[Advertisements⬇️]

MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 6 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 6
rayuwar da, don haka na yanke shawarar cetoka, domin tace gwara ta tsine maka gaba daya tasan wai duniya ta haifawa kai…” 
. Ya daga kai cikin firgici yana kallon Malam Abbagana tare da cewa. 
“Subhanallahi, meye ya yi zafi har haka, wallahi ko da bata kawo ni gurinka ba, zan yi duk abin da tace, nasan ba zai wuce akan maganar neman aure ba, ba ta taBa umartata da na nemi aure na’qiyi ‘ba, sai dai idan auren ya kusa sai a samu matsala daga Bangaren wadanda nake nema, sai take ganin laifina ne amma don Allah a taimake ni a taya ni lallaBata malam”. 
Ya girgiza kai cike da gamsuwa da bayanin Mukhtar din, sannan yace. 
“Ai komai yazo Karshe, daga wannan karon burinta zai cika kai ma kuma nake fatan hakan ya zamo sanadin wanke duk wani laifi a gurinta Domin a yanzu za a daura maka aure da qanwarka Falmata na kammala shirin komai…” 
, A karo na biyu ya sake daga kansa sai dai wannan karon firgicinsa yafi na dazun bayyana, yace
“Malam aure kuma?” 
Malam Abbagana ya tsare shi da ido yana fadin, “k0 ba ka so ne? Ko kuma zargin da Mariya 
ke maka na matarka ta mallakeka ya tabbata ke nan?” 
Cikin rawar murya yace “Wallahi ba haka bane malam… am… am… am”. 
Duk jikinsa ya kama rawa ya hada gumi kamar wanda ya hadiyi Kunama. 
Malam ya yi dariya yace “amma kuma me? Kuma sakaci ‘da addu’a sai an yi magana ku dinga kiran kunfi mu ilimi da komai, amman bakuda tsarin komai matanku su dinga juyaku, yanzu ba zai zama abin kunya ba ace babban’ mutum kamarka dake koyarwa wasu’tarbiyya mahaifiyarsa na kuka da shi ba? Ka tashi kajw naji an fara addu’ ar daurin aure, idan mun kammala zan nemeka mu wuce can gida tare”. ‘ 
Haka ya mike kamae wanda kwai ya fashewa a ciki, sai ya keJin kamar an kwance wani babban qulli a cikin ransa. ya dinga jin zuciyarsa tana haske  yana son yati farin ciki, amma wani tsoro da fargaba suna hanawa. Haka nan ya koma gefe yana sauraron  addu’ar daurin auren har aka daura na Yakura da Zuhaida da Sakina gami da Zahra’u.. Yanajin an fara  addu‘ar nashi  gabansa . ya fara faduwa, sai yaji kamar ya kwasa da gudu  yace ya fasa, amma rauyin malam bazai barshi ya iya  aikata hakan ba mutumin da yake matsayin uba a gurinshi bazai iya kunyatashi cikin dubban jama,arnan ba shin ya zaiyi da fa,,,la yasan ko zai ko zai kwana yana mata bayani bazata taba yarda ba
Ya dafe kai yan fadin ya salam a cikin zuciyarshi daidai lokacin da aka shafa fatihar qarshe falmata ta zama matarshi fakat
Yana kallo anata raba goro da alewa mutane nata amsa suna addu,a da sanya Albarka shidai zaune yake yana kallonsu cikin wani irin yanayi da bazai iya fassarashi ba har malam ya qaraso gabanshi dasu bulama da sani abinda yafi bashi mamaki bai wuce ganin yayyensa da suke uba daya ba su auwa kabir harda muhammadu da saminu
Kai harda wasu abokan mahaifin nasa ma
Hakanan ya dinga yaqe ya isa suna gaggaisawa 
Dasu,,,, babban wansa malam auwal ne yace barka yau dai munci goron auren qaninmu saurab suka fashe sa daria suna fadin lallai kam domin sunyi Alqawarin sun daina nema masa aure don sun neman masa aure yafi sau goma 
Amman ana fasawa kullum da abinda zai bullo sabo yau dai Allah ya fatila Alqadarin fatila
Abin da ya qara bashi mamaki bai wuce ganin ‘yan uwanshi mata har da mahaifiyarsa a gidan ba ana ta sabgar biki, wato kowa dai yasan da maganar bikin, -shi da. Fatila ne kawai ba su sani ba ké nan? ‘ _ 
Ya hango mahaifiyarsa sai aiki ta keyi cike da farin ciki da nishadi, malam Abbagana ne yace masa, “Ka shiga ku gaisa, sannan ka wuce babban falon baki zan sanya a turo maka amaryar ku gaisa” . . 
Ya wuce yana amsawa da, “Toh” . Tunda 
suka shigo hankalin da. yawan matan ya yi kansa Hajja Basma ta bazama ta yi dakin Hajja Yakolo, can uwar daki tatarar da ita da gulma, tace mata. . «Fita kiga ‘cutar da aka yi miki kina nan ‘ sankame a daki, Muntari ne ya shigo gaba d‘aya ya haske .-gidan nan kamar wani farin wata sha kallo dan daren goma-sha hud‘u”. , 
Ba ta ma kula da mutanen da suka cika dakin ba domin idanunta sun rufe tsabar gulma da hassada dake nuqurqusar zuciyarta, don ma dai duk ‘yan uwan Yakolon ne a d‘akin. ‘ 
Ita ma Hajja Yakolo babu ko tunani, ta bi ta suka nufi waje suka tsaya daga bakzin qofar sashinsu suna hangensa yana gaisawa da mutane fuskarsa kamar gonar auduga. Tabbas ya yi kyau. 
mutum mai cike da kamala da kwarjini, kowace mace zata so ace ya zama surukinta. 
Bayan ya gama gaggaisawa ya nufi inda aka ce ya je ya zauna, daman tuni Malam ya yiwa Hajja Iyami waya ya ce a tura Falmata can babban falon baki mijinta ya zasu gana. 
Hajja Iyami da kanta ta nufi dakin Falmata inda yake cike da qawayenta irin su Yagana, Alabura da sauransu. Ita kam amaryar tana can kuryar gado ta tuge gwaggwaron da aka sanya mata ta nade kamar mara lafiya, ‘yanmata tun suna tsokanarta har suka koma tausayinta ganin yadda ta koma abar tausayi. 
Hajja Iyami ta shiga da ‘sallama, da sauri Falmata ta mike tana goge hawayen dake idonta tana fadin, “Lah! Hajja yanzu nake cewa bari na je na gaisa da su Anti Jamila”. 
Ta taBe baki, “Ke dai kika sani kuma, ga mijinki can ya shigo yana babban falon baqi, kije ku gaisa, sannan kuma idan kinje ki nuna masa ba kya sonshi har ya gano ya sanar da Malam”. Tana kaiwa nan ta juya ta fice. 
Falmata ta yi tagumi idonta ya kuma cikowa da kwalla, ji take yi kamar ta dora hannu aka ta fasa ihu ko taji dadi amma haka nan ta tashi sumi sumi ta dauko wata lafiyayyar lafayya ta fara nade
jikinta da ita, ‘yanmatan suka bita da kallo, Yagana ce ta daure ta yi magana. ” ‘ 
“Gaskiya idan kika yi haka ba ki kyauta ba, . kwalliyar da akafi bukatar ango ya gani sama da kowa zaki rufe? Don’ Allah ki cire laffayar ki dora gwaggwaron ki tafi haka”. 
Ta zoBara baki gaba tana fadin, “Wallahi sai ki sanya na ciré lafayyan ma na maka zumbudeden gyale k0 hijabi, ai wanda kake so shi kake yiwa kwalliya, don’ ka burge shi. Taso muje ki rakani ma don Allah”. ‘ 
. Yagana‘ ta riKe baki cike da zolaya, tana fadin “Rufa min asiri, wace ni shiga tsakanin 
ma,’aurata na sani ko zai yi sirri da matarsa, ko ya 
kika ce‘ Alabura?” . 
Suka sheke da dariya gami da tafawa. 
Ta kawo iya wuya don haka ba takuma ce musu ko qala ba ta fice da sauri suka .bita da dariya, Alabura tana fadin
“A.dai saki jiki har a samo mana baby”
Suka kuma kwashewa da dariyarsu, ita dai ba ta kula su ba ta wuce abinta. 
Ta jima a bakin qofar falon tana tunanin ta yadda zata shiga, shin wane irin miji aka bata, fari ne ko baqi ne,  Gabanta ya dinga faduwa, sai da tayi addu’a ta shafa sannan ta shiga 
Da sallama. . _ . Kansa yana can gcfe ya amsa sallamar, ita kam kanta a durkushe ta shiga dakin ta sami guri ta zauna. . ,Ta kasa dago kai ta kalle shi, cikin sanyin nuryarta wadda dama haka take, ”sai kuma Karin kukan da ta sha jiya da daddare da ya Kara narkar da muryar tata ta koma kalar tausayi sosai, tace . “Ina wuni‘?” Muryarta ta ja hankalinsa matuka, ya waigo da sauri yana dubanta. ‘ Gabansa ya yanke ya fadi, zuciyarsa ta shiga wasu-wasi, bakinsa. ‘yana rawa ya ambaci sunanta ‘ da wata irin rikitacciyar murya. . 
“Falmata, daman kece mata‘ta?” 
Ta daga kai da sauri ita ma domin’ko, a cikin mafarki ta ji wannan muryar sai ta bude idanuwanta, k0 da tayi sallama ma ya amsa mata 
sai da tayi tunanin kamar ta san muryar, daurewa kawai tayi ta tsananta ba amma yanzu da taji ya ambaci sunanta ta tabbatarwa kanta wanda take zargin ne ya haye muhallin  farin ciki da ya cikata, anya kuwa ba mafarki nakeyi ba‘? Ta ayyana hakan ,a ranta. Malam Muhammud mai darasu shi ne daman mijinta ‘? Shine Muntarin da ake ta fadi? Meya sanya ba,a taba ce mata shine ba  Bnkinta yana rawa tqce
“Malam daman kaine Muntari? Kaibe dan gidan Inna Mar‘wa?“ 
Ya d‘aga mata kai, “Tabbas nine nine danta ashe kece  matata falmata,,  Kai har naji sanyi ‘ cikin raina wallahi, da ina tsoron wacecc aka had‘ani da ita auren da ban shirya ba, amma ina ganin kece naji sanyi da farin ciki sun mamaye dukkan illahin‘n jikina“. ‘ 
Ba tasan lokacin da bakinta ya kufce tace “Daman kana sona kai ma?” 
Sai tayi saurin rufe fuskarta tatuna irin baram baramar  ‘da tayi. , 
Yayi murmushi cike da jin dadi yace “Kina tunanin akwai mutumin da zai ganki yaji baya sonki ne Falmata?” ‘ Ta qara Boye fuska tsakanin cinyoyinta tana dariya, ta rasa inda zata sanya ranta taji dadi don farin ciki, duk ta dimauce ta ma rasa me ya dace ta yi, amma dai cikin ranta sai godiya take yiwa Allah da Ya nuna mata wannan rana mai tarin albarka mai kuma kundin tarihin da baya goguwa. 
Ya dinga janta da hira kunya ta hanata sakin jiki da shi, har dai ya mike yace 
“Bari naje guein su Abba kada su jini ’ shiru
idan anjima kafin mu wuce masaukinmu zan kuma dawowa mu yi hira, sai dai ina fatan ba za,a kuma yimin irin wannan kunyar tayanzuba,kinsanni fa mijinki ne yanzu k0?” 
Ta daga kai alamar, “Eh”. 
“Shi ke nan, sai na dawo”. Ya nufi qofar
‘ Ta daga kai tana kallonsa, wani irin nishadi ‘da jin dadi suka durar mata. ta mike da sauri cike da doki ta nufi dakinta. ‘ 
Tana isa ta rungume Yagana tana dariya, tace, “Alhamdulillah, na godewa Allah da ya nuna min wannan rana Yagana”. 
Cikin dariyar ita ma Yagana tace “Lallai wannan ango ya shigo da Yaseen a gidan nan, cikin ‘yan mintina qalilan har ‘ya same ki haka?” 
Ta sake yin dariya mai nuna farin cikinta a sarari, tace “Wai kin san waye mijina kuwa Yagana? Malam ne fa?” 
Da mamaki Yagana tace “Malam? Wanna ke nan, kina nufin Malam Bukar ne mijin naki?” 
“Bafa shiba, malam mai darasu fa, ashe shi me dan gidan Inna Mariya, ashe shi ne Muntari? Su Muntari suke ce masa, kai Alhamdu lillah ashe Allah Ya .amshi addu’,ata nima zan yi auren farin ciki, auren tinqaho, auren kece raini, auren da kowacce mace taje fatan tayi irinsa? Ashe dai ni 
ma zan more miji a rayuwata, wanda zai zamo abin alfaharina?” 
Ita kanta Yaganar farin ciki ya cikata, ta rungume Falmata a j ikinta suna ta murna, Alabura ma ta cika da murna, domin ita ma tasan waye malam ‘mai darasu. ‘ . 
Sai ga amaryar ta ware laffaya ta maida gwaggwaro ta dora har da qara gyara fuska, tace da Yagana. 
“Ku bikin na farin ciki ne, bari naje  mu gaisa da ‘yan uwa wallahi”. 
Suka dinga tsokanarta tana dariya ta fice, nan aka dinga hotuna da daukar bidiyo da ita, tayi ‘kyau’kamar ka sureta ka gudu; ita da Zahra kam sunfi kowa murna,‘ sai kawa da komowa suke su Yakura kam ana cikin d’aki kamar za a dige don kuka 
Abin da tayi din kuwa ya burge kowa, musamman mahaifiyarta da Hajja Kaltum, su sun yi zaton tsabar biyayya ce ta sanyata farin ciki! ba su san dawan ‘garin ba, ba su san harda son angon nata na gaskiya ba tunda ta ganshi. . 
Tunda yamma aka fara shirye-shiryen kai amare gidajcnsu. Falmata tana ta kiciniyar shiryawa rakiya, tunda ita ba a tsaida ranar tarewartaba. Hajja Yakolo kam kamar zata hadiyi zuciya ta mutu don takaici, su Yakura kam sai kuka ake yi 
idanuwa sun yi luhu-luhu. 
Sai ga Falmata an shiga wanka da ruwan turare, ta fito ta tsara kwalliya sai kamshi ta ke zabgawa kamar ita kanta ce turaren, aka kashe dauri gwanin sha’awa, Hajja Iyami ta dinga kallonta da sha’awa, diyar tata ta yi kyau matuka kamar ka saceta ka gudu. 
Sai daime? Suna gab da tafiya kai amare don har ta shiga mota taji wayarta ta fara qara, abin da ya bata mamaki bai wuce ganin bakuwar lamba ba, ta yi kamar ta share amma dai sai ta daga taji k0 waye. 
Daga sallamarsa ta game mai maganar duk jikinta ya yi wani irin sanyi, kamar an tsinke mata Iaka. Ta dan saci kallon Yagana da ta zuba mata idanu. 
Cikin kwantar da murya yace, “Ina fatan baki cikin tawagar ‘yan kai amaryan nan da suke jeren gwano
Taji dumm!!! Ta dan dake tace “Har dani mana gamu har mub shiga mota
Ya sha kunu kamar tana gabansa, yace “To da iznin wa kika futa? Kin dai san nike da iko dake k0?” 
Tayi yake, a ranta tana fadin, “Ikon Allah 
Sai kace wanda ke wani son auren 
Kaida ka samu komai a sanga ta fadi a ranta amman a fili sai  tace,“Tuba nakeyi namanta ban tambayaba”. 
Yace,“Aikuwa baki isaba ,saidai wani lokacin. Ki fito gani inajiranki a falon baqi”. 
Gaba daya jikinm yayi sanyi, ranta ya Baci, yaddataci burin kai amarennan ace yayi mata bakin ciki? Amma gaskiya bai kyauta mata ba… 
Maganarshi ta katse mata dogon tunaninta. “KO sai kinje ne?” ~ 
Da sauri tace “Lah Gani nan zuwa fa”. 
Ta kashe wayar tana kumbura baki gaba. ta kalli Yagana. 
“Kinji mutuminnan zaitakuramin wai yana falon baqi naje shikenan yanzu ba za,akai amare dani ba
Idonta ya ciko da kwalla don takaici. 
Yagana tana son yin dariya, amma ta dake tana fadin, “Ai aikin lada zakuje kiyi, mEye na takaici kuma?” ‘ 
Wani abu ya kuma tsaya mata kamar ta mangare Yagana, kawai saita fice  daga motar, Yagana ta shake da dariya har da tafa hannu‘ ta ‘ galla mata harara ta wundo tana fadin “Wallahi 
zamu hadu sai kin sani, Allah”, Ta shiga falon ta kumbura ta yi fam! Kamar 
zata fashe dakyar ta iya yin sallama, kanta yana qasa tace “Ina wuni?” 
Ya tsare ta da ido, tunda ta shigo yake Karewa surarta kallo, sai yanzu ya gano ainihin kyawunta, da yake ba Hijab kuma babu abaya k0 laffaya a jikinta, gyale ne ta yafa. 
Doguwa ce sambal! Sai dai tana da kugu ‘da shap, tana kuma da tarin dukiyar fulani, sune kedan sanya a ga cikar idonta, tana da doguwar fuska siririya mai d‘auke da dogon hanci da qaramin baki, amma IeBenta baqi ne irin na barebari. Idanuwanta manya ne masu kamar an diga musu zaiba don kyau, tana da yalwar gashin gira da saje, wanda hakan ke nuna yawan gashinta na kai. Sai dai baka ce amma irin bakin nan mai walqiya, tana da hujen hanci irin na bare-barin asali, ma’abociyar kananan kitso ce koba a yi maka bayani ba kasan babarbara ce Falmata.’ 
Ya dan yi yaKe yana fad‘in “Sai na ga kamar na batawa amaryar tawa rai k0?” 
Ta dago da sauri tana qokarin boye fushinta ta hanyar Kakalo dariya, tace “Kai‘ba haka bane, ban yi dai zaton yanzu zaka shigo bane
Ya karkata kai yana qara Shakar Kamshin da take fitarwa sannan yace “Amma nace miki zanzo muyi sallama k0? K0 baki son mu fahimci juna ne  Falmata?” 
Ta narke masa cikin shagwaBa take fadin, “Ni fa ba haka ba ne, ka yi hakuri”. 
. Ya yi dariya yacc, “Shi kenan gaya mini, samari nawa na kasa? Don dai budurwa mai kyau da ilimi irinki nasan ba zata rasa samari ba”. 
Ta Boye kai cikin cinyarta tana dariya, sai taji wani irin farin ciki ya cikata. 
Ya yi dariya ya kwanta jikin kujera, sai wani nishadi yake ji, zai iya cewa tunda yake a rayuwarsa bai taba shiga irin wannan yanayin ba, na tsananin shauki da soyayya ba. 
Tunda safe ya ga Falmata kuma a matsayin matarsa ya gaza sukuni, gaba daya yaji sonta ya cika ransa, tabbas tun ranar da yaga yarinyar yaji ta burge shi, komai nata ya yi masa, amma saboda takunkumin da aka makalawa zuciyarsa sai ya ji ya kasa fassara komai a zuciyarsa game da ita, illa ya yarda kawai tana burge shi, sai dai daga safiyar da . ya ganta zuwa yanzu ya amincewa ransa yana son Falmata, duk da sau da ‘dama idan ya ambaci so a ransa yakan ji gabansa na faduwa. 
Ya daure ya tattaro nutsuwarsa yace, “Falmata ya kike mini rowar kanki ne‘? Don Allah ki dago fuskarki na kalla na more, kinga gobe da safe mu zamu wuce Kano, ga shi ni da ganinki sai 
randa na dawo. Sai dai na dinga jin muryarki ta waya, ko da yake ai rowar lamba ma aka yi mini, sai gurin Abba na amsa”. Ta dan dago amma ta kasa hada ido da shi, 
tace, “To ai ba ka tambaya bane shi yasa”. 
Yace “haka ne, ba ni wayar taki na gani”. 
Ta tashi ta mika masa ta dan durkusa da hannuwa biyu. Ya kurawa hannayenta ido wanda suka sha jan lalle, qamshinta ya cika shi, sai ya ji kamar ya janyota jikinsa ya rungume, amma dai ya dake ya amsa, ya fara bincikawa. Daya bayan daya ya dinga tambayar sunayen wadanda ke kan wayar yana goge wadanda bai gamsu da bayanin da ta yi ‘ masa ba. ‘ ‘ Sanda yazo kan Malam, Bukar ya ga ta sanya, my teacher B, ya kurawa sunan ido nan da ‘nan kamanninsa suka sauya zuwa matukar kishi, 
amma ya dake yace “Falmata wakika taba so a rayuwarki? Wa kuma kika fara so?” Yadda ya tsareta da ido ya sanya gabanta ‘ bugawa, da zata iya,  cewa zata yi ‘kai na fara so, kai kuma na taba so’, amma ba zata iya ba, don haka ta yi shirun tana wasa da yatsun hannunta. . Ya yi yake mai ciwo, yace “Da gaske kin taSa son teacher B k0?” 
Ta daga kai da sauri don ta gano abin da yake nufi,amma ta kasa magana, ya kuma goge lambar malam Bukar yana fadin
“K0 shi kike so ya rasaki, a yanzu ni ya dace ki fara so, tun ranar da na fara jin muryarki na ji wani abu a raina, balle ranar dana fara ganin fuskarki, don haka na tabbatar na fishi sonki”. 
Wani haushi ya tokare wuyanta, kuji don Allah wannan shi ne ta baya ta rago, ta ya ya zata yarda yana sonta, mai ya sanya bai furta yana sonta ba a wancan lokacin? Da ace an aurar da ita ga wani ba shi ba. fa? Shi bai san yadda Malam Bukar ke sonta ba, don dai ita Allah bai dora mata sonsa ba k0 dai-dai da kwayar zarra ba. 
“Kin’ yi shiru Falmata kin barni ina ta magana, koda yake an fara gaya mini halinki wai miskila ce ke k0?” 
Ta girgiza kai da sauri tana fadin, “Bafa haka bane, wanda ya yi min bahaguwar fahimta kawai ke zaton haka”. 
Ya yi dariya yace “Idan ba haka bane to ya ya ne? Ni ma ana~cewa miskili ne, amma na kasa yin miskilancin nawa a gabanki, ko don ina sonki ne? Kai wannan mutumin da bada kunya yake ita kam duk kunya ta cikata, domin bata saba jin 
Hmm falmata da malam mai darasu sun samu abinda sukeso,,,,,,,,, mai zai faru mu tara domin ci gaba da sauraron wannan qayataccen littafin

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]