MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 14

Advertisements

_____

MEYE ILLAR YAYA MATA
CHAPTER 14
Tace kar kiyi tunanln zan amshl wanI abu daka garekl, bazan taba amsan abu daga wajan wanda sukai sanadin mutuwar mijina ba, dan Allah karki kara shiga cikin wani al’amari n na ro’keki badan niba ….. Ummi ce ta daka mata tsawa tare da fadin miye haka zainab sa’arki ce!? Sannan ki daina wannan tunanin domin Amina bata da hannu wajan kashe miki miji, cikin kuka tace ummi itace ma take da hannu Sosai domin tasan komai tasan yayanta shine ya kashe min miji amma taki fad’a duk kuma saboda ita yayi, Amina tace zainab Wlh ban San saleh zai kashe yazeed ba ban taba tunanin haka ba dan Allah ki yafe min badan niba…. Da gudu zainab ta haura Sama Tana kuka Yan uwanta mata suka mara mata baya Am ma Kafin suje harta rufe kofar, haka suka barta. 
Amina jiki a sanyaye tabar wajan, alh Ibrahim zama yayi wanda kwana biyu baya cikin kwanciyan hankali, domin da tunanin y’arsa yake kwana yake tashi, mama ta kalleshi tace lafiya kuwa Ibrahim naga kayi shuru ka zabga tagumi, d’ago dakai yayi cikin damuwa sannan yace mata Wlh Ina nadaman abunda na aikata na tsanan y’ay’a mata ne duk wannar abunda su Amina da saleh suka aikata lefi nane, Harda halin da y’ata take ciki a yanzu, mama tace wace y’artaka? Yace mata yarinyar Amina bata mutu ba, mama tace kaman ya? Labarin abunda ya faru yaba ma mama da kuma ummi da hindu dake zaune, sai yaranshi mata dake sama suna kallonsu Suma duk sunji abunda ya faru, kowa ya girgiza da Abun da saleh yayi ma yar kanwarsu daya kaita gidan karuwai , mama tace ya kamata muje mu dawo da ita gida sannan shi kuma saleh tunda yana hannun hukuma zasu hukuntashi dai dai da abunda yayi …… Muryan zainab sukaji Tana fad‘in nasa a sakeshi domin bana son hukuma ta hukuntashi nafi son Allah ya hukuntashi yanzu haka zanje inyi signing ne na rufe case din, alh Ibrahim yace zainab kin san abunda kike fad’a kuwa? Tace eh na sani Abba, alh Ibrahim yace karki kuskura ki fara sakawa a sako shi, ki bari a hukunta shi, tace Abba duk hukuncin da za’a ma saleh Wlh bazai sa in daina jin ciwon abunda yayi min ba, dan Allah Abba ka barni inje inyi signing nafi son Allah ya hukunta shi, Abba shuru yayi can yace muje tare, haka suka tafi ita da alh Ibrahim har police station inda tayi signing aka rufe case din tare da sakin saleh. Alh Ibrahim da mama dasu khairat da zarah sai ummi da Amina suka shirya domin zuwa dawo da y’ar amina Mai suna rahma, zainab dai tana gida ita da Anty hindu da aysha, koda su alh Ibrahim suka je garin a waje suka ganta Tana shan Fanta ga wasu maza nan a zagaye da ita suna ta manna mata kudi, Amina kuka ta Fara tare da fadin saleh ya cuceta ya bata mata rayuwa rahma dake zaune ta hango alh Ibrahim da sauri ta tashi ta nufeshi tana fadin au ka dawo ne, kallon su mama tayi da suke ta kallonta, ga Amina dake ta faman rusgan kuka, ummi ce ta matsa kusa da ita tace dan AIIah muna son muyi magana, kallon ummi tayi wacce tayi mata kwarjini tace muje cikin gidan suka shiga inda maza da mata keta shaye shaye, wani d’aki suka shiga suka zauna, ummi tace da Farko dai Kinga 
mahaifinki nan ta nuna alh Ibrahim sannan ga mahaiflyarki ta nuna mata amina dake ta faman risgan kuka, kallon Amina tayi na wajan minti biyu sannan tace bani da iyaye domin kuwa inda inada iyaye bazasu taba kawo ni nan ba dan haka ku tashi kuje kawai, zarah tace babu inda zamu sai tare dake, domin ba zamu ci gaba da kallonki cikin wannan rayuwan ba dan haka kizo mu koma Gida tare, rahma tace babu inda zani na fad’a muku banda iyaye ban da iyaye muryan saleh sukaji yana fad’in sune iyayenki, kowa waigowa yayi yana kallonsa, yace rahma nine najefaki cikin wannan halin Labarin abunda Ya faru ya bata, rahma kuka ta farayi tare da fad’in Kun cuceni Kun bata min rayuwa, kallon Amina tayi tace ban zaci koda a mafarki uwa zata ma yarta haka ba dan kawai miji baya bukatar y’a mace, Amina tace dan Allah ki yafe min Wlh kullum da tunaninki nake kwana nake tashi Wlh Ina sonki, zarah tace sis kiyi hakuri kizo mu koma Gida tare domin can ne yafi dacewa dake ba wannan kazamin wajan ba, alh Ibrahim ya kamo hannun rahma yana hawaye yace duk laifi nane dana nuna kyamata akan y’ay’a mata , na manta Allah shine mai badawa kuma Mai hanawa, duk son d’a namiji na sai gashi Allah ya nuna min ban isa ba sai ya bani y’ay’a mata har biyar, ki yafe min rahma, cikin kuka ta Fara kokarin yin magana amma ta kasa bakinta sai rawa yake alh Ibrahim ya janyota jikinshi ya rungume y’ar tasa yana kuka saida ta nutsu sannan tace lnajin kunyan abunda na aikata ranan daka Fara gani na Abba dan Allah ka yafe min yace babu komai yanzu mu tafi Gida tace bari ta dauko kayanta, alh Ibrahim yace sam baya bukatar ta dauki wani abu daya cikin wannan gida haka suka flta, sale ya matsa kusa da alh Ibrahim yana fadin nagode da kasa aka sakeni Ina son kamin izin 
in zauna daku cikin gidanka ……. 
Alh Ibrahim wani kallo yamai Mai kama da inda inada hali dana kashe ka, saleh duk da irin kallon da alh Ibrahim yamai bai hana yaci gaba da fad’in abunda yake son fad’i ba, yace saboda ni gashi yanzu rahma zata koma Gida, kuma nayi nadaman abunda na aikat…. Alh Ibrahim ya dakatar dashi da fadin ya isa haka ya isa nace, Bari kaji in fad‘a maka daka yau karka bari in sake ganinka ko kuma Layin gidana ko wajan iyalina inko ka Bari hakan ta faru saina sa an daureka, mara mutunci ko yanzu da Kaga an fito dakai zainab ce taso hakan amma ka guji sanda zaka kara aikata min wani laifi mara mutunci yana fad’in haka Ya shige mota su mama dama sun dad‘e da shiga, driver ya tada suka wuce gida, koda suka isa Gida a falo suka Tarar dasu zainab kallo daya aysha tama rahma tace sis domin kamanta d’aya dana mamanta, zainab tashi tayi ta nufeta tare dayin hugging dinta tace Barka da dawowa sis, dariya rahma tayi cikinjin dad’i tace nagode, rahma sai kallon gidan take lallai mahaifinta Mai kudi ne jiba wannan katotan gidan Wanda sai a India ko saudiya ake wannan manya manyan gidajan amma yau gashi gidan mahaifinta babba, zama sukai Anata flra inda itama rahma aka ware mata nata d’akin. 
Yau Aneesa ta tashi dana kud‘a, wanda tun asuba take ta faman nishi, magajiya ganin Abun yaki cinyewa yasa ta nufi d’akin faruk taita bugawa farida ce ta tashi ta bude, magajiya tace kira faruk yazo yakai Aneesa asibiti zata haiyu, da sauri farida ta koma ta taso faruk wanda ya fito cikin sauri tare suka nufi d’akin Aneesa din daukanta faruk yayi sukai kasa ummi jin hayaniya yasa ta fito taga abunda ke faruwa da sauri ta koma tasa hijab ta fito suka tafi asibitin tare suna zuwa akai labour room da ita, bata wani dad’e ba ta tsintilo d’anta namiji santalele kyakyawa dashi, koda Dr ya fito ya musu albishir faruk sai murna yake yana jin dadi, da aka bada izinin shiga shine na farkon shiga ya dauki baby din yana juya shi yana fad’in dani yake kama, farida ta matsa kusa dashi tana kallon baby din gwanin sha’awa sai taji dama d’anta ne, magajiya ce ta amshi baby din dan taga yana kokarin bama farida, ganin haka yasa farida ta koma baya ummi ta amshi yaron wajan magajiya Tana fad’in Kai tubarkallah yaron kyakyawa, ummi ta kalli faruk tace ya kamata ka kira gida ka fad’a musu, yace Kai Wlh nabar wayana a gida, Shigowan Dr ne yasa ummi ta nemi ya bata Aron waya dan ta kira, number din mijinta ta kira ya dauka yana jin muryanta yace Ina kika shiga tun dazu muna nan hankali tashe, tace kwantar da hankalinka muna asibiti Aneesa ta haiyu cikin fara’a yace Alhmdlh Mai aka samu? Tace d’a namiji yace Kai Barka Bari in fad’a masu Amina, yana kashe wayan ya fara Sanar dasu, murna suka fara su duka daka nan kuma aka had‘a abinci aka nufi asibitin dashi, sai daukan yaron suke tayi suna fad’in yaron kyakyawa, Aneesa dake kwance tana kallonsu tace duk ku gama ni Nasan maina shirya muku da yamma aka sallameta sukai gida. Aneesa tunda suka koma Amina take bata wani kulawa na musamman, yaron kowa na sonshi, farida ganin haka yasa itama ta shiga damuwa taji tana son ta haiyu gashi ko bari bata taba yiba, faruk tunda akai haiyuwar bini bini yana d’akin Aneesa, bashi ma da lokacin farida Sosai haka dai akai suna wanda alh Ibrahim ya kashe naira domin yayi hakan ne dan 
Kar faruk din yaga an canza Mai danshi alh Ibrahim har gobe a matsayin d’a ya dauki faruk alh Ibrahim yayi ma yaro huduba da Muhammad sai suke cemai Anan. 
Tunda Aneesa ta haifi d’anta take sa faruk yake mata abubuwa masu yawa tun yanayi mata dai dai karfinshi harya Fara gajiya, alh Ibrahim harya Lura da kwana biyun nan yanda faruk yake kashe kudi masu yawa dan haka yasa aka canza mishi pin dinshi, koda faruk yaje ciran kudi yaga yasa pin kuma dai dai aka cemai incorrect pin ya kara sawa ATM din ya makale ya dai gane abba yasa an canza pin, ga Aneesa taita damunshi ya mata Abu gashi bashi da kud’i, da dai ya gaji ya fito ya fad’a mata abunda ke faruwa tace inda dane Kafin ya gane kaiba dansa bane ai bai taba Canzawa ba sai yanzu dan kawai Kai ba dansa bane Wlh kasan abunda zaka tatsa tun Kafin dare yayi maka Inba haka ba zaka tashi tutar babu domin yau yana mutuwa baka da gado alh Ibrahim da yazo wucewa yaji tana maganar d’akin ya shigo yace ta tattara nan da minti biyar tabar Mai gida inko ba haka ba saina lahira ya fita jin dad’i mutuniyar banza kawai kina son ki canza ma d’ana tunani faruk har gobe dai dai yake da Yaran dana haifa yana fadin haka ya fita, magajiya kam ba’kin ciki ne fal cikinta tunda taji ance subar gidan faruk shima fita yayi Aneesa ta Fara had’a kaya dan barin gidan …….. 

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 21

Advertisements _____ MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 21 Washe gari kaman yanda rahma tace hakan …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *