[Advertisements⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 10 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA
CHAPTER 10
Iyalan Alh Ibrahim ne zaune akan kujerun falo suna hlra, yar karamarwayar Amlna ta kad’a alaman kira ya shigo, tashi tayi tabar wajan saida taje d‘akinta sannan ta dauka tare da fadin wai miye ne kake ta kirana? Yace na fad’a miki kudi nake so ya kamata kizo Ki aiko min dashi, d’an tsaki tayi tare da fadin saleh gaskiya kana son takura min nace maka ka Bari ldan na sami daman fita sai inzo in kawo ma, yace zuwa yaushe? Tace ldan na fito zan 
fad’a maka, kashe wayan tayi tare da zama akan gadon d’akin. 
Su zainab sunsha soyayya Sosai,ta yarda da irin son da mijinta ke mata, yanzu haka suna cikin jirgi suna hanyar dawowa hannunta na manne da nashi, koda suka dawo Nigeria driver gidansu yazeed ne ya daukesu zuwa gidan mum dinshi, inda suka sami tarba mai kyau, duk wata kulawa mum din yazeed na bata tare da nuna mata kauna itama shi yasa zainab din ta sakin jiki da ita, satinsu biyu suka koma gidansu lokacin zainab an kara kyau ga wani haske data kara kowa na gidan yaji dadin yanda yaga ta koma, su aysha Suma sun tafl katsina gidan iyayen mijinta. 
Yau kowa na falo Alh Ibrahim yayi gyaran murya tare da fadin nayi ma faruk mata bikin ranan juma’a mai zuwa ne, Amina tace kaman ya? Yace eh kaman yanda kike tunani na zaba mishi yar gidan mutunci dan bazan kara yarda da zabinshi ba, faruk kam tunda aka fara maganan wutar dake kanshi ta dauke dan bai taba zaton haka ba, amma babu yanda ya iya dan yasan wannan auren tunda Abba ya fad’a dole sai anyi, ummi tace toh ya kamata ai mata su shiga Abun a had’a akwati Abba yace na basu komai sun had’a mata kawai daurin aure ake jira, faruk tunani yake yanzu ldan Aneesa ta Sani Ya zasu kaya? Tashin hankali dole inyi nesa da Aneesa na wani lokaci haka yaita tunani Kala Kala Ya sa’ka wannan Ya kwance, kaman dai yanda Alh Ibrahim ya fad’a hakan k0 ta faru domin a kwanakin da yace aka daura auren inda aka kawo amarya gidan mai suna Farida, Farida kyakyawa ce ajin Farko gata fara doguwa ga manyan ido, koda faruk ya shiga d’akin ya ganta yayi mamaki da irin kyanta mai daukan hankali, lokaci d’aya yaji zuciyarshi ta Fara bugawa da karfi sonta yana shiga cikin ranshi, a ranan dai faruk kasa hakuri yayi saida suka raya daren, yaji dadin yanda Ya samu Farida a budurwa sai yaji Ya kara Sonta Sosai, soyayya yake nuna mata Sosai da kulawa tunda yayi aure baije wajan Aneesa ba, gashi inta kira baya dauka. 
Magajiya ce ita da Aneesa suna zaune magajiya na wanki Aneesa na kusa da ita, magajiya tace wai maike damun faruk daya daina zuwa baya kuma daukan waya, Anya lafiya kuwa? Ya kamata muje mu duba fah, aneesa tace hakane ni a wannan karan gidan zan koma ma gaba d’aya dan na gaji da zama a nan gskiya magajiya tace yauwa ko kefa, inda za kiji shawarata dama Kin tashi kinzo mun tafi yanzu, aneesa bata musa ba tace magajiya ta 
had’a musu kaya,jiki na bari magajiya ta Fara had’a kaya, Bayan ta gama suka nufi gidan 
Alh Ibrahim, da yake yau lahadi yana Gida dan babu office, nocking suka ji zainab taje ta bude baki ta saki lokaci d’aya kuma tace maiya kawo ku? Kowa dake falon ya kalli kofar ganin aneesa da magajiya yasa kowa ya tashi yayi hanyar kofar, ciki harda faruk, alh Ibrahim yace mai ya kawo ki gidana maza fita, tace Abba na dawo nan da zama ne domin Ina dauke da cikin faruk, kowa dake wajan mamaki yake ita kam Amina wani dad’i taji zata samu jika, alh Ibrahim yace dan kina da cikin faruk bazan baki daman zaman min a gida ba, dan haka ku fita,Amina tace haba haba ina zata jikanmu nefa a cikinta ta kalli mama tace mama dan Allah kiyi mishi magana, mama tace Ibrahim ka Barta ta zauna, shuru yayi can yace naji zan barta tunda yanzu faruk yana da mata dam kirjin aneesa ya buga, wato aure yayi ……. Katse mata tunani yayi da fadin amma Idan ta haiyu zata bar min Gida yana fadin haka ya haura sama kowa ma dake wajan yabar falon faruk yazo zai wuce tasha gabanshi tare da fadin abunda naji gaskiya ne aure kayi? Kai ya d’aga mata alaman eh, wani abu taji ya tokare mata wuya gashi faruk din yabar wajan, d’aki suka nufa ita da Magajiya aneesa tana ta sintiri tare da fadin magan ganu, ni faruk zai ma haka ina Raye zai kara aure, saina Nuna mishi ni karuwa ce, sai yayi nadama har yana cemin eh aure yayi magajiya zuciyata zata buga Wlh Ina son faruk Sosai amma saina hukunta sa akan abunda yayi min shima yaji aneesa bata yafiya duk ‘kan’kantar abu Idan akayi min sai na Rama faruk yayi min lalfi mai girma bazan taba bari in had’a dan da zan haifa da wasu yaran ba 
dan bazan bari Ayi yan ubanci ba …….. 
Magajiya tace toh mai zakiyi? Aneesa tace zaki gani nan bada dadewa ba dan Wlh bazan bari ya haiyu da ita ba, magajiya d’an murmushi tayi tare da fadawa kan gado tana fadin kiyi duk abunda ya dace, nidai ban son mu kara barin wannan gidan dan najijiki komai ni nakeyi, aneesa tsaki ta danyi tare da fadin ai wannan gidan tunda na shigo shi bana tunanin zan barshi kuma dan haka Kima daina wannan maganan, magajiya tace yauwa ko kefa. 
Farida tazo wucewa saiga aneesa itama ta fito, Fuska aneesa ta tamke kaman bakin kumurci, ita kam Farida sai addu’a take domin tana tsoran aneesa tunda taji labarinta, gabanta Aneesa ta tsaya Tana kallon Farida sama da ‘kasa tazo zata mata magana saiga khairat nan ta flto ganin haka yasa Aneesa ta wuce ba tare data kula Fan’da ba, khairat ganin irin kallon da tayi ma Farida da kuma yanda faridan ta tsaya Tana kallonta yasa ta gane wani abu ya faru, amma sai tayi kaman bata gani ba, da murmushi a fuskanta tace Farida lafiya kuwa naga kin tsaya kaman mai tunani? Itama kago murmushin tayi tare da fadin laflya sauka kasa sukayi tare suna d’an tattaunawa, zama sukai a falo suna fira saiga faruk ya shigo gidan wani irin kallo yama Farida Wanda yasa ta kalli khairat da sauri taga ko ta gani amma ganin bata gani ba yasa ta mayar mishi da martani, hannunshi yasa a baki yayi kiss ya huro mata lumshe ido tayi tana d’an murmushi, waigawa khairat tayi taga faruk tace yaushe ka shigo dariya yayi tare da zama kusa da Farida yace yanzu duk wannan abunda akeyi a idon Aneesa tana sama tana kallonsu ba’kin ciki ne ya cikata dan haka tayi d’aki da sauri inda taga magajiya na kwance tana sharban bacci abunta tsaki taja tare da fadin ita bacci nema a gabanta zama tayi tana huci tare da tunanin hanyar da za tabi dan ta Fara nuna musu basu isa ba, tana cikin wannan tunanin saiga faruk ya shigo d’akin Tana ganinshi da sauri ta tashi dan batayi zaton zai zoba, murmushi ya sakar mata amma saita daure fuska ganin haka yasa ya karaso cikin d’akin yana fadin Ya jikin ki? Tace ai baka damu ka sani ba, yace kaman ya? Tacejiba yanda kake shareni tunda nazo gidan nan kake nunawa kaman dani da Banza duk d’aya ne karka manta fah Ina dauke da cikin ka a jiki na, yace ban manta ba Aneesa inaso ki kara hakuri Abba yayi min warning akan Karyaga Ina shiga harkan ki so Kinga dole in kiyaye, d’an shuru tayi can tace hakane ya tambayeta koh tana bukatar wani abu? Tace a‘a sannan ya flta, yana Flta ta Fara surutai tare da fadin dakyau ai mai rabani da faruk sai Allah dan haka bada dadewa ba zan dawo matarshi. 
Birthday din faruk yazo Anata shirye shiryen birthday ranan birthday din harda aysha tazo itama, yazeed yazo wucewa traffic ya tsayar dashi ya hango Amina tana siyan gift na faruk can ya hango ta dauko wani sarka an rufe mata, yazeed yace Toh wa zata bama na matan, yace Kai akwai wani abu, Dan haka koda traffic ya nuna musu alaman wucewa faka motarshi yayi a gefe, sanda yaga ta fito ta shiga mota ya fara binta a baya taf‘lya driver yake da ita shima yana binsu wani anguwa driver din ya faka ta flta da d’aya daka cikin abunda ta siya na gift din, wani lungu ta shiga yazeed shima Ya flta Ya bita, kai tsaye wani gidan sama ya hango ta shiga binta yayi gidan babu komai sai datti da kura, sama ya haura inda yaji magananta da saleh tana fadin saleh nace ka daina yawan kirana a waya amma bakaji, 
yace dole in kiraki dan kudi nake bukata, bashi kudi tayi tare da fadin gashi dan Allah ka daina yawan kirana, dauko dan karaminjakar dake hannunta data siyo ta mi’ka mishi tace yau birthday din yarinya ta gashi ka Kai mata, amsa yayi yana murmushi tare da fadin hakane rana d’aya aka haifesu da faruk, Ina tsoran ranan da alh Ibrahim zai gane faruk yaro nane sannan yasan yarki na wani waje ya zaiji? Amina tace Kai Dallah ka cika wani tunani taya zai sani Inba ka fad’a mishi ba tunda kace Dr din data amshi haiyuwar ka kamata Kaga babu Mai fad’a mishi dariya yayi da fadin hakane, tace ni zan wuce kasan ana can ana celebrating birthday din faruk tana fadin haka ta fita, yazeed dake labe yaji komai wani irin zufa ya keto mishi kenan faruk yaron sale ne, amina mace ta haifa sai suka Kai yarinyar wani waje, lallai ya kamata in fadama zainab Kafin inje gida,fita yayi yana kokarin kiran zainab amma bata jinshi dan garin akwai hadari network na rawa ga kuma karan kid’a fita tayi amma still bata jinsa, saleh yazo zai fita ya hango yazeed, yace Kai da sauri ya kira Amina yace yazeed yaji komai fah Dan ya ganshi kuma yaga yana kokarin waya da kaman zainab, Amina cikin rudewa tace yanzu miye Abun yi? Yace karki damu duk Wanda yaji wannan maganan Nasan mai zan mishi, tace Mai zaka mishi? Yace karki damu kawai kisan yanda za kiyi Kar ki bari yayi waya da zainab, yazeed ganin kaman babu network yasa ya shiga matarshi yabar wajan, Bayan ya fita ya tsaya a wani waje yana kokarin waya Bayan zainab ta dauka ya fad’a mata yana waje kaza gashi bayajinta kuma an fara ruwa, tanajin abunda yace tace ga tanan zuwa, fita tayi tasa driver ya kaita saida ta fadama khairat inda zata sannan ta wuce, lokacin data karaso ta hangoshi dan haka ta flto shima fltowan yayi duk da ana ruwa yazo zai tsallako wata babban mota tazo ta bigeshi Wanda yasa yayi sama dashi sannan ya fado kasa, Wanda ba kowa bane yayi wannan aikin sai saleh ganin ya fado jini na zuba tako Ina yace bye yazeed sai mun had’u kuma duk ta glass din motar yake hangoshi Dan bai tsaya ba, ita kam zainab tunda ta saki ihu ta kasa komai ganin mutane sun taru akanshi yasa taje inda yake ……. Hmmm masu karatu muje zuwa shin yazeed Ya mutu?Asirin Amina da saleh zai tinu kuwa duk ku biyo ni.. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]