[Advertisements⬇️]

MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 36 THEND - Bankinhausanovels
Thu. Mar 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MATACCIYAR RAYUWA

THEND KARSHE
CHAPTER 36 last chapter

tunani ta nufi kofa, tabbas ta shiga tsaka mai wuya.
Daren wannan ranar kam bata ‘runtsa ba, kwana tayi rokon Allah
A daren ranar ya juya Kano domin gano iyalinsa da kuma zuwa ofls dinsa.
Washegari da safe Abba ya kirata domin jin shawarar da ta yanke kanta yana kasa tace. ‘ “Abba kamar Muntari zaifi k0?” Abbagana ya yi dariya cike da farin ciki yace “Tamkar kin san abin dake’ cikin zuciyata ke nan,.a gaskiya duk kwani miji da zaki aura bazansoshi kamarMnkhtariba. Allah ya yi miki albarka, :Ya sanya KARSHEN WAHALArki kenan ameen:
Farin ciki ya cikata yadda ta farantawa mahaifinta; rai tace “Ameen Abba. na gode, amma sai kuntaimaka mini da taddu’oi
Abba yace“Allah yana sane da lamarinki, ina .ji a. jikina wahalarki ta zo karshe insha A11ah Falmata,ba~wani taro za,ayi ba gobe idan Allah Ya kai mu bayan an sauko daga masallaci za a daura auren, ki turo min Kader zan lallashe shi, kada yaga kamar an yi masa ‘yan ubanci ne”.
Ta mike tana fadin, “To Abba”. Ta fice daga dakin. Abbagana ya bita da kallo cike da farin ciki.
Malam ya jima yana yiwa Kader nasiha, da nuna masa muhimmancin komen Falmata gidan Mukhtar, k0 domin rayuwar ‘ya’yanta. Kader ya yi shiru cike da tsananin damuwa, tabbas yaso falmata, amma kuma yadda Abba ya tsara masa maganar ya yarda Mukhtar yafishi bukatarta, don haka yace
“Abba na hajura da Falmata, amma don Allah zan roKi wata alfarma a gurinka”. Abba yace “Insha Allah idan ina da ikon yi maka zan maka AbdulRadir”.
Kader ya gyara zama yace“Don Allah Abba ina son a bani Aminatu, domin na kwadaitu da son zuri ar gidan nan”. Abba ya yi murmushi ya ce. Na yi maka alkawari Kader, domin ba ni da matsala da ‘ya’yan Iyami na san Amina ba zata bani kunya ba, don haka kaje ka shiryo kazo auran Amina”.
Kader ya cika da farin ciki, dama a satin zai koma gida domin kwanakin 13 Ya diba sun cika, sanda gidan suka ji abin‘daya faru kowa ya yi farin ciki, Amina ce ma an _ kasa gano cikinta, domin taKi murba kuma ta ki yin kuka. .

******************

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Washegari bayan an sauko daga masallaci Abbagana ya Kara biyan sadaki aka maida auren Falmata. da Mukhtar a karo na biyu. . Sai bayan an sauko daga masallaci, sannan ya kira lambar wayar Hajiya Mariya ya sanar da ita. Farin ciki ya cika Hajiyan har ta rasa inda zata tsoma rayuwarta, sai ta dauki wayar Mukhtar ta’ kira shi, lokacin yana falonsa yana danne-danncn computer Fatila tana zaune a kusa da shi cike da farin cikin sa a kusa da ita tana rangwada da iya yi. Kiran Hajiyarsa ya shigo wayar, da sauri ya dauka ya kara a_ kunnensa yana sallama. Hajiya Mariya tace “Sai ka zuba ruwa a kasa ka sha, Falmata dai ta dawo hannunka, yanzu Abbagana ya sake daura muku aure”. Sai ya ji abin kamar mafarki, banda’ mahaifuyarsa ce ta sanar da shi da ya ce tsokanarsa ake yi, to ya san tsakaninsu babu wasan tsokana. Cikin d’aga murya ya ce. “Alhamdu 1i11ahi, Allah na gode maKa. Hajiya na gode da wannan albishir mai dadi na yi miki aIkawari a wannan karon zan riKe Falmata da daraja fiye da baya!” Fatila ta dafe kirji jin ya ambaci Falmata, k0 ba a’ yi mata bayaniba ta gano abin da yake nufi. Ya kashe wayar yama rasa mai zai yi, banda yamma ta yi da a yau zai tafl Maidugun’ amma ya bar wa gobe. Idanun Fatila suka ciko da kwalla, tace Ba dai aurenka aka maida da Falmata ba?” .
Cikin farin ciki ya ce mata, “Haka ne, Allah Ya sake ba ni Falmata a karo na biyu, bayan tsawon wahalar da nasha. Allah na gode maKa”. _  Ya mike da sauri bai jirayi yanayin da , ta sauya ba ya yi waje.
Ita kam fashewa ta yi da wani irin kuka tana jin tamkar zuciyarta zata Balle ta flto . daga Kirjinta, yau ita Mukhtar ke sanarwa an daura masa aure da Falmata babu kunya balle shakka, tabbas duk wani asiri k0 sihiri da suka yiwa Mukhtar din ya karye, babu sauran abin da ya rage. Ta kira wayar Hajiya Kumatu tana kuka, ta sanar da ita abin da ke faruwa.
“Tabbas kwanakina sun kare a duniya, Hajiya na shiga uku!”
Hankalin Hajiya Kumatu ya tashi ainun, ta ce.
“Maza ki kira Diyana ki ce mata gobe ta yi shiri za mu je kauyen Kwarkwasa gurin sabon bokan da aka sanar dani, ba zan yarda ina raye ki yi zaman boranci ba”.
Washegari da sassafe Mukhtar ya yi shirin tafiya Maiduguri, ya fice a motarsa, kamar jira suke yi ya fita suka iso gidan su ma sukai ficewarsu cikin shigar da suka saba tamkar ba matan aure ba. ‘ Yau kam Allah Ya kaddara dubunsu zata cika, domin suna tsakiyar gudu a daji tayar motar gaba guda daya ta fashe, kafin Fafda ta yi wani Kokari motar ta fara juyi akan titi, nan suka dinga ihu babu salati balle kiran sunan Allah, har sai da motar ta yi birki cikin wani kwazazzabo, mutanen da ke kan hanyar suka fara sallalami, suka kawo musu dauki da kyar aka zazzakulo su. Hajiya Kumatu kam ta amsa kiran Allah, domin kanta ne ya fashe duk kwakwalwarta ta zube a kasa, Fatila da Diyana kuma ba su san a halin da suke ciki ba, sai dai kafar Diyana guda daya tun daga gwiwa ta cire fit, wannan shine karshen masu aikata mugun fasadi. Haka nan aka kwashe su da taimakon ‘yan Rungiyar road sefty da Allah Ya sanya suka zo wucewa a cikin motarsu aka yi asibiti da su.
Mukhtar bai yi nisa ba aka kira lambarsa ana sanar da shi maza yaje asibitin Murtala akwai iyalinsa da suka yi hatsari, bai kawo Fatila ba ce, ya yi zaton k0 ‘yan gidansu ne, don haka babu shiri ya juyo da motarsa ya dawo cikin garin Kano. Sanda ya isa asibitin tuni an kai Hajiya Kumatu matuware, F atila da Diyana suna zube a cikin Emergency room abin tausayi, yana isowa dakin ya ci karo da Fatila da Diyana aka kuma sanar da shi mutuwar dayar k0 bai tambaya ba ya san Hajiya Kumatu ce. Idonsa ya cika da kwalla, da aka sanar da shi a dai-dai inda suka yi hatsarin, wato Fatila ta yi satar jiki ta fita Allah Ya kamata banda zuciya irinta musulunci da cewa zai yi bai sansu ba, amma haka ya biya kudin komai aka fara duba su, sannan ya yiwa kanin Fatila waya yace su zo su dauki gawar babarsu.
lta kam Fatila da yake buguwa ce kawai ana jona mata Karin ruwa ta farfado, ganin inda suke ne ya sanyaja tuno abin da ya faru, sai ta fashe da kuka mai tsanani, domin ba ta san halin da mahaifiyarta ke ciki ba, dai-dai lokacin da malam din ya shigo dakin tana ganinshi ta kuma fashewa da kuka tana fadin
“Ka yafe’ min Mukhtar na tuba, ka yafe mini”.
Ya kalle ta cike da takaici yace, “Na yafe miki Fatila, sai dai idan ba ki manta ba, _ akwai wani lokaci da na taba sanar dake idan kika Kara fita ba da izinina ba sannan baki fita da hijab ba, to na yanke igiyoyin aurena a kanki, ban kuma janye wannan maganar ba, don ‘haka a yau kin tabbata ba matata ba, na sake ki Fatila”.
‘ Ta rushe da ihu tana masa magiya amma bai ko kulata ba, ya juya ya nufi kofa ta fin cike karin ruwan da ke jikinta ta mike ta yi kanshi tanai roKonShi, amma k0 taku uku ba ta yi.ba ta yanke jiki ta fadi, a take a nan kafafuwa da baki suka shanye, Shatin jikinta ‘ Ya shanye wato paralize ta kamata. . Ya waiga
da sauri, ganin halin da ta ke ‘ciki ya sanya kira ma’aikatan gurin dai-dai lokacin da wata kanwar babarta ta iso gurin tana kuka, domin sunzo daukar gaWar Hajiya Kumatu ne, yana ganin an rufa a kanta ya zame ya fice a ransa yana addu’ar Allah Ya sauwake mata.
Bai fasa ba duk da rana ta yi masa haka ya dauki hanyar Maiduguri, sai dai za a iya cewa sun yi sabani, domin su Inna Furera da Ammi da wasu dangin sun taho da falmata domin Abbagana yace baiga amfanin zaman nata ba tunda an daura aure ta wuce gidan mijinta kawai. _Ya bada kudin da za a Sake yi mata siyayyar komai na gidanta.
Sanda malam ya isa Maiduguri ya ji yadda aka yi, sai ya ji kamar ya koma Kanon a daren amma haka dole ya haKura ya kwana, washegari da sassafe ya kuma juyowa Kano, kafin ya je ya yiwa Hashim waya ya ce ya turo masa kudi ta account dinsa maza kafin~ya iso garin a wuce gidan Falmata a fara fenti. Ya sanar da mai fentinsa suje su fara aikin. Sanda ya isa garin Kano kai tsaye can gidan nasa ya wuce, ya tadda ana ta fentin har sun kusa kammalawa, amma dole sai gobe za su qarisa. Ya juya kan mota ya nufi babban gida, duk yadda yaso ganin Falmata Hajiyarsa ta hana shi, ya dinga dariya yana fadin.
“Haba hajiya sai kace wani sabon aure zaki dinga Boye ta?” ‘
Hajiyar tasa ta fatattake shi tana fadin
“Koma dai meye ba ka isa ka ganta ba”. Kwanékin ‘yan Maiduguri uku suka kammala gyarawa Falmata gidanta tamkar sabuwar amarya suka juya garinsu, Ammi ma mijinta ne yazo ya dauketa suka wuce Nijar domin ciwon mahaifiyar Isofu din na so ga ya tashi, har abin ya kwantar da ita matuka kamar ba zata tashi ba, shi ne tace don Allah Ya kawo mata Ammi ta nemi gafararta. Sai Falmata taji kewar Ammi ta cikata, domin sun shaku kwarai da gaske. Kwanaki suna ta ja amma Hajiya ta hana malam matarsa, duk da suna da labarin abin da ya faru ga Fatila har ma sun shiga gidan nasu sun musu gaisuwa, amma Fatila har lokacin tana asibiti, domin baki ya murgude, Barin jiki ya shanye.
Da dai ya ga da gaske Hajiyar tasa ke yi, sai ya tattaro kayansa ya dawo gidan ya tare a dakin Rannensa da suka yi aure, hakan ya sanya Hajiyacewa yazo ya dauki matarsa, domin dama tana shiryata ne, yanzu kam ta gama shiryata tsaf sai ta tafiya.
Sanda suka tafi a mota Falmata ta Ki yarda ta had’a ido da shi, ya kula kunyarsa ta ke ji, bai matsa mata ba shi ma sai dai kallonta da yake yi yana dariya kawai. Ransa wasai yana jin kamar yafi kowa farin ciki a yau, a haka suka isa gidan nasu.
Falmata ta sha mamakin yadda aka sake komai na gidan, tayi zaune a gefen gadonta tana Rarewa dakin kallo, yau itace a gidan mijinta masoyinta babu Fatila, yanzu ita kadai ke da shi Allah Sarkin baiwa kenan.
Shigowarsa ce ta katse mata tunaninta, ta sunkuyar da kai kasa. Ya isa kusa da ita ya zauna ya kama hannunta yana wasa dasu yace. Falmata me kike ji a ranki a yau? Ni kam inajin tamkar an mini albishir da gidan aljanna ne, ina jin na fi kowa farin ciki, Falmata na sha wahalar rashinki”.
Jikinta gaba daya ya mutu jin yadda ya sake murza yatsun nata, ta dinga jin wani irin yar tsakiyar kanta, jin yana neman ya sauya darasin ya sanya tace. “Ba muyi sallar godiya ga Allah ba fa malam Ya yi dariya ya ce, “Sunana Mukhtar ba malam ba’, don Allah aci gabada cemini Mukhtar dina yafi”.
Ta rufe fuska tana dariya Kasa-kasa, bata son: tuno abin da ya faru a baya, haka Suka mike suka dauro alwala suka gabatar da sallar godiya ga Allah. Malam jikinsa bar rawa yake yi domin shi kadai yasan irin azabar da ya sha na rashin Falmata na tsawon wannan lokacin, ita kanta Falmata ta yarda ta yi rashin mijinta, sai suke jin kamar karma gari ya waye.
Sabuwar soyayya ce ta barke a tsakaninsu, suna jin kansu kamar yanzu suka fara auran juna, domin basu da fargabar komai.
Kwanakin su bakwai hutunsu ya kare, don haka suka fara shirin komawa Madina, basu yi yunkurin amsar yaran su ba duk da suna son tafiya da su din, haka suka tafl suka bar wa Hajja Iyami su.
A can madina ma sabuwar soyayya ce ta Barks kullum shi ke tafiya da ita a motarsa, ya dawo da ita ita kuma. Ammi sai ta ji ba zata iya zama gidan Ambassador  ita kadai babu Falmatn ba, don haka ta tare a dakin makaranta, duk da Falmata taso ta zauna a gidanta, amma tace ba zata iya zama tsakanin masoya ba, gaba daya rayuwarsu ta sauya, sun zama tamkar Larabawan gaske.
Ina labarin su Hajja Yakolo ne?
Da farko sun yi zaton Abbagana zai yi hakuri ,ya maida auransu, saboda haka basu bar gidan ba, a nan suka ci gaba da yin iddarsu har suka kammala Abba shiru, duk mutanen da suka dinga aikawa Abba yace shi fa a rabu da shi ya gama aurensu, domin shi kadai ya san irin azabar da ya fuskanta a gurinsu. ‘ Haka suna ji suna gani kowacce ta ‘ kwashe kayanta suna kuka da dana sani,ace kamar su gemai-gemai an sake su za su koma hannun iyayensu, me yafi wannan bakin ciki?
Zubaida tuni ta koma gidan mijinta ta kwantar da kanta tana zaman lafiya da shi, hakan ya sanya Abbagana ke yi mata duk wani abu da ta bukata.
Yakura da takurar Abbagana ta isheta sai ta fidda wani cikin zawarawanta aka daura musu aure, ashe mugun dan Kwaya ne irin direbobin nan ne masu lodi gari-gari, kuma matansa biyu ita ce ta uku, ga shi gida d’aya ya hade su sai bayan an daura auren sannan ta gano dan karya ne sanda aka je jere kuwa kowa ya tausaya mata, domin gidan nashi ko filista babu, dakunan ma kowa falle-falle ne don ma dai dakunan manya ne, amma fa babu cin yau balle na ‘gobe, kullum sai ya fita ya samo. Ga Abbagana yace in dai ta kara kaso aureuta sai dai ta nemi wani gidan, ba gidansa ba ga shi mahaifiyarta ita ma zaman karo take a gidansu, domin iyayenta sun rasu sai matan yayye a gidan abin da zata ci ma da jyar take samu, sai Zahra ce ke taimaka mata da Zubaida, kuma tana zuwa gidan ta sami ciki, don haka ,zama ya kamata dole.,,,,,, 
Duk wani abu da Yakolo da Hajja Basma suka yiwa Hajja Iyami na cusgunawa sai ga shi ita ma kishiyoyin nata suna yi mata gasu duk jahilai ne basu da wani ilimi, don haka take kwasar bakin ciki kamar ta mutu, idan bakin ciki ya ishe ta tayi kuka ta more, don ma shi mijin yana sonta tana dan samun sassauci daga gurin§hi, ita da kanta ta san hakKin Falmata da mahaifiyarta ne. ‘
A wannan karon cikin da Falmata ta samu ya sanya ta’ kuma shagwabe wa Malam, ji ya keyi da matarsa kamar ya lasheta, har Allah Ya sauke ta lafiya aka sami Madina, ranar suna ba wani taro aka yi ba, daga ‘yan gidan Ambassador  sai Ammi da janwarta Amina, domin tibi aka yi bikinsu da Kader.
Sun sha shagalin sunansu, wasu kawayensu Larabawa da suke karatu sunzo, yarinya taci suna Mariya sunan hajiyarsa.
Malam yana ji da Mariya tamkar ransa fiye da su Abba, da yake so suma sun dawo hannunsu. Rayuwa ta koma yadda suke so,sai addu’ar cikawa da imani.
F atila kuwa ta zama abar tausayi, domin a shagide take tafiya, Diyana kuwa wannan jinyar tata ita ce karyewar alkadarinta mijinta bayan ta dawo daga asibiti ya rangada aurensa, abin da ‘yan uwansa ke fata.
Duniya dai tayi musu gwatson mage, sai mu ce Allah Ka raba mu da MATACCIYAR RAYUWA. Ameen🙏
ALHAMDU LILLAH
Anan muka kawo karshen littafin MATACCIYAR RAYUWA
Allah ya bamu ikon Amfani da darussan dake cikinsa

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]