[Advertisements⬇️]

BARIKI NA FITO CHAPTER 21 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

BARIKI NA FITO
CHAPTER21
Ku ka tayi Mai isarta, sannan ta wanke fuskanta tare da shafa powder dan KarYarima ya gane, saida ta tsaya ta seta kanta sannan ta fita ….. 
Tunda ta fito yake kallon fuskanta wanda dama tunda ta shiga idonshi nakan kofar gidan, tun Kafin ta karaso ya gane tayi kuka domin idonta yayi ja, dan farar mace Indai tayi kuka sai an gane dan 
fuskanta zata canza tayi ja ja …… Isowarta ne yasa tunanin da yake ya kawar 
Bayan ta bud’e motarta shiga da sallama muryanta a dashe…. 
Amsawa yayi tare da fad’in my princess yau kwata kwata na rasa gane maike damunki? Mai yasa kikai kuka da kika shiga ciki? 
Gabanta taji ya fad’i ya akai yasan nayi kuka toh kodai ya biyoni ciki ne kai Anya a’a Toh y …… 
Katse mata tunani yayi tare da kiran sunanta da zainab 
Da sauri ta d’ago ta kalleshi dan tasan magana zai Mata Wanda yake bukatan hankalinta tunda ya 
kirata da sunanta…. 
Yace I don’t know why yau kaman you are not happy, plz ldan kina da wani matsala ko damuwa let me know, ban son kiji shakkan fad’amin wani abu da kike bukata ko kunya, plz tell me maike 
damunki? 
Muryanta na rawa tace Yarima Ina son inyi maka 
wata tambaya, ina son Kuma ka bani amsa… Murmushi yayi tare da fad’in go ahead…. 
Tace kasan al’amarin aure yana da abubuwa da dama, yau ldan akace mutum zaiyi aure sai ayita kushe shi, k0 kuma azo ana ya’da Labarin karya 
akan mutum yan ….. 
Dakatar da ita yayi da fad’in enough my princess it seem like wannan mafarkin da kikayi yasa kike wannan maganan, na fad’a miki zina ne kawai zaki aikata in fasa aurenki ….. Bayan haka banga abunda zaki aikata ba ince na fasa auranki ba, sannan ina so ki sani sonda nake miki ba Wanda wani zaizo ya fad’a magana akanki bane in yardal 
trust you nasan bazaki taba bani kunya ba 
A hankali tace in fah wani yazo yace maka ni 
karuwa ce ya 2 …….. 
Yace ya isa haka ya isa yana maganan ne cikin jin haushin abunda tace, yace karki kara danganta kanki da wannan Kalman infact ma ban son ki karamin wannan maganan plz ….. Let change the 
topic 
Shuru tayi ba tare da tace komai ba, Satan kallon Yarima tayi wanda taga gaba d’aya yana yinshi ya canza alaman ranshi a jagule yake ….. 
Katse mata tunani yayi tare da fad’in Zainab kinsa naji babu dad’i, mai yasa zaki damu da mafarkin 
da kikayi haka har kike zargin wani abu? Har kike dan ganta kanki da wannan mummunan Kalman, Zainab duk Wanda ya kiraki da wannan Kalman sai Nayi karanshi dan ba haka kike ba, I trust you more than my self, ina jin kaman na sanki tun tuni karki manta tun a mafarki na Fara ganinki ban taba ganin Fuskanki ha a mafarki ba sai a zahiri na ganki sannan na gane Kece ….. Hannunta duka biyun ya ri’ke yace Zainab nasan had’uwa na dake had’in Allah ne, babu wani abu da wani zaice a kanki yayi tasiri a wajena Indai ba gani nayi da ido naba, so inaso ki daina duk wani tunani akan sonda nake 
miki 
Wani hawaye mai zafi ne ya fito mata daka ido, gaba d’aya jikinta yayi sanyi, tana son Yarima kuma tana son fad’a mishi ko ita wacece gashi ta d’auko hanyar fad’amai ya dakatar da ita, lallai in Yarima yasan wacece ita bazai aureta ba, zan Bari saiya aureni in fad’a mishi koni wacece na tabbata zai fahimce ni S …….. 
Katse mata tunani yayi tare dasa hannunshi yana goge mata hawayen idonta, yace Zainab bana son 
ganin wannan hawayen naki, kina min asaransu ….. 
Murmushi tayi tare da fad’in na daina Yarima na 
daina bazan kara ba. 
Hancinta yaja tare da fad’in yauwa my princess Murmushi ta saki 
Yace ya maganan Walima dinki? Mai zamu shirya? Tace banda wani Abun cewa sai yanda kace. 
Yace Nop ina son in San mai kike so ….. Yauwa you 
never tell me what you like nd dislike Tace Yarima komai kake so shi nake so Murmushi yayi tare da fad’in toni ke nake $0…. 
Dariya tayi tare da fad’in ni kuma? 
Yace eh ke nake so,duk wannan abunda suke 
hannunshi na ri’ke da nata 
Sakin hannunta yayi tare da matsawa ya d’auko wani karamin akwati ya bata yace gashi sai kiyi abunda ya dace, sannan akwai check a ciki nasa iya kudin da za’a cira amma ban sa suna ba Wanda zai cira sai yasa sunanshi, kiba ma islamiyya din, 
gudun mawarki…. 
Tace Yarima nagode Allah ya saka maka da gidan 
Aljanna ban San wani…. 
Ya dakatar da ita tare da fad’in ya isa haka my princess 
Tace Yarima amma kaman hidiman yayi yawa 
Sosai 
Yace komai na miki baiyi yawa ba, u deserve it Tace ngd 
Ido ya kura mata yana kallonta ko kyaftawa bayayi 
Ganin irin kallon da yake mata yasa tayi saurin yin 
k’asa dakai 
Hannunshi yasa ya d’ago Mata fuskanta yace my 
princess d’ago ki kalleni…. 
Ido ta rufe domin bazata iya kallon idonshi ba, dan 
yana mata wani irin mugun kwarjini Sosai 
Ganin ta rufe ido yasa yayi murmushi tare dakai bakinshi kusa da kunnenta yace I want my kiss now, Bayan ya fad’a mata hakan yayi baya tare da kallon fuskanta yaga haryanzu idonta a rufe, iska ya hura mata a fuska tayi saurin bud’e ido, murmushi ya sakan mata idonsu duka yana kallon na juna, fuskanshi ya fara matsawa kusa da nata kaman zaiyi kissing dinta ganin haka tayi saurin rufe ido, murmushi yayi yakai mata peck a goshi jin a goshi yayi mata yasa ta sauke ajiyan zuciya har yana ji, baya yayi tare da fad’in I don’t want the 
kiss now 
Kallonshi tayi suka had’a ido da sauri tai k’asa dakai 
Murmushi yayi yace wannan kunyan yayi yawa but very soon zan rage miki shi 
Murmushi tayi ba tare da tace komai ba Yace Zainab very soon you will be mine 
Ganin taki magana yasa yace bari inzo mu wuce 
tunda my princess ta k’osa in tafi 
Da sauri tace nifa bance haka ba… 
Murmushi yayi yace kina son in zauna? Murmushi tayi tare da fad’in wannan tambayar.. Sai kuma tayi shuru 
Yace Inaji fad’a min? 
Tace Mai zance? 
Murmushi yayi yace say you love me 
ltama murmushin tayi tare da fad’in yaushe zaka tafi?.. I 
Dariya yayi yace oh saboda karki fad’a kike korana koh? 
Tace a’a nifa ba haka nake nufi ba 
Yace anyway ya kamata inzo in gudu naga yamma 
yayi Sosai gashi an kusa kiran sallah magrib… Tace toh ka Bari in kukai sallah saiku tafi. 
Yace OK my princess, yace banga mutumina ba 
yau? Tace habib? Yace eh 
Tace baya nan amma zaka iya ganinshi ya fad’o 
yanzu 
Yace OK…. Dan shuru yayi Kafin yace naso inzo 
saukan ku but I will try in samu inzo 
Tace a’a Yarima basai kazo ba, ka Bari kawai duk abunda akayi zan turo maka, ranan fah shine Washe garin auranka kaga karka shiga hakkin 
amarya 
ldonshi na kanta yace Kema ai tawa ce, sannan ldan abun murna ya sameki dole inzo in tayaki 
Tace Yarima plz basai kazo ba Wlh na yafe maka, abunda bazan so ya faru akaina ba banso Ayi ma 
wata akai na Yace really? Tace eh 
Yace Sai yasa nake sonki, but amma duk da haka 
Zanzo 
Tace shikenan tunda haka kace, but Ina son Yarima 
na ya zama mai adalci, tunda ni nace na yafe 
Murmushi yayi tare da fad’in shikenan Yarima dinki 
zaiyi adalci insha Allah tare da ja mata hanci Tace akwai zafi fah ‘ 
Murmushi yayi yace am so sorry my princess,jin 
ana kiran sallah yasa ya fita dan yayi sallah 
Itama gidan ta shiga tare da ajiyejakan da Yarima ya bata, zama tayi tana tunanin firansu Tana murmushi, Yarima I promise ranan daka aureni zan 
fad’a maka koni wacece Bazan bari ka aureni ba sai 
fad’a maka koni wacece Bazan bari ka aureni ba sai Nayi istabra’i zama tayi tana ta tunani dan tana fashin sallah, karan wayanta yasa ta d’auka ganin Sunan Yarima tayi ta danna tare dakai wa 
kunnenta Yace come out in ganki mu kama hanya 
Tace OK tare da kashe wayan tana murmushi fita 
tayi a waje ta ganshi a tsaye 
lnda yake taje yana ta murmushi a tsaye suka tsaya 
yace my princess zan wuce sai yaushe kuma? Tace sai Bayan bikin ka 
Murmushi yayi yace bazan iya ba, Kema kin sani Tace Yarima dakajibi fah zaku Fara abu 
Yace how did you know? 
Tace naji Ai kana fad’ama amaryanka 
Yace hakane na k’osa ma a kawo ta, yana maganan yana kallon bariki 
Ganin ta d’an bata fuska yasa yaci gaba da fad’in bari inje in samu muyi waya ma…. 
Gaba tayi tana fad’in saida safe tana fad’in haka 
tayi cikin gidan 
Murmushi yayi tare da girgiza kai kiranta yayi amma taki d’auka 
Message ya Mata tare da fad’in haka za muyi 
sallama din? 
Ganin batai reply ba kuma bata fito ba yasa ya shiga mota yace suje, kara tura mata message yayi yace ok na tafi kin San hanya zamu kama but kinsa na tafi ba tare da munyi sallama Mai Kyau ba, may be ma wannan ne last maganan mu …… 
Tana ganin message din ta fito da sauri amma ina 
motocin sunyi gaba… 
Yarima yana kallonta murmushi yayi tare da fad’inl 
love you my princess 
Bariki komawa tayi ta doka ma Yarima kira amma yaki d’auka, message ta tura mishi Tana fad’in plz pick my call I need to talk to you 
Yarima yana ganin sa’kon yayi murmushi tare da kashe wayan dan yasan zata kara kira kuma bazai d’auka ba harsai yaje gida, domin bazai iya waya da princess dinshi ha a gaban driver domin sarautarshi bazai Bari driveryaji Kalan kalaman da 
zaima baby dinshi ba 
Bariki kara kira tayi taji wayan a kashe kanta taji ya Sara, jiki a sanyaye ta had’a kayanta tabar gidan dan zuwa d’akinta, tana zuwa d’aki ta ajiye kayan tare da had’a tea tasha, jakar da Yarima ya bata ta bud’e kud’i ta gani makil da yawa dubu d’aya d’aya bandir bandir harguda ishirin million biyu kenan, ido ta d’an zare tana mamaki check din ta d’auka shima taga million uku ya rubuta, a hankali tace Yarima kud’in yayi yawa har5mil, hawaye ya zuban Mata tace yanzu duk wannan Abun karya nayi maka ka d’auki wannan kud’in kaban, ba tare daka nemijikina ba lallai Yarima inna Bari na rasaka Nayi babban rashi, duk yanda zanyi dole In boye koni wacece har sai ka aureni zan fad’a maka Nasan zaka fahimce ni, wani hawayen ne ya kuma zubo mata ……. Muje zuwa muga ko Asirin bariki zai rufu ko kuma akasin haka 

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By Ismail

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]