[Advertisements⬇️]

MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 29 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 29
maganarsu Hajja Yakolo, abin da kE yiwa mahaiflyarta ciwo, sai dai a can kasan zuciyarta tanata mamakin abinda ya hana mukhtar zuwa ya maidata fidan aurenta tayi zaton hajia zata matsa masa ya maidata dole amma dai ta tattara komai ta barma Allah zataci gaba da addu,a
Haka tabar yaron nata a hannun hajja iyami tanata kukan zuci suka wuce harda abba yan rakiyarta da babban yayansu su hajja yakolo sai a lokacin suka samu labari wohoho ina wuta su turata bakin ciki kamar ya kashesu gashi babu sararin zuwa ayu asiri falmata dai tabar Nigerian cike da tsananin kewan yayanta
Dr usman ne ya kula da halin da malam ke ciki ya tsareshi da tambayoyi da farko yaqi ya sanar dashi saida ta matsa ya kwashe komai na halin da yake ciki ya sanar dashi 
Dr usman ya cika da mamaki yace Dr mukhtar kamar kai ka shiga cikin wannan matsalar koda yake Allah shike jaraba 
bawansa da komai, sai ya toshewa mutum hanyar da zaiga komai, amma Docta tabbas kana cikin matsalar sihiri babu makawa…” 
Malam ya zaburo yana fadin, “Docter Usman ban gano abin da kake nufl ba, kana nufin sihiri ake mini? To waye yake yi mini?” 
Dr. Usman ya tsare shi da ido, yace “Ka yi hakuri da abin da zan gaya maka, a gaskiya natarka Fatila ba ta barka haka ba, ina zargin ita ce ke maka sihiri, amma banda haka ka saki mace tsawon wannan lokacin baka taBa damuwa da yaranka ba? Haba mukhtar sai ka ce shegu? To tsaya laifin me suka yi maka su da mahaiflyarsu kaji ka tsane su?” 
Mukhtar ya yi shiru yana sauraro. Ya daga kai ya kalli Dr. Usman yana fadin, “Mutane da dama sun sha sanar dani Fatila na mini asiri, amma na kasa yarda, sai dai a wannan karon ni kaina na fara zarkgin hakan”. 
Ya kalli Dr. Usman hankalinsa a tashe yace
Docter me kake bani shawarar yi yanzu?” 
Dr. Usman ya ce, “Masha’Allah kai mai ilimi ne kasan ayoyin karya sammu da sihiri, don dai ba kayi be. To yanzu sai ka dage ka yi ta yinsu sannan ka yi ta bin mahaifiyarka har ta yafe maka, sannan ka yi gaggawar zuwa ganin ‘ya’yanka k0 da ba ka dawo da mahaiflyarsu a yanzu ba”. 
T abbas ya ji dadin wadannan shawarwarin da abokinsa ya ba shi, ya dinga godiya sai ya ji ransa ya faIa sanyi, tun daga yanzu ma. . . 
F almata kam sai da Abba ya tabbatar harta fara .lacca sannan suka koma Maiduguri. 
Cikin d’akin kwanan dalibai take dakinsu su biyu ne ita da wata ‘yar Kasar Nijar ce Hajara Amma, amma da Ammi ake ce mata diyar babban Malami ce ita ma a can Nijar din, tana da aure amma bata taBa haihuwa ba. Da farko Falmata ta yi zaton Ammi balarabIya ce, domin kalarta irin tasu 
ce da yake asalin mahaifanta Abzinawa ne masu matukar kyau tamkar Larabawa, ga yanayin shigar’ta da dabi’arta duk irin tasu ce, k0 don kusan a Kasashen Larabawa suka rayu? Sai daga baya ta ji ita din wai ‘yar kasar. Nijar ce. . 
Ta yi mamaki a hankali sabo ya fara shiga ‘tsakaninsu, F almata kam tun bayan Yagana ba.ta kuma jin kawar da ta tsaya mata a rai kamar Ammi ba, don haka ta saki jiki da ita matuka. , 
‘ Ammi ta sanar da Falmata tarihin; 
rayuwarta da yadda take son mijinta matuka, sai dai mahaifiyarshi sam ba ta kaunarta, domin yana tsananin sonta kamar zai mata‘ durkuso bai son Bacin ranta, ga shi diyan Sarkin Damagaran ne. ‘ 
Falmata kam ta ga alama domin idan batada lacca kusan wuni suke yi hira da shewa. A zamansu na wata uku kuwa zuwansa uku ‘ garin kusan duk wata sai yazo da kyar kuma Yake komawa. 
F almata tana mamakin irin soyayyar da yake gwadawa Ammi, har ta ke ganin anya kuwa daman akwai irin wannan soyayyar da gaske? 
Wata rana sun kammala waya Ammi na kula da Falmata da ta tsare ta da ido. Tana ajiye wayar ta kalle ta tana dariya, ta ce, “Ya ya dai?” 
Falmata ta yi dariya cike da kunya, ta ce, “Ina mamakin yadda mijinki ke sonki ne”. . Ammi tayi dariya ta matsa kusa da ita, 
tace Kema idan kika hadu da mai sonki zaki yi mamaki F almata duk namijin da ya fada tarkonki zai jima bai fita ba, har ina tausayin wanda zai aureki ya fara lasar zumarki, ina .. ganin zai iya zama kamar shashasha”. 
Falmata ta yi dariya tace Wai ba ki san bakin jini ne da ni ba kamar me?” 
Ammi ta zaro ido waje, ta ce, “Ki daina fadib wannan magana domin k0  yana fadin irin haka a kanki”. 
Falmata ta yi murmush‘i ta ce, “Ammi 
nafa  taba aurehar da ‘ya’ya biyu, amma mun rabu da mijin”. 
Ammi ta zabura cike da mamaki tana fadin, “Da gaske, wane irin sauna ne ya sake ki Falmata? Don Allah bani labarin wawan nan, ina yaranki kuma?” 
‘ Falmata ta yi shiru idonta ya ciko da hawaye a hankali ta fara bai wa Ammi labarin komai. Ammi ta yi wani irin ihu cike da bakin ciki, ta ce, “Na rantse da Allah wannan shegiyar matar ce ta raba ku, amma 
Mukhtar yana sonki”. _ Ta Kurawa Falmata ido cikEda tausayi, ta ce. “Falmata don Allah kina son Mukhtar 
har yanzu?” 
Falmata ta yi munnushi tace “Ai har duniya ta nade ba zan daina son malam ba, kuma ko da na auri wani namijin zan zauNa da shi nai masa biyayya, amma sona yana ga malam” . “ . Ammi tace “Kina son komawa hannun’ 
mijinki kenan?” F almata ta kalle ta da sauri tace “Ba na 
wannan fatan har abada, bana sha’awar Kara 
zaman aure da Mukhtar, domin ba zai iya hada son Fatila da kowa ba, don haka na ji gwara na yi ta ilimi na rayu a haka”. 
Ammi tace, “Wallahi ba son Fatila yake ba, illa sammu. Idan kin yarda na sanar da mahaifina duk da mahaifinki malam ne amma nasan mahaifina zai fishi sanin irin wadannan tarkunan, wallahi k0 tsafi take sai an karya shi” . 
Falmata tace “A’ a ki dai barta kawai da aniyarta”. 
Ammi ta ce, “Sai kuma ki yi, idan anjima zan sanar da Baba komai” . 
Duk yadda F almata ta so dogewa Ammi ta Ki yarda dole ta Kyaleta akan ta sanar masa din, ‘ .  . .Malam kam ya kama addu’a babu ji babu gani, ita kanta Hajiya ba ta zauna ba, ‘ domin Abba ya tabbatar mata ba za su zuba masa ido ba dole su taimake shi, don haka shi ma’Abba yi yakeyi iyakacin karfinsa, cikin ikon Allah sai ga sammu da tsafin ya fara wargajewa, sai ya fara ganin bakin Fatiia da gidanta, a sannan dabi’unta suka fara yi masa muni, sai ya fara kafa dokoki kala-kala a ransa yana jin F almata kuma matuka. 
Daga inda suka fara tsiya daga wani yini da ya yi a gidan ranar lahadi yaga har yaje ya dawo daga masallaci Fatiia ba ta tashi ba, sai ya kama fada. Abin kam sai ya kama bata mamaki ganin yadda duk ya sauya mata, sai kuma ga fita ta taso ita ma ya ce sam sai ta koma ta sanya hijab wannan ai shigar ba’ ta ’ dace ba sam. 
Ta dinga kallonsa da mamaki baki hangame, can ta daure tace “Wai laflya kuwa Hubby, wane irin hijab ana zaune Kalau? Ni bayan na sallah ai ba ni da hijab, .ko ka manta?” 
Ya yi mata banza ya kauda kansa gefe _ ya ci gaba da aikinsa, ”hakan ya ba ta mamaki matuja, ganin yadda ya share ta ta yi fushi ta nufi kofa kai tsaye
Ya daka mata tsawa yana fadin, “Na sanar da ke kada ki flta kin dage sai kin fita ko, . to ina mai tabbatar miki in dai kika f1ta a haka a bakacin igiyoyin auranki”. 
Ta waigo a gigice kamar zata fasa ihu, shin da gaske ne abin da kunnenta ke jiyo mata k0 kuwa gizo ne? Ta dawo ta zauna a kujera tana kallon sa, fatanta ta ji ya janye wannan kudirin’ nasa, amma sai ta ga ko Kara kallon inda take ma bai da niyyar yi. 
Wayarta ta fara kara tana dubawa ta ga sunan Diyana ne, ta mike’ da hanzari ta nufl daki tana huci. 
Diyana ta fara masifar “Wai ina kika shiga ne har yanzu’ ba ki fito ba, ina ta jiranki?” 
Ta hadiyi zuciya ta ’ce, “Bari ke dai Diyana, yau wani abin al’ajabi ne ya same ni”. Ta kwashe duk yadda aka yi ta sanarwa Diyana. 
Mamaki ya kama Diyanan, tace “Na gaya‘miki yarinyar nan ba zata kyale ki ba, kinfi kowa sanin waye ubanta, wallahi na tabbatar su ne ke karya mana duk aikin da muka yi”. . 
Fatila tace, “To wai yanzu yaya za,ayi, kin san fa ni ba ni da hijab fa”. 
Diyana ta ce, “Balle kuma ni, ina ganin abin da za a yi zan turo Ummi yanzu ki bada ko dubu biyu ne na siyo yadin hijab’ din na dinko miki’sai mu tafi”
Fatila ta ce, “Haka za a yi, maza turota”. 
Amma da yake ‘yan tsiyar suna kanshi ne, sanda Diyana ta iso gidan da hijaban Fatila ta amsa ta sanya suka fito ya kalle ta sama da Kasa, yace“Ina zaki ne Fatila?” 
Mamaki ya cikata, tace “Harka manta zan flta gidan suna ke nan?” 
Ya kalli agogo wanda ya nuna shida saura na yamma, yace “Ai yamma ta yi, ki hakuri ki koma kyaJe daga baya ki yi musu barka”. 
Ta cika fam kamar zata fashe, ta kalli Diyana wacce ta kanne mata ido sannan ta matsa kusa da shi da zummar rarrashi, amma duk yadda ta bullo sai ya buge musu, ga shi gurin da zasu guri ne mai muhimmanci a rayuwarsu’, da dai ta kula abin nasa ba na 
rarraShi bane, sai fa bude wuta ta fara masifa. 
Ai kamar wanda yake jira, sai ya mike yana kumfar’ baki har da nunata da yatsa daga karshe ma yace ya sanya doka nan da sati guda ma ba ta isa ta flta ba, don ya gaji da yawonta na tsiya. 
Nan fa ta ‘kuma hasala ta kama zagezage, shi dai ya wuce ya barta a nan tana tijara, Diyana ta girgiza kai ta ce, “Lallai sai kin yi da gaske, gaba daya ya sauya miki
Datanaso dabata so hakata zauna a gidah tsawon sati guda sai dai ta tura Diyana ‘ da Hajiya Kumatu gurin bokan, shi kam ya kula’ a yanzu ba shi da sauran dabara domin 
duk aikin da ya yi k0 awa ba zai yi ba zai‘ 
lalace, idan y‘a gaya musu gaskiya kuma ya daina cin kudi, don haka ya dinga gilma musu karya irin ta bokaye’. 
*****
Kwatsam malam yana zaune a offis ya ji kewar ‘ya’yansa da bala’in sonsu suna yawo a ransa ranar ‘haka ya wuni ga wani irin son Falmata dake ratsa kwanjinsa ya kudire a ransa dole gobe ya tafl Maiduguri. 
Yana isa gida ya fara shirin tafiya, Fatila ta tsare shi da tambayar ina zai je. Bai k0 dubeta ba balle ta yi zation zai yi shakkarta yace, “Maiduguri”. 
Tamkar ya watsa mata ruwan dafafflyar dalma ta waro ido waje tana kuma ,tambayarsa, ya waigo yana kallonta, yace. “Idan dai ‘ba ki sami matsala -a , kunnenki ba neba na tabb’atar kin ji abin da nace, zan je Maiduguri ne gurin ‘yayana
Ta zame ta zauna akan .kujera ranta yana zafl, sai kawai ta mike ta bazama daki ta kirawo wayar’boka, umarni ta ba shi akan ba ta. son yaran nan su Kara kwana d’aya a duniya. ‘ 
Ya ce, ta tura kudi zata ga aiki, nan da nan ta kira wayar Hajiya tace a kaiwa boka kudi. 
Sai dai abin da ya firgitata, duk da makud’an kudin da ta kashe ko gezau bai yiba a tafiyar washegari, ta kuma dinga baza kunne 
ta ji ance yaran nan sun cika, amma har ya kammala shirinsa ya fice shiru makatau, don haka sanda ya yi mata sallama sama-sama ta ji shi. Yana flta ta figi gyalenta ta fice ita ma. 
Da sassafe ne amma duk da haka sai da ya fara biyawa gidan iyayensa, sanda Hajiya ta ganshi sai da gabanta ya fadi, ya gaisheta. ta amsa a daqile cikin faduwar gaba yace. 
“Muna bukatar addu’ arku domin zan wuce ganin su Muhammad yanzu insha ‘Allahu ” . 
Wani irin dadi ya cikata har sai da ya bayyana a fuskarta, wannan wace irin magana ce mai dadin saurare? cikin farin ciki ta ce, “Lallai ka ce doguwar tafiya zaka yi? Bari na bada sallahu a kaiwa maigidan nawa”. 
. Sai ta mike da azama. Sai ya ji ransa ya yi sanyi ’ganin sakin fuskarta yau gare shi. Ta dinga hado kaya kama daga turare, darduma , kayan zaKi kai da tarkace kala-kala sai da ta cika wata katuwar jaka tace a kai musu, har bakin Kofa ta rako shi tana masa addu’a, wannan ya f1 komai yi masa dadi a ransa, don 
haka koda ya sauki hanyar Maiduguri jinsa yake cike da nishadi da walwala. 
Fatila kam tana isa gidansu ta sakawa mahaifiyarta kuka. Hajja Kumatu ta nisa tace“Wallahi har na gaji da abin nan Fatila; wai ni ya ya kike son na yi da rayuwata ne?” 
Ta kalli mahaiflyar tace, “Au haka ,kika ‘ ce Hajiya? Kin san ya tafl Maiduguri kuwa yanzu, kuma kin san daga can zai dawo da 
ita?” 
Hajiya ta kada kai cike’ da baKin ciki ‘tana fadin “Kai Wannan yaro an yi jarababbe ‘ wallahi, muyi ya karya, mu yi ya karya yanzu abu daya ya rage mana Fatila, tunda kina son Mukhtar ba za a kashe shi ba, amma kije ki yi ta hakuri idan ya dawo da ita daran da aka :dawo da ita zamu tura‘ yan fashi su kasheta bayan yi mata fyade kawai mu huta :da wannan jidalin”. 
Sai a sannan ta ji sanyi a ranta, tace Haka za a yi Momy, idan ba haka ba kuwa 
Kina gab da rasan‘i wallahi” . ‘ 
Da wannan shawarar suka gama kulle Kullensu. 
Da ya isa Maidugurin sai da ya sami masauki sannan ya sake yin wanka ya yi sallah, ya sake kwalliya cikin wani tattausan 
yadi ruwan madara mai kananan zare da 
taushi, wanda aka yi masa siririn aiki wuya da hannu ya yi masa kyau ainun ya sanya, burinshi ya ci karo da Falmata ya burge ta. 
Ya .isa gidan an kammala sallar isha’i, don haka ya shiga masallaci ya-yi tasa, tunda ya shiga Abba ya hango shi, farin ciki ya cika Abba matuKa, don haka koda ya idar ya ji an ambaci sunansa, ya daga kai ya kalli Abba da ke shirin ficewa, kunya ta cika shi. Ya mike sumi-sumi ya bi Abban a dakinsa na saukar baki suka sauka, tun kafin su gaisa Abba ya sanya aka dinga kawo masa abinci kala-kala, duk da ya ciwo abinci daga hotel ya saki ciki ya ci sosai, don ya sanya Abba farin ciki. 
Bayan ya kammala cin Abban ya ce, “Yau kake tafe garin namu ke nan?” 
Ya sunkuyar da kai yana murmushi, ya ce, “Wallahi, wai nazo ganin su Muhammad ne
 Abba ya yi dariya ya ce, “Masha Allah, ai hakan ya yi kyau, bari a kawo maka su”. 
Ya mike ya shiga cikin gidan, can jimawa sai ga shi da yaran, Abba karami har ya fara dabo. Mamaki ya cika shi, wata irin soyayyar yaran ta cika shi, ya dinga daukarsu yana yi musu wasa. An yi sa’a kuma ba sa kiwya sam, don haka suka saki jiki da shi. Ya jima gurin yaran suna wasan yana son yace a kirawo ‘mamansu su gaisa, amma ya kasa. Haka ya tashi ya tafi cike da farin cikin ganin yaransa. 
Washegari kuwa sanya su ya yi a mota suka yi ta yawo, ya sai musu wannan ya sai musu wancan, sai yamma likis suka koma ya wayance da zai shiga zai gaida mutan gidan malam ya yi masa jagora, su Hajja Yakolo ana farfajiyar gidan ana ta hada turaruka masu dauke da abin suka ganshi katsaham sai da suka flrgitaYakura taji gabanta ya fadi, ganin mijin ‘yar uwana ita sai yau ne ma ta yi masa kallon tsaf, sai ta ji ina’ ma zai dawo yace 
Hmm bari mu tsaya anan asiri dai ya daina tasiri akan falmata da malam mai darasu shin me zai faru ku biyoni cikin tsanaki don ci gaba da sauraron wannan qayataccen littafin

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]