MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 25

MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 25
Kafin ta haihu namiji ke zuwa dakinta da zarar ta haihu kuma sai ta fara zuwa turakar maigida k0 ba haka bane
Tayi dan  dariya, tace“Au ai bansan haka bane  daga yau zan dinga zuwa kayu  hakuri”. 
“Ya wuce amma daga wannan karon bazan  kuma hakura ba”. 
_ Sun jima suna hira abin yana ta ginnamawa Falmata a ranta, sai da ya kammala cin abincin ta kwashe kwanukan kaf. 
Sanda ta isa falor tuni Muhammad ya yi bacci, don haka ta amshe shi ta jc ta sake shirya shi da parnfas itama ta yi shiri mai kyau da tsari, domin ‘tana tunanin yau ne zata nemi lada mai dama na aure. “Tabbas_turarukan da take amfani dasu masu dadin Kamshi ne dake sanyaya ran mai shakarsu, ba zaka iya tantance takamaiman kam’shin da ta keyi ba. don shi kansa Muhammad turarensa daban ne 
Sanda ta fito falon, ta tadda tuni jidda ta wuce dakinta, ta kalli agogo goma sau‘ra ta san lokacin kwanciyarta ne ya yi. Kai tsaye ta wuce dakin maigidan nata. 
Yana kan computcr yana ta aikin da kullum 
bai rabo da Shi, ta shiga da sallama, kamshinta ya ~ 
dakeshi, ya daga kansa da sauri yana kallonta tabbas yaugaba gaba daya ta sauya masa, kcwarta ta ishe shi tunda ga shi har ta hana shi fita gurin Fatila yau, wacce keta neman wayarsa tun dazu ba ta samu ba, saboda kashe wayoyinsa da ya yi gaba daya ya sanya su acaji. 
Daga yanayin kallon da yake mata ta tabbatar yau kam komai ya wanku a zuciyar mijinta idan ma laifi ta yi masa kenan. 
A wannan daren kam sun tabbatar da sun yi kewar juna sosai, shi kuwa Muhammad bawa‘n Allah da_ma yaro ne mai tsananin hakuri, don haka har asuba bai farka ba, kamar yasan iyayen nasa yau suna shan amarcinsu ne daman. 
Fatila kam tana can kamar zata fashe ta cika fam, ta tabbatar yana gurin matarsa ne saboda haka tsanar F almata kullum kara cika ranta yake tabbas yarinyar ta zame mata babbar baraZana, kuma masifa arayuwarta, shin ta ya ya zata yi maganinta? 
Yadda suka kwana faranta ran juna, haka ita ma Fatila ta hanawa idonta bacci ta kwana kuka da bakin ciki, shegen kishinta na masifa ya hanata motsawa ;. . dama zata hadiye zuciyar tata ta huta gaba (faya. 
*** *** 
Tun daga wannan ranar abubuwa suka fara dawowa dai-dai, tabbas Falmata ta san Allah kadai ke amsar addu’o’inta. Abu daya ke damunta, rashin ko’in’kula da Mukhtar din bai yi da dansa, wannan abu kam yana mata ciwo ainun, sai dai tana ta addu’ar Allah ya kawo sauKin abin shi ma. 
Fatila kam ta kula da sun shirya da matarsa, domin yanzu ba ya shantakewa a gurinta kamar yadda ya saba a da, amma tana tsoron yi masa maganar k0 Korafl, domin mahaifiyarta ta gargadeta da yin hakan a gare shi, kada garin neman gira su rasa idanun duba, su yanzu fatan da suke bai wuce ya yi maganar komawarta gidanta ba, domin sunyi masa magana ya nuna sai dai su Kara hakuri, domin dole sai ya sanar da mahaiflyarsa, wacce yaje tsoron tunkararta da maganar, domin har yau ya kasa tunkarar wani ya sanar masa da ya maida Fatilar don bai san yadda za su dauki batun ba. 
Falmata kam sai shirin tafiya ganin gida take yi cikeda doki da zumudi, wata yana Karewa kuwa kamar yaddah ya yi mata alkawari yayo mata 
tsaraba mai dama, da Jiddah suka shirya zasu tafi domin har lokacin basu koma makaranta  ba. 
Hajiya Mariya ma ta bata tsarabar farar shadda masu dankaren kyau da tsada kala biyu da turaruka tace a kaiwa Abbagana. Taji  dadin hakan Kwarai da gaske. 
Har tasha ya kai su, sai da ya tabbatar motarsu ta tashi sannan ya juya gida da kewarsu, wannan taflyar ita ta haddasa komai ga Falmata, wanda har ta yi da na sanin tafiyar tata. 
Su Hajiya Kumatu kam suna da labarin tafiyar’Falmata din, domin suna bibiyar lamarinta sau da kafa, don haka sun yi alkawarin ta tafi kenan, ita da Kano sai dai tazi da ziyara, don haka suka ci gaba da dukufa aikata mugun nufinsu a gare ta. 
Watarana da daddare yaje gurin Fatila yaci abinci, wanda aka barbade shi da sinadan’n sanya matsananciyar bukata, hatta lemon da aka ba shi. sai da aka sanya wannan sinadarin, don haka yana kammala cin abincin maganin ya fara ajkinsa a gare shi. Bai yi wata-wata ba ya kama Fatila yana dariya da nufin isar da abin da kwakwalwarsa ke ingiza shi yi. 
Dama a shlrye take, sa1 tace
ba zai yiwu ba suyi wani abu a gidansu,ba sai dai su tafi can gidanta., 
Bai yi musu ba ya mike yace ta dauko makullan can gidan, ta shiga ta yi ‘yan mintina ta dawo wai bata ga makullin ba. Da yake tini sun amshe na hannunsa akan wai bata ga nata ba. 
.’ldanunsa sun sauya launi ainun, yace
“To yanzu ya ya kike so a yi? Kin san kamar ni bai dace a ganni a hotel ba Fatila, ki taimaka mini”. 
‘ Da yaudara tace“Wannan ma ai bai taso ba, tinda kace falmata ba ta nan mai zai hana mu tafl can gidan nata tunda babu kowa a gidan?” 
Bai yi musu ba ya amince da wannan shawarar tata, domin idonsa ya rufe ainun, haka suka flta tana dagawa mahaifiyarta hannu, wacce ta san komai. 
Sanda suka isa gidan ta so ace dakin Falmatan na bacci suka nufa, amma taga sun wuce dakinsa, duk da haka ba ta damu ba, domin shirin da suka yi na kwana ne don haka ta bi shi can dakin nasa. 
Bayan komai ya kammala sai gaji daya jikinsa kuma ya mutu, wani irin bacci mai nauyi yakeji, ta kada kai da kissa tana fadin. 
Amma ya dace Ka maida ni gida k‘afin ka yi baCCinka ko?” 
 Ya yi mika yana lumshc ido, yace‘Ki yi hakuri F atila na baki kudi ki d’auki drop mana”. 
Ta waro ido waje tana fadin, “Kasan karfe nawa kuwa yanzu? Sha biyu saura kwata, a ina zan sami motar haya yanzu?” 
Ya langaBe yana fadin, “Tokiyi kwanciyarki a nan mana?” 
Ta yi wal da ido tan’a fadin, “Amma ba ka tunanin abin da Momy zata cc, k0 mutane su ga mun kwana a nan?” 
Ya janyeta daga jikinsa yana fadin. “Momy ta san ke matata ce ai, su kuma mutane za su iya haramta abin da Allah Ya halatta ne? Don Allah kwanta mu yi baccinmu”. 
Ba tayi musu ba ta kwanta tana dariya cike da jin dadi tabbas yau burinsu zai kammala cika, ta F almata kuma ta kare! _ 
Tana jin sanda bacci ya daukc shi, ta yi shieu a jikinsa kamar baccin ta keyi ita ma, sai da ta tabbatar baccin nasa ya yi nisa sannan ta janye jikinta daga gare shi, lokacin qarfe saya da wani abu na dare. Ta mike ta fara aiwatar da abin da 
.sukayi na hade-haden tsafin nasu 
na raba tsakaninsa da baiwar Allah Falmata, wacce ke can ba ta san wainar da ake toyawa ba. Ta shiga dakin Falmata ta gama bincike ta kwashe mata gwala-gwalai har da  kuda denta, sannan ta Dauke rigunan wasu manyan atamfunanta ta watsa waje can tsakiyar unguwa, k0 tsoro ba ta ji ba, sannan ta fara barbadawa da 6oye asirin da tazi da shi. Sai da ta kammala sannan ta Koma ta kwanta. 
Da gari ya waye ya farka da jin tsanar gidan, sai yake jin kamar ana watsa masa garwashin wuta a zuciyarsa, gaba daya gidan ya ishe shi da wani irin mugun zafi. har da wari-wari ma, don haka ya azalzali F atila da ta shirya su bar gidan, tamkar zai cinye ta don masifa lallai sai sun bar gidan. Ita kam farin Clki ne ya cika mata zuciya, domin ta tabbatae aikinsu yayi tasiri ke nan? 
Haka suka fuce yana flta harabar gidan, sai ya ji kamar an masa rahama ne, ya dinga ajiyar zuciya. F atila ta kula da shi, amma sai ta nuna kamar bata kula din ba. 
Yana ajiyc ta a kofar gidansu, ya wuce ofls. ‘T‘a shiga gidan da ihu tana sanar da mahaif’lyarra da Ditana wacce ta yo sammukon zuwa gidan donjin abida ya faru suka dinga ihu da tsallen murn sai kace
ba zasu mutu ba, Sun dauki rayuwa da zafl, sai dai mu bisu da addu’a kawai
Kamar yadda ya saba kowama gidan, ya koma don ya yi wanka ya sauya kaya, amma yana shiga gidan ya ji abin da ya dinga ji da safe na yanzu ma har yafi na d’azun. don haka kasa yin komai ya yi ya fice daga gidan da hanzari cike da damuwa. 
Ya jima a motarsa yana tunanin abin yi ya gasa, haka ya ja motar tasa ya nufl gidan su F atila, s‘ai da ya kwashé tsawon lokaci don har wajen sha biyun dare ta wuce sannan ya nemi hanyar gidansa. 
Sai dai tun daga bude Kofar gidan ya ji tamkar an watso masa ruwan dalma. Da sauri ya maida kofar ya rufe yana huci. Ya jima tsaye a bakin kofar kafln ya kuma kwatanta budwwa yaji irin abin da ya ji da farko, daga karshe dai a cikin motarsa ya kwana. 
Hashim da ya shirya‘ tafiya makaranta da wuri, ya yi mamaki da yaga Yayan nasa kwance cikin mota da alama a nan yayi bacci, ya nufe shi da sauri yana kwankwasa glass din motar don ya tabbatar da k0 lafiya? 
Ya tashi yana mutsukc ido da salati, ganin 
Hashim tsayea ya tuna abin dake faruwa yayi dan yaqe yana fadln. 
“Makullin gidan na yar kada ka damu babu komai” .  
Hashim yace Amma Yaya malam ai da kake ka kwankwasa min da na bude maka dakina ka kwanta, kwana a mota ai bai dace ba”. 
Yace, “Na gode ba ni makullinka zan shiga dakin naka na yi wanka, amma don Allah jeka gurin mai wankin can na gidan kasa kace idan ya kammala wankina k0 kala daya ne ya baka sai ka kai mini d‘akinka”. 
Hashim ya amsa da, “To”. Ya wuce aiwatar da abin da yayan nasa yace
Da daddare da ya isa gidan su Fatila yace lallai dole ta tare a gidanta gobe Mamaki da dadi ya cika su, tace “kai da kace sai ka sanar da Hajiyarka?” ‘ 
Ya sha kunu yana fadin, “Ni dai ga abin dana ce kawai, k0 ba zaki bi umarnina ba bane?” 
Ta yi fari  da ido da salonta na yaudara tace, “Wace ni? Allah Ya kai mu goben”. 
Daren kam a dakin Hashim ya kwana, washegari tunda safe su Fatila akaje aka kama gyara gidan da ‘yan binne-binne da aka saba, don haka daga office gidanta kawai ya wuce
MAIDUGURI 
Falmata kam ta isa Maiduguri cike da tsananin farin cikin ganin danginta da iyayenta, duk yadda Iyami ke jin kunya sai da ta yi murna da zuwanta musamman ganin yadda diyar tata ta murje ta yi kyau, ga yaronta shi ma bu1-bu1 da shi, hakan ya nuna mata tana cikin kwanciyar hankali
Shi kansa Abba ya cika da muena, haka ta dinga bai wa kowa tsarabar da tazo da ita,‘ sanda ta isa sashin Hajja Yakolo ne kam taga kallon banza, domin kamar ta shaketa ita da ‘ya’yanta, don wata biyu ke’nan da mutuwar amen Yakura, shi kuwa Abbagana yace babu ruwansa, domin har ya gaji da kawo Karafr da mijinta yake, kullum su kenan masifa. Daga Karshe baya gari ta rotsawa kishiyarra kai jini ya dinga zuba suka kai ta police station, sanda Abbagana ya ji sai da ya yi hawaye don bakin ciki, darajarsa ya sanya aka saketa bayan ya kashe kudi
Maimakon da ta koma ta saduda sai ma abin da ya karu, shi kansa mijin ba ta barshi ba, da ya dawo ya ga abin da ta yiwa matarsa har da dinki ya hauta da fad‘a ita kuma ta dinga zaginsa, haka ya hakura ya gyale ta. 
Sai dai wani darw ranar girkinta dOn uwargidan ta shiga dakinsa sanar da shi wani sako, lokacin ita kuma Yakura ta fita daga dakin ta dawo ta tarar da su, ai kuwa sai ta fasa ihu wai ta kama kwartaye, ‘yan gidan suka shiga a tsorace sun zaci wani abu ne. Bakin ciki ya cika maigidan .ya kama yi mata fada ta kama zaginsa, ya dalla mata mari da yake a gaban ‘ya’yansa da matansa ne kawai sai ta ci kwalarsa tana rashin mutumci, da yaga abin ya yi yawa sai ya saketa
Ya je ya sanar da Abbagana duk abin da ya faru. Takaici ya cika Abban ya dinga ba shi hakuri, domin dai ta kunyata shi, don haka Abba bai taBa cewa yaya aka yi, ashe auren wance ya mutu ba har yau, su kuma ba su ce masa auran nata ya mutu ba ga shi har tsawon wata biyu, dama tunda ta tare a gidan take tsarin iyali don tace ba zata haihu a gidan yawa ba. 
Ita kuwa Zubaida yaji tayo, ga shi tana da ciki, ita ma Abban ya ganta amma ya tattara ya watsar, domin ya yi fadan har da duka akan yin yaji, amma a banza. Su a zatonsu bai san tana gidan ba, don duk wata hanya da za su hadu ba ta Yarda bata san tun washe garin da ta taho ba mijinta yazo biko yana bawa Abban hakun’
sanar da shi abin da ta ke masa. 
Abba ya cika da mamaki domin hatta kwana a gidan ba a sanar da shi ba, don haka yace da mijin yaje kawai abinsa ya kyaleta ita da uwarta duk randa suka sanar da shi tana gidan ya yi masa magana, shi kam mijin nata daman darajar Abban taci har yazi bikon, don haka sai ya ji did ya huta kwana biyu. 
Sanda Falmata ta gansu ta d’an yi mamaki, tace“Laa Yakuxa da Zubaida ashe kun zo gidan, ina shirin gobe naje gidajen naku?” 
Suka galla mata harara, Yakura tace “Ke rufe mana baki, mun san ai munafukar uwarki ta sanar daje muna gida za kizo da wani guntun tsigudidinki”. 
“Ku rabu da shegiya yadda suke murna kuna gida wallahi ita ma sai auren nan ya mutu, in dai ina raye… To wai uban me ma kika shigo yi min ne?” Hajja yakolo ta doka mata tsawa. 
Da hanzari tace“A’a, dama nazi gaishwki ne, ga tsarabarki nan”. . 
Ta kuma katseta, “kada ki sake ki ajiye mini komai a dakina k0 an gaya miki ni ma matsiyaciya ce irin uwarki? lye? Kwashe tsiyarki ki bar mini daki”, 
Haka F almata ta kwashe kayan ta nufi waje ranta a Bace taga randa ,wadannan mutanen za su koma yin rayuwa mai tsafta irin ta kowa. Sun kasa gane kullum MATACCIYAR RAYUWA mara amf‘ani suke, al’amarin nasu kam yana bukatar addu‘a matuka. ‘ 
A sashin Hajja Busam ma hakan ce ta kasance, ta gama zazzaga mata masifa ita ma ta fice a ranta tana a haka dai za a kare, Allah dai ya shirya’. 
Sashin Hajja Kahum ta. sami amsa ta gari, ta Zauna suka dinga hira, hajjah tana ta tambayarta ‘yan Kano, anan yayyenta suka dinga shigowa har da masu auran suna matukar son Falmata don haka har da su aka dinga hirar, ba ta koma sashinsu da wuri ba sai da ta jima, don ma dai ta baro Jidda da a nan sashin Hajjan zata kwana. 
Sai washegari Yagana ta ji labarin zuwanta, domin ba ta dawo da wuri ba, ranar ma kwana ta yi a makaranta, ta shigo gidan tana ihu da‘ tsalle, domin ba taje suna ba lokacin suna tsaka da jarabawa, sun dan yi. hutu tana shirin zuwa kano aka kuma komawa makaranta, Falmata ta yi murmushi ‘ har ta gaji son idan ta kira Wayarta bata dagawa. Nan ta dinga lallashi da ban baki da
‘ Falmatan tace da Jidda kada ta Sake ta bata Muhammad din ma, sai randa ta je Kano ta ganshi. Da kyar ta samu ta. lallaso Kawar tata suka koma hirar yaushe gamo, F almata tana na tambayar kawaycnsu. 
Tunda ta zo kullum sai Yagana ta shigo gidan idan ta dawo daga makaranta. 
Tunda ta dira a garin ta dinga bi tana gaida dangi, duk inda zata ta kan tafi da tsarabarta. Kwananta biyar a garin ,,,,,,,,,,,, ta haihu, dama tunda taje gidan ta ga yadda take takawa da kyar ta san lallai ta kusa haihuwa, hankalinta ya tashi, domin’ sati daya mijin nata ya yarda ta yi, ga shi saura kwana biyu su juya. duk da mijin nata ba ya kiranta domin tun bayan jin sun iso laflya bai kara nemanta ba, haka bai hanata yanke shawarar tuntuBarsa ba ,ko zai barta ta yi suna. 
Sai da ‘daadare ta kwanta ta yi kiransa, lokacin suna falo shi da F atila suna hira, sarai yaga kiran nata yaKi dagawa har ta kira sau biyu hakan kuwa ya yiwa Fatila dadi. don yadda ta ga ya hade rai ta -labbatar kiran wayar F almata ne, sai a kira na uku shi ma har ya-kusa tsinkcwa sannan ya daga ransa a Bace yayi sallama. Gabanta ya yanke ya fadi jin yadda gakc amsawa a dakile ta dakc tace
“Ina wuhi malam?” ~ 
Ya amsa a dakile, “Laflya kalau”. 
Tayi dum-dum cike da tsoro, can ta daure tace “Dama Zahra ce ta haihu yau Shi ne na ce kabani’  alfarma k0 zaka barni har a yi suna?” 
Shi sam ya ma manta da batun randa zata dawo, balle don ta wani Kara kwanaki don haka yace Ki yi sunan mana”. 
Duk da yadda ya yi lafazin babu wani nuna kulawa hakan ya yi mata dadi  don sai da ta doka tsalle tana godiya, shi dai yakashe wayar-yana kallon Fatila da ta bade rai matuka, tamkar zata fasa ihu ta keji. Ya koma kokarin rarrashinta ta hanyar janta da hira, ‘da Kyar ya samu ta dan saki ranta suka ci gaba da hirarsu. 
Falmata kam dadi ne ya cikata sai dai a can kasan ranta tana tunanin yadda Malam bai damu da ita ba tabbas sai a yanzu ta yarda matar shige ba ta daraja, a ganinta hakane ya sanya mijin nata bai damu da ita ba. 
Amma dai ya ya ta iya da ranta, tunda dai ya barta ai ta godewa Allah da ya sanya aka barta
Hajiya Mariya da Hajiya Binta sun sami Zuwa sunan, domin an sanar da su. Abba kam ya ji dadi matuka da suka zo din, don zama yayi a 
dakin da aka sauke‘ su daren sunan suka yi ta hira. 
Washcgari kam gurin suna Falmata ta f1to shar, kowa ya kalleta ya san tan cikin rufin asiri matuka, domin daga suturar da taje jikinta har ta danta sun nuna hakan, balle gwal din da ta dankara ‘yan uban nata kam sai buntsura baki suke ana habaici, ita kam ko a jikinta, ita da maijego suka dinga sha’aninsu cike da farin ciki. 
Tabbas mijin maijegon’Zahra ya yi rawar gani, komai ya yi mata gwanin sha’awa, babu wanda zai raina masa.
Bayan suna da kwana biyu su Hajiya Mariya suka yi shiri har da su Falmata za su taho, an hada musu goma ta arziki, musamman Jidda ta sami alkhairi da yawa, don Abba sanyawa ya yi aka siyo mata laffayu masu kyau da dan karen tsada kala uku, su kuma’ matan gidan musamman Hajja Iyami da Hajja Kaltum ‘suka cika ta da turaruka masu kamshi irin wanda takeso, ga kayan shafa irin na , ta yi murna matuka da gaske. 
_ KANO 
Har gidanta Falmata aka sauketa da yake da direban gidan suka tafi, sun shiga gidan a gajiye tobus suka fara watsa ruwa. 
Falmata kam duk sai ta ji gidan ya yi mata kunci, amma sai ta kunna karatun qur’an, cikin ikon Allah ta ji komai yana sanyi a ranta, duk da ta gaji sai da ta shirya, don ba ta sani ba.ko maigidan zaizo da bukatarsa, sai dai abin da ya bata mamaki bai wuceganin har dare ya tsala bai iso ba. ita dai har bacci ya dauke ta ba ta ji duriyarsa ba, bayan kuma‘tunda suka taso ta sanar da shi bayan sun iso ma ta gaya masa. 
K0 da ta tashi da asuba ma ba ta ji motsinsa ba, mamaki mai tsanani ya cikata na rashin kwana a gidan, ba zata yarda mijinta yana bin mata ba, domin tasan mutum ne mai ilimi da matukar tsantseni, amma tana tunanin inda yake kwana din. 
Da safe Hashim ya shigo karyawa domin tun dare yasan sun dawo a nan ne ta yi karfin halin tambayarsa. 
“Hashim yayanka daman bai kwana a gidan ne?” ‘ Hashim ya kalle ta yace “Ina jin bai san kun dawo ba, tun rannan makullinshi ya fadi, ina ganin shi ne dalilin da ya hana shi kwan’a a gidan. 
‘ Rabta yayi dan sanyi jin abin da Hashim yace, duk da tasan suna isowa garin Hajiyarsa tai masa wayan cewar mun iso kalau. Yayi musu sannu da zuwa. 
Har yamma tana zuba idon ganin ya shigo gidan amma shiru kamar ta kyale shi, amma sai taga gwara dai ta Kara sanr da shi k0 bai san har da u aka dawo ba? 
Ta kira wayarsa ta jima tana Kara kafin ya daga k0 daya dinma yadda ta ji muryarsa a dakile tasan bai yi farin ciki da jinta ba. Bayan sallama sai ya yi wani jim cike da ” Bacin rai. ‘ Tayi iarfin halin gaishe shi, ‘shi ma da kyar ya amsa ya dora da cewa, “Lafiya dai k0?” . Ta tattaro dauriya tace“A’a daman cewa nayu bari na sanar da kai mun dawo tun jiya…” Ya katseta da sauri, “Ai na sani, ayyuka ne suka min yawa  shi ya sanya ban shigo ba”. Ta yi dan jim, sannan tace, “Shi kenan, 
Allah Ya sanya ayi aikin lafiya”. 
Bai .ce komai ‘ba ya kashe wayar. Ta kalli wayar cike da tsananin mamaki, ta jima tana kallon wayar to ita kuwa wacce irin kiyayya mijin mata ne‘? Tunda take dashi bai taBa 
kwana‘ a offis saboda aiki ba. duk yawan aiki yakan dawo gida ya yi shi; amma dai komai yayi zafi maganinshi Allah
Hmm ana juya malam mukhtar kamar waina
Bari mu dakata anan don banga page 109 da 110 ba zan bincika sosai donmu dora daga inda muka tsaya afwan please ? 

About Ismail

Check Also

MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 33

MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 33 Faransa ne, don haka suje da wayewa da dabi’u irin na …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *