[Advertisements⬇️]

BARIKI NA FITO CHAPTER 38 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

BARIKI NA FITO
CHAPTER 38
Bariki gida tayi, tana shiga ta doka ma habib kira akan yazo, kallon uwarta ta bariki tayi tace Umma ….. Amsawa tayi da fad’in ya akayi? Yau dai Kedai shar 
Bariki tayi dariya, tare da fad’in ina son miki magana Allah yasa zaki amince…. Umma din tace name fah.? 
Bariki tace akan abbana, Mai zai hana kuyi aure, inaga Zaifi muku. Umma tace aure? Dawa Rufamin asiri, barni inyi abunda ya kawo ni. Bariki tace kin fiSO ki zauna babu aure?? 
Tace a’a ina so inyi mana inna samu dai dai ni,,, Bariki tace gashi kin samu 
Dariya tayi tare da fad’in shiya ce miki zai aureni? Ko Kece kike son had’awa?? Bariki tace shiya Aiko ni inyi miki magana, kuma naga Wlh auran shiya dace daku. Tace hakane, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, saiki fad’a mishi na amince 
Bariki tace Alhmdlh, amma dan Allah Ayi bikin Kafln aurena ….. Nan dai sukai ta tattaunawa suna cikin fira habib ya fad’o kaman anjefoshi 
Bariki tace miye haka ko sallama babu 
Tsaki yayi tare da flta ya tsaya a kofar d‘aki yana gafaranku dai masu d’aki, tare da kuso Kai Bariki tace wannan ne sallama??? Ai b…. 
Yace dakata Malama, nifa ban gane miki ba, tunda Yarima ya fara soyayya dake kika koma wata iri iri, in ke kin zama ustaziya ni barni yanda nake ….. Bariki tace Allah ya shirya, ni bama wannan ba zauna kaji ….. 
Kallon tara saura kwata ya watsa ma bariki, sannan yace wlh Ina gab da in Tsiga miki rashi mutunci, ldan kina kaini jinsin da ba nawa ba ….. 
Tace Allah ya baki hakuri, zauna dan Allah Zama yayi yana bud‘e hanci wai shi a dole ranshi a bace yake Bariki tace iyayen Yarima sun Aiko har Sun tafi 
Yace haba dan Allah?? Gud‘a ya saki tare da fad’in inama inada duwawu babba dana tashi nayi rawa da duwaiya guda d’aya…. 
Bariki dariya tayi tare da fad’a ma habib yanda aka yanke bikin nan da wata biyu Habib yace Wlh bariki ban San mai yasa ba, ina sonki da Yarima,… Bariki tayi dariya tace ngd kawata, nan suka shiga tsara yanda za‘a gudanar da bikin da 
yanda za’a samo kawayen Haya duk habib yace abar komai a wajanshi …… 
Sannan maganan gyaranjiki irinsu dilka, maganin Mata bariki tace y’ar Maiduguri take So,da yar Sokoto 
Suma habib yace duk zai Kawo, cikin satin nan dan a Fara , sunyi magana Sosai inda tabi habib suka je maraban jos domin ta Fara had’a kayanta wanda take bukata wanda bata so
Koda suka je sunga haulat ita da hjj babba suna magana, ganin bariki yasa haulat ta nufi bariki Tana fad’in Indai za’aga wannan kina wajan ….. Habib yace Wlh Haulat zan miki bura uba, ban so Tabe baki Haulat tayi tana bashi hakuri, 
bariki kam wajan hjy babba ta nufa tana fad’in haka hjyta haryanzu fushin ake dani?. Hjj babba yace kyaji dashi, ni Kinga karki batamin rai yanzu da yamman nan 
Bariki tace haba hjyta kiyi hakuri mana 
Hjj babba yace Wlh bariki kina bani mamaki, da kyanki da kuruciyarki da laflyanki, amma kice zakiyi aure, keda ake rububinki haba bariki 
Bariki tace hjyta adai yi hakuri hjj babba yace ya wuce yana tabe baki Bariki tace godiya nake tare dayin gaba ta nufi d’akinta ….. Tana cikin had’a kaya haulat tazo, ganin bariki nata aikin had‘a kaya yasa haulat tace badai bikin yazo ba?? 
Bariki tace eh Wlh, Kinga wata biyu aka sa, gwara in fara had’a kaya, in kyautar dana kyautarwa inbar na Bari 
Haulat tace hakane, ni haryanzu ba’a fad’amin dan wani gari bane ko sunanshi 
Bariki tace saurin Mai kike ki jira koma Waye zaki gansa in lokaci yayi 
Haulat tace Allah ya kaimu, nan ta Fara taya bariki had‘a kaya, haulat ta d’auko wata Leda nan kayan suka zube dan ledan ya fashe, Aiko ayabar roba suka fado …… Haulat d’auka ta farayi taga har guda biyar tace bariki dama kina dasu?? Ah ba banza ba kika daina harka da maza ba, ashe kina da abunda yake d’ibe miki sha’awa 
Bariki kai ta girgiza tare da cema haulat ki d’auka duka na baki, ni ban taba amfani dashi ba, yanda aka bansu haka na ajiyesu dan banda abunda za suyi min 
Haulat ta dinga godiya tare da fad‘in amma wanda ya baki yasan kina son babban ayaba tunda harya baki…. 
Bariki tace Alh madu Yaban dan iskan tsoho, ci gaba da had‘a kayanta tayi harta  gama taba haulat kyautan kayanta da yawa. 
Haulat tana ta mata godiya duk yanda haulat taso bariki ta fad‘a mata wa zata aura amma bariki ta’ki Tadai fad’a mata dan gidan sarauta ne, abunda kawai bariki ta fad’a mata Kenan
A kwana a tashi babu wuya wajan ubangiji, bariki ta gama istabra’i, sannan iyayenta sunyi aure, mai martaba ya siya musu Gida Mai  4bedroom a u/kanawa inda anan iyayen nata na Bariki suka tare, sannan bariki tace ta bar musu gidan halak malak, domin suna Mata aiki yanda ya dace, bariki ta K’ara kyau da haske domin ana mata gyaran jiki Sosai
Yau bikin bariki da Yarima baifi kwana Goma ba, Yarima yanzu ba kullum yake zuwa wajanta ba, domin aiki sunyi mishi yawa, ga hidiman biki, gana asibiti ga fItinar zinatu, abubuwa sunyi mishi yawa Sosai ….. Yana office ya Gama duba patient yaji yana bukatar ganin Zainab dinshi dan haka ya tashi ya nufl gidansu, wanda yanzu in yazo ciki yake shiga dan akwai falon ba’ki a gidan, kiran Zainab din yayi yace ta sameshi a waje basai y’a shiga ba. 
Fita tayi inda ta sameshi a mota ta bud’e ta shiga tare da gaidashi Mai makon ya amsa sai yace Kai my princess Kinga yanda kike K’ara kyau kuwa?? Gskya ana gyaramin ke dakyau, 
Murmushi tayi cikinjin kunya sannan tace Kai Yarima wani kyau nake karawa?? Tayi maganan a shagwabance 
Yace Zona nuna miki tare da janyota jikinshi, wani irin kamshi ne ya daki hancinshi Wanda tunda ta shigo yakeji, amma daya janyota jikinshi sai yaji kamshin ya fito Sosai, gaba daya yaji jikinshi ya fara weak domin kamshin turaren yasa jikinshi ya fara yin sanyl’ ….. ltama ta gefenta wani iri takeji domin maganin da ake bata ya tsumata Tana matukar bukatar namiji amma babu yanda ta iya dole sai mijinta Bayan tayi aure, gashi yanzu Yarima yana son tada mata bala’i…. Yarima Aliyu hura mata I’ska yayi a fuska da sauri ta d’ago suka had‘a ido peck yakai mata a goshi tare da furta I love you my princess Da sauri ta lumshe ido Ganin haka yasa Yarima ya kura mata ido yana kallonta tare dajin wani irin mugun sonta n K’ara shiganshi…. Jin shuru yasa ta bud’e ido a hankali idonta ya sauka cikin kwayar idonshi da yake kallon nata idon ….. Dukansu wani irin yanayi mai wuyan misaltuwa suka shiga ……. Karan wayar Yarima yasa ya saketa ta tashi da sauri daka jikin nashi ta koma ta zauna dakyau ….. Daukan wayan yayi ya duba, ganin mai kiran yasa bai d‘auka ba, zinatu 
Bariki kam gaba d’aya ta birkice, dan  dan tabata da Yarima yayi har tana jin zuban ruwa a cikin pant dinta, lallai ya kamata Yarima ya rage zuwa, ko kuma ya daina tabata…. Domin Indai hakan zaici gaba da faruwa zata sha wuya, ido ta lumshe tasan ba komai yake sata yawan sha’awa ba sai maganin da take sha, wacce y‘ar Sokoto take bata ….. Yarima ne ya Katse Mata tunani da fad‘in, my princess zan gudu, bata sim yayi guda d’aya tare da cewa ta cire nata, baya son ta kara amfani dashi ….. 
Amsa tayi, tace toh dama tun tuni take da burin canza layi, amma tana tsoran Kar Yarima yace Mai yasa, yanzu tunda ya kawo mata, hankali kwance, sannan ya bata check na 3mil yace a K‘ara gyaranjiki domin naga suna gyaramin ke dakyau …… 
Tace Yarima kafa ban kud’i cikin kwanakin nan, kaban a kalla wajan 7mil kace in siya kaya akwati, kuma gashi kace May be gidanku su Kawo nasu gobe kojibi, kai kamin gashi gidanku zasu kawo, ga kud‘i kuma kana karamin, gskya abun yayi yawa, ka barshi ….. 
Bata fuska yayi tare da fad’in in kin ciro kud’in ki zubar a bola tare da ajiye mata check din
Ganin yanda ya bata fuska, yasa tace Yarima kayi hakuri, wlh ba haka bane, naga hidimar tayi yawa ne Sosai, Kaga y ……
Yace enough, komai na miki, kin can Canta inyi miki shi, and karki manta am your husbar to be, waya kamata inyi ma Abu Inba keba?? In my life ban taba kyauta ko wani abuba a nuna ba’a soba sai ke.. 
Da sauri tace kayi hakuri plz na tuba, ngd Allah ya saka da alkhairi…. 
Jin ta fad’i haka yasa yaji dad’i ….. Ba komai yasa Yarima ya bata wannan kud’in ba, sai 
sanin da yayi ba masu hali bane su, and y’an uwanshi zasu Kawo akwati, ance ana bada kud’i, sai yasa ya bata wannan kud’in dan iyayenta su bada tukwici… Ajiyan zuciya yayi tare da fad‘in zan taf’l sai munyi waya, 
Tace OK Yace kin dai ki zuwa kiga gidanki koh? Tace Yarima saurin Mai kakeyi?? Ka Bari har a kaini mana 
Murmushi yayi domin kin amincewanta yasa ya kara yarda damai tarbiya da kuma kamun kai zai aura, sabanin matan yanzu da suka lalace suke ganin haka shine wayewa, tab kunji Yarima shi’a dole zai aura ustaziya Hmm
Sallama ya Mata sannan ya wuce …… 
Bariki gida ta shiga jiki a sanyaye lallai Yarima yana matukar sonta da yawa, hawaye ne ya gangaro daga idonta, tare da tausayin kanta yanda zai dauketa in yasan ko ita wacece …… Anata shirin biki musamman ta gefen ango, domin dai ita amarya rufa rufa take ma auran ba kowa bane ya sani, sai dai zargi da wasu sukeyi …… Ranan da za’a kawo akwati saida bariki da habib sukai hayan mata guda biyar, An kawo akwati guda ishirin da hud’u, dozen biyu kenan, kaya ne makil na Kece raini masu tsadan gaske ….. Ganin yawan kayan yasa umman bariki taga 1mil yayi kad‘an dan haka ta sami bariki dake boye cikin wani d’aki, tace ya kamata a K‘ara kud’in nan Kinga uban kayan kuwa? Bariki kara 1mil tayi ya zama 2mil, nan aka basu kud’in tukwici, tare da abun ciye ciye da aka tanadar musu, bayan sun fito sis din Yarima Fatima tace Kai ance yarinyar talakawa ne amma har da bata 2mil, Aini ban d’auka zasu bada koda dubu d‘ari ba, daria sukayi sannan aka canza firan, 
Bayan sun tafi bariki ta fito tana kallon kayan, itama Abun ya bata mamaki ganin kaya masu uban yawa da tsadan gaske, yanzu ga akwati ishirin da hudu, gashi kudin da Yarin ya bata itama ta siya guda sha biyu, duka talatin da shida kenan ….. 
Ummanta ta bariki tace Kai gskya ki gode Allah y’ar nan, Yaron nan yana sonki Sosai, ji uban kaya sannan kayan d‘aki yace baya bukatar komai, kai Kinji dad’i wlh 
Bariki murmushi kawai tayi jiki a sanyaye, domin sai yanzu ta Fara jin tsoran abunda take kullawa na auren bariki, da tana ganin abun kaman wasa, amma tunda hartaga akwati  an kawo ta tabbatar Abun dagaske ne, d‘aki tayi ta Fara risgan kuka tare da fargaban abunda zai biyo baya ….. Hmmm Allah ya kyauta dai zan iya cewa 
Biki ya kan Kama amma amarya bata cikin nutsuwa kullum tana cikin fargaba, harta rame saboda damuwa, kullum bata da wani aiki sai kuka tare da K’ara tsanar rayuwar bariki …… Tana cikin wannan kukan Yarima ya kirata, da sauri ta seta kanta dan Kar ya gane sannan ta d’auka… 
Gaidashi tayi Amsawa yayi tare da fad’in ya naji muryanki haka?? Da sauri tace mura nakeyi Yarima 
Yace toh fah, Allah ya sawake zan Aiko miki da magani. Tace nasha tun dazu Yace 0K, toh ya shirye shirye? Tace Alhamdullilah Yace za‘a Aiko miki da kayan da zaki saka a dinner sannan masu makeup za suzo suyi miki ranan, lil sis taban sa’ko in fad‘a miki Bariki tace ok Allah ya kaimu Ya amsa da Ameen, sun d’an taba fira Kafin sukai sallama ….. 
Yana ajiye wayar gimbiya zinatu ta shigo, Tana fad‘in yanzu Yarima saboda cin fuska a ciki gidan nawa kake waya da wacce zaka aura??? Kuka ta fashe dashi tare da fad‘in haba Yarima Wlh kana cimin fuska da yawa maina maka haka da kake Yimin wannan abun?? 
Ganin yanda take kuka sai yaji ta bashi tausayi, rarrashinta ya farayi ….. 
Gimbiya zinatu ji take kaman ta tureshi Dan tsabagen kishi, Allah ya sani da badan gimbiya Amina tana kokarin hanata wani Abun ba da Wlh babu abunda zai hana tayi ma Yarima mugun tujara, amma Gimbiya Amina tace tayi hakuri ta Bari Ayi auran zata nema Mata mafita, yarda da gimbiya Amina da tayi shine yasa hartake dan jurewa, amma ji take kaman zata mutu dan kishin Yarima take Sosai, bata son ganin ko wace mace kusa dashi
Toh biki ya rage saura kwana biyu, inda a yau za’a gudanarda dinner, bariki da habib sunyi hayan kawaye Wanda sune kawayen amarya, cikin kawayen harda haulat da khairat, zuwan haulat gidan iyayen bariki yasa ta gane yanda bariki ta shirya auranta, ta gano tay amfani da iyayen bariki, haulat ta kalli bariki tace gskya kinyi dabara, nima Ina tunanin haka zamma farhan, in same iyayen bariki 
Bariki ganin Haulat ta gano komai, yasa tace inko za kiji shawarata karki Fara yin aure da iyayen bariki, gwara ki koma Gida wajan danginki Haulat tace Hmmm kedai kawai Ayi sha’ani, 
Anyi ma amarya makeup na Kece raini,tayi mugun bala’in yin kyau, gaba d’aya makeup din da aka mata yasa ta canza, ta kara mugun kyau dama yaya balle an kara da wanka, an shiryata cikin wani tsaddan material Mai Kama da less anyi mishi dinkin doguwar riga, k’asan kuma anyishi da fad’i kaman weeding gown, an saka mata head maroon kayanta kuma golden, ba karamin kyau tayi ba, kawayenta kuma sunsa kaya red head golden, ba karamin kyau bariki tayi ba, da kawayenta, 7 dai dai aka turo motoci dan d‘aukan amarya da kawayenta zuwa wajan dinner da za‘ayi a cikin garin kaduna, duk y’an uwan ango suna kaduna, an d’auki amarya an nufi hall da ita, inda motarsu na zuwa na ango yazo, dan har Yarima ya fito ya nufl motar da Zainab ke ciki, Yarima daya ganta ido ya kara bud’ewa gani irin kyan data K’ara kaman ba ita ba, dama yasan tana da kyau gashi anyi mata makeup, lokaci d’aya kuma sai yaji yana kishin ta shiga Ayi ta kallonta, ya dad’e a motar yana nazari akan baiso ta shiga ….. Itama ta gefen amarya fargaba take, karta shiga taga Wanda ta sani, asiri ya tonu ….. Jin Yarima shuru yasa usman yazo yana buga glass din motar 
Bud’ewa Yarima yayi tare da fad’in Usman gskya aje abama mutane hakuri, an fasa wanna dinner din, suci abinci kawai su wuce 
Usman yace Yarima. Kasan Mai kake fad’a kuwa?? Plz Yarima ku fito mu shiga Yarima yace kasan inna fad’a magana bana canzawa koh?? Usman shuru yayi yana nazari can yace dan Allah Yarima kayi hakuri ka duba girman Allah karka bamu kunya …… 
Yarima ya dakatar dashi da fad’in am telling you kayi abunda nace, wannan umarni ne…. Karan wayanshi yasa ya d’auka ganin lil sis 
Yana d’auka tace Bros ku shigo mana kowa najira, dan Allah kuyi sauri 
Yace sis am sorry bazan zo ba, kuba mutane hakuri ….. 
Tace what? Tare da tashi ta fito waje dan taji dakyau, hango usman tayi da Yarima a tsaye da sauri ta nufesu, tana fad’in bros miye haka plz kuzo ku shiga…. Zaiyi magana tace plz koso kake ace akwai matsala ne?? Yace let people say what ever, nidai bazan shiga wannan wajan ba. Hafsat tace bros akan wani dalili? 
Yace ban son ayita Kalle min Mata, inada kishin iyali na 
Hafsat hannu ta d’aura a Kai, alaman takaici, danta d’auka wani abune akayi mishi da yas yace bazai shiga ba, motar da bariki take Hafsat ta nufa, sai gata ta fito 
Ganin amarya a waje yasa Yarima ya fara yima Hafsat fad’an Mai yasa zata fito mishi da mata…. Hafsat tace bros nifa bani na fito da itaba Kallon bariki yayi yace Oya muje in kaiki gida 
Tace Yarima plz muje mu shiga, zaiyi magana tace dan Allah, karka sa mutane suyi zargin wani abu tana maganan tare da kokarin San zubar da kwalla ….. 
Ganin haka yasa yayi dan tsaki tare da fad’in karki Fara cewa zakiyi min kuka a nan, dan naga kina da Arhan hawaye, babu yanda Yarima ya iya dole ya shiga shida abokanan shi d amarya da kawayenta, cikin hall din yayi mugun tsaruwa, wajan zaman amarya da ango daban su biyu, y’anjarida da masu hoto sai d’auka suke, kowa yana fad’in amarya da ang‘ sun dace dinner din ya had’a manyan mutane ciki harda Mai martaba, Yarima bai San zaizo ba saida Ya ganshi shida abokanan shi, harda Mai girma governor da wasu masu mukami gwamnati sun halarta, anyi watsi da naira kaman baza‘a mutu ba, an yanka cake daganan akace amarya da ango suzo suyi rawa, nan suka fara rawa duk da bariki ba a sake take ba, dan tana jin tsoran ko akwai wanda ya Santa a wajan, nan aka fito ana watsa musu naira mum din Yarima tayi musu liki Sosai, a cikin masu likin idon bariki ya sauka akan Alh madu dam gabanta ya fad’i, musamman irin murmushin da taga yana sakarmata,gaba d’aya jikinta taji ya saki babu kwari, Yarima kaman ya Lura da ita gashi kuma mutane sunyi yaw: k0 ince maza dan haka Yarima yaja hannun Zainab suka koma suka zauna, Anci ansha kowa ya watse, Yarima yakai bariki gida da jikinta yake a muce ganin Alh madu a wajan dinner, yanda ta gode Allah ta canza layi ma balle ya mata barazana, toh inya fad’a ma Yarima fah?? Nan taji gabanta ya fara fad’i 
Bariki harta Washe gari tana cikin zullumi Kar asirinta ya tonu, haulat Dai da khairat sunyl Mata kara domin a gidan suka kwana, dasu kuma ake komai, bariki na kwance haulat tace wai lafiya kuwa naga kinyi shuru?? 
Bariki tace kalau nake Haulat tace dan bani wayarki in bud’e hotspots banda data gashi Ina son tura Abu. Password din wayar bariki ta cire sannan ta mi‘ka ma haulat wayan ….. Toh rana dai bata Karya inji masu iya magana yau juma’a aka d’aura auren Zainab musa d angonta Yarima Aliyu, akan sadaki naira dubu hamsin inda dubban jama’a suka shaida ….. Bariki tunda taji an d’aura take ta godema Allah, domin anyi auranta cikin nasara ba tare da Yarima yasan gaskiya ba, a hankali tace yau zan fad’a maka koni wacece Yarima Indai aka kawo ni gidanka, ….. Karfe hud’u dai dai aka zo aka d’auki amarya inda aka tafi da ita Zaria a can zata zauna Kafin a dawo da ita kaduna, gefen Yarima Nan aka kaita inda aka gyarashi harta wanda suka kawo amarya bariki hayansu tayi, an karrama amarya da danginta wajan su abinci da duk abunda suke bukata, nan sukace zasu wuce tunda sun kawota, anyi musu shatara na arziki Kafm nan suka wuce …… 
Wajan karfe 9 Yarima ya shigo d’akin amarya ba tare da Aboki ko d’aya ba, dan yace kallon da suka mata wajan dinner ya isa haka, bariki na zaune akan gado Yarima ya shigo tunda ya shigo gabanta ke faman fad’i, inda take ya nufaeta tare da cire mata gyalen dake kanta yace Alhmdlh tsarki ya tabbata ga Allah daya nuna min wannan ranan,janyota yayi jikinshi yayi mata wani irin runguma, har tana jiyo ajiyan zuciyarshi, lokaci d’aya ya saketa tare da d’agota ya sauketa k’asa yace my princess muje muyi alwala muyi ma Allah godiya ….. Gabanta taji yana fad’i yaka mata Yarima yasan gaskiya Kafin wani abu ya shiga tsakaninSu wayarshi dake ajiyu yayi kara d’auka yayi yaga bakuwar number kaman Karya d’aga, sai kuma ya d’auka, ban san mai aka fad’a mishi ba naga ya kashe da sauri tare da fara danna wayar duk wannan abunda ake suna tsaye shida bariki suna kallon juna amma shi idonshi nakar wayan… Lokaci d’aya hawaye ya fara zuba a idonshi tare da fad’in today is our wedding night, the day dat I have waiting for since d day dat I have meet u, but you destroy my life, you have cheated me ….. Cikin tashin hankali tace Yarima maiya fa… Yace keep quiet tare da ri’ke kirjinshi alaman yana mishi ciwo yana kokarin yin magana ya fara tari Sosai lokaci d’aya yayi k’asa …… 
Hmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]