[Advertisements⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA CHAPTER 1 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MEYE ILLAR YAYA MATA 
CHAPTER1
labari ne akan kiyayya soyayya butulci makirci da Abun tausayi da kuma ban 
dariya 
Gida ne babba kana ganin gidan kasan gidan wani hamshakin mai kudi ne wanda ya tara Abun duniya, shiga cikin gidan Nayi dan inga ya yake, gidan sama ne Katoto babba mai dauke da dakuna da yawa ga kaftareren falo, wata mata na gani mai ciki zaune a falon kusa 
da ita wata yarinya ce da bazata wuce shekara biyar 
ba tana ta wasa, wani mutum ne ya shigo gidan kana ganinsa kasan shine mai gidan, fuskan matan cike da fara’a ta tashi ta nufeshi duk da cikinta yayi girma haiyuwa yau k0 gobe, rungumeshi tayi cike da fara’a yake mata sannu tare 
da kara riqota yace Maman soja nace
ki dinga zama waje daya, dariya tayi tace ai motsa jiki game Ciki abune mai kyau, yace hakane amma naki motsa jikin yayi yawa, karaman yarinyar nan ce tazo ta rungumeshi ya dagata sama tare da fadin zarah kaninki ya kusa zuwa, mun kusa samun soja a gidan, zarah sai dariya take tayi, ajiyeta yayi sannan ya kalli matarshi yace kubra Ina mama? Tace Tana …… Kafin ta karasa abunda take son fadi saiga wata tsohuwa Tana saukowa daka kan step, fuskanta dauke da fara’a, kusa da ita Ya nufa yana fadin sannu Mama tace yauwa Ibrahim, dinning suka nufa inda matarshi tayi saving dinsu, kowa abincinshi yake ci babu Mai cewa komai har suka kammala sukai ciki. Washe gari da safe 
hjj ummi tana kitchen ita da masu aikinta saiga Alh Ibrahim nan ya shigo ciki,baik0 bi takan kowa ba Ya kamo hannunta sukai falo, zaunar da ita yayi sannan yace dan Allah ummi 
ki daina wannan yawan aikin bana so, kin San duk wani abu dazai taba lafiyan yaron nan Wlh ba kaunarshi nake ba, shuru tayi tana dan tunani mai yasa mijinta in zaiyi magana yake cewa yaro Bayan bai san abunda zata haifa ba,ta rasa mai yasa yake son haiyuwan da namiji bayan da mace dana miji duk Wanda Allah Ya baka ka gode mai dan baka san mai jin qanka ba, itama da kanta a wannan Karon tana son haiyuwan da namiji kodan saboda mijinta amma ita 
a nata ra’ayin tafi son yay’a mata dan sunli tausayi akan d’a namiji …….. Katseta yayi da fadin ladiya naji kinyi shuru? Kai ta daga mai alaman eh dan murmushi yayi tare da fadin 
Idan kika haifar min namiji zan miki babbar kyauta, tayi dan murmushin Yake sannan tace toh fah wani irin kyauta? Cikin 
fara’a yace zan baki rabin abunda na mallaka, sannan sauran rabin daya rage zan rubuta shima zan barma yaron da zaki haifa, idonta ne Ya ciko da kwalla mai yasa mijinta idonshi ya rufe akan da yake fada bai mayi koda tunanin zarah ba, hawayen da take kokarin taga bai zubo ba,shine ya gangaro mata, da sauri yasa hannu yana goge mata Wanda shi a nashi tunanin hawayen farin ciki 
take, amma ita ba haka bane babu komai cikin ranta sai bakin ciki da takaici, zarah ce tazo inda suke tana kuka, daukanta tayi tana fadin zarah mai nene? Cikin yar hausanta mai kama da gwaranci take magana tace yunwa nake ji, dan murmushi tayi tare da fadin shine harda kuka muje in baki abincin, kiran sunanta yayi da ummi wanda yasa ta waigo da kallonta gareshi, yace na fada miki bana son kina aiki koh kadan, tace zarah zan bama abinci, yace ki zauna masu aiki su bata akan cikin nan naki zan iya komai, mama ce ta amshe da fadin Dan haka ya kamata ki dinga kula saboda lafiyanki dana yaronki, ummi shuru tayi tana sauraransu Wai *MIYE ILLAR Y’AY’A MATA ne* da yasa mijinta yake nuna shifa namiji yake so, abun takaici ma harda Mama itama tana biye mishi, jin maganan mai aikin da tayi ne yasa ta dawo daka duniyar tunanin data fada, Alh Ibrahim yace ma mai aikin ta dauki zarah taje ta bata abinci, daukan zarah tayi sukai kitchen, wani irin ihu ummi ta saki tare da riqe cikinta da sauri ya nufeta yana fadin lafiya maike damunki? Mama tace ka mata muje 
asibiti na’kuda ce, da sauri ya kamata sukai mota driver ya tuka suka nuti asibiti, suna zuwa akai labour room da ita, Alh Ibrahim gaba daya ya kasa zama sai sintiri yake yana fadin Allah Ya sauketa lafiya tare da fadin Allah yasa yaron yayi kama dashi jin ihun baby yasa ya 
gane ta haihu da sauri ya koma kusa da wajan Ya zauna yana Jiran litowan Dr Dan yaji Mai aka haifa duk da yasan namiji ne, Dr ne Ya fito cike da fara’a yace congratulation matarka ta sauka lafi …… Katse Dr yayi da fadin namiji aka samu? ……. Toh ku biyo ni dan jin mai aka samu yawan 
comments shine zai nunamin kuna son cigaba 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]