[Advertisements⬇️]

BARIKI NA FITO CHAPTER 24 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

BARIKI NA FITO
CHAPTER 24
Babu abunda take a halin yanzu saida na sani, duk da abunda aka mata yasa ta aikata hakan ido ta lumshe tana kokarin tuna baya, da sauri ta bud’e idon dan bata son tuna abun ba’kin cikin daya faru da ita, lallai mutane basa ansan kaddara ldan ya faru akan wani sai dai in akansu ne mai yasa ba’a amshi abunda ya faru da ita a matsayin kaddara ba kuka ta saki mai sauti, ina gatan da aka nuna mata ina kulawan da aka nuna mata Mai yasa da kaddara ya fad’a mata ba’a amsheta ba n ……. D’an tsagaita wa tayi da kukan da takeyi tare da fad’in lallai shima Yarima ban tunanin zai amshi kaddara tunda iyayena sun kasa amsa lallai Yarima shida ya ganni daka sama bazai amshi kaddara ba Mai yasa na rayu Mai yasa ban mutu ba tun ranan dana had’u da wannan mummunan abun Mai yasa naci 
gaba da rayuwa kuka ta kuma saki mai sauti… 
Kuka take Sosai lokaci d’aya idonta ya kumbura tare dayin ja, duk duniya babu wanda yakai mahaifinta Sonta inta cire mum dinta, haka shima mahaifinta duk duniya yafi Sonta cikin yaranshi amma shine mutum na farko daya Fara kyamarta da mummunan kaddara ta sameta Wanda bata san Ya akai ya sameta ba, mahaifinta shine mutum na 
farko daya Fara nuna mata kyama saboda gudun 
kunyar duniya duk da mutum ne mai sani amma 
baiyi amfani da sanin shiba 1a…. Jin karan wayanta yasa hankalinta yayi kan wayar Sunan Yarima ta 
gani harya tsinke bata d’auka ba kara kira yayi 
shima bata d’auka ha a 
ldo ta lumshe son Yarima Aliyu yayi mata yawa tana matukar sonshi sai dai bata tunanin shima zai amsheta a yanda take Dan yanda yake ta nanata mata bazai auri mace mazinaciya ba ido ta lumshe mai yasa son Yarima yayi saurin shigana? Mai yasa so yayi min shigan sauri tana maganan tana kuka Jin karan wayanta alaman sa’ko yasa ta d’auka ta bud’e ganin Yarima ne yasa ta bud’e dan taga Mai yaceuu 
Zainab maina miki? Yau true out kinki d’aukan phone dina, kin San yanda nakeji kuwa? And I know kina ganin kirana in baki d’auki phone dina 
ba zaki ganni cikin daren nan. 
Tana karantawa ta Fara kokarin kashe wayanta saiga kiranshi nan ya kuma shigowa k‘in d‘auka tayi dan a halin da takejinta yanzu bata tunanin zata iya magana gashi inta d’auka yaji muryanta saiya tambaye ta Mai yasa take kuka, wata zuciyar 
tace in yazo fah? Da sauri ta doka Mai kira k’in 
d’auka yayi sannan bai kirata ba ganin haka ta kara kiranshi amma ya’ki d’auka hankalinta ne ya tashi cikin sauri tasa dogon hijab tare da d’aukan wayanta tayi waje tana fita koh tayi Sa’a taga habib shida jamil suna zaune da sauri ta nufesu taja hannun habib sukai gaba
Habib yace lafiya kuwa? Kikejana kaman wata kububuwa? 
Bariki cikin dashewan murya tace yarima, yarima Habib yace maiya sami Yariman? Tace yana hanya zai iya fad’owa koda yaushe 
Habib yace na shiga uku cikin wannan tsohon daren karfe Goma saura fah yanzu Mai zai zo yayi 
miki kodai shima kin bashi zumar ne yasha? 
Bariki tace a’ah saboda ya kira naki d’auka S ….. 
Karan wayan habib ne yasa bariki yin shuru 
Ciro wayan habib yayi cikin wata karamanjaka daya rataya yace lah Kinga d’an halak Wlh shine ke kira na, d’auka habib yayi ban San mai Yarima yace Mai ba naji yace eh Tana nan marabanjos, tare da kashe wayan. Habib kallon bariki yayi yace toh Yarima dai yana hanya dan haka saimu karasa 
gidan da yake ganinki 
Bariki tace dare yayi bari in kara kiranshi banso yazo yanzu Kar wani abu ya sameshi ….. Kiran Yarima tayi harya tsinke bai d’auka ba message ta 
mishi tare da fad’in 
Plz Yarima pick my call, plz am begging you pick my calls 
Kara kira tayi baiyi picking ba, gaba d’aya ta shiga damuwa message ta kara mai 
Plz Yarima karka zo dare yayi karka biyo hanya plz 
Shima shuru babu reply 
Kallon habib tayi tace ina tsoran ya taso yanzu dare yayi karfe nawa zai zo Ya koma dan Allah 
kirashi kace karya zo ….. 
Habib yace nifa bariki ban son rashin mutunci na 
fad’a miki ki daina kainijinsin da banawa ba Bariki tace yakuri dan Allah ki kira min shi 
Tabe baki yayi tare da fad’in yanzu kikai zance tare da Doka ma Yarima kira harya tsinke bai d’auka ba, habib yace Kinga Ya’ki d’auka nasan yana hanya 
dan haka sai kizo mu karasa 
Babu yanda ta iya dole gidan suka karasa inda suka shiga ciki dan gidan na wata tsohuwa ne da y’arta guda d’aya itama y’ar duniya ce amma tana da aure basu yi koda 20mnt ba saiga Yarima yana 
kiranta da sauri ta d’auka…. 
Kafin tayi magana ya rigata da fad’in come out Ina 
waje yana fad’in haka ya kashe wayan 
Kallon habib tayi da yake ta fira shida masu gidan 
tace ina zuwa yazo yana waje Habib yace ok bari in jiraki a nan 
Fita tayi amma abun mamaki bata ga motocin 
Yarima ba sai wata mota data gani kiranjeep tana 
shek’i gashi motar gaba d’aya baka ganin wanda 
ke ciki, harzata koma taji ana mata horn ganin 
haka yasa ta gane Yarima ne a ciki motarta nufa 
tare da bud’e baya taga ya’ki buduwa gaban motar taga an bud’e gaban ta shiga tare da mamaki ganin 
shi yayi tukin yazo ba tare da kowa ba… 9 
Kallonta yai tayi idonta duk ya kumbura yayi wajan 3mnt yana kallonta ba tare da yace komai ba, haka itama tunda ta shigo bata ce mishi komai ba 
Hannunta ya kamo tare da janyota jikinshi yayi hugging dinta, bakajin karan komai saina motar dan a kunne yake saboda AC yana kunne, sai kuma sautin numfashin su…. 
A hankali yace my princess Mai yasa kika k’i d’aukan wayana? Kin San yanda na damu kuwa? Mai yasa kike son d’agamin hankali? Kin San yanda nakeji Idan na kiraki baki picking ba? Dame kike son inji da auran da ake kokarin …… Shuru yayi tare da d’agota daka jikinshi yace my princess tell me maiya faru yasa kika k’i d’aukan wayana? Tell me 
Kokarin magana takeyi amma ta kasa domin muryanta a dashe yake ganin haka yasa ta fashe da kukauu 
Yarima Aliyu gaba d’aya ya shiga damuwa, yace 
Zainab plz stop it, mai yake faruwa?
Ganin taki magana kuma taki daina kukan yasa ya d’aura hannunshi akai cikin damuwa kanshi yaji yanajuya Mai ga sautin kukanta da baya sonji ….. Matsawa yayi kusa da ita ya rungumota tare da fad’in plz stop it bana son jin kukanki tell me maike damunki plz my princess… 
A hankali tace Yarima Ina tsoran abunda zai faru gaba Ina Sonka ban son in rasaka, ina tsoran kaki amsan kaddara Nasanban dace dakai ba m ….. 
Dakatar da ita yayi tare da fad’in wani irin kaddara? Kalli idona tell me maike damunki nd i promise zanyi accepting dinki a duk inda kike saboda ina 
sonki 
Tace you promise komai nace zakai accepting dina koda nace na taba zina…. 
Ido ya lumshe cikin bacin rai yace my princessl have tell you so many times ki daina danganta kanki da wannan kazaman Kalman, karki manta na fad’a miki zina kawai mace zata aikata in fasa aurenta domin masarautar mu bazatai accepting haka ba, let me tell you something ldan mace tayi aure a masarautar mu bama saki har sai kayi laifi biyu shima sai an ganka zina da kisan Kai wannan laifin shine zaisa a saki mace, Kinga zina tana d’aya daka cikin manyan laifi ko a addinance bazan iya auren macen data bada mutuncinta a waje ba na tabbata Zainab ke bakya d’aya daka cikin wannan matan marasa kamun kai kin samu tarbiya…. “ 
Ina da matukar kishin abunda nake so, Zainab mai kike son fad’a min? 
Bariki jikinta yayi sanyi, domin jin kalaman Yarima lallai Indai masarautarsu basa saki ya kamata ta aureshi kaman yanda ta tsara tun Farko fad’a mishi yanzu babu abunda zai haifar sai dai ma yasa ya tsaneta ko kuma ya barta har abada, lallai ya kamata in boye komai sai bayan auranmu in bashi 
Labarin kaina ….. 
Katse mata tunani yayi da fad’in inajinki…. 
Tace Yarima Ina tsoran Kary’an uwanka Suki yarda dani a matsayin matarka iyayena basu da karfi, na shiga damuwa Sosai Yarima kafi karfina sai yasa nake son ka amshi kaddara kayi hakuri dani ta 
karasa maganan cikin kuka 
Ho ho ho ho zo kuga yanda Yarima ya rud’e tare da fad’in my princess saboda wannan abun kike ta saka kanki cikin damuwa, yace kalli idona, bata ko motsa ba balle ta kalli idon nashi Dan bama iy
kallo za tayi ba 
D’ago Mata da fuska yayi suka had’a ido tana kokarin kawar dakai ya ri’ke mata fuskan tare da fad’in don’t move, yana magana yana kallon idonta yace I can’t live without you my princess you are the girl that I love in my life, ki daina tunanin akwai abunda zai sa in fasa aurenki howl wish aurenmu za’ayi jibi, dana nuna miki how much I love you, but lokaci kad’an nakejira soon u will be mine forever, ke nake so only you ba wani abu ba, bana bukatar komai sai ke. 
Tunda yasa idonshi cikin nata gaba d’aya ta daburce, domin ta rasa mai yasa Yarima Aliyu yake 
mata kwarjini Tana jin abubuwa da dama akanshi 
Wanda bataji a sauran mazan da tayi hulda dasu, ido ta lumshe domin bazata iya juran kallonshi 
cikin ido ba. 9 
Ganin ta lumshe ido yasa ya saki murmushi tare da fad’in my shy Princess Bride to be Mrs Yarima Aliyu insha Allah 
Bud’e ido tayi tana murmushi 
Yace baby ina bukatar inzo Walima dinki, u say ranan Saturday right? Baki bani Kati bama ko am I 
not invited? 
Murmushi tayi tare da girgiza kai tace u r invited but amma na yafe basai kazo ba, tunda I promise 
zan tura maka komai na wajan, Walima din 
Yarima yace hakane but ranan dole In ganki coz Nima zan tayaki murna tunda an hanani zuwa
wajan walima 
Murmushi tayi tare da fad‘in ai yanzu ni ban isa 
ince karka 20 ba inma nace sai dai in ganka 
Dariya yayi tare da fad’in toh ya zanyi your love drive me crazy bana ji bana gani, Indai Anga nutsuwan Yarima Toh yaga zainab dinshi 
Dariya tayi tare da fad’in Rufam’m asiri 
Yace ai a rufe yake my princess 
Tace Yarima dare fah yana yi, wlh Ina tsoran dare Kaga kuma kai d’aya kazo ko in had’aka da habib 
ku koma tare? F 
Murmushi yayi tare da fad’in ashe you care for me Uhm kawai tace 
Yarima yace my princess karki damuwa zan koma ni d’aya, tare da danna wayanshi yaga 11:15 yace Kai dare yayi Sosai ashe her 11:15 
Bariki tace toh kazo ka koma Mai yasa kazo kai 
d’aya?
Yace ke kika sani mana tunda bakya d’aukan 
wayana, ai dole inzo in ganki inga ko lafiya Tace Bari in shiga ciki saida safe koh? Murmushi yayi yace korana kikeyi? 
Tace a’a ni inda babu damuwa Aida ban Bari ka 
kama hanya ba, saboda ina tsoro Yace Toh ko zaki raka ni? 
Ido ta zaro alaman ni kuma, lokaci d’aya kuma tace 
a’ah kaga saida safe tare da kokarin bud’e motar 
d’ayan hannunta ya kamo Yace korana dai kikeyi yau 
Tace Yarima ba haka bane dare yayi kuma you are alone Kaga yanzu lokaci tare da danna wayanta 11:20 tace dan Allah Yarima ban son ka kara bata 
lokaci a nan 
Yace OK my princess peck ya Mata a hannu tare da fad’in good night saura in kira k’iki picking 
Tace dole inyi Murmushi yayi tare da jan motaryayi gaba. Saida ta Bari ya fita daka Layin Kafin ta shiga cikin gidan 
Tana shiga tace ma habib muje tare da yima masu gidan sallama. 
Bayan sun fita habib yace wai bariki ya kuke ciki ne da Yarima? 
Tace kawata ai yanzu abunda muke ciki shine ka nema min wanda zasu tsaya a matsayin iyayena sannan a anguwan kanawa kasan nace mishi nake, ina son gidan da zamu zauna ya zama na talakawa 
Sosai sai mu kama hava 
Habib yace an gama karki damu zan sami dattawan mutunci masu kamala su tsaya a matsayin iyayenki sannan zani wajan sarkin anguwan kanawa muyi magana saiki tanadi kud’i dan kin San abun na kud’i ne 
Bariki tace indai kud’i ne Babu damuwa ko nawa 
zan kashe Indai zan sami Yarima na 9 
Habib yace ah Yarima yayi sa’ah ayabarsa tama bariki 
Duka takai ma habib tare da fad’in ban son iskanci, yauwa Ina son in dan had’a Walima amma fa na mutunci dan hijab za’a saka 
Habib yace na shiga uku an fasa aurena miye wani hijab za’a saka kice wannan ba namu bane yana maganan yana bud’e hanci ,wlhbariki naga kina neman komawa ta Allah 
Tace toh da ni ta wacece Habib yace kin fini Sani 
Tace Yarima na kira na kaga nayi gaba da gudu tayi gaba dan ta isa Gida Kafin kiran ya tsinke ….. 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]