[Advertisements⬇️]

HARSASHEN SO CHAPTER 5 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

HARSASHEN SO
CHAPTER 5
Cikin natsuwa shalele yake tafiya harya isa dakinsa, a sikwane ya isa bakin gadonsa, zama yayi a gefen gado tare da dora hannayensa saman cinyarsa ya tallabe fuskarsa da duka hannayensa, A hankali ya lumshe idanuwansa, daren jiya tar ya sake dawo masa a cikin kokon kansa, 
siffar Mubarak tsaf yake so ya siffanto amma abu ya gagara, A hankali ya kwantar da bayansa saman gadon kansa yana kallon silin din dakinsa tunani sosai a zuciyarsa wanda baisan dalilinsa nayin hakan ba! Yana cikin wannan tunanin ne mai gida ya shigo cikin dakin fuska a hade hargowarsa tasa shalele tashi da sauri gaba daya ya mike tsaye tare da sadda kansa ya kalli kasa alamar girmamawa, 
Mai gida yaci gaba da cewa sakarcin banza sakarcin wofi, har na fada maka an kashe min dokin da nafi kauna a duniyar nan har zaka wani zo ka kwanta kana wani nazarin banza da wofi? Wannan shine matsalar da kake nema ka saka kanka sakaran banza ci baya a cikin mazaje, 
Duk dan halak yana kokarin cika burin mahaifinsa amma banda kai, da na fara alfahari dakai amma yanzun kam na sauke, banga amfanin dan da baya cika burin mahaifinsa ba, idan har bakaje ka ramomin kisan da akayi wa dokina ba ka kashe duk wasu dawakai dake gidan makiyina ba to ban yafe maka ba, na shafe ka a cikin jerin abinda nake so a duniya na gogeka daga sunan da a wurina zan mayar dakai makiyina f’lye da yanda na mayar da wancan dakikin kuma zan mayar dakai abin farauta ta kullum harsai nayi nasarar rabaka da rayuwarka! Rawa jikin mai gida ya farayi fuskarsa har kyarma takeyi saboda masifa, daidai zuciyarsa yakai duka wanda harsai da tsoro ya bayyana a fuskar shalele cikin tsoro yace kayi hakuri mai gida, dakawa shalele tsawa yayi wanda harsai da “yan cikinsa suka kada idanuwa shalele ya zaro sosai sannan ya kara cewa tuba nake mai gida, 
Tubar banza tubar wofi babu hakuri babu afuwa haka kuma babu yafiya babu imani k0 tausayi a kan makiyina idan har ka bar Bashirya yini a cikin farin ciki ban yafe maka ba, saina kashe kaina tunda har na haifl dan da bazai iya saka farin ciki ba a zuciyata, yana kaiwa daidai nan yayi jifa da wuka wanda harsai data caki kafar shalele yayi waje yana mai ci gaba da fadan sa! ! 
A hankali shalele ya duka ya dauki wukar da mahaifinsa ya jefe sa da ita ba tare daya duba inda yaji ciwon ba, cikin dakiyar zuciya ya fara tafiya, amma idonsa da zuciyarsa suna tuno masa abinda ya faru a daren jiya, Hannunsa yakai daidai zuciyarsa ya taba 
murmushin karfin hali yayi yana mai jin tsoro a cikin zuciyarsa, amma ya zamar masa dole kozai mutu saiya daukowa mahaifinsa fansa, Da sauri ya flta daga cikin dakin, mama dake tsaye a kofar dakin tabi shalele da kallo, jikinsa ya bashi ana kallonsa tsayawa yayi ba tare daya juyo ba, gyara damararsa yayi sannan yayi gaba cike da jarumta! Daga nesa ya jiyo maganar mahaifinsa yana cewa wuta nace ka kunna idan kaje ka babbakamin gidan makiyina idan har ka dawo baka cinnawa gidan nan wuta ba ni zan kone 
ka dakaina na kaji na fada maka, shalele baiyi magana ba ya haye doki ya fara tafiya cikin zafin rai, zuciyarsa tana mai tuno maganar mahaiflnsa, 
Tafiya mai nisa yayi sannan ya hadu da balaga tafiye a doki da gudun mai tada hankali, da sauri shalele yaja dokinsa ya tsaya wannan dalilin yasa balaga dakatawa amma babu wanda ya sauko daga saman dakinsa, Ina mai zanen yake ne? Shalele ya tambayi balaga, Ranka ya dade baya nan yayi tafiya, balaga ya bashi amsa, me yasa kake gudu haka ne? Inji shalele ya sake tambayar balaga, murmushi yayi sannan yace ba komai ma’I gida,toka tafi a hankali, an gama ranka ya dade, jeka saina dawo, godiya Balaga ya sakeyi sannan yaja dokinsa yayi gaba! 
Har Balaga yayi nisa yajuyo ya biyo shalele da gudu yana kiran karamin mai gida,,,, gudu yakeyi sosai saboda shalele yayi masa rata da yawa! Ganin shalele bazai tsaya ba yasa Balaga ya fara cewa karamin mai gida tsaya na fada maka abinda yasa nakeyin Wannan gudun Karka kaje wani mutum yana shigowa garin nan cikin motar naji yana tambayar wanda ya sanka karkaje tsaya ka tsaya don girman Allah karamin mai gida,,, Gudu sosai balaga yakeyi kamarzai shide, a lokacin har shalele ya isa gidan Bashir da dokinsa ya shiga ciki haka yayi tabi takan mutane yana wucewa, duk wanda yazo kusa dashi  harbi yakesha duka kawai shalele yake saukewa idan mutum yayi gigin zuwa kusa dashi, idan kuwa aka ‘taba masa doki wuka yake sawa ya yanki hannun mutum, 
Haka shalele yayi ta sukuwa saman doki ba tare daya sauka ba yaci gaba da kacaccala duk wanda yazo ta kusa dashi, saida ya saka gajiya ajikin kowa sannan ya nufi wurin da ake daure dawakan gidan, suma suna ganin shalele suka fara haniniya suna samarya saboda suma kansu sunsa akwai gaba tsakaninsu, 
Dirowa yayi daga saman dokin sannan yasa hannunsa a aljihu ya ciro ashana, dukawa yayi wurin da yake da yayi ya cinna wuta, a hankali wuta ta fara ci, mikewa yayi cike da izza ya rike kugunsa yana kallon yanda wutar take ci kamar ana watsa mata fetir dan Bashir baya nan yaransa kuma duk yaci ubansu. 
Bakajib komai sai karar wuta sai kuma haniniyar dawakai da suke wani irin ihu saboda azabar wuta, kakkabe hannu shalele yayi sannan ya sake rike kugunsa yace duk zakuci ubanku zaku hadu da nayin wajo a can, wato dokin babanshi da aka kashe, Jin karar motar yasa shalele saurin juyawa cikin tsoro yabi motar da kallo kirar ‘Bugatti’ a kidime ya ruga dan hayewa saman dokinsa ya gudu, da sauri Mubarak ya fito daga motar dan a lokacin har shalele yahau doki ya fara masa kafa alamar ya tafi Irin abun jiya shalele ya gani, ga kuma doki yayi ma kafa a daidai lokacin da dokin ya mike yayi haniniya da sauri shalele ya rumgume dokin da hannu daya dayan hannunsa kuma ya dafe zuciyarsa, hawaye ya fara FIta a idonsa na zugin da yakejI’ a zuciyarsa wani jirwaye jirwaye haka yake gani Mubarak, 
Kallon shalele Mubarak yayi sannan yayi masa alama da hannunsa ya sauko, girgiza kai shalele yayi alamar A, a, tare da goge hawayen idonsa da bayan hannunsa, tsaki Mubarak yayi danshi a duniya ya tsani yayi abu ya sake maimatawa, 
Dukawa yayi ya dauki wata igiya ya wurwurata sannan ya jefata a saman wuyan shalele ya figo shalele ya fado kasa! Da sauri shalele ya dafe kansa da duka hannayensa danjin kwalwar kansa ta juya,jansa Mubarak yayi ajikin motar sa ya daure igiyar daya daure shalele sannan ya koma motar yaja abunsa da gudu ….. , 
Ba abinda ya dami Mubarak ko wani dutsi ko wata kaya shidai wucewarsa yakeyi abunsa hankalinsa kwance shalele nashan azabar gurza a kasa saboda hannayensa ya daure idan shalele yaji azaba saiya juya bayansa, Kansa shalele ya sanda kasa yana girgizawa cike da bakin ciki hawayen azaba na zubowa sosai a idonsa, shi kuma Mubarak yayi haka ne dan ganin karyar jarumta da harzai hana masa uba zaman lafiya, Hmm
Duk taurin rai da kangarar shalele kafin suje inda zasuje harya suma saboda bala”i, Mubarak kai tsaye gidansa ya nufa, bayan yayi parking ya fito, zagayowa yayi inda shalele yake kwance cikin jini da kafarsa ya halbasa, tsaki yayi tare da cewa ku tafI dashi ku kulleshi a wuri mai tsananin zafI! 
Kwance shalele sukayi daga jikin igiyar suka jefashi motar suka tafi dashi, saida suka fita a gidan sannan Mubarak ya wuce ciki da tafiya irinta gwarazan maza masu aji, Kamar yanda Mubarak yace haka sukayi, wurin da ko dabba aka daure a wurin saita bukaci tafIya lahira a wurin aka rufe shalele, duk yinin ranar nan shalele bai farko ba saboda babu ta inda iska zai shigo wurine mai zafin gaske kamar gidan gasa biredi, Balaga kuwa bayan ya koma gida ya fadawa mai gida yaga wani mutum ya shigo da Motar yana neman shalele amma yabi shalele ya fada masa kuma basu hadu ba, danshi Ba balaga daga haka baisan komai ba! Cike da gadara mai gida yace jarumi zaiji da kowa yafi karfin duk wasu kananan kwari inaji a jikina ko ya dauki shalele zai maidoshi da kansa dan daukar shalele hatsari ne, kallon balaga yayi sannan yace ka taba ganin wanda ya zabarwa kansa mutuwa a kan rayuwar? 
Balaga yace A, a, mai gida yace kabar shi da shalele baisan ajalinsa bane yake nema, yana fadin haka ya mike yabar wurin, A gidan Bashir kuwa yana dawowa yaga abinda ya faru a gidansa ranshi ya baci sosai yaransa suna so su fada masa Mubarak ya tafi da shalele amma ya hanasu suyi magana fada yakeyi ta ko ina, cike da bacin rai ya fara kiran wani lafiyayyen kare bakikkirin dashi mai kalar ban tsoro, dakinsa ya koma ya dauko wani abu ya cusa a cikin bakin karen sannan yace ’MAKIYINA‘ wata irin girgiza karen yayi sannan ya fita daga gidan da gudu yana daga bindinsa! shalele kuwa saida tsakar dare ya farfado dukjikinsa ciwo yake masa kamar ya mutu haka ya ganshi, a hankali yakai hannunsa saman cikinsa da yake masa azaba mai azaba, da 
sauri ya canje hannunsa daga wurin saboda zafi, ‘ Daga kwance ya fara kokarin cire kayansa, amma sai ya tuno maganar mai gida cewa karka kuskura kaje wani wuri ka cire kayanka na fada maka, kuma idan baka gida ko a toilet idan ba naka bane ban yadda ka cire kayan ka ba! 
A wahalce ya juya jikinsa, tare da dora hannunsa saman idonsa Mubarak yake gani, murmushi yayi sosai sannan yace waye kai kuma? Waye ya kawoka  cikin rayuwata ne? Me kake nema? Kyawunka da kwarjininka ya wuce kazo a matsayin mai cuta, ajiyar zuciya yayi a wahalce sannan yace bara kazo inji laifin me nai maka, Jin zafi na namen kaishi lahira yasashi tashi dolejan jikinsa yayi harya lalubo kofa dukan kofar ya farayi amma shiru kakeji babu mai jinsa bare ma asan yanayi, A gidansu shalele karen da Bashir ya tura bai samu kowa ba a waje amma yayi barna sosai irin wanda shalele yayi a gidansu daga farko, duk wasu dabbobi yaci uwasu sannan ya koma gida yana zalzalo harshe alama ya aikata abinda aka saka shi, Har gari ya waye rana tayi tangaram shalele baisan dare ba baisan rana ba, saboda duhu ne sosai a wurin ga zafi kamar yana cikin wuta kasan kanshi zafi gareshi bare wurin ko bango kajingina azabar zafi kakeji, 
Yana cikin wannan akubar da tunanin a wane hali yake yaji ana bude kofa, da sauri ya tashi tsaye idanuwansa ya rufe saboda hasken fitilar da aka haskoshi dashi, cikin “yar siririyar murya yace waye? Ka fito, a hankali shalele ya fara taflya cikin wahala harya fito daga cikin wurin, Tafiya sukeyi shalele yana dan dora hannunsa saman idonsa dan har yanzun idonsa bai dawo normal ba har suka fito, motar aka saka shalele dan Mubarak yace a dauko shi yayi 
masa kashedi yau zaiyi tafiya ne, A wani katon palo aka kai shalele mai dadin sanyi da kamshi, duk da a gidansu suna da komai irin na “yan birni bai hana shalele yin kauyanci ba, dan a gidansu basu da A C, ga kuma wata barkekiyar plasmer maisa mutum yaji juwa komai dai ya burge shalele murmushi yayi a daidai lokacin daya hango Mubarak yana saukowa daga saman benen palonshi, Cikin wani yare wanda Shalele baisan abinda ake cewa ba Mubarak yayi magana baisan abinda yace ba amma yaga sojojin sun dan dukar da kansu sannan suka girmama shi suka fice 
a palon, Zama Mubarak yayi a daya daga cikin kujerun palon a nesa da shalele, zaman da Mubarak yayi yama shalele kyau dan haka ya sake kallonsa sosai sannan yayi murmushi mai kyau, daure fuska Mubarak yayi sannan yace ya sunanka? 
‘SHALELE’ amma anfi sani na da ‘JARUMI’ dan gajeran tsaki Mubarak yayi sannan yace jarumi ko mahaukaci ka tabajin jarumi da muryar “yan daudu? Duk da shalele baisan miye kalmar daudu ba yasan an rage masa mukami, dan haka yace kaine dan daudu ko an fada maka inajin tsoron wani ne, murmushi Mubarak yayi wanda baisan ya fito ba yabi shalele 
da kallo wallahi abu yake irin na mata, 
Mubarak yace kai zauna, zama shalele yayi cikin bacin rai, Mubarak yace to ko a kaina zaka nuna jarumtar ne? Shiru shalele yayi Mubarak ya tattaro da natsuwarsa ya tsare gida sosai sannan yace idan na sakejin labari kayi wani abu wanda bai kamata ba zanzo dakai na na dauko ka kamaryanda na daukoka a saflyar jiya duka zan maka sosai wallahi, idan ka mutu kuma na cillaka a ruwa kifaye su cinyeka banza kazami, Cikin sanyin murya shalele ya kalli Mubarak sannan yace nine banza? Ya fadi maganar tare da nuna kansa, yanda yayi abun yasa Mubarak ya dora hannunsa a saman baki yana murmushi, bata fuska shalele yayi sannan yace wallahi kullum sai nayi wanka yaune kadai banyi ba wallahi ni ba kazami bane, kallo Mubarak yabi shalele dashi amma baice masa 
komai ba, harya gama shirmen sa irin na kananan yaran mata idonsa akanshi yake! 
Saida shalele ya gama sannan Mubarak yace to yayi amma fadamin miye sunanka na gaskiya? Nazari shalele yayi sosai sannan yace suna na ‘UMMU SULEIM” ummu suleim kuma? Mubarak ya maimata, da sauri shalele ya rike bakinsa dan tuno hudubar mama cewa karka kuskura kace sunanka Ummu suleim, cikin damuwa shalele yace yi hakuri suna na ‘ABDUL SULEIM’ cikin rashin fahimta Mubarak yace ya kuma Abdul suleim? Kallo mai tsayi Mubarak yayi ma shalele yana nazari tare da san gano wani abu a tattare dashi, jinjina kansa yayi sannan yace tashi tsaye mikewa shalele yayi Mubarak yace matso nan, a hankali ya matsa kusa dashi Mubarak yace sauke wannan abun na saman kanka, cikin faduwar gaba shalele yace dan girman Allah dan Allah karkamin haka kayi hakuri dan san da kake ma annabi insha Allah bazan sake ba! Kallon idonsa Mubarak yayi sannan yace idan ka sake zan cire maka kaya a cikin mutane ka yadda? Na yadda shalele ya fada, Mubarak yace wuce ka tafi, cikin tsoro shalele ya juya a hankali ya furta cewa ‘INA SAN KA‘ wanda Mubarak baiji abinda yace ba, shalele na fita aka daukeshi a motar dan mayar dashi gida wannan kuma umarnin Mubarak ne! 
Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]