[Advertisements⬇️]

MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 12 - Bankinhausanovels
Thu. Mar 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 12
ya dinga shiri ba ya jin k0 offices zai iya zuwa ba tare da ya je yaga Fatila ba, ga shi tun asuba yake neman wayoyima amma duk suna kulle
Karfe bakwai da rabi ya fice. Kamar daga sama suka fara jiyo horn sinsa, da yake gidan babu maigadi sai dai a bude wa mutum, Fatila cikin doki ta ke fadin. 
“Momy wallahi horn din motar Mukhtar ne, jeki kuma ki gani, ga shi bana son ya ga gazawata da naje na bude masa, da an san zai zo ma ai da da wuri zamu bude kofar ma”. 
‘ Hajiya Kumatu ta mike da sauri ta nufi kofar ta bude, ai kuwa sai ga motar Mukhtar, ba tace masa kanzil ba ta koma cikin gidan, shi kuma ya sami guri ya yi parkmg ya fito ya nufi , gidan gabansa yana ta faduwa. 
Ya jima jikin kofar yana bugawa sannan Fatilan ta zo ta bude, ta wani kalle shi a sheke kamar ba ta yi ‘murna da zuwan nasa ba, shi kuwa wani sanyi ya ji a cikin ransa, sai ya ji kamar ya rungume ta don dadi. Ya kalle ta yana dariya. 
“To a bani hanya na wuce k0?” 
“Ka wuce ina? Ai nan gidanmu me ba naku ba 
Ya yi dariya, “To masu gida, ai nan sai dai kice gidan Momy ne, gidanki yana can Rijiyar Zaki k0?” 
Ta kwaBe baki ta koma cikin falon. 
_ “Wace ni, gidan Mukhtar dai mijin . Falmata, ni komai na ya gama zama a gidan”. 
Jin ta ambaci sunan Falmata sai ya ji kamar an watsa masa wuta gaba daya ransa ya Baci, domin tunda gari ya waye ya ji babu abin da ya tsana a duniya sama da ita, ko sunanta bai son ya jima balle ya ganta da idonsa. . 
Ganin yanda ya sake gumtse fuska daga ambaton sunan Falmata ya faranta mata rai, ta tabbatar lallai aikinta ya yi kyau. 
Ya sami guri ya zauna ita kuwa ciki ta yi shigewarta, ya bita da kallo kamar ya kamota yake ji. Kusan minti goma sannan ‘Hajiya Kumatu ta iso falon ya gaishe ta a mutunce yana wani sunne kai. 
Ta dube shi da kulawa, tana fadin, “Sai kuma ga Fatila a gida, idan gajiya ka yi da 
aurenta ai sai ka kawota da kanka kamar yadda kazo ka aure ta”. 
Ya dinga rantse-rantse da neman ya kare kanshi. Ta dinga yi masa yawo da hankali domin ta ga yanda aikin nasu ya yi da shi. Da kyar ta hakura tace bari ta kirwo masa Fatilan ya ji idan za ta koma. 
Gabansa ya dinga faduwa, sai ga shi 
yana’ta addu’ar Allah Ya sanya ta koma din, kada ta ce ta rabu da shi, da kuwa ya ga ta kanshi lallai. ‘ Sanda ta fito ta dube shi shekeke ta ce, “Gaskiya Mukhtar babu inda za ni, domin na riga na yankewa kaina shawarar sai dai ka zaba tsakanina da matarka, domin ban yarda zan iya hada ka da wata ba”. ~ 
Ya Kara kidimewa, yana fadin, “Haba Fatila, kina tunanin gaki zan iya kallon wata ne? Ni wannan aure daman ba da sanina aka yi shi ba, yanzu kuma ina tabbatar miki da ko 
sunan yarinyar ba na kaunar na ji, don haka ki kwantar da hankalinki, duk yanda zan yi zan rabu da yarinyar nan…” 
Kukanta ya katse masa maganar cikin kuka take fadin,“‘Ai dai kowa yasan Allah ke bada haihuwa, don kawai bana haihuwa sai danginka su tsangwame ni, to ni kam na gaji gwara kawai ka sauwake mini” . 
Jikinsa har rawa yake yi, ya matsa kusa da ita yana fadin, “Don Allah ki yi hakuri, na miki alkawarin zan zauna dake a duk yanda kike, shin sun san waye mai laifin ne a tsakaninmu? Ki kwantar da hankalinki, ke nake so, zan kuma rabu da yarinyar nan cikin ruwan sanyi insha Allahu”. 
Wani irin .dadi ya cikata, amma duk da haka sai da ta ja shi sosai, daga Karshe dai ya lallaBata suka. shirya, .wai Hajiya Kumatu ce ke musu nasiha su yi haquri da juna, shi dai da ya samu ya dauki matarsa ya ji dadi kome ye ma zai biyo baya karami ne. 
A hanya suna tafe wayar shugaban masu ginin gidan nasa ta shigo. Ya d‘aga a hankaii, ta tsare shi da ido gabanta yana faduwa don ba ta san ko wayar waye zai amsa ba, cikin ladabi yace
“Alhaji mun kusa kammala aikin nan, sai dai fenti da alama ba zai isa a yi a can bayan gidan ba, k0 zaka zo ka gani ka karo?” 
Ya kalli Fatila da tayi saurin dauke kanta, sannan yace. 
“Ai kawai ku bar aikin nan, domin na fasa amfani da gidan ma, ka zo anjima gida ka same ni da makullan gidan sai na baku cikon kudinku
‘ Mamaki ya kama shugaban masu ginin, domin ya ga yanda ya .azalzali su kammala aikin domin a gobe ne za a kawo masa amaryar amma kuma ya ce haka, anan ya daure ya ce, “Alhaji ai.. 
Ya katse shi da sauri, “Ka ga ka yi abin da na sanya ka kawai, bana son wani tsari, sai anjima”. 
Ya kashe wayar da sauri ya kalli Fatila da ta hade girar sama da ta kasa yana fadin. 
“Masu gyaran gidan da yarinyar can zata zauna ne da, suka sanar dani kayan wai sun kare, nace musu su kawo mini makullan na fasa . 
Ta taBe baki a ranta maganar tayi mata mugun dadi, amma bata son ta nuna masa a fuska, sai da ya kai ta gida sannan ya nufi otis dinsa. Yana isa kiran wayar mahaifiyarsa ya shigo. Da sauri ya dauka yana gaishe ta, ta amsa cike da kulawa, sannan ta dora da cewar. 
“Maganar tafiyar nan, jiya na yi zaton zaka shigo da daddare, k0 yau da safe shiru, kasan gwara a tanadi komai a hannu koka tanadi motocin da za a yi tafiyar ne?” 
Baya son a yi masa duk wata maganar da ta danganci Falmata, amma don kada ta gane halin da yaké ciki ya sanya yace 
“Eh to, daman dai aikin gidan ne ba a gama ba, ina tantamar anya kuwa goben za,a je daukota din kuwa, k0 za, a daga ranar har in gama kammala gyaran gidan ne?“ 
Mamaki ya kama mahaifiyar tasa, amma dai tayi kokarin Boye zargin dake ranta, tace, “Amma me ya sanya ba ka sanar da mu ba tun jiyan ka ga harna aikawa mutane kuma duk kowa ya shirya tafiyar‘ shin ka gayawa iyayen Falmatan ma? Nasan suma can suna ta shirinsu”, 
Ya kwantar da kai yana fadin. . “Ki yi hakuri Hajiya, ni kaina  banyi zaton za a sami akasin haka ba’. “To ka kirawo mahaifin nata ka sanar da shi, don kada suyi ta jiranmu Ya sosa keya yana fadin, .ki tainaka mana .kiyi masa bayani domin nauyinsa nakeji
Ta yi jim tana tantamar kada zarginta ya tabbata, amma dai sai ta ce, “Shi kenan zan kirawo shi din, kai kuma ka maida kai a kammala cikin satin nan”._ 
. Cike da farin ciki kamar an yi masa‘ albishir da gidan aljanna yace, “To Hajiya, na gode. 
Da haka suka yi sallama, a take a nan ta .kirawo wayar Malam Abba Gana ta yi masa . bayani. Bai ji komai a ransa ba, yace “To Allah Ya nuna mana’ sanda za a kammala, idan 
an kammala din ‘ ‘ ’ . saiya sanar dani, sai a sanar dasu ranar da zasu zo dun
Suka yi sallama a mutunce, ya tattaro matan nasa yana sanar dasu maganar daga 
tarewar Falmata. Yakolo da Basma suka kalli juna suka yi murmushia 
Hajja Kaltum da mahaifiyar Falmata kam . ba su kawo komai a ransu ba ‘suka ce dai Allah Ya kai mu lokacin kawai. 
Falmata tana daki duk ranta babu dadi, domin tun jiya take sanya ran kiran wayar Mukhtar amma shiru, ga shi yau ma har gari ya Waye bai nemeta ba, haka nan ta daure ta tura masa sajo, don ance jiki da jini amma shiru bai ba ta amsa ba, bai kuma kirawota ba, hakan ya sosa mata rai, sai kuma ga labarin daga tariyar tata yazo kwatsam. ‘ 
Ta dan firgita da jin hakan, amma sai ta daure ta danne abin da ya dace ta tambaya bai wuce sai yaushe zata tare din ba yanzu, amma kuma kunya ba zata hana ta tambaya din ba. 
Haka nan ta hakura ta ci gaba da zurawa wayarta ido ko Mukhtar zai kirawota ya gaya mata dalilin daga tariyar da aka yi. 
Fatila kam an sami abin da ake so, don haka ta qara fito da salo da kissa kala-kala na 
mallake maigidan nata. 
Shi kam k0 tuno Falmata ba ya yi, duk sanda ta turo sako kuwa sai yaji wani takaici a ransa, bai iya dubawa ba sai ya goge kawai. 
A haka kwanaki suka ja har sati guda,. mahaifiyarsa ma ta gaji da zura masa ido, don ’haka ta yanke shawar tuntuBarsa da maganar. 
Falmata kam ta rude ta fita daga hayyacinta, zaman daki ya kuma auranta, tabbas son Mukhtar ya zame mata tashin hankali, ba ta san laifin da ta yi masa da ya zaBi wulakantata irin haka ba, domin ta yi masa sako yafi guda hamsin babu amsa, balle ta sanya ran zai kirata; 
Yau tana gado ta nannade kanta son mijinta ke yawo a ranta, ga Yagana da ke dan debe mata kewa ta sami admission a jami’ar Maiduguri, ta fara zuwa makaranta, don haka ba koda yaushe take zuwa gurinta ba.
Ta dauko wayarta tana dubawa zuciyarta tana sanar da ita kawai ta kirawo shi taji dalilin da ya sanya yayi mata haka, wata zuciyar kuma tana gargadinta kada yana gida. Hawaye ya dinga biyo kumatunta, tama rasa abin da ya dace ta yi. 
Can kawai sai ta yi shahada ta fara kiran layin. Bugu daya ta dauka, lokacin yana gida yana ta aiki bisa konfuta yana tura sakonni .akan ‘wata tafiya da zasu yi anjima da daddare .. zuwa Sudan. Fatila tana gefensa ana ta zuba iya yi ta ji wayarsa ta fara kira, da sauri ta dauka, number ce babu suna don haka ta kara a kunnenta. 
Ita kam Falmata jin an daga tayi wata ajiyar zuciya da hanzari ta manta k0 sallama ma bata yi ba, tace. 
“Malam kana lafiya? Me nayi maka ka 
shareni haka?” . ‘ “Wai wace ce ke magana ne? Kawai daga bugo waya sai ki kama surutu ratata ba tare da kin san k0 da wa kike magana ba, wace cc ke ne?” 
Fatila ce ta ke maganar cikin Bacin rai, wani irin kishi yana yunkuro mata kamar zata mutu domin jin muryar Falmata kadai masifa ne a gurinta. 
Jikin Falmata ya kama kyarma, domin daga ji babu tambaya matarshi ce da yake tsoro
kamar mutuwarsa. Da kyar ta daure tace “Nice Falmata, ki ba ni shi don Allah…” 
“An Ki aba ki shi din” Ta katseta da zafin rai, ta ci gaba., “Banda ke Jaka ce tunda . kika ga ya share ki ai baya yi ne, meye kuma ‘na nacin kiran wayar tasa? Malama ki sama mama lafiya kinji k0, yanda kuka san yanda kuka yi kuka daura auran sai kusan yanda zaku yi ku warware, domin mijinaba ya neman matar shige”. 
Wani irin abu mai zafi ya dinga yiwa Falmata yawo a ranta, daga can tana jiyo muryar Mukhtar yana fadin, “Wai keda wa kike fada ne Fatila?” 
Ba ta tsaya jin amsar da zata ba shi ba ta kashe wayar tata, ta fada gado ta kuma sakin kuka domin dai ta kula a gabansa ne matarsa ke mata wannan cin zarafin, kuma lafiyarsa kalau kawai tsabagen wulakanci ne ya sanya ya 
watsar da ita da rayuwarta. 
rayuwarta? Tabbas ita son da take masa bana ‘ wani abu ba ne sai don Allah, yanzu yaya zata yi da ranta idan har Mukhtar ya barta ta shiga .uku, don sai yanzu ne ma take sonsa, take kuma son kasancewa tare da shi. 
Soyayyarsu ta kwanaki ta dinga bijiro mata, ta toshe kai cikin filo tana kuka, tabbas tasan ciwon son Mukhtar ne zai kashe ta. 
Kamar daga sama ta dinga jiyo ana kiran sunanta. Ta daga kai dasauri don ganin mai maganar, Yagana ce, sai ta fada jikin Yaganar tana kuka. Cikin tashin hankali Yagana ke tambayarta abin da ya faru. 
Cikin kuka ta ce, “Yagana Mukhtar ba sona yake yi ba, wani abu yake bukata ashE a jikina tunda ya samu kuma shi ke nan ya watsar dani, yaya zan yi da raina? Ki taimake ni don Allah”. ‘ 
Hankalin Yagana ya tashi, amma dai ta daure tace, “Kinga kwantar da hankalinki ki sanar da mi abin da ya faru, ni shaida ce tabbas mijinki yana sonki, sai dai idan wani abu ne ya sanya ya yi miki abin da kike zargi, ki yi hakuri ki sanar da ni”. 
Ba ta Boye mata komai ba tun daga sakon da take tura masa har abin da Fatila ta yi mata yau. 
Jikin Yagana ya yi sanyi, lallai da wa‘ta a Kasa, amma don kada ta kuma tayarwa kawar tata hankali ya sanya ta dake tace
“Amma kin ba ni mamaki, ke yanzu har zaki yarda da kaidin mace, ai wallahi gwara kisan yanda zaki zauna da mijinki, domin kishi ba a yinsa da wasa, kuma bana raba d’aya biyu duk abin da ya yi miki da sanya hannunta…” 
Ta waro ido waje, tana fadin, “Kina nufin ita ce ta ke sanya shi yayi min?” 
“Ki jiki, ai ba sai ta sanya ya yi miki ba za. a iya binsa ta karkashin kasa, kina jin fa abin da ake fadi akan matar tasa, kin san ba zata dauki lamarin da wasa ba, shawarar da zan baki ki mike da addu’a, idan ba haka ba kina ji kina gani malam Mukhtar zai kubuce miki, domin da alamu babu imani a tattare da matar tashi”. 
Ta yi shiru tana sauraron maganganun Yagana cike da mamaki, can ta daure tace, “Wai Yagana kina nufin mutum kamar malam 
sai a yi masa asiri ya kama shi, ki tuna irin 
iliminsa na addini fa, mutumin da ke koyar da wasu ace an yi masa asiri kuma Yagana, ni fa ina ganin kawai daman biyan bukatarshi yake nema a gurina, kuma ya samu me zai zauna kuma ya yi min?” 
“Kinji wautar taki ba, to Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wassalam ma anyi masa sannan ya kama shi balle wani malam, kuma ki sani irinsu asirin ma yafi cinsu, domin su gani suke kamar ba za a iya yi musu asirin ba, kina jin abin da ake fadi shi bai yarda matar tasa tana asiri ba ma, to ba sai ka yarda da abu ba sannan zaka dauki mataki akai ba, kuma da yawan malamai zaki ga Allah Yana jarabtarsu da shaidanun mata, har ki ga mutane suna ‘ mamakin yanda aka haihu a ragaya, ke dai ki dage da‘ addu’a kawai, amma tabbas malam yana sonki”. ‘ 
Maganganun Yagana sun dam karfafa mata gwiwarta, har ta rage zargin da take masa, ta kuma yi alkawan’n ganin bayan mai son raba ta da mijinta insha Allahu. 
Hajiya Mariya kam ta kulu iyakacin kuluwa burinta Allah ya kawo shi yau, komai dare sai sun jeya nuna mata gidan taga me ya rage a gidan da yaketa yi mata yawo da hankali ne haka? 
Tabbas zarginta ya fara zama gaskiya. domin ta kula yanzu ko maganar Falmata ba ya kaunar a yi masa, sai ka ga ya kama wani kwana-kwana, yau kam za ayi ta ta kare. 
Sai dai me? Wajen isha’i ta jiyo kiran wayarsa, ta daga ranta a bace da kyar ta amsa gaisuwarshi, ya kwantar da murya yana fadin. 
“Ki yi hakuri wallahi wata tafiya ce ta kama ni da gaggawa zuwa Sudan, yanzu haka muna filin jirgi nan da minti biyar jirginmu zai tashi, na so na shigo amma babu lokaci, don Allah kiyi haKuri”. 
A kule tace“To idan ban yi hakuri ba Baba ya zan yi da kai? Tunda dai kai ka zama dan kanka yanzu yaushe zaku dawo kenan?” 
Ya kalli abokan tafiyar tasa dake hawa 
jirgi, ya ce, “Eh to, ba zance ga kwanakin da zamu yi ba, domin wani aiki ne na gaggawa ya taso amma dai bana jin zamu kai sati guda ma”. 
Ta cc, “Shi ke nan, Allah Ya dawo da ku lafiya, amma ina fatan ka bar sallahun karashe aikin gidan nan k0?” 
Ya ji wata irin faduwan gaba, ita dai Hajiya ba ta da magana sai ta tariyar nan, amma sai ya dake yace mata. 
“Eh sun kusan kammalawa, ranar dana dawo washegari za a je a daukota, ki sanar da masu tafiyar su zama cikin shiri”. 
‘ Wannan ya dan faranta ranta, har suka yi sallama cikin kwanciyar hankali. 
                     *****************************
Abu kamar wasa karamar‘ ‘magana ta zama babba, domin tafiyar da aka ce ba za a kai sati daya ba sai ga shi an share wata guda‘ cur. 
Falmata tafi kowa shiga damuwa, duk da iyayenta sun dan’fara damuwa amma tafi su, domin ko waya bai kira wani yace ga dalilin da ya hana shi zuwa ba, sai Hajiya Mariyan ce ke sanar dasu tafiyar da ya yi. 
Ita kam kunyar duniya ta ishe ta, don tana gudun kada auren nan ya lalace a haka ta 
Hmmm naga alamun mukhtar dinnan shima dan duniya ne da😀😀

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]