[Advertisements⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 13 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA
CHAPTER 13
Amina tace ta mutu? Lokaci d’aya kuma tayi murmushi tare da fadin ban yarda ba inaji a jikina y’ata bata mutu ba, alh Ibrahim shuru yayi yana mai jin radadi a zuciyarshi, bai kara cewa komai ba sai d’aki daya wuce, shima Abubakar ciki ya shiga danya huta, Amina tana ganin ya shiga ciki ta fita direct inda ake tsaron saleh ta nufa inda ta sameshi a zaune, yana hangota ya tashi tsaye tare da fadin maiya kawo ki? Tace saleh ka cuceni ka gama dani dama y’ata dana haifa ta rasu shine baka fadamin ba? Yace mene? lnjiwa? Waya fad’a miki? Tace Alh Ibrahim dakanshi yaje nemanta, dariya saleh ya saki tare da fadin ai dama na sani, Toh Bari kiji y’arki tana Raye bata mutu ba, tunda na dauketa Tana jaririya na kaita gidan karuwai anan ta girma babu arabi babu boko sai karuwanci kawai take zubawa, sha’ko Mai wuya tayi tana fadin saina kashe ka Wlh ka cuceni saleh ka gama dani saleh kokari yake ya kwaci kanshi daka shakan da tamai amma ya kasa dan ba shakan wasa tamai ba, ihu take Tana fadin Wlh saina kashe ka kaci amanata police ne suka zo da sauri tare da alh Ibrahim daya biyota dan yaga fitan ta, dakyar suka fisge Amina tare dayin waje da ita, Alh Ibrahim yace Amina miye haka? Kuka ta Fara tare da fadin Wlh ya cuceni ya gama dani yaci amana ta, cemin yayi y’ata tana hannu Mai kyau har kudin abincinta nake bashi ashe ba haka bane, alh Ibrahim yace tunda Kinji y’arki bata mutu ba inaso kibar maganan a nan banso kowa ya Sani, amina tace Wlh bazan iyaba Ina bukatary’ata kusa dani, babu komai tare dani sai nadama, alh Ibrahim yace tabbas Nima Ina bukatar ta kusa dani domin na tsorata da rayuwar dana ganta a ciki, Labarin abunda ya faru ya bata Amina babu abunda take sai kuka, dakyar ya lallasheta tayi shuru, tare da alkawarin zasu koma harda ita ko zata yarda 
ta biyosu, da wannan shawaran suka koma Gida. Aneesa ce zaune da magajiya cikin d’aki, Aneesa tace nifa Wlh Ina cikin damuwa, magajiya tace name fah? Aneesa tayi tsaki tare da fadin abubuwa da dama, ni yanzu babban damuwa ta inga na sauka lafiya, sannan in mallaki dukiyar gidan nan gaba d’aya, wanda hakan zaiyi matukar bani wahala, tunda faruk ba d’an alh Ibrahim bane, Kinga kuwa koya mutu bashi da gadonshi, Wlh ni nama rasa miye Abun yi, magajiya tace mudan basu lokaci muga yanda Abun zai kaya tunda yanzu kowa baya cikin hayyacinshi, suna cikin magana faruk ya shigo d’akin Wanda yasa sukai shuru cikin sanyin jiki yake magana yajikin naki da lafiyan baby din? Tace ni ba Tani nake ba takai nake faruk, tun jiya na kasa sukuni tunda naji abubuwan da suka faru ko abinci na kasa ci Wlh, faruk yace akan wani dalili karki manta fah yanzu bake d’aya bace kin San Idan wani abu ya sameki zan shiga cikin wani hali fiye dana yanzu, dan Allah Aneesa kici wani abu Kar wani abu ya sameki keda baby, tace bazan iya ciba faruk Ina cikin damuwa fita yayi Jim kad’an sai gashi da abinci ya kawo mata kamo ta yayi ya fara bata farida da tazo wucewa ta hangosu ta window yana bama Aneesa abinci wani irin kishi taji yana shigarta mai zafi Aneesa ta hangota sai wani narkewa take Tana mishi shagwaba da sauri farida tabar wajan tana kuka, koda ta shiga d’aki kuka take ta rusgawa babu kaukautawa lokacin da Aneesa taga farida tabar wajan da gudu ta saki wani shegen murmushi tare da fad’i cikin ranta yanzu aka fara, ita kam Farida baiwar Allah gajiya tayi da kukan tare da fadin duk akan ciki yake mata haka Nima zanje inga likita ya dubani yaga lafiya ta, tana cikin wannan halin faruk ya shigo da sauri ta kawar da idonta 
dan karya gane tayi kuka, gashi yana cikin damuwa, zama yayi kusa da ita yace farida 
amsawa tayi da na’am yace Ina son in fara wani business Kafln in sami aiki, da sauri t‘a kalleshi cikin mamaki tace aikin office din Abba fah? Yace daka yau na yanke bazan kara zuwa ba domin bai kamata inje ba hatta zama a gidan nan inaso mu Bari, alh Ibrahim da yazo wucewa yaji suna maganan dan bai rufe kofar ba, tausayin faruk yaji Wanda yasa ya shigo d’akin tare da fadin faruk sameni d’aki na, tashi faruk yayi yabi bayansa Bayan sun shiga Alh Ibrahim yace naji abunda kake fad’a faruk har gobe kai d’ana ne, bazan taba canza kaba sannan duk wani abu da nake maka bazan daina ba domin son da nake maka bazai taba canzawa ba, Kar in karajin kayi wani tunani irin wannan kaji? Kai ya d’aga alaman Toh tare da fadin kayi hakuri Abba amma inajin kunyan abunda mahaifina ya aikata Nasan zainab bazata taba yafe Mai ba ina tsoran Kar laifinshi ya shafeni, alh Ibrahim yace ko d’aya zainab bazata ji haushinka ba, dan haka ka saki jikinta. 
Zainab ce zaune a falo tayi jugum duk ta rame ta fige tayi duhu, yanzu harta magana ma bata cika yiba, sai dai ta zauna tai tabin ku da ido, in Kaga tayi magana to abun daya zama dole ne tayi magana akai, zarah ce tazo da wani karamin Abu anyi raping dinshi gift ta mi’ka ma Zainab dake zaune a falo tare da fadin happy birthday sister, amsa tayi cikin murmushi domin ta manta yau ne ranan zagayowan haiyuwarta, haka khairat da aysha ma suka bata, alh Ibrahim shima ya bata nashi kyautar da Anty hindu da ummi da mama, farida itama ta bata nata harda Aneesa data kusa haiyuwa, faruk ne yazo da nashi yana d’an boyewa yana tsoran zuwa ya bata, kiran sunanshi tayi da faruk mai kake boyewa? Jin ta kirashi yasa ya sami kwarin Giwa ya nufeta tare da bata yana fadin happy Birthday amsa tayi tana murmushi tare da fadin thanks bros, Amina ce itama ta mi’ko mata amma taki 
amsa tashi tayi ta amshi Abun tayi jifa dashi kowa dake falon kallonta yake cikin mamaki 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]