai zafl ya zubo mata da sauri takai hannu zata goge dan karya gani, amma ya riga ya gani da sauri ya tashi tare da riqe hannun nata yasa nashi ya goge mata, yace farida bakimin komai ba, kawai Ina damuwa ne akan yarona shi yasa gashi Abba yasa yayi nisa dani, farida tace abunda Aneesa tayi shi yasa Abba ya koreta amma insha Allah komai zai daidaita, yace Ina fatan haka, farida zama tayi tana tunani tare da ro’kan Allah akan ya bata ciki itama,. 
Alh Ibrahim ya tura aje a ciro kud’i akace babu kud’i, Abubakar ya kira yace yaba faruk yakai, koda alh Ibrahim ya tambayi faruk kasa magana yayi saida yaga alh Ibrahim yayi fushi Sosai sannan ya fara bashi hakuri tare da fad’a mishi Abun da yayi da kud’in, ran alh Ibrahim ya baci Sosai inda yace a ina ya siyan musu gidan? Fad’a mishi yayi, ranan alh Ibrahim daka office direct gidan ya nufa inda Ya samesu ita da magajiya suna fira, basu ga shigowanshi ba sai ganin shi sukai da yaro, da sauri suka tashi ya kalli Aneesa yace saboda wannan yaron kike bata ma d’ana tunani, toh daka yau zai koma gidana Aneesa kasa magana tayi har Alh Ibrahim Ya fita, sai a sannan ta bishi da gudu amma kafin ta karasa ya shiga mota ya tafi, ihu ta saki tare da komawa gidan da gudu ta dauki wayanta ta kira faruk amma bai d’auka ba haka taita kiranshi bai dauka ba,jifa tayi da wayan, alh Ibrahim gida ya nufa da yaron kowa tashi yayi yana kallonsa domin abun ya basu mamaki,kwala ma faruk kira yayi wanda yasa ya fito da sauri shima ganin yaron yasa mamaki ya kamashi, alh Ibrahim mi’ka Mai yaron yayi yace saboda d’anka kuma jikana kake mu’amala da Aneesa har take kokarin canzaka Toh gashi nan daka yau ya dawo nan kenan, sannan tana kokarin ta nuna kaiba d’ana bane inna mutu baka da gado, bari kaji tun ranan da naji kuna magana harna koreta duka dukiyata Nayi signing ya koma naka dan nasan ko Bayan Raina zaka ri’ke iyalina, kuka faruk ya fara yana bashi hakuri akan ya yafe mishi, alh Ibrahim yace babu komai, daukan yaron yayi yai sama dashi dan yakai ma Farida sannan ya kira Aneesa mama ta kalli alh Ibrahim tace Anya abunda kayi kana ganin shine dai dai kuwa? Alh Ibrahim yace name mama? Tace Taya zaka mallaka mishi dukiyarka duka yaranka fah, murmushi yayi tare da fad’in mama ina sane dasu ban manta dasu ba, mama Ina son y’ay‘a na Sosai yanda bakya zato bazan taba yi musu abunda zai cutar dasu ba, na tabbata koda Bayan raina faruk zai kula dasu Sosai bazai Bari susha wahalan rayuwa ba, mama tace toh Allah ya taimaka ya amsa da Ameen tare da tashi ya haura sama, koda faruk ya haura yaga misscall din Aneesa da yawa kiranta yayi ta dauka cikin kuka take mishi 
bayani hakuri yaita bata akan gobe zai kawo mata yaron tare da fad’a mata kyautar da alh 
Ibrahim yayi mishi inya mutu, sallama sukai akan gobe zai zo. 
Washe gari kaman yanda faruk ya fad’a haka Ya shirya shida yaron ya fita, alh Ibrahim da tun jiya yaji wayan da yakeyi yasa ya bishi a baya, wani waje ya nufa inda ake Gina gada amma ba’a gama ba motoci basa bi, a nan suka had’u da Aneesa da magajiya inda Ya bata yaron tana ta murna ganin alh Ibrahim ne yasa duka sukai shock, domin basu zata ba, alh Ibrahim yace faruk ban zaci haka daka gareka ba Banyi zaton zaka bijire ma magana taba, tun jiya da naji kana waya na canza ra’ayi na a kanka na fasa mallaka …… Faruk yace abba kayi hakuri tare da matsowa kusa dashi yana zuwa alh Ibrahim ya wankeshi da Mari alh Ibrahim yana kokarin matsawa aiko ya fad’a amma Allah ya soshi ya riqe wani karfe magajiya da Aneesa suka saki baki faruk da sauri ya riqeshi yana kokarin ya janyoshi amma ina ya kasa alh Ibrahim ya fad’o daka katuwar gada Mai nisa Sosai, faruk kuka ya saki Aneesa tace faruk ka kashe mahaifinka da kanka zo mubar nan wajan, faruk babu abunda yake sai kuka ya 
kasa k0 motsi dakyar Aneesa taja shi suka bar wajan cikin sauri… 
Iyalan Alh Ibrahim ne zaune sunyi jigum domin har yanzu bai dawo gida ba, gashi number dinshi Anata kira anki dauka wasa wasa har dare ya farayi hankalin kowa ya tashi domin baya Kai irin wannan lokacin a zaune, Abubakar ne yace bari yaje ya Sanar da police yanda ake ciki, hakan k0 akayi suka tafl harda zarah da khairat,koda ya Sanar ma police sunce za suyi bincike duk yanda ake ciki zasu jisu, hakan koh akayi, suka dawo gida, wasa wasa har gari ya Waye shuru babu alh Ibrahim babu labarinshi faruk kam tunda Aneesa taja shi sukai gidanta duk ya tsorata musamman da tace shine ya kashe mahaiflnshi, amma daka baya ta Fara kwantar Mai da hankali tare da fad’in ita Tana sonshi zata rufa Mai asiri, sannan tace Mai dad’i ya kamata kaji tunda Alh Ibrahim ya mallaka maka duka dukiyarsa Kaga yanzu komai naka ne tunda Nasan ya dade da taflya rami yanzu, haka taita fad’a Mai magana wanda yasa yaji d’an sanyi sanyi harya bashi karfln giwan komawa gida, kuma koda yaje har lokacin ba’a ga alh Ibrahim ba. 
Washe gari da sassafe police suka zo gidan, da mummunan labari, domin sun tsinci gawan alh Ibrahim a kasan gada, wanda suka tabbata daya fad’o ne akan gadan, gaba d’aya iyalan gidan kowa Ya girgiza da sukaji alh Ibrahim ya rasu, mama fad’i take mutuwa mai yasa zaki min haka ni ya kamata ki d‘auka ba d’ana ba haba mutuwa mai yasa kika Fara daukanshi lokaci d’aya kuma ta saki kuka, police sunyi bincike akan gawan alh Ibrahim inda suka mi’ka musu gawan Bayan sun gama aka mishi wanka aka kaishi gidansa na gaskiya, tunda aka Sanar da Labarin mutuwar alh Ibrahim Aneesa da magajiya suka dawo gidan da zama da Sunan sun zo gaisuwa, da yake mutuwar na cinsu babu wanda ya iya magana dan mutuwar mahaiflnsu yafi komai d’aga musu hankali, faruk kam kaman yafi kowa shiga damuwa, police sun dawo sunce alh Ibrahim ba fadawa yayi da kansa ba, amma za suyi bincike, faruk yace miye amfanin binciken tunda wanda ya mutu ba dawowa zaiyi ba, mama tace hakane koma Waye ya aikata sun barshi da Allah, haka akaita zaman makoki, ranan da alh Ibrahim yayi kwana bakwai da rasuwa aka tara duka iyalanshi domin barrister dinshi yazo ya fad’a abubuwan daya bayar ga magada, kowa ya hallara a falon ciki harda su Aneesa, inda barrister ya fara magana kaman haka alh Ibrahim ya mallaki dukiya kadarori company da gidanshi da yake ciki, alh Ibrahim yace inya mutu a raba madaran kud’i daya Bari kashi biyar aba hindu kashi d’aya mama kashi d’aya hindu kuka ta Fara Sosai tare dayi ma d’an uwanta addu’a faruk da Aneesa kuma suna zaune suna son jin na faruk din sai murmushi sukeyi, barrister yaci gaba da fad’in sannan aba amina kashi d’aya, kashi d’aya aba ummi itama, kashi d’ayan kuma daya rage a raba shi kashi biyu d’aya yaranshi mata su raba su biyar d’ayan kashin kuma Abubakar mijin zarah ya d‘auka, sannan company dinshi da gidansa faruk wani irin murmushi ya sake amma Jin barrister yace ya mallaka ma y’ay’anshi mata Su biyar yasa faruk da Aneesa mamaki, zarah tace barrister Anya ka duba dakyau kuwa? Sunan faruk ya kamata ya zauna a wajan ba namu ba, barrister yace dai dai na duba abunda mahaifinku ya fad’a Shina rubuta, zainab tace bamu yarda da wannan rabon ba dole a bama faruk, barrister yace koda Kun yarda koda baku yarda ba babu abunda zaku iya domin koda kunce kuna son a muku rabon gado faruk bashi da gado dan 
haka gwara Kubar abunda mahaifinku ya baku zaifi, shuru sukai su duka barrister yayi 
musu sallama ya tafi, faruk tashi yayi ya nufi d’aki, yana shiga ya saki kuka, dama na sani karya kake min baka sona ka tsaneni baka kaunata alh Ibrahim Ka nuna niba d’anka bane kuka yake Sosai kaman ranshi zai fita Amina da tun Tashin shi ta biyoshi duk taji abunda yake fad’a hakuri ta Fara bashi akan alh yana sonshi ya dauka kaman shike da dukiyar nan tunda su zarah sun daukeshi matsayin d’an uwa, haka taita bashi baki amma shi ina bama 
jinta yake ba. 
Yau akai kwana arba’in din alh Ibrahim, faruk ne ya fito cikin riga da wando, zarah ta kalleshi tace office dinfa? Yace zarah daka yau Na daina zuwa office, Ummi tace akan wani dalili? Yace Ummi Abba ya barma su zarah company din nan, yana son su kula dashi da kansu shi yasa ya basu, naga gwara in bar musu, zainab tace faruk dan Abba ya bar mana company din nan bawai yana nufin mu zamu dinga zuwa ba, faruk yace tunda har Abba ya baku yana son kuje tunda yanzu baya nan Waye zai zauna matsayin shi kunga dole sai ku, zarah tayi murmushi tace shikenan munji zamu amma harda Kai dan haka sai kaje ka shirya domin kasan bamu San komai ba dole sai an tayamu zaiyi magana zarah tace Ashhhhh ya isa haka maza Jeka shirya, badan yaso ba Ya shirya suka tafi su duka matan dashi da Abubakar, suna zuwa company din ma’aikatan wajan suka taso cikin girmamawa suna taya su murnan Fara zuwa office, koda suka shiga office din mahaifinsu jikinsu yayi sanyi musamman da suka ga tankamemen hotan mahaifinsu, zainab ta Fara hawaye tare da fad’in Abba zamu ri’ke wannan company din da kyau ta yanda koda kana Raye za kayi alfahari, faruk yace Indai suna son ya dinga zuwa shima zai shiga cikin Sahun ma’aikata dai dai da kwalinsa hakan ko akayi aka bashi office din da bai Kai nashi ba, wata rana faruk yana ma wani ma’aikaci magana akan Mai yasa kullum yake zuwa latti nan ya fara gayama faruk magana ina ruwanka in nazo late kaima fa yanzu yanda nake haka kaima kake dan haka ka fita cikin hanyata, zarah najinsu, sai taji farukdin ya bata tausayi, gashi ran nan da tazo wucewa taji wasu ma’aikata na gulma akan yanzu mata ne ke shugabantan company din ba lallai bane su iya abunda namiji zaiyi ba, wanda tasan gaskiya suka fad’a dan aysha ta kusa komawa gidanta kuma sauran kannen nata aure za suyi bata san ko wani gari za’a kaisu ba lallai ya kamata a matsayinta na babba ta kula da company din dakyau. 
Faruk yanzu Ya rage magana in suna falo baya zama, Amina abun na damunta Sosai, dan haka ta yanke wani hukunci ba tare da shawaran kowa ba, su zarah na zaune cikin d‘akin khairat suna flra Amina ta shigo ta samesu, zama tayi itama tace fIran Mai akeyi haka? Aysha tace muna firan Abba ne rayuwa kenan, Amina tace nikam da zaku yarda da kunba faruk komai ya dinga kula dashi inaga hakan zaifl, zarah tace na fad’a mishi haka amma yaki yarda, Amina tace gaskiya ne bazai yarda ba inda zakuyi signing ku dawo mishi da 
komai ya zama nashi inaga zai yarda sannan zaku sami kulawa kaman mahaifinku na Raye, 
rahma tace mum gaskiya hKan bamai yiwuwa bane, Amina tace saboda me? Faruk yaja jikinshi daku da kuma kowa saboda yaga mahaifinku bai Bashi komai ba, Kuma ana gobe alh Ibrahim zai rasu yace yaba faruk duka dukiyarsa kunga inda bashi da niya bazai fad’a ba, zarah tace hakane zamu bashi komai ya kula dashi tashi tayi Jim kad’an sai gata da takarda da Biro tace ni nayi signing ko wacce tayi na amince da abunda Anty Amina ta fad’a, ta mi’ka ma kannen nata ko wacce tayi signing wanda dakyar rahma tayi …….. Ku biyoni yanzu Wasan ya fara ga dai dukiya ta dawo hannun faruk koya za’a kaya? 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]