[Advertisements⬇️]

BARIKI NA FITO CHAPTER 31 - Bankinhausanovels
Thu. Mar 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

BARIKI NA FITO 
CHAPTER 31
Yarima cire hannunshi daka fuskanta yayi idonshi ya sauka akan yaron, ganin irin kallon da yake Mai yasa yaron Ya daburce ….. 
Tare da fad’in sir aikoni akayi na fad’a mata shine tace zata taga Waye, shine yace ince Bariki ta Katse shi da fad’in ya isa haka,q kallon Yarima tayi wanda fuskanshi ke d’aure alaman bacin rai tace Yarima na yazo yace in bashi number dina shine ….. Labarin abunda ya faru ta bashi…. Yarima Aliyu baiyi magana ba sai d’aukan wayarshi da yayi ya danyi danne danne sannan yasa a kunne yana fad’in ina restaurant dinka kazo yanzu coz ina sauri, yana fad’in haka ya ajiye wayar…. Ganin haka mutumin daya kawo abincin ya zube a k’asa ya fara ro’kan yarima danya tabbata Mai wajan ya kira, yace plz sir forgive me Wlh Aiko ni akayi saida nace bazan zoba matar aurece, amma yace dole sai Naje ko yasa Mai wajan ya koreni, sir In baka 
yarda ba kazo muje ka ganshi…. Tashi Yarima Aliyu yayi yace muje ….. 
Da sauri ya tashi ya shiga gaba amma suna zuwa wajan da yace mutumin na ciki suka ga wayam, babu kowa. Yarima Aliyu ya kalli mutumin yace yana Ina? 
Mutumin yace sir Wlh a nan yake sai dai in fita yayi, hakuri yaita bama Yarima…. Bariki tace Yarima kayi hakuri kazo muje ….. 
Jan hannun bariki yayi sukai waje Bayan ya biya kud’in tare da cema habib dake zaune ta waje muje ….. 
Bayan sun shiga mota Yarima tuki yake cikin bacin rai domin shi gaba d’aya laifln Zainab din ya gani damme zata tsaya Tana magana dashi har tace tana son ganin mutumin yanzu inda ban dawo ba zuwa za tayi ….. Wani irin gudu ya saki…. ’ 
Habib dake baya yace cikin ranshi Kar yaje ya kasheni ina cin gajiyar kuruciyata da sauri yace Yarima zan sauka a kawo zan amsa sa’ko… 
Yarima yace ok suna zuwa kawo Yarima ya faka habib ya fita tare da fad’in a gayas haka kawai aje a kashe ni ban shirya ba …… 
Yarima bai tsaya ba sai marabanjos, da yake yau sati mutane nata kaiwa da komawa cikin shigar banza, Yarima shidai ya rasa mai yasa baya son wannan anguwar shi inda so samu ne baya son tana zuwa kwata kwata domin anguwar bata Mai ba, ga motoci dake ta shigowa waima damma ba tanan bane Layin da bariki take ba …… 
Bariki kallon Yarima tayi ta fuskanci babu alaman wasa ….. Tace haba Yarima kofa abincin baka ciba, aiya kam …… 
Yace ya isa Zainab plz, ban son dogon magana, sauka kije zan tafi ….. 
Kallon mamaki take mishi ganin yanda yake mata magana duk da hakan ya bata tsoro amma saita dake tace haba Yarima, wannan fushin fah, karka manta kazo tayani murna ne 
bai kamata ka sani cikin damuwa ba 
Shuru yayi ba tare da yace Mata komai ba, a tunaninta ya sauko ne, dan haka tace yanzu Mai zaka ci in n ….. 
Ya dakatar da ita da fad’in Zainab plz leave my car…. Tace Yarima Mai ….. Yace I said leave my car plz 
Hawaye ne ya fara zubo mata, garin yayi duhu, baya ganin hawayen da takeyijin Tana sheshekar kuka yasa ya gane kuka takeyi ….. Bud’e motar yayi ya flta domin bazai iya sauraranta ba Tana kuka ba uwa uba kuma abunda tayi ya bata mishi rai, a duniya babu abunda ya tsana kaman yaga ana taba abunda yake so, wanda yake ganin kaman Zainab din ta raina shine tunda hartayi magana da wani ya tabbata inda bai dawo ba zata iya sauraranshi tunda harta yarda Tana son ganinshi din, wata zuciyar tace amma tayi maka 
bayani…. D’an tsaki ‘yaja tare da nufa masallacin dake kusa da wajan dan yin sallah isha’i
Bariki kam tana cikin motartana kuka, wanda ba kukan komai take ba saina tausayin kanta, musamman abunda taga ya faru yau, jibi yanda Yarima yayi fushi har yake nuna kishinshi a fili, tabbas ldan Yarima yasan wacece ni ban tunanin zai ragamin ko kad’an, lokaci d’aya taji kanta ya fara mata ciwo, lallai Ina son Yarima bana tunanin zan iya rayuwa ba tare dashi ba, sonshi yasa na daina aikata zina sonshi yasa na daina aikata abunda Nayi niya dan inga na kuntata ma iyayena, wani sabon kuka ta kuma saki ….. 
Yarima ne ya shigo cikin motar jin Tana kuka Sosai yasa yaji jikinshi yayi sanyi, duk da ranshi har yanzu a bace yake, domin Yarima namiji ne mai mugun kishi ya wuce duk yanda Mai karatu yake zato ….. Janyota yayi jikinshi tare da fad’in plz stop it, bana sonjin kukanki, Zainab Ina fushi dake inda kin San yanda nake sonki da kuma kishin ki da ldan wani namiji yazo inda kike zaki nuna mishi ke kurma ce, yanda ma bazaiji sautin muryanki ba, inda 
banzo a time ba only god knows what will happen …… 
Bariki cikin kuka tace Yarima Wlh abunda na fad’a maka gaskiya ne, nace mishi ya fad’a ma mutumin inason ganinshi tunda nace ni matar aurece yace duk da haka a bashi number 
dina, nayi hakan ne in kazo muje tare dakai amma badan wani ab …….. 
Yarima Aliyu yace ya isa haka mubar maganan yanzu kije gida ki huta, Nasan yau Kin gaji Sosai…. 
Cikin sanyin murya tace toh amma Yarima baka ci abinci ba?? Yace don’t worry, zanci in naje gida…. 
Kai ta d’aga alaman Toh, tare da fad’in Yarima hope u trust what I said? Nd ina fatan ka hakura? Yace Zainab plz nace mubar maganan go and rest, muje in raka ki bud’e kofar motar yayi…. 
Ganin ya fita itama ta bud’e kofar motar ta fito har kofar gidan da tace mishi na y’an uwanta ne ya rakata saida ya Bari ta shiga ciki sannan ya dawo ya shiga motarshi yayi gaba cikin gudu 
Bariki kam tana ganin ya wuce ya fito danta nufl inda take, taflya take tana tunani domin ita bata yarda Yarima ya hakura ba, dan inda ya hakura da baiyi reaction haka ba, lallai Yarima yana da kishi, duk ranan da yasan wacece ni ban tunanin zai zauna dani a matsayin matarshi koda ya aureni ….. Wata zuciyar tace mata kin manta gidan sarauta basa saki, sai an Kama Ka da lam biyu? Bata san lokacin da tayi murmushi ba wannan tunanin da tayi shi yasa taji karfln giwa tare da kara d’aura dammaran rufe sirrinta har sai ta auri Yarima dan tana sonshi kuma tasan indai ya sani Bayan aure bazai saketa ba tunda ba’a saki …… Yarima Aliyu na tabbata kai mutumin kirki ne, soyayarka a gareni gaskiya ce kaman yanda nima nake maka, Idan na tuna abunda ya faru dani Ina takaici, tabbas Yarima ni Nasan baka dace dani ba, kafi karflna domin irin rayuwar mu ba d’aya bace, duk shirin da nakeyi na auranka lnayi ne kawai amma bawai dason raina ba, ina ganin kaman zan cuceka ne Sonka yasa na zama mai son kaina, ban taba tunanin duk duniya akwai wanda zan boyema halin da nake ciki ba tunda har iyayena sun sani kuma sun kasa yin komai akai, duk da ransu yana baci amma babu yanda za suyi domin burina in rama abunda sukai min na rashin d’aukan kaddaran daya fad’amin …… Jin ana mata magana yasa ta waiga 
Driver din alh madu ne yake mata magana, yace sannu hjy tun dazu nazo ai inata jiranki, 
mai gida yace ya kira baki d’aga waya ba, gashi hjy babba wayanshi shima baya d’aga wa. Bariki tace Indai wajan hjy babba kazo yana filin rawa Nasan zaka iya dubashi a can , Tana fad’in haka tayi gaba …… 
Binta driver din yayi yana fad’in a’ah Wajanki nazo oga yace inzo in d’auko ki shi yasa 
Bariki tace kaje kace Mai nace bazan zoba, and kuma daka rana irin tayau karya kara kirana domin ni yanzu Allah ya shiryar dani na daina wannan banzan rayuwar aure zanyi 
Driver din alh madu yace Kai Alhmdlh Wlh naji dad’i Sosai, dama Wlh tunda na ganki naji Ina takaicin wannan rayuwar da kikeyi gaki yarinya karama amma babu daman inyi magana karki fad’ama oga ya koreni, wlh Ina takaicin wannan abunda yakeyi Wlh sai muje garin abuja muyi wata biyu uku amma baije yaga iyalanshi ba, sai dai wancan macen tazo wancan tazo ta sameshi a guest house dinshi, ni Kece ma naga yana bi kina Mai wulakanci, gashi mutum ya girma Mai makon yabi Allah yaita istigfari amma shi ina kullum hanyar bata ita yake bi 
Bariki tace Allah dai ya shirya, nidai ka fad’a mishi sa’ko na, Tana fad’in haka tayi gaba 
Driver din alh madu yace Kai Alhmdlh Wlh naji dad’i Sosai, yanzu kam zani in fad’ama wannan tsohon banzan sa’kon yarinyar nan 
,,,,,,,,,,
Yarima Aliyu saboda gudun da yayi kaman zai tashi sama 20min ne ya kaishi Zaria, Allah ya 
taimakeshi ya sauka lafiya, domin gudun fitan rai yayi yana tuki yana tuna abunda wanna yaron yazo yana cewa ‘he said that you can come he is waiting for you’ Yarima Aliyu Wanda yaga Abun a matsayin kaman Zainab ta raina shine dan taga yana Sonta da yawa tsaki yaja tareda shiga gefenshi inda yaga gimbiya zinatu a falo tana zaune tana danna waya tasha wata doguwar riga y’ar kanti yayi mata kyau Sosai, kauda idonshi yayi daka kanta kaman bai ganta ba… Tashi tayi da sauri ta nufeshi tare da rungume shi tana fad‘in Yarima inata kiranka baka d’auka ba, tun dazu nake cikin damuwa tare da fargaban Allah yasa lfyDanjanyeta yayi daka jikinshi tare da fad’in plz allow me to go and rest ,gaba yayi abunshi Gimbiya zinatu binshi tayi da ido alaman Mai yake nufi, kodai ya gano gaskiyan al’amarin ne? Kai a’a bazai taba ganewa ba domin jinin daya gani zai sa ya tabbatar da ita budurwace, kafada ta d’aga alaman shiya sani Nasan wani wajan ne aka bata mishi rai, chatting dinta taci gaba dayi ita da gimbiya Amina. 
Yarima kam yana shiga bedroom dinshi wanka yayi tare dasa jallabiya, ya fito yaga gimbiya nata danne danne dan tsaki yaja mara sauti yakan yi mamaki Idan yaga mutum yana bama waya muhimmanci fiye da komai, danya Lura da gimbiya zinatu Tana son bama waya lokacinta Sosai, dinning ya nufa dan yayi dinner…. 
Gimbiya ganin ya zauna akan dinning yasa ta tashi ta danna wani abu saiga kuyangi nan sun shigo, sun San abunda za suyi dan haka shi suka farayi zuba ma Yarima abinci, Bayan sun gama suka barwajan, Yarima Fara ci yayi amma bayajin dad’in abincin dan ranshi a bace yake, yau princess dinshi ta bata mishi rai Sosai, gimbiya zinatu zama tayi itama akan dinning din tare da kura mishi ido tana kallon yanda yake cin abinci kaman baya son ci …… D’ago kai yayi yaga tana kallonshi a hankali yace stop starring at me like that, Gimbiya zinatu tace in ban kalleka ba wa zan kalla? 
Yarima shuru yayi ba tare daya kuma cewa komai ba, ya rasa mai yasa yake tantama akanta Sosai, abunda yasa har yanzu yake ganin kaman akwai wani abu tare da gimbiya zinatu shine lokacin da yayi sex da ita bai San sanda ya fara ba,hakan yana nuna mishi baya cikin hayyacinshi, yaga Abun kaman mafarki har yake ce mata ita ba virgin bace, abun daya d’aure mishi kai kuma shine yanda ya farka yaga jini ajikinta alaman she is virgin, wannan Abun yana d’aure ma Yarima kai, ido ya d’an lumshe lallai gimbiya she is a virgin Inba virgin bace taya zanga blood? Bai kamata Ina tantama akanta ba, I have to believe in what I see, tunda if she is not a virgin bazanga blood ba, duk da Nasan bako wace mace bace take zubar da jinin budurci ba kuma budurwa ce, but da yake Allah yana son nuna min sai gashi ita gimbiya Tana d’aya daka cikin masu zubar dajini a daren farkon su, sabanin wasu matan dasu baya zuban musu kuma suma virgin ne, ba lallai bane Idanjini bai zuba ba ace mace ba budurwa bace, wata baya zuba wata yana zuba, shi budurci ba daka jini yake ba, yanda kaji cikin mace Idan ka shiga zaka jishi a matse tun daga farko har ciki, wannan shine budurwa, wacce kuma ba budurwa ba koda tayi matsi ana ganewa, domin wajan ne zai matse cikin kuma yana shiga yaji kaman ya fad’a rami, dan haka y’an mata ku daina rud’an kanku kuce AI akwai maganin dana miji bazai gane cewa ni budurwa bace wannan maganan karya ne wlh, domin budurci budurcine in kika rasa shi har abada kin rasa shi bazai taba 
dawowa ba komai zaki ma wajan. domin abun daga Allah ne, kuma budurci shine kimarki 
wajan mijinki daka yaji ya sameki kofa a bud‘e an burmaki har abada bazai dinga ganin kimarki ba sai dai in a bisa tsautsayi kika rasa budurcinki tayiwu yaji tausayinki ya d‘aga miki kafa, shima ba lallai ba domin in bakiyi wasa ba wata rana saiya goranta miki 
Indai namiji ne, shi yasa yana da kyau duk wani waje da zaki Indai kin San wajan ba tsaro ki guji wajan Kar ki jaza ma kanki bala’i ……. Yarima tashi yayi dan baya jin dad’in abincin d’akinshi ya nufa ya kwanta,jin karan 
wayanshi yasa ya d’auka yaga zainab ce kashe wayan yayi gaba d‘aya dan baya bukatar magana da ita a halin yanzu ……… 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]