[Advertisements⬇️]

BARIKI NA FITO CHAPTER 47 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

BARIKI NA FITO 
CHAPTER 47
Bariki ihu ta saki cikin tashin hankali, nan mum ta fita da gudu kiran Dr, yayin da Falmata take ta zunduma ashar kan cewa Bariki zata kashe mata miji, Bariki kam kuka take tana mannejikin Yarima, Falmata k’okarin cafko Bariki take, Yarima kaman ya Lura da hakan 
yasa ya dawo da Bariki baya tare da shiga gaba. 
Dr shigowa yayi inda ya bu’kaci su mum damai martaba da Falmata su matsa danya samu ya duba patient din, nan Dr Ya fara duba sheik musa monguno, cikin ikon Allah ya Farfado nan ya fara kuka tare da zufa dake faman keto mishi, tashi yayi tare da nufa wajan da Bariki take inda ya fara kuka yana neman gafaranta akan abunda yayi mata, wanda yace Wlh bai San 
ya akai har shida kanshi ya koreta ba, 
Dr fita yayi domin yaga ba wani serious ciwo bane, suma yayi and kuma ya Farfad’o, ganin Dr Ya flta yasa su mum shigowa. 
Falmata ganin mijinta ya tashi yasa ta Fara rusa kuka lokaci d’aya kuma ta Fara dariya tare da fad‘in Nina sa akama Zainab ciki saboda ka tsaneta Wlh nice nasa aka mata hahahaha hahahaha sai kuma ta saki kuka lokaci d’aya kuma taci gaba da fad’in 
Nice nasa mata kwaya cikin juice tasha, tayi bacci Mai nauyi, Nasa driver ya mata ciki, hahahaha bayan nasashi na koreshi, daka karshe ya faramin barazana nasa aka kasheshi har lahira, wlh nice nasa aka mata ciki, saboda ta’ki yarda dani, ni kuma ina sonta Sosai ina son in lashi zumarta, Wlh Ina Sonta Sosai dan Allah ku bani ita, ko ku aura min ita, sai kuma ta k’ara fashewa da dariya taci gaba da fad‘in abunda yasa nasa aka mata ciki saboda ina son Dad d’inta ya tsaneta, yace ta d’auko mishi abun kunya, kuma Nayi wannan tunanin ne saboda Kar wata rana ta tona min asiri dan yana jin magananta, kuma in ya tabbatartana da ciki zai daina yarda da ita, bayan nasa anyi mata ciki, nasa akaje min maiduguri wajan wani boka inda na amso mugun sihiri Wanda na rufe mishi ido da baki sai abunda nace, duk da lokacin sihirin baiyi wani tasiri Sosai ba, dan Bayan ya koreta yaita fama da ciwo tare da damuwa yana mamakin Wai shine ya Kori y’arshi da kanshi, ganin irin damuwan da yakeyi gashi ana kawo mishi hotanta da shigar banza, hakan yasa hankalinshi ya tashi Sosai, ganin irin halin daya shiga yasa na tafi maiduguri dakai na wajan boka, gashi ina takaicin ban haiyu dashi ba, yau Idan ya mutu ba wani kud’i zan samu Sosai ba, inda Nayi mishi bayani, tare da cewa Ina son a cire mishi tunanin Zainab harta danginshi kona mamanta karsu nemeta, boka yace wannan aikin akwai hatsari Sosai sannan akwai zunubi Sosai, domin raba y’a da iyayenta babban aiki ne, nan nace ma boka na d’auka, boka yace dad din Zainab yana matukar son y’arshi Sosai koda anyi aikin muddin ya ganta komai zai 
lalace, Indai kina son aikin yayi tasiri karki bari su had’u, nace ma boka babu damuwa 
Yace an gama, za’a tura mishi Aljani, wanda zai dinga juyashi, nan na amince boka ya k’ara min kashedi Idan na Bari suka had’u komai ya faru dani Kar ince bai fad’amin ba? Nace na 
amince domin a lokacin idona ya rufe. 
Bayan na dawo Abuja naga aiki yayi, domin a lokacin tunanin Zainab yasa dad d’inta ya rage ibada, domin yana cikin ciwo, wannan ne yasa nayi nasara akanshi, har Aljani ya shige shi, saboda ina fargaban karsu had’u nasa muka koma misra gaba d’aya inda na bu’kaci Nima Ina son inyi karatu a can, wannan ne dalilin komawarmu k’asar misra yana business dinshi ta Nigeria da kasashen da yake yi, amma maganan zuwa Nigeria gaba d’aya nasa an cire mishi a rai, kwasam sai gashi yace min zaizo Nigeria amininshi yana nemanshi zai gabatar mishi da wani lacca, a lokacin na tsorata domin kuwa harta wa’azin da yake zuwa nasa an hanashi, sai gashi ya kawo min maganan zuwa Nigeria yayi lacca, da Farko naso in hanashi sai kuma Nayi tunanin muzo dan Ina son zuwa maiduguri wajan boka inji ya akayi k0 aiki ya fara sanyi ne, ashe asiri ne zai tonu.. Dariya ta saki Tana fad’in Wlh koda zan mutu saina ciki Zainab Ina sonki. 
Kowa dake wajan salati yake cikin takaici tare da jimami, da Allah wadai da halin Falmata 
Dad d’in Bariki nan take yace Falmata na sakeki saki uku, kuma insha Allah sai Kinga abunda kika aikata, kin cuceni kin batamin rayuwar y‘ata, lallai Falmata sai nasa an hukunta ki W ….. 
Mai martaba yace kayi hakuri, baka ga halinda take ciki ba, Mai martaba ya lura da Falmata kaman ta haukace. 
Falmata tace saime cikin ihu, ni dama ba Sonka nake ba, saboda kud’i na aureka, da naga y’arka sai naji Ina Sonta, tunda naga irin suranta kuma Wlh sai na cita,hahahha Kaga koda ka mutu nida ita zamu zauna muci kud’inka, sannan ta dinga biya min bukata, Hahahahahaha sai kuma ta saki kuka tare da fara k’okarin cire hijab d’inta, nan mum ta k‘ara flta ta kira Dr. 
Koda Dr yazo dakyar aka ri’keta tana ta fusge fusge, andai samu an d’aureta dakyar inda sheik musa monguno yace zai sa a maidata maiduguri domin wlh ko sisi bazai bada wajan yi mata magani ba. 
An ro’ki Dr akan su Fara dubata inda Mai martaba ya bada umarni tare da fad’in ba’a saka sharri da sharri, Dr yace gskiya wannan asibitin mahaukata za’a kai‘a, mai martaba yace babu damuwa a kaita, zai biya k0 nawa ne, nan akai Gaba da Falmata. Kai rayuwa kenan wannan shi ake cema sakayya, lallai Allah ba azzalumin kowa bane, sai wanda ya cuci kanshi, duk irin abunda Falmata tayi gashi ya koma kanta, kai Mata mata Wlh muji tsoran Allah. 
Sheik musa monguno kuka yake tare da ri’ke hannun Zainab yana tambayanta akan ta yafe mishi 
Cikin kuka tace babu abunda yayi mata, tace Dad niya kamata in nemi gafaranka, dana biye ma shairin zuciya, tare da kokarin San in kuntata maka, ta wajan aikata aikin sabon Allah, Dad na cuci kaina da yawa, dan Allah ka yafe min dad ta k‘arasa maganan cikin kuka 
Janyo y’ar tashi yayi tare da rungumeta su duka suna kuka abun tausayi. Yarima Aliyu jin kukan hafsat din yake har cikin ranshi. 
Hafsat da tun ihun da Falmata ke zabgawa yasa ta tashi ta zauna, nan itama ta fad’o daka 
kan gadon d’akin ta zube a gaban iyayenta tana kuka akan su taimaka mata su yafe mata. 
Mai martaba yace duka su tashi suyi gida, acan za’ayi magana, hafsat jikinta yayi sanyi ganin mahaifin nata ko kallonta baiyi ba, lallai ta aikata babban kuskure na yarda da Umar wajan bashi jikinta, kuka take Sosai, inda gaba d’aya suka flta Bayan an tambayi Dr k0 akwai wani damuwa, Dr yasa anba ma Hafsat magani sannan yace Bariki tana bukatar hutu Sosai, inda so samu ne ma a bata bed rest, da Farko Yarima Aliyu yace ta koma a bata gado, amma tace a’a a gida zata fi samun hutu, babu yanda ya iya dole ya biye mata itama aka bata maganin suka nufi Gida, duka a babban falon Mai martaba suka zauna inda Mai martaba ya kira waziri akan yazo, domin yana son yin magana yau wanda tun tuni yake son yi. 
Kowa ya hallara, inda Mum tace ina zinatu ya kamata tazo itama, mai martaba yace Aliyu yaje ya kirata. 
Yarima Aliyu fita yayi amma bai soba, domin duk zuwa asibiti da yayi bata tako k’afa tazo ba, and yanzu kuma maganan daya shafi Zainab za’ayi sai yake ganin kaman bai kamata 
tazo wajan ba, tunda kishiyar Zainab dince ita. Direct gefenta ya shiga tun Kafln ya k’arasa d’akinta yakejiyo maganansu ita da gimbiya Amina, wanda yama manta tazo, gimbiya zinatu tana fad’in ai Wlh inda badan wannan maganin dana sama Yarima yayi mishi karfi ba, toh da Wlh zai gane niba virgin bace, ki duba fah ki gani baya cikin hayyacinshi har Ya iya gane niba virgin bace, dariya gimbiya Amina ta saki tare da fad’in hmmm ai tunda yaga wannan jinin na tabbata dole ya yarda ke 
budurwa ce. Gimbiya zinatu tace yauwa wai jinin miye kika Aiko min dashi? 
Gimbiya Amina tace Wlh fadawa naba kud’i suka kawo min, nace musu kona dabba ne kona mutum suje asibiti su siya, bayan sun dawo suka cemin Sun yanka raguna uku, shine suka kawo min jinin 
Dariya gimbiya zinatu ta saki tare da fad’in ashe jinin rago ne, yarima ya d’auka jini nane, 
kai gskya anyi bidiri, dariya suka saki. 
Gimbiya Amina tace shidai duka baiyi dace ba, ita wancan amaryan tashi ba budurwa ba, Kema gaki, yatsa da ayabar roba yasa kin rasa budurci. 
Gimbiya zinatu tace uhm Kedai bari, ni bada sanin namiji ba budurci ya gudu, hmm inda Yarima bai saki matarshi ba Aida tasha gori wajena Wlh da habaici 
Gimbiya Amina tace toh Kema dai Kibi sannu a hankali, domin wlh idan Yarima ya gane kin 
mishi wannan yaudaran kashinki ya bushe, shi yanzu yana miki kallon budurwa ne 
Yarima Aliyu dake tsaye yana jinsu cikin tashin hankali, gaba d’aya jikinshi yayi sanyi,ji yayi kaman ya juya amma wata zuciyar tace ka shiga ka nuna musu kaji komai, dan haka ya kutsa Kai kalman Innalillahi’wa inna ilaihirajiun ya iya furtawa, ganin gimbiya zinatu da 
gimbiya Amina zindir haiyuwar uwarsu jikinsu manne dana juna.
Yarima Aliyu tunda ya furta wannan Kalman na Innalillahi wa inna‘ilaihirajiun bai k’ara cewa komai ba, sai hawayen dake idonshi dake zuba, tare da fad’in wannan wace irin jarabawa ce cikin ranshi, juyawa yayi ya fita jim kad’an sai gashi da mum d’inshi itama Abun ya bata mamaki, gimbiya zinatu da gimbiya Amina, Sun kasa koda motsi ne 
Yarima Aliyu kuka yake yana fad’ama mum dinshi abunda yaji, suna fad’a tare da fad‘in mum ban kasance mazinaci ba, amma Allah ya bani Mata fasikai,mum.. Kuka ya hanashi k‘arasa abunda yayi niyan fad’a. 
Mum rarrashinshi take tare da fad’in yayi hakuri ya d’auka wannan shine jarabawan shi na rayuwa, uhm su mum kenan yanzu an gane kaddara da jarabawa uhm. 
Yarima yace mum bazan zauna da macen dana Kama tana aikata mad‘igo ba, na tabbata duk macen dake aikata lesbians kallon hoto take ma mijinta, tana mishi kallon sakarai, mum bazan iya zama da itaba, lallai laifinta yafi na kowa muni, mum kice ta tafi bana son ganinta, 
Zinatu da sauri ta taso tana kuka tare da ri’ke kafan Yarima tana bashi hakuri akan bata dad‘e da fara aikata wannan aikin ba, dan Allah Yarima ka yafe min Wlh yi kawai nakeyi, amma bawai Inajin dad’inshi ba, kuka take Sosai tana bashi hakuri 
Mum tace tashi kisa kaya ki samemu falon Mai martaba, tare da kallon gimbiya Amina tace ke kuma ki shirya ki koma Gida, abunda kuka aikata dakai na zan fad’ama iyayenku, tana fad’in haka taja Yarima suka fita, tana fad’a mishi karya sake yace zai rabu da matarshi, tare da fad’in a farko tayi kuskuren raba shi da wacce yake mutuwar so, bazan k’ara Bari ka saki matarka ba, itama Zainab Ina neman hanyar da zaku dawo tare ne. 
Koda sukaje cikin falon idon Yarima Mai martaba ya kalla, yace maiya faru? Mum shuru tayi haka shima, yarima, muryan Gimbiya zinatu suka ji Tana fad’in dan Allah Abba kuyi min rai Nasan na aikata mummunan laifl, wlh shairin shaidan ne, dan Allah Abba kaba Yarima hakuri karya rabu dani Ina sonshi, wlh ban taba aikata mad’igo ba sai shekaranjiya, duka salati suka saki kowa kallonta yake cikin jimami da Tashin hankali . 
Jin kowa na salati yasa gimbiya zinatu kallon mutanan dake d’akin, wanda idonta ya rufe bata ko Lura dasu ba, sai yanzu cikin jin kunya tare da tsanar kanta da kuma gimbiya Amina 
da tasa ta Fara aikata wannan abun. 
Mai martaba ne yayi gyaran murya tare da fad’in Innalillahi’wa inna ilaihirajiun, kai duniya kai duniya Mai take son zama ne, da farko dai zan fara da Zainab yanzu Zainab zaki bi dad 
d’inki ne ko zaki zauna a nan harsai kin haihu? Bariki cikin sanyin jiki tare da zubar da hawaye tasan ta rasa Yarima har abada tace Abba zanbi Dad Dina 
Da sauri Yarima yace ban amince ba, wanda bai San maganan ta fitO ba Kowa kallonshi yayi, 
Mum kam kuka take k’asa k’asa domin tasan d’anta bazai jure rashin Zainab ba, kai ta cuci 
d’anta, ta rabashi da farin cikin shi Mai martaba yace Aliyu karka manta yanzu Zainab ba matarka bace. Yace Abba Zainab har gobe tana matsayin matata 
Mum da sauri ta d’ago tana kallonshi, bama mum ba duk wa inda ke falon, yace Abba sanda mum tace in saketa na rubuta mata saki biyu Naji bazan iyayi mata uku ba, bayan na bata takardan naga mum bata damu data duba takardan ba hakan yayi min dad’i amma ganin yanda mum ta korata yasa naji ajikina kaman mum bazata taba Bari in dawo da ita ba, lokacin dana Fara ciwo nan take na dawo da ita, Zainab yanzu tana matsayin matata, 
takardan dana bata yana hannunta Mum wani irin ajiyan zuciya ta sauke tare da furta Alhmdlh, Allah na godema. 
Bariki tace Yarima Wlh sanda kaban takardan ban duba ba, harna yaga shi saboda ba Abun kallo bane, ashe saki biyu ne sai kuma ta saki kuka. 
Mum ta tashi taje kusa da ita tana fad’in kiyi shuru zainab, wlh nafi kowa murna, inda Yarima saki uku yayi miki, dana shiga uku, kai Allah na gode ma, naso in aikata kuskure a rayuwa, naso bata rayuwar d’ana da kaina, shi yasa akace ba’a yanke hukunci cikin fushi, yau gashi naga yanda naso jefa yarana halaka sai kuma itama ta saki kuka, Bariki ganin haka sai ta dena Nata kukan ta Fara rarrashin mum. 
Mai martaba yace yanke hukunci cikin fushi babu abunda yake haifar wa, sai dana sani, A kullum ana son Kafin ka yanke hukunci ka Fara bincike inka tabbatar, saika zauna kayi tunani akan maiya kamata, inko kace zaka yanke hukunci cikin fushi lallai zakai dana sani, Allan yasa kun fahimta. 
Mai martaba ya kalli sheik musa monguno, ya fara bashi balarin irin rayuwar da y’arshi ta shiga, 
bayan ya koreta har zuwa auran Yarima da tayi. 
Sheik musa monguno kuka ya fara tare da fad’in Falmata ta cuceni, ta batamin rayuwa ta data y’ata, kallon Zainab yayi tare da fad’in ki yafe min inda ban aureta ba da hakan bai faru ba. Mai martaba yace ka daina fad’in haka, sheik k0 ka manta Idan Allah yasa abu zai zo gareka dole sai yazo, sannan sheik asiri yana bin hali ne, na tabbata koda Falmata bata maka asiri ba, zaka iya Koran Zainab, domin lokacin kana cikin fushi, zaka yanke hukunci cikin fushi, domin zaka ga a matsayinka na babban Malami y’arka ta kwaso cikin shege na tabbata koda babu asiri zaka iya koranta, daka baya kayi dana sani, shi yasa akace ba’a yanke 
hukunci cikin fushi, a lokacin duk da akwai sihiri a kanka Bayan ta tafi aika nuna kayi 
nadama, tare dason ganinta. 
Sheik musa monguno yace hakane, tabbas asiri yana bin hali, asiri yana taflya ne da halin mutum, Allah ka k’ara tsare mana imanin mu, kallon Yarima yayi tare da fad’in lallai Aliyu ban San da wani baki zan gode maka ba, domin kayi babban jahadi na ceto rayuwar Zainab, duk da kasan irin rayuwar da tayi daga baya, bayan tayi maka k’arya kaci gaba da zama da ita, lallai ban tunanin duk irin sonda nake mata cewa nawa yafi maka, lallai ka fini son Zainab, tunda harka iya zama da ita, sa’banin nida nake mahaifinta sanda take bukatar kulawata Sosai lokacin na juya mata baya, duk saboda fushi tare da kunyar duniya, kai 
kaico na, Yarima Allah yayi maka albarka. 
Yarima ya amsa da Ameen tare da kallon zainab wacce itama shi take kallo, Yarima ido ya kashe mata, da sauri tayi k’asa dakai tana murmushi tare da tsoran Allah yasa wani baiga sanda ya kashe mata idon ba. 
Mai martaba kallon waziri yayi tare da fad’in, Ina son aje a sauke sarkin u/kanawa daka kan kujeranshi, domin bai kamata a barshi yana shugabantan al’umma ba, a sami wani kamili Dattijon arziki a saka, amma yau nake son a bashi takardan murabus, domin duk mutumin da zaiyi Abu saboda kud’i ciki harda yaudara ba mutumin arziki bane, bai kamata ya dinga 
shugabantan al’umma ba, nan take waziri yace an gama ranka ya dad’e 
Mai martaba kallon hafsat yayi tare da kiran sunanta da sauri ta d’ago cikin faduwan gaba tace na’am Abba, tana hawaye 
Yace hafsat Mai kika rasa? Mai kika nema kika rasa? Hafsat wani irin tarbiya ne bamu baki ba? Dama kin San kina da ciki shine kike k’okarin yin aure da cikin wani? Hafsat kin bani 
mamaki matuka. Cikin kuka tace Abba ka yafemin Wlh cikin Umar ne 
Mai martaba shuru yayi cikin jimami da takaici, Amma babu yanda ya iya, wannan abunda ya sameshi kaddara ce. 
Yace hafsat gashi Umar ya rasu, yanzu kina tunanin zaki sami wanda zai aureki, Bayan kin bata rayuwarki? 
Sheik musa monguno yace mai martaba, yanzu ka gama bayani akan hakuri da dangana, da kuma d’aukan kaddara, kayi hakuri, ka cinye wannan kaddaran taka kaima. Mai martaba yace hakane, Allah yasa mu dace, zan nemi iyayen umar din muyi magana dasu 
Kallon gimbiya zinatu yayi sannan yace zinatu kinyi matukar bani mamaki, kin San bala’in dake cikin aikata mad’igo kuwa? Bari kiji daka aikata mad’igo gara kayi zina duk da shima babban bala’i ne har gwara mai aikata zina akan mad‘igo Bari kiji illar dake cikin zina 
kawai Kafin muzo wajan mad’igo 
Mai zina mace da namiji akace ayi musu bulala d’ari, kuma kada aji tausayinsu akan bin hukuncin Allah, Indai kayi imani da Allah da Ranar lahira, sannan ana son jama’a mumunai 
su halarci azabarda za’ayi musu, wannan in saurayi da budurwa ne wanda basu da aure. 
Manzon Allah (S A W) Yace: Mai zina ba zaiyi zina ba, yayin da yake zina sai an cire mishi imani… Wa’iyazubillah yanzu Idan kana aikatawa Allah ya d’auki rayuwar mutum kunga ya mutu a kafiri Innalillahi‘wa inna ilaihirajiun, Allah yasa mu dace. 
Yace zina ta had’a dukkan sharri gaba d’aya, zina bala’i ce babba, tana haifar da bala’i Mai girma, Tana sa rashin tsoran Allah, tare da haifar da cututtuka da mutuwar zuciya, Tana sa zuciyar mutum tayi ba’ki da tsatsa ,tana sa mutum kullum ya jishi cikin damuwa da rashin kwanciyan hankali, sannan tana haifar da talauci, da zubewar mutunci, mazinaci dukiyarshi bata albarka, saboda kullum yana neman mata yana basu, Suma matan basa iya tara dukiyar saboda suna ganin wani zai basu, a haka za suyi ta zama har su daina samu, kowa ya’ki taimakon su. 
Manzon Allah (S A W) Yace mutum bakwai Allah ya tsine musu, kuma bazai kallesu da 
rahma ba ranan Al’Qiyama zaice musu ku shiga wuta Innalillahi’wa inna ilaihirajiun.. 
Mai yin zina da dabbobi Mai yin luwadi da mad’igo Wanda akeyi dashi 
Mai yin zina da uwa Sannan kuma yayi da y’arta Mai yin wasa da al’aurarta Ko maiyin wasa da gabansa 
Masturbation kenan Zinatu cikin kuka ta Fara fad’in wlh shekaranjiya na fara wannan mummunan abun, da 
masturbation nakeyi Ashe shima babban laifi ne, wayyo Allah na tuba Mai martaba yace Yana d’aya daka cikin laifukan da mutanan Annabi LUD suka aikata, sannan an ruwaita duk maiyin haka Indai harya mutu bai tuba ba zai tashi ranan alkiyama hannayenshi d’auke da ciki 
Yarima Aliyu yace Abba sannan duk maniyin da aka fitar dashi da gangan baya fita gaba d’aya wanda ya rage saiya daskare ma mutum cikin mara, sannan yana sa rashin haiyuwa wannan daskareren maniyin yana kashe kwayoyin hallita daga jikin namiji ko mace, sannan likitoci sun k’ara fadada bincike akan hakan yana haifar da mugayen cutuka kamar haka 
Saurin yin realising mutum nan da nan yaji ya Kawo, Yana saka raunin ido, mutum Idan yanayi zai iya rasa idonshi har abada, yana sa mutum yawan mantuwa, raunin al’aura, wannan y’ana d’aya daka cikin abunda masu wasa da yatsa ko masu aikata mad’igo yake 
haifarwa, bance duka ba shi yasa yanzu mata yawanci suke fama da rashin haiyuwa, wata 
ita lokaci ne baiyi ba, wata kuma tana aikata mad’igo Wanda maniyin daya fita sauran ya daskare mata a jiki, Abba tunda na Fara aiki a asibiti Ina had’uwa da abubuwan al’ajabi da dama sai dai muce Allah ya shirya ya ganar damu hanyar gaskiya. 
Mai martaba yace Zinatu ana son bawa koda yace ya tuba, yayi tuba na tsakani da Allah 
yanda bazai K’ara aikata wannan mummunan aikin ba Allah gafurul rahim ne, Allah mai yafiya ne ga bayinsa, Allah yana son bayinsa masu tuba. 
Zinatu ta kalli Yarima tace dan Allah Yarima kamin rai karka ce zaka rabu dani, wlh Ina Sonka, dan Allah ka yafemin Wlh na tuba, Yarima Ina Sonka dan Allah kayi hakuri. 
Yarima Aliyu shuru yayi yana nazari, can yace Zinatu Allah ya sani bazan iya zama ina kallonki da wannan abun ba, domin duk macen da zatai sha’awar mace y’ar uwarta, Toh kallon hoto take ma mijinta 
Da sauri mum tace Aliyu kayi hakuri ka d‘auki komai yazo maka a matsayin kaddara, nasan Kaga jarabawa, Allah yasa daka wannan sai jin dad’i,. 
Yarima Aliyu wani hawaye ne mai zafi ya fito mishi tare da fad’in ya zanyi mum? Babu yanda zanyi tawa kaddaran kenan sai hakuri, Allah ya bani ikon cinyewa, zan zauna da Mata na zan basu dama na biyu, Indai zan yafe ma d’aya dole In yafe ma d’aya, amma daka 
ranan da suka k’ara aikata wani aiki irin wanda sukayi, bazan iya d’auka ba, amma d ….. Shuru yayi yana kallon Bariki yace mum dole In k’ara aure, 
Da sauri Bariki ta taso ta nufeshi tare da fad’in Wlh ban yarda ba, tama manta suwaye a falon saida taji dariyan su sannan taji kunya tare da barin falon da sauri, ganin harda gudu takeyi yasa Yarima yabi bayanta da sauri Karta illata mishi unborn child dinshi, dan yaga 
kaman ta manta tana da ciki, kuma ance tana bukatan bed rest, shine take wannan gudun. Bata tsaya ba sai cikin gefenta, a bedroom ya sameta ta kwanta akan gado tana sauke nishi, d’agota yayi tare da fara fad’a kin manta bake d’aya bace Zainab har kike wannan gudun. 
Kuka ta sakar mishi da karfl tare da ihu Tana fad’in na shiga uku ….. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]