[Advertisements⬇️]

BARIKI NA FITO CHAPTER 41 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

BARIKI NA FITO 
CHAPTER 41
Lallai dama duk Wanda yabar Allah yana tare da tabewa da Asara, duk Wanda ya zabi sabama Allah, amma babu komai zan jure insha Allah, zan d’auki duk wani hukunci ukuba da Yarima zaiyi min …… Da sauri ta tuna da abunda habib ya Mata, lallai habib yaci amanarta rayuwa wanda ka yarda dashi shine mai cutanka …… D’auko wayanta tayi duk da dama Yarima ya canza mata layi gab da bikinsu Tana da number habib dana su haulat …… Kiran habib tayi duk da lokacin wajan karfe biyar saura an kusa kiran sallah asuba ….. Cikin muryan bacci ya d’auka daka gani baima ko duba sunan ba ….. Jin muryan bariki yasa habib fad’in harya koroki ne??? 
Tace habib kaci amanata Tana magana tana kuka, mai yasa kamin haka, duk irin yardan da nayi maka??? Yace dakata ki daina kaini jinsin da ba nawa ba Mlm, Tace an kaika d’an daudun banza da ham… Maci Amana Habib yace dakata bariki, miye zancan cin Amana?? Au dama bariki akwai Amana ne?? Toh gaskiya Indai haka kika d’auka bai kamata a dinga ce miki bariki ba, karki manta kud’i na flto bid’a, kuma da Farko Aina rufe miki sirrinki, da aka Biyani naira na dukan Naira har million biyar na fad’i gaskiya, sannan wacce taban tace in kira Yarima in fad’a mishi gaskiya, Kamin ki fad’a mishi, sannan ta tura mai hotunan ki da kikai da maza, da sim d’inta na kira kuma ta wayarta ta tura hotunan, dan haka aikin kud’i nayi, ke kina tunanin saboda in rufa miki asiri zanki amsar million biyar, haba bariki ai kin yaudari kanki, Bariki babu Amana ko yarda ….. Da Farko na ri’ke miki amana daka baya kud’i yasa na canza, dan haka Kar kiga Habib yace Ina ja miki kunne ki daina kaini jinsin daba nawa ba, sannan Bari kiji ita wacce ta Biyani so tayi Yarima ya koroki ita ta aureki domin y’ar lesbians ce, bari in fad‘a miki sunanta, sunanta hjy Umaima abunda yasa na fad’a miki koda Kema zaki Biyani ki nemeni dan ki rama, ko yaushe ina free Danni da kika ganni y’ar kasuwa ce ya k‘arasa maganan tare dayin shewa ahayye ……. Ita haulat da bata da k‘ashin arziki Aida ita akaso ayi aikin ta Fara yima matar kwana kwana ….. Bariki kashe wayarta tayi domin bazata iya jin wannan tsinannan ba …… Kuka take Sosai wato hjy Umaima itace tayi komai tare da amfani da habib, toh taya tasan habib din?? Taya suka had’u?? Lallai haulat ya kamata taban amsa, kiran Layin haulat tayi bata d’aga ba, k’ara kira tayi harya kusa tsinkewa sannan haulat ta d’auka cikin muryan Da sauri Bariki tace haulat maina miki keda habib da hjy Umaima ….. 
Haulat da bacci ke idonta jin haka yasa ta tashi tare da cewa bariki, Kece?? Mai kike fad’a Nan Bariki ta bata Labarin abunda habib yayi mata 
Haulat tace Bariki wlh Wlh ban San hjj Umaima zatai miki haka ba. da Farko dai taso taje 
wajan boka danta miki asiri ki yarda da ita, har nayi niyan taimaka mata a lokacin, sanda na dawo kaduna in zaki tuna wata rana Aina amshi wayarki?? Toh Ina cikin duba hotunan da nake turawa sai gashi an turo wani keda Alh madu tsirara, nan nima na tura, in baki mantaba data dinki a kunne take ranan, ganin na tura na Alh madu saina had’a dana wani da kika kwana a kirjinshi, ina gamawa na baki wayarki, dama Nayi magana da hjy babba akan Alh madu ya bashi aikin ya gano wa zaki aura, yace yana son in tayashi …… Jin haka saina kira hjy Umaima akan Kartaje wajan boka na bata labarin halinda kike ciki, akan auran da za kiyi akwai wanda yake son rusa auran, harda hotunan dana tura cikin wayarki ta bu’kaci in tura mata tunda na bata labari, nan na tura mata harda number din habib dan na fad’a mata shine yasan komai da kike shiryawa …… Bariki tun ranan da kikai min wa’azi tare da nasiha Wlh daka ranan naji jikina yayi sanyi tare dayin nadama, kuma harga Allah na cire hannuna daka son cutar dake, wlh bariki ban taba tunanin hjy Umaima zata nemi habib ba, dan tunda tamin magana nace tayi hakuri kawai ta bari kiyi aure in yaso daka baya sai ta nemeki, na fad’a mata hakan kawai danta kyaleki ne Ashe bata hakura ba, kai amma wannan matar akwai y’ar iska amma karki damu bariki zan dau miki mataki Wlh, Shima kanshi Alh madu da kanshi ya kira hjy babba yace a daina maganan ya barki kawai ……… 
Bariki kashe wayan tayi bata taba tunanin hjy Umaima ko habib za suyi mata haka ba, lallai makashinka na tare dakai, ta yarda da habib amma yaci amanarta, lallai gaskiya habib ya fad’a bariki babu Amana, sannan komai kayi sai Anci amanarka Indai a bariki ne,jin kiran sallah asuba yasa ta tashi dakyar kanta kaman zai fashe da ciwo, toilet ta nufa dakyar tayi alwala, tazo tayi sallah …… 
Bayan ta idar gaba d’aya ta kasa bacci , ba komai take tunani ba sai irin matakin da Yarima zai d’auka wanda ta tabbata za taji jiki, dan murmushi tayi tare da fad’in indai wannan hukuncin da Yarima zaimin zaisa ya yafemin Zanjura, koda zaiyi ta azabtar da rayuwa na Indai Ina matsayin matarshi zan jure…. Kuka ta kuma saki tare da fad’in Yarima Ina maka son da Sonka a jini na yake, zan amshi duk wani horarwa daka gareka …… Tashi tayi ta fita falo da niyan ta Fara aikin bauta daka yau,tana shiga taga Yarima kwance akan kujeran falon yana rawan sanyi, da sauri ta nufeshi cikin Tashin hankali idonshi a rufe kaman yana bacci amma ba bacci yakeyi ba …….. Hannunta tasa akan goshin shi taji zafi Sosai.. Ido ya bud’e a hankali idonshi ya sauka akan Nata gaba d’aya kallon juna suke cikin ido …… Sunyi wajan minti uku suna kallon juna Kafin ta tashi da sauri taje ta samo ruwa da towel tasa towel din tare da matsewa, ta Fara k’okarin sama Yarima akai cikin murya irinta mara lfy
yace don’t you dare try to touch me. Cikin kuka tace Yarima plz allow me to do it, you have a fever ….. Yana k’okarin yin magana tayi sauri tasa Mai towel din akai tana d’an matsa Mai,jin haka yasa ya kasa maganan da yake son yi ….. Amma cikin ranshi babu komai sai k’una tare da tuna hotunan da aka turomai bariki akan namiji tana kwance ga wani kuma yana tsirara ya ri’keta, da sauri yasa hannu ya ture ta
K’asa tayi ruwan dake kusa da ita ya zube, yace karki k’ara zuwa inda nake,i have told you, I hate to see your face…. 
Kuka take Sosai tare dayin nadama akan irin rayuwar data jefa kanta, dan kawai ta kuntata ma Dad d’inta, wanda inta mutu bata da wata hujja, lallai dama irin bala’in dake cikin zina harda rashin ganin k’imar mutum, sannan ba’a ganin darajan mazinaci Wanda gashi shine 
take gani yanzu, ta tabbata bata ga komai ba yanzu, sai nan gaba ….. Yarima ne ya daka mata tsawa cikin tsana tare da fad’in I said leave from here. Jiki a sanyaye ta tashi tana kuka harta kusa shiga d’aki yace stop …… Cak ta tsaya 
Yace zoki goge wannan ruwan, wa kika bari ya goge?? And make sure ki cire carpet dinnan dan ruwa ya tabashi shima, kije ki shanya a waje …… 
Kitchen ta nufa ta d’auko mopper ta Fara gage ruwan, carpet din yana da girma kasa d’auka tayi, duk abunda Zainab keyi Yarima na kwance yana kallonta, ganin bazata iya 
d’auka ba yasa tace Yarima cikin dashewan murya bazan iya d’aukan carpet dinba yayi min nauyi ….. ‘ 
Murmushi yayi tare da fad’in inda sex ne ai kina iya yi, harda kwanciya akan k0 wani namiji kin iya, kindai iya karuwanci …… 
Ido ta lumshe domin maganan Yarima Aliyu ya dakar Mata zuciya, harga Allah Kalman daya fad’a ta iya karuwanci taji Kalman har cikin zuciyarta, tunda take ba’a taba ce mata karuwa ba tunda ta fitO karuwanci Abun ya dameta, ita da takeso a dinga ma kiranta da bariki, amma yau shine rana na farko da aka ce ta kware da karuwanci Abun yayi mata ciwo…. Wani zazzafan hawaye ne ya zubo mata ganin in bata fitar da carpet dinba zaiyi ta fad’a mata magana shi yasa ta Fara k’okarin ta d’auki carpet din domin ta kaishi waje din, kaman yanda yace…. Fara ja tayi tana son tayi k’okarin ta d’auka tasa akai, santsin tiles din wajan dabai bushe ba ya di’beta zata Zame, gaba d’aya ta sadakarta fad’i ji tayi an ri’keta, idonta dake rufe saboda tsoro ta Fara bud’ewa tayi a hankali idonta ya sauka akan na Yarima da shima din ita yake kallo, sunyi wajan minti biyar a haka suna kallon juna , sannan ya d’agota gaba d’aya tare da fad’in stop making and excuse da zaki dinga sawa ina taba wannan kazamin Jikin naki ….. Bata ce komai ba shima yana tsaye yana kallonta, kokarin d’aukan carpet din ta farayi …… 
Hannu yasa shima tare da kama mata duk da baya jin dad’in jikinshi , har kofar waje suka Kai ganin fadawa a wajan, gashi ko hijab balle Gyale bata saba sai dan kwalin dake kanta najallabiya, yasa yace sake carpet din kibar nan…. 
Bata musa ba, dan in tayi magana zai iya yi mata ihu, ga fadawa kuma tana hangowa ita yanzu tsoran halin Yarima take, d’auke roban ruwan tayi takai kitchen ta flto kenan shima yana shigowa falon, kallonta yayi tare da kawar da idonshi daka kanta, daga ya kalleta sai ya tuna irin karyan da tamai, Ashe duk ba sonshi take ba, dan kud’i ta aureshi dan k’aramin tsaki yaja tare da wucewa d’akin da yake matsayin nashi danya kwanta yabar ganinta domin wani irin tukukin ba’kin ciki yake cika shi tare da mamaki Wai itace take da wannan 
munanan halin ….. Gimbiya zinatu Tana farkawa ko sallah batai ba ta doka ma gimbiya Amina kira ……. 
D’auka gimbiya Amina tayi tare da fad’in zinatu laflya da asuba, badai Yarima bane ya miki wani abu?? 
Tace ko d’aya labari na kira in baki da dumi duminsa Gimbiya Amina tace bani inji kodai yarima ya Kori Matar daya aura ne?? 
Gimbiya zinatu tace kusan haka, nan taba gimbiya Amina Labarin abunda Ya faru ….. 
Gimbiya Amina tace Kai amma wannan labarin yamin dad’i wlh, toh kodai ya sameta a bude ne?? Hala ba budurwa bace an gama cinyeta a waje, shine yaci yaji kofa a bud’e shine nasan yasa lokaci d’aya ya tsaneta, amma labarin nan yasa ni nishad’i…. Su Yarima manya shidai Mata duk ba virgin…. Dariya suka saki su duka, gimbiya zinatu tace ni tunani sunyi min yawa wlh, na farko dai bamu tabbatar k0 virgin bace ko akasin haka ba, kinga bamu da tabbas and sanda yake 
kwance ita taje tayi magana dashi, har Dr yana cewa tare da taimakon ta, yasa zuciyarshi ta Fara harbawa…. Wlh am compuse ‘ Gimbiya Amina tace haba zinatu karki sama kanki tunani, ke dama miye burinki badai Yarima yafl sonki bane, koma ya saki matar daya aura ba?? Zinatu tace eh shine burina My love 
Gimbiya Amina tace toh ki cire tunanin komai, na kusa zuwa Zaria din insha Allah, zamu shirya komai, yanda zata bar gidan gaba d’aya ……. Yarima koda ya shiga d’aki kasa bacci yayi sai juyi yake, gashi kirjinshi na mishi mugun zafI, ga zazzabin har yanzu yana ji, zainab ta gama dani, ta cuceni, but zan rama abunda tamin Wanda nan gaba zata kiyayi yaudaran wasu ….. 
Farhan ya kammala karatu inda ya taso da maganan auranshi da haulat, nan hjy habiba ta tasar da bala,i akan bai isa ba, babu yanda mijinta baiyi ba akan ta fad‘a mishi dalilin rashin yarda amma ta kasa bashi amsa, dan haka yace dole sai farhan ya auri haulat …… 
Haulat tana d’an waya da Bariki kuma tana neman shawaran bariki duk da bako da yaushe bariki take d’aukan wayanta ba, wata waya da sukayi Bariki taba ma haulat shawaran ta fad’ama farhan gaskiyan lamarin abunda suke ciki ita da mum dinshi in yana Sonta may be ya aureta inko baya Sonta sai su hakura, inda bariki ta fad’ama Haulat ita gashi karyan da tama Yarima gashi tana shan wuya yana nuna mata tsana a flli, haulat ta d’auki shawaran bariki. Farhan yazo kaduna inda suka had’u da haulat kaman yanda bariki ta fad’a mata haka ta fad’ama farhan, nan da nan idonshi ya kada yayi ja, baiko tsaya sauraranta ba yayi gaba abunsa ……. Koda haulat ta kira bariki tana fad’a mata bariki tace aiki godema Allah da kika fad’a mishi Indai har son gaskiya ne zai dawo, sannan zunubin da kika aikata keda mum dinshi Kinga saiku nemi gafaran Allah tunda kince min kin daina yanzu, 
Bariki taci gaba da fad’in ni saida na shiga gaskiya ta fito gashi ina cin ubana Kai haulat da badan so ba dana bar Yarima kuka ta saki Tana fad’in ina son Yarima Sosai wanda sonshi yasa nakejure irin azabtar dani din da yakeyi ……. 
Yarima Aliyu ya warke babu laifi, amma har yanzu yana nunama Zainab tsana, yau Yarima Aliyu yaje fada domin ganawa damai martaba, bayan yaje waziri ya fita Kafin in shiga aka rufe kofa girib, wannan shine yasa ban sami shiga ba ban kuma San mai suka tattauna Koda Yarima Aliyu ya flto direct gefen bariki ya koma domin duk irin abunda yake mata lndai ran girkinta ne yana kwana a gefenta ….. 
Bariki na zaune akan gadon d’akinta saiga Yarima ya shigo wanda rabon daya shigo d’akin tun sanda aka kawota sukai rigima, sai dai su had’u a falo, Bariki kallo d’aya zaka mata kaga ta rame Sosai, kallonta yayi tun daka sama har k’asa Shima ya Lura data rame, yace ina son Kimin alfarma ko ince kiyi ma kanki ……. Da sauri tace Yarima fad’i abunda kake so zan maka lndai za kaji dad’i ….. Yace ina son ki kaini kotu ki nemi in sakeki …….. Da sauri ta kalleshi tare da hawayen dake zubar Mata a fuska ….. Kai ta Fara girgizawa tare da fad’in Yarima bazan iyayi maka wannan abun ba …… Yace why?? Tell me why?? You don’t love me, you marry me only for money, ban San in baki wuya I try to send you away from me without hurting you and you are telling me bazaki iya abunda nace ba?? Cikin kuka tace Yarima zan zauna matsayin matarka har karshen rayuwa na koda zaka dinga yankan Namanjiki na, Yarima kana ganin kaman baka min horo ba. Yarima kasan rashin kulani da bakayi tare da maidani kamar Mai maka bauta kasan yafl min komai zafl da ciwo …….. 
Yace keep quiet ….. Don’t try to show me affection, you always telling me lies,Zainab you don’t love me just go away from my life ……. Tace Yarima Wlh koda zaka kasheni bazan Barka b ….. Tsawa ya daka mata tare da fad’in why tell m ……. ltama da karfi tace because I love you ….. Da sauri ya kalleta suka had’a ido, hawaye na zuba daka idonta taci gaba da fad’in Yarima I can’t live without you ….. Yarima kayi punishing dina dako wani irin hukunci zanyi accepting amma karka kara cewa in rabu dakai, Yarima I will die without yo ……… Da sauri yasa mata hannu a baki alaman ta daina fad’in haka shima hawayen ke zuba daka idonshi 
duka kallon juna suke cikin ido suna hawaye. ………. 
Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]