[Advertisements⬇️]

BARIKI NA FITO CHAPTER 45 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

BARIKI NA FITO
CHAPTER 45
Mum da sauri ta nufeshi, ganinjini na fita a bakinsa Idan yayi tari, kukata saki tana fad‘in shikenan Wlh tayi ma d’ana Asirin y’an Bariki…. Yarima Aliyu takaicin abunda mum din nashi take fad’a yayi, k’okarin kamashi tayi tare da fad‘in Yarima bari muje asibiti cikin tashin hankali take maganan. Yarima kai ya girgiza mata, dakyarya iya fad’in nafl son in mutu a gida tari ya kuma rik‘eshi Sosai, k’okarin tashi yake amma ya kasa saboda tarin da yakeyi, mum kamashi tayi, tare da taimaka mishi ya tashi, tace muje asibiti… Kai ya k’ara girgiza mata alaman a’a k’okarin tafIya ya farayi lokaci d’aya ya fad’i k’asa. 
Wani irin ihu mum ta saki tare da fad’in Yarima, da sauri kuma ta fita, saiga fadawa nan, suka Kama Yarima Aliyu akai asibiti dashi, koda suka isa asibiti emergency akai dashi domin a Fara bashi taimakon gaggawa.. 
Bariki kam tunda fadawa suka rakata harwaje, tafe take tana hawaye duk inda ta gani yarfa k’afa take bata ma San inda take biba, lallai rayuwar Bariki baiyi ba, duk a sanadin Bariki nake fuskantan wannan matsalan, lallai rayuwar mace k‘alilan ce, muddin kika aikata rayuwar banza koda kin tuba sai an goranta miki, wasu mutanan basa ansan tuban mutum gaba d’aya, lallai wa inda sukai sanadin lalacewarta sai Allah ya saka mata, kuka ta tsugunna tanayi Sosai, tare da tuna baya, yanda ta tashi taganta da ciki wanda bata san Wanda yayi mata shiba, wani hawaye mai zafl ne ya fito mata daka ido, tunawa tayi da Yarima ko yana cikin wani hali yanzu?  takardan daya bata ta Fara yagawa tare da watsar dashi k0 dubawa batayi ba, domin wannan ba’kar takardan ba Abun kallo bane, lokaci d’aya ta tashi taci gaba datafiya,tafiya taketana kuka,jiri taji yana d’ibanta lokaci d’aya ta fad‘i k‘asa kaman gawa. ’ 
Yarima kam likitoci ne a kansa suna k’okarin ceto rayuwarsa, so suke numfashin shi ya dai daita amma abun yaci tura. Mum tana asibitin Tana ta sintiri tare da hawaye mai zafl, saiga Mai martaba nan cikin tashin hankali, yake tambaya maiya sami Yarima? Cikin kuka take fad’a mishi abunda ya faru tun daka kan tura mata hotunan bariki da akayi haryanke hukuncin da tayi. 
Mai martaba kallo d‘aya zaka masa ka gane ranshi a bace yake, amma ya daure a matsayinshi na sarki Mai shugabantan al‘umma baice komai ba sai hakuri da yayi taba mum akan tayi mishi addu’a ne zai tashi insha Allah. Amma ran Mai martaba yayi mugun baci da irin wannan hukuncin da mum ta yanke ba tare da saninshi ba, lallai komai ya sami Yarima itace, domin itace ummul aba’isin wannan abun, yaka mata tunda taga Abun ta fad’a mishi a matsayinshi na mijinta bawai ta yanke hukunci ba, duk da Mai martaba shima ranshi ya baci da Zainab din akan abunda tayi, musamman iyayen Bariki data samu, kenan su waziri basuyi bincike dakyau ba? Ko ince sarkin anguwan, lallai zanyi bincike akan wannan al’amarin. 
Zaunar da mum yayi shima ya zauna, duka babu Mai cewa komai, gaba d’aya suna jiran fitowan Dr. Suna nan zaune baka jin kukan kowa sai na mum tare da tsanar matar Yarima da take ganin irin wannan son da d’anta yake mata kaman asiri tayi mishi, tunda karuwa ce, and kuma karuwa babu abunda ba zatayi ba. Fitowan Dr ne yasa Mai martaba ya tashi tare da nufan Dr yana fad’in yajikin nashi? 
Dr d‘an shuru yayi tare da fad’in ranka ya dad’e muje office, mai martaba da mum suka bi Dr, fadawa Suma suka bi bayansu, koda akaje office din Dr mum da Mai martaba ne suka shiga, inda fadawa kejiransu awaje. 
Bayan su mum sun shiga Dr yace su zauna, dakyar mum ta zauna. Mai martaba yace ya jikin nashi? Dr yace gskiya sai a hankali, mudai munyi iya yin mu, amma gaskiya yana cikin danger rayuwa ko mutuwa, ko wanne zai iya faruwa, tun sanda ya sami bugawan zuciya da farko, abun ya taba zuciyarshi, wanda rashin samun abunda yake so, ko kuma ganin abunda baiyi tsammani ba, ko yaji, zai iya saka shi cikin mugun wani hali, lallai bai kamata ku d’aga mishi hankali ba, irin haka wani ldan aka mishi abun damuwa sai zuciyarshi ta buga nan take yake mutuwa, amma shidai bai mutu ba amma bazanyi alkawarin zai tashi ba ko akasin haka, domin anything can happen.. Kukan mum ne yasa Dr yin shuru mum tace Dr do what whatever you can, but make sure Yarima ya tashi, shi d’aya ne d’ana namiji dan Allah Dr ka ceci rayuwar d’ana dan Allah, tana maganan tana kuka Sosai, tace Dr ko Nawa kake so zan baka but make sure Yarima ya tashi pl ….. Kuka yaci karfinta ba tare data k’arasa abunda take son fad’a ba, ganin haka Dr ya fita ya barsu a office din. 
Bayan fltan Dr Mai martaba yace Khadija wannan kukan da kikeyi bashi bane maflta, aiko mai ya sami Yarima ke kikaja, dan haka ki bar wannan kukan cikin kuka tace haba Mai naja Mai Nayi da za’a d’aura min laifiMai martaba yace akan wani dalili zaki rabashi da matarshi bayan kin San sarai abunda ya faru abaya, wlh Khadija komai ya sami Yarima Kece, akan wani dalili zaki yanke wannan babban hukuncin ba tare da kin fad’amin ba, ai gashi yanzu ldan kika rasa d’an naki saiki huta. Cikin kuka tace haba Mai martaba yanzu abunda nayi shine Nayi laifI?? Karka manta nifa uwa ce, sannan abunda nayi shine duk wata uwa zata aikata, taya zan yarda d’ana dana haifa cikin cikina ya dinga zama da karuwa a matsayin mata, wacce ‘ta gama yawon gantalinta, sannan Bayan haka tayi mana Karya tare da wasa da mu, ta wajan Kawo iyayen bariki, haba Mai martaba miye laifina dan nace Yarima ya saki wannan fasi’kan yarinyar, kaida kanka ka sani wannan abun yana d’aya daka cikin abunda in mutum yayi ake saki cikin masarautar nan ….Dakatarda ita yayi tare da fad’in, kin ganta da idonki ne?? Komai ta aikata tama kanta kuma wannan tsakaninta ne da Allah, yanzu tunda ta riga ta auri d’anki, miye amfanin cewa ya saketa, bayan sarai kin San irin sonda yake mata… Tace babu wani so, aikin Asiri ne, sannan Wlh bazan yarda d’ana ya zauna da karuwa ba, koda kuwa mai zai faru.. 
Mai manaba yayi murmushi tare da fad’in in baki yarda ba, yanzu da kika saka ya saketa duk inda taje za’a ce tsohuwar matar yarima Aliyu Yaron Khadija d’an gidan Murtala, Toh koda kuwa mai zai  Toh mai kikayi? Khadija yau kin bata min rai yanda bakya zato, kin nuna ban isa ba har zaki yanke hukunci ba tare da sanina ba, toh amma Bari kiji idan kina ikirarin bazaki yarda d’anki ya zauna da karuwa ba kinsa ya Mata saki uku, yanzu saiki shirya kukan mutuwar d’anki dan Kinji abunda Dr yace, sannan a matsayina na mahaifin Aliyu Idan wani abu ya sameshi lallai saina hukunta ki, tunda Kece sila, kinsa ya mata saki uku kin datse zamansu na har abada, na tabbata hakkinsu bazai barki ba, dan kina matsayin uwarshi, Nima ubansa ne, inada hakki akansa, amma ki ro’ki Allah ya tashi lafiya, yana fad’in haka ya fita 
Mum kam kuka take Sosai tare da k’ara tsanan Bariki, wlh koda Yarima ba saki uku yayi mata ba, bazata Bari yaci gaba da zama da karuwa ba, wacce ta gama ballazar da kanta a 
Bariki kam inda ta fad‘i mutane sukayi kanta aka zagaye ta, wasu kam d’aukanta hoto suke a Fara yad’awa a media, duk yawan mutanan da suka zagaye ta babu wanda yayi kokarin ya d’auketa koya taimaka mata, yayinda wasu harga Allah tsoran taimakonta suke, domin yanzu duniya ta zama Abun tsoro, saika taimaki mutum ya cuceka, wani mutum ne da yazo wucewa yaga dandazon mutane, dan haka ya faka tare da tambayan maike faruwa? Nan wani ya fara bashi amsa da abunda ya faru, nan mutumin ya kutsa cikin mutane ya ganta a kwance, da sauri ya nufeta tare da daukanta ko kallon mutanen baiyi ba Ya sata a mota, nan wasu daka cikin mutanan suka fara fad’in ka Santa ne?? 
Mutumin yace koda ban santa ba, shi taimako yana dakyau, ta fad’i kuma ba mutuwa tayi ba, yaka mata ace kun taimaka mata, amma dukanku babu wanda yayi wannan  Idan yau ya faru akan wata anyi mata haka, toh gobe kaima a kanka zai faru, dan haka ya kamata ku gyara, yana fad‘in haka yayi motarshi domin ya kaita asibiti, yabar mutanan cikin tunani yayin da wasu kuma suke fad’in kaji dashi kaida kaga zaka iya. 
Mutumin direct asibiti yakai Bariki, itama din de emergency aka kaita, nan aka fara bata taimakon gaggawa cikin ikon Allah numfashinta ya daidaita, bata ko 30min ba ta farka tare da fara bud’e idonta, ganinta a kwance yasa ta gane a asibiti take, gefenta ta kalla da sauri ta tashi domin ganin Yarima Aliyu a kwance, tsige Abun drive din da aka saka mata tayi, jini ya fara zuba da sauri tasa hannunta ta toshe, tare da nufa wajan da Yarima Aliyu yake kwance rai a hannun Allah, da sauri ta ri’ke Mai hannu tana kuka tare da fad‘in Yarima maiya sameka? Kuka take Sosai cikin tashin hankali, Yarima Aliyu dake kwance lokaci d‘aya ya fara numfashi da karfl alaman numfashin shi yana son dai daituwa, ta dad‘e a ri‘ke da hannunshi tana kuka kanta na k’asa. 
Ji tayi yasa hannunshi akanta, Tsagaitawa tayi da kukan, domin tana son ta tabbatar shi dinne yasa mata hannu akai, lokaci d’aya ta d’ago dakai a hankali, cikin mamaki taga yana sakar mata murmushi, itama murmushin ta sakar mishi tare da rungumeshi tana kuka, Tana fad’in Yarima maiya sameka? Bai bata amsa ba, sannan bata damu ba ita tunda taga ya farka hakan yafi mata komai, tana kwance jikinshi abunda ya faru ya fara dawo mata, yanzu ita ba Matar Yarima bace? 
Da sauri ta tashi daka kan jikinshi tana hawaye Mai zafl, idon Yarima na kanta yana mamakin irin Tashin da tayi cikin razana tare dayin baya dashi, gaba d’aya ya kasa magana, domin bakinshi yayi mishi nauyi yana son yi mata magana ya kasa, sai hannunshi da yake mi’ka mata alaman tazo, ga jinin daya gani a hannunta yana zuba, duk da shima ta bata shi da jinin, Bariki kam ganin yana mi’ka mata hannu alaman tazo yasa ta Fara fad’in Yarima kayi hakuri na haramta a gareka, Yarima Nasan bazan iyajuran rasaka ba, Yarima Ina ro’kan ka dan Allah kaima ka tashi kaci gaba da rayuwa kaman kowa, Yarima Sonka a jini na yake, amma an yake duk wata jijiya da zai had’ani dakai, na tabbata Yarima Sonka shine ajali na amma ya zanyi kaddara ta riga fata, Yarima Indai dagaske kana sona ka tashi daka wannan yanayin da kake ka koma kaman da, Nasan Yarima namiji ne mai cikar laflya, namiji ne mai kwazo, karka bari wannan ciwon y ….. Kuka yaci karflnta lokaci d’aya kuma tace Yarima ka yarda dani a matsayin kaddara lokacin da kasan koni wacece, yanzu Ina son ka yarda da rabuwa na dakai shima a matsayin kaddara S…. Kuka take Sosai ga Yarima dake kwance hawaye na zubar mai hannunshi yana tsaye yana kiranta tazo amma ta’ki,gashi ya kasa magana. 
Bariki da sauri tabar d’akin ganin fadawa a waje damai martaba yasa ta dawo da sauri, tare da hawa window ta dirka ….. Tana dirka cikinta ya murd‘a mata alaman ciwo. Yarima kam gaba d’aya kasa tashi yayi domin jin kafarshi yake kaman an d’aureshi da igiya, sai hawayen takaici yake, yana son magana da Zainab ya kasa Shigowan Dr ne yasa Yarima Aliyu kallon kofar Dr ne da mutumin daya kawo Zainab din, Dr yace Ina tayi kuma“
Mutumin yace ikon Allah, nan Dr yace May be ta farka ne ta tashi , ganin jikin Yarima da jini, itama gadon da take da jini yasa Dr saurin ‘karasawa wajan Yarima, lokaci d’aya kuma ya saki murmushi Dr din ganin oxygen din yana taflya dai dai alaman numfashin Yarima ya koma dai dai, duk da idon Yarima a lumshe yake, 
Dr Ya kalli mutumin daya kawo Bariki, yace lallai ka tabbatar ka nemota, domin tana bukatar bed rest, cikinta sati uku da kwanaki, in bata huta ba zai iya zubewa gaskiya. Mutumin yace Dr nima a hanya naga ta fad‘i n ….. 
Yarima Aliyu da tunda yaji ance ciki Zainab take dashi ya bud’e ido, lokaci d’aya wani karfl yazo mishi,jinshi sukayi yana fad’in Dr kana nufln Zainab Tana da ciki?? 
Su duka suka bishi da ido alaman mamaki, tashi Yarima Aliyu yayi zaune,yace Dr she is my wife plz tell me is she pregnant??.. 
Dr yace yes she is pregnant, but where is she?? 
Yarima Aliyu cire oxygen din dake hanncinshi yayi tare da tsige Abun drive din dake hannunshi, da sauri Dr yace Aliyu ka tsaya, da sauri Dr din ya nufeshi tare da ri’ke Mai hannun dake zubar da jini, Yarima Aliyu yace Dr leave me I will handle it, am a Dr too.. Dr yacel know but plz ka tsaya kasan yanayin da kake ciki, bai kamata ka fita haka ba, u need to rest Yarima Aliyu yace how will I sit hare and rest matata da unborn child d’ina suna cikin had’ari bayan kace cikin zai iya fita, I have to go and find her. Babu yanda Dr ya iya dole yabar Yarima ya fita, inda yana flta yaga mai martaba da mum da fadawa. 
Mum ganin d’an nata ya fito yasa ta saki wani murmushi Tare da furta Alhmdlh, nufanshi tayi tare da rungumeshi tana kuka, mai martaba shima tashi yayi yana fad‘in Aliyu ya jikin naka, amsawa yayi da Alhmdlh Abba, mum sakinshi tayi tana fad’in ya jikin naka ya amsa da Alhmdlh mum, tare dayin gaba da sauri. 
Mum damai martaba binshi sukayi da ido, ganin Dr yasa suka nufeshi suna fad’in ina zashi, nan Dr Ya fara basu Labarin Yarinyar da aka shigar da ita d’azu matarshi ce, and tana da ciki Yadai basu Labarin komai, tare da fad’in abunda na Lura is lyk kaman itace wacce lokacin da yayi irin wannan tayi mishi magana ya tashi koh?? 
Mai martaba yace eh Dr itace, nan Dr yace gskiya yana mata son da, dukansu bazasu iya rayuwa babu dayansu ba, dan haka ku tabbata Yarima duk inda zashi ko ince kar’ayi abunda zasu rabu dajuna, ban taba ganin irin wannan son ba sai a Fina finai ko a littafai, ashe yana faruwa da gaske, duk da Muma a karatun mu anyi mana wajan, but ban taba d’aukan abun serious ba dan Banyi tunanin zai faru ba, sai gashi na gani yanzu, and shawaran da zan k’ara baku shine ku tayashi dubata, domin Indai bai ganta ba gaskiya I don’t know wat will happen, nan Mai martaba yace mun gode Dr, Dr yace babu komai ganin matar tashi shine lafiyanshi Mum kam gaba d’aya duk abunda Dr yake fad’a babu wanda ya shiga kunnenta, ita tunda d’anta ya tashi Alhmdlh, sannan maganan a nemo matarshi bai taso ba, tunda ya Mata saki uku, and kuma cikin dake gareta ta tabbata bana d’anta bane, sai dai in wani ya Mata ciki y’an iskan samarint…. Mai martaba ya Katseta da fad’in Kinga ikon Allah koh? Kina tunanin kin rabasu amma Akwai ajiyar jikanki ajikinta, Kinga haryanzu ala’ka bai ‘kareba tsakaninsu, Idan babu ala’kan aure Akwai na abunda zata haifa, lallai kl godema Allah da yasa sai da akayi auren kika san ko wacece, domin na tabbata inda kin San ko wacece basuyi auren ba Nasan bazaki amince ba, not even you Nima da kaina bazan amince ba, Kinga Ashe Akwai rabon wannan cikin, kuma rabo na kisa, and inma baiyi kisa ba za’a kawo mana jika babu aure shi kuma wannan sai muce me?? 
Duk abunda kikaga Allah yayi, karkiyi jayayya akan abun, yanzu kina murna kin raba d’anki da matar da kike kira karuwa, gashi a karo na biyu ta k’ara taimaka mishi, lallai Khadija keda kanki kike son kashe d’anki, yanda d’anki yake Sonta itama take sonshi in bakiyi wasa ba za kiji suna zaman dadiro ko kiji yasa tayi auren kissan wuta, daka k’in gaskiya sai bata 
yana fad‘in haka ya tafl ya barta domin yaga wani hali d’an nashi ke ciki 
Hmmm Tashin hankali mum duk maganan da mijinta ya fad’a mata, babu wanda ta d‘au ka domin idonta ya rufe, lallai Asirin bariki yayi tasiri har akan mijinta, domin gaba d‘aya taga baya ganin laifin kowa sai Nata, wacce take ganin abunda tayi shine dai dai, lallai dole ta nemi maganin karya sihiri taba d’anta da mijinta, itama binsu tayi domin taja d‘anta suyi gida, dan tasa a Fara mishi addu’a, 
Yarima Aliyu taflya yake cikin haraban asibitin jiki babu kwari sai waige waige yake, kallo d‘aya zaka mishi kasan yana cikin Tashin hankali tare dajin zafIn ciwo, gaba d’aya cikin asibitin baiga mai kama da Zainab ba, dan haka ya flta waje, nan mutane suka fara tareshi ana fad’in yarima Aliyu, mai jiran gado, gaba d’aya mutane sun hanashi yin gaba suna k’okarin gaisawa dashi, ganin haka fadawan dake binshi a baya suka zo suka fitar dashi suka sashi a mota, koda Mai martaba ya fito ganin abunda ke faruwa shima motarya shiga yace su nufi Gida,Yarima idonshi nakan titi ko zaiga Zainab amma baiga koda Mai kama da ita ba, haka har suka k‘arasa gida, Yarima Aliyu hannunshi ri’ke dana Mai martaba suka shiga gefen mahaifin nashi, suna shiga Yarima ya fad’a kan kujeran falon ya fara hawaye tare da ri‘ke kirjinshi dake faman mishi zugi da rad‘adi, ganin haka Mai martaba ya Flta tare da kiran waziri akan suje su duba gidan iyayen yarinyar na k‘arya may be tana can, nan su waziri suka amsa da angama ranka ya dad’e suka tafl. 
Bariki kam tunda ta flta daka asibitin cikinta na Mata ciwo Sosai, samun wani waje tayi akwai rumfa ta kwanta, domin babu komai a hannunta, harta wayarta bata hannunta, gashi yanzu babu bank sun tashi da taje ta cira kud’i ta check book, haka ta kwanta a wajan domin ciwon cikin yana damunta Sosai, ita bata ma San tana da ciki ba, Hmmm Bariki babu riba, lallai rayuwar mace kalilan ce, zakiyi iskanci lokaci kad’an kiyi sanyi a daina yi dake, in kinso shiriya mutane su dinga nuna miki kyama da hantara, tare da goranta miki, inma kin samu mijin aure kin haiyu aita miki gori ana ma y’ay‘anki gori, daka fad’a ya had’asu da wani aita musu gori, y’ar uwa Mai yafi wannan ciwo da zafi? Gashi kullum in kika flta miji yaita zargin ki, kai Wlh Mata iskanci da fitsari bashi bane wayewa, babu abunda yakai kame Kai da tsare mutunci dad‘i, ldan ke ta’kamarki bin maza kina bud’e musu k‘afa suyi lalata dake, daka ranan da kikace d’aya daka cikinsu ya flto ya aureki, zaki ga yace shi dan iska ne da zai aureki? Bayan kin gama bin maza ai inada kishin kaina, daka ranan ma in bakiyi wasa ba yabar kulaki, mai wayau kuma zaiyi ta miki Karya tare da alkawarin zai aureki, inya gama cin moriyarki ya gudu, ke koda shine ya fara saninki kuma shi d‘aya kike bi, wlh bazai iya auranki ba, domin shifa a kullum tunani yake kina bin wasu mazan, zaki ce ai maza nawa sukayi lalata da Mata suka auresu Toh Bari kiji Wlh Mata da yawa y’an duniya wanda suka amsa sunansu y’an Bariki, akwai namijin da suke nunamawa 
su ustazai ne basu taba sanin namiji ba, daka anyi aure yaji kofara bud’e take sai kuji ya saketa, aure kuga k0 sati baiyi ba Ya mutu, wasu kuma asiri suke ma mazan su auresu, Hmmm kuma duk abunda aka had’a da asiri baya ‘karko domin asiri dai yana karyewa daka ranan daya karye ranan zaki gane shayi ruwa ne, y’ar uwa komai zakiyi ki yishi akan gaskiya, da yawa zaki ga y’an duniya suna hulda da malamai, amma daka karshe ya rayuwarsu take k’arewa? Idan har kin San miye rayuwa kuma kina nazari kina kallon abunda ke faruwa, wlh zakiji tsoran duniya da rayuwa kiga ba komai bace, yanzu maza yawancin su babu abunda suka iya sai soyayyarshan minti, daka sunje wajan Yarinya zasu Fara mata maganan banza da rashin kunya, daga nan sai a fare tabe tabe, wani ma so yake ya aureki, amma yana gwadaki daka ya taba yaga kin biye mishi, sai yace y’ar hannu ce shida yazo da niyan aure sai ya nemi kwanciya dake daka kin bashi ya gudu, ke kina ganin hakan shine wayewa, 
Wlh mata ku kiyaye, shi yasa yanzu y’an mata sukai yawa, babu mazajan aure, domin mazan suna mana kallo a d’age, suna ganin kaman duka d’aya muke, yau Idan namiji yazo Wajanki yayi k’okarin tabaki kika rufe ido kika ci mishi mutunci kika tafi kika barshi, wlh Indai aurenki zaiyi gobe zai dawo, domin zaice kinci jarabawan shi, amma daka ya tabaki saiki bada Kai bori yahau, kai Wlh Mata masu irin wannan halin aji tsoran Allah, domin duk iskancin namiji so yake ya auri nitsatsa ba ballagaza ba, wacce kowa ya Santa, Allah ya kyauta. 
Koda su waziri suka isa gidan iyayen Bariki na k’arya, mamanta tace ai tunda tayi aure bata zoba. 
Koda su waziri suka koma suka fad’ama sarki, Yarima babu abunda yake sai kukan zuci, domin yanzu hawayen dake fuskanshi Ya’ki fita, saboda yana cikin Tashin hankali da damuwa, fiye da tunanin mai karatu, Yarima Aliyu yasan rashin matarshi kaman barazana ne ga rayuwanshi, gashi ba ita d’aya ba, tana d’auke da cikin shi, lallai Mum ta gama dashi da tasa ya saki matarshi, inda tasan irin son da yake mata da bata ce ya saketa ba, mai yasa mutane basa d’aukan kaddara Indai ba’a kansu ya fad’a ba?? Mai yasa mutane basa ma wasu uzuri Indai basu bane suka aikata?? Mai yasa duk abunda ba damuwarka bane mutane basa d’auka da muhimmanci?? Shin Mum tasan zan iya rasa raina akan Zainab tayi k’okarin rabani da ita? Shin tasan Sonta ajini na yake? Lallai Indai banga Zainab ba komai zai iya faruwa domin yanzu dauriya kawai nake, Yarima Aliyu lokaci d’aya ya fara girgiza kai domin tunawa da yayi Karta koma ‘Irin rayuwarta ta da, tashi yayi da sauri. Mai martaba yace Aliyu lna zaka? 
Yace Abba neman Zainab, zani in dubata, Abba Ina tsoran ta nanata irin rayuwar da tayi a baya, Abba ban son ta k‘ara bata rayuwarta ….Mai martaba yace Aliyu zoka zauna, nasa a nemota, Aliyu zama yyi tare da fad‘in Abba Kirjina tare da ri’ke wajan ya kasa magana, da saur’I mai martaba yayi kansa…. 
Habib ne zaune gaban hjy Umaima yana fad’in, na samu Labarin Yarima ya saki bariki, dama shi yasa na fad‘a miki iyayenshi basu sani ba, gwara da kika turama uwarshi, Kinga yanzu aiya saketa, 
Hjj Umaima dariya tayi cikin jin dad’i tare da fad’in yanzu sai a nemo min ita 
Habib yace hjy aiki kwantar da hankalinki ita da kanta zata kawo kanta, tunda Yarima ya saketa ai dole ta dawo gidan jiya, dama saboda shi ta shiryu, yanzu Kinga tunda ya korota ai dole a dawo gidan jiya, ko dan a sami na rufin asiri. Hjjj Umaima tace hakane yanzu abunda ya kamata shine, ka koma kaduna nasan for sure zata koma gidan barikin da take tana zuwa call me, Zanzo kaduna din. Habib yace an gama, ai hjy Wlh bariki komai kika ce mata yanzu zata yarda domin bata da wani zabi, saina abunda kikace, tunda komai ya cabe Mata, yace hjy inada y‘ar tambaya? 
Hjj Umaima tace inaji Yace hjy ldan kuna wannan lesbians din dad’i kukeji? Hjj Umaima tace Kai ldan ana cinka ta baya dad‘i kakeji? Habib yace na shiga uku, Nayi gamo amma gaskiya banji dad’in wannan zancen ba, wlh har kinsa naji kunya, wai anyi da mutum yaji ‘ Hjj Umaima tace Aiba k’arya Nayi ba, ni kaga k0 Kinga zance dan Allah kama hanya zan maka transfer yanzu dan banda cash, koya ake ciki call me, inma bata zo ba make sure ka nemo min ita zuwa gobe, Yarinya sai shegen kaflya, Nayi Asirin amma shuru, aiki ya’ki kamata, ni Allah yasa tana da ruwa ma,koda yake ko bata dashi yanda na kwallafa rai sai naci ko ana ha maza ha mata saina d’ana, tunda na Kwadaita 
Habib yace ah wannan zance yafI karflna, Kinga Nayi gaba, inji alert , domin komai danshi nakeyi. 
Hjj habiba iya tashin hankali ta shiga, farhan tunda yabar gidan sai cikin dare ya dawo, a falo yaga mum din tashi, wani irin kallon tsana ya Mata tare da d’auke idonshi daka kanta, dan baya bukatar yana ganinta ko kallonta, domin abunda ya gani shine yake dawo mishi. Ganin yana k’okarin wucewa yasa ta tashi ta nufeshi tare da fad’in farhan plz ina bukatar magana dakai, dan Allah ka saurareni. 
Yace plz matsa min a hanya, I hate to see ur face, bana bukatar koda muryanki inji, sai kuma ya saki kuka. 
Hjj habiba tace farhan Nasan dole zaka tsaneni amma Kafin nan ina son kaji dalili na, kayi min uzuri kuma tare da adalci 
Yace babu abunda zan saurara daka gareki Wlh inda kin San hukuncin abunda kika aikata da bakiyi ba, lallai mum shaidan ya gama dake, kiyi gaggawan tuba tare da ro’kan gafaran Allah, karki bari mutuwa ta riskeki kina Mai aikata wannan mummunan aikin zunubin, wlh mum da kin San irin bala’in dake cikin wannan abun da baki aikata ba, mad’igo wai Uwar data haifeni ita take aikata wannan mummunan abun, amma babu damuwa Allah zai hukunta ki, sannan tun a duniya zaki gani, ko ince kin Fara gani, domin Allah ya jarabci d’anki da son wacce kuke aikata wannan mummunan aikin, kuma Wlh Indai Kinga ban auri haulat ba Allah yasa ba matata bace, ko kuma ni na mutu ko ita ta mutu, saiki shirya amsan abokiyar lalatanki a matsayin surukar ki matar tilon d’anki yana fad’in haka yayi gaba, Tashin hankali …….. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]