[Advertisements⬇️]

BARIKI NA FITO CHAPTER 30 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

BARIKI NA FITO 
CHAPTER 30
Kallonshi tayi cikin tsoro tare da fad’in Yarima plz ka barshi Kawu nane yake kira, so yake Inba ma Abba, wayan Abba ne ya sami matsala in an kira yanaji amma ba’a jinshi, inna d’auka nace bana gida zai iya zuwa har gidan ya sami Abba da Umma yayi musu fad’a akan Mai yasa zasu dinga bari Ina flta da yamma, kuma yanzu inna shiga Gida Umma bazata Bari 
in kuma fita ba, dan yanzu tana tunanin ina d’akin makwabciyan mune ….. 
Yarima Aliyu ajiyan zuciya ya sauke, lallai Zainab gidansu gidan tarbiya ne, sabanin yanzu da iyaye suke sakin y’ay’ansu suna abunda suka ga dama, har ma wasu zaku ga kaman su sukejuya nasu iyayen sai abunda sukace iyayen nasu keyi ….. Amma a flli sai yace Mata my princess na fad’a miki tun Farko ai ki bani dama inga Abba kinki, yanzu Idan yazo ya 
gammu ya kike so inyi??? 
Cikin sanyin murya tace bazanji dad’i ba, domin na tabbata Abba zaiyi fushi Sosai, amma 
Yarima tunda harna yarda yau kazo gidanmu hakan ya kamata ya nuna cewa Ina sonka
Wani irin murmushi Yarima ya saki cikin jin dad’i tare da furta Kalman Alhamdullilah cikin ranshi, domin wannan maganan da Zainab tayi mishi yasa shi cikin farin ciki Sosai ….. 
Kallonta yayi cikin ido tare da fad’in my princess kin tabbata kina son inga Abba??? 
Ganin bazata iyajuran kallon cikin idonshi ba yasa ta kawardakai gefe tare da fad’in eh Ina so ka ganshi, domin hakan ya kamata Ayi tun Farko 
Murmushi yayi tare da fad’in zan iya ganinshi yau? 
Tace eh amma sai dai ka tura wani yaje ya maka sallama dashi duk da ban tunanin ya dawo 
amma kuma hala ya dawo din dan lokacin dawowarsa yayi ….. 
Dariya Yarima yayi tare da fad’in am joking bazan iya zuwa ni d’aya ba, but zuwa jibi Zanlo da Usman da wasu friends dina sai mu ganshi mu nemi izinin zuwa zance Kafin manya su 
shiga Murmushi tayi tare da fad’in Allah ya taimaka Ya amsa da Ameen, tare da fad’in where is my promise? 
Kallonshi tayi taga shima ita yake kallo da sauri ta kawar da kanta gefe tare da sakin 
murmushi sannan tace wani promise?? Yace abunda ya faru wajan Walima. 
Dariya tayi wanda ya kara mata kyau sannan tace Yarima ban samu daman d’aukan komai ba saboda jama’a Wlh kunya duk ta hanani gashi mune masu saukan ….. Amma munyi hoto a gida da kawaye na Wanda mukai saukan tare 
Yace OK Nasan duk kim yin kyau Tace a’a tare da danna wayarta tace na tura maka ta whatsapp 
Murmushi yayi ya d’auko wayanshi ya fara dannawa, yace my princess duka sun sa nikaf Kema Aida kinsa ko so kike ayi ta kallemin ke ‘ 
Dariya tayi tace a cikin gida nefa babu Mai kallo na sai Kai ta karasa maganan tare da rufe Fuska Murmushi yayi tare da fad’in my princess yunwa nakeji banci komai ba tunda safe ….. Da sauri ta kalleshi tare da fad’in mai zakaci in kawo ma? Yarima taya zaka zauna haryanzu 
bakaci komai ba ulcer zai kamaka plz mai zaka ci?? 
Murmushi yayi cikinjin dad’i domin ganin yanda ta nuna kulawanta akanshi, ya tabbatar 
mishi da cewa tana sonshi Sosai …… 
Katse mishi tunani tayi da fad’in Yarima ko in kawo maka tea kasha Kafin in dafa maka 
wani abu?? Yace a’ah ki barshi zanje Inci abinci yanzu Shuru tayi tana d’an nazari can tace ko in kira habib yaje ya kawo ma wani abu kaci? 
Hannunta ya kama tare da ri’ke mata su duka biyun yace my princess karki damu zanje 
wani waje Inci, ko zaki raka ni? 
Da sauri tace eh muje Kafin Abba yasa Umma ta kirani a d’akin da take tunanin ina ciki inya dawo Karyasa a kirani yaga bana nan koda yake Nasan ma ya dawo ganin habib Nasan bazai damu daya ganni ba. 
Murmushi yayi yace No p Bari inje alone banso Ayi miki fad’a my princess 
Tace Yarima plz muje kaci abinci habib na nan bari in kirashi sai muje tare zance ma Abba zani maraban jos In kwana bazai hana ba sai muje kaci 
Yarima yace ok my princess 
Fita tayi ta shiga cikin gidan Jim kad’an sai gata ita da habib da abbanta na Bariki Sun fito daka gani ya flto raka habib dinne a yanda Yarima ya fahimta kenan har bakin titi ya rakasu sannan ya dawo ya shiga gidan yarima yana kallonshi cikin ranshi yace wannan daka gani Dattijo ne yana yin kamalan shi ya nuna ma Yarima hakanan kai ana abu aduniya shi yasa akace sometimes abunda ka gani bashi bane gaskiya …… Yarima tada motar yayi shima ya nufa titi bai gansu ba kiran Zainab dinne yasa ya dauki 
waya tare da fad’in my princess where are you? Tace muna gaba wajan NDA Abba saida muka shiga mota ya koma shine muka sauka a nda 
Yarima yace ok ga ninan zuwa, Yarima juyawa yayi ya nufi nda din ya d’aukesu ta shiga gaba habib kuma baya, Yarima ya kalleta yace Ina zaki kaini Inci abinci?? 
Ido ta d’an zaro tare da fad’in ni Ina na sani tunda ba zuwa nake ba 
Habib dake Bayan motar yanajinsu cikin ranshi yace bariki ko y’ar iska ke inane baki Sani ba cikin garin kaduna yanda kuka san map din garin ne 3 kanta amma yanzu tana wani nuna ita ta Allah ce …..
Yarima wani babban restaurant ya faka motarshi wajan yayi mugun had’uwa gashi babu irin tarkacen mutane a wajan, daka ganin alama wajan ba kowa ke zuwa ba sai y’an gayu na gaske, private waje suka zauna, shidai habib cewa yayi cikin mutane zai zauna danya 
dinga ganin masu shiga da fita Bariki tace muje tare mana Yace ke barni in zauna nan ko zanyi kasuwa 
Bariki dai dariya tayi sannan ta nufi ciki inda Yarima yake domin yace baya son su zauna inda akwai mutum ko d‘aya dan baya son ana kallon mishi ita ……. 
Yarima ya fad’a abunda za’a bashi bariki kam tace ta koshi Yarima yace dole taci wani abu, babu yanda ta iya tasa a kawo mata snack dan a koshe take shima take away tace tana so, yarima yace abar snack din in Sun tashi fita zata zaba abunda take so. Wajan 15min aka kawo ma Yarima abinci lokacin ana ta kiran sallah magrib tashi yayi ya Kalli bariki tare da fad’in bari inyi sallah. Tace 0K tare da kallon Wanda ya kawo abincin tace maida kayan inya dawo sai kayi warming din abincin ka kawo. 
Mutumin yace ok ma, Yarima bai barta”: ba saida yaga mutumin ya fita dan ya Lura dashi yanda yake kallon zainab kaman yana son yi mata magana ….. 
Yarima Aliyu na fita kam saiga mutumin ya dawo da sauri yana fad’in ma plzl need to talk to you. Bariki tace ok maiya faru? Yace ma ance in amso phone number d’inki ne 
Tace what? Are you mad da aurena inzo da mijina kazo kace min in baka phone number 
dina get lost frm here Kafin mijina ya dawo ya ganka 
Mutumin yace sorry ma Nima na fad’a mishi kina da aure saboda irin shigarki amma yace babu damuwa koda kina da aure in amso mishi number d’inki 
Bariki tace Waye zan iya ganinshi? Yace let me go and ask him in yace in kawo ki sai kizo Bariki tace ok yana tafiya saiga Yarima ya dawo Allah yasa bai ganshi ba 
Bariki tashi tayi tare da fad’in har an idar kiran mutumin tayi da baiyi nisa ba yazo tace Kawo Mai abincin Yace OK ma 
Bai dad’e ba saiga abincin ya kawo, Yarima coffee ya fara sha sannan ya kalli bariki yace my princess feed me plz 
Dariya tayi tare da fad’in feed ur self ur not a baby Yarima kallonta yayi tare da fad’in oh really? Ni baby dinki ne ldo ta rufe alaman jin kunya 
Hannunshi yasa yana kokarin cire mata hannunta da tasa ta rufe fuskanta ….. Muryan Wanda ya kawo abincin ne yazo yana fad‘in ma he said that you can come he is waiting for 
Hmmm lallai 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]