BARIKI NA FITO CHAPTER 15

Advertisements

_____

BARIKI NA FITO
CHAPTER 15
Jin tayi shuru yasa Yarima Aliyu fad’in, lafiya kuwa? 
‘kago murmushi tayi tare da fad’in sunana Zainab musa haifaffiyar garin kaduna, gidan mu yana u/kanawa mahaifina yana sana‘ar rini, duk da bashi da karfi ya bamu tarbiya dai dai gwargwado sannan har yau yana kokari wajan bamu tarbiya, mahaifina Talaka ne amma yana da Kawa zuci,zaiyi abunda wani mai kud‘in ma bazai iyayi ba, mu biyu iyayena suka mallaka sai yasa duk wani burinsu da kudirunsu yake kammu nida dan uwana,wajan ganin mun sami rayuwa mai in ganci kuma Alhmdlh tunda yau saukan mu ranan sati mai zuwa ne insha Allah zan haddace a’qur’ani Mai girma, shi yayana mai suna Saddiq ya dad’e da sauke al’qur’ani, sannan fannin boko inada matakin secondary domin mahaifina bazai Bari Inci gaba da karatu a gidansa ba sai gidan mijina, wannan dai shine labari na. 
Yarima murmushi yayi sannan yace yan Zaria ne kenan ku? 
Gabanta taji ya fad’i dan in tace su y‘an Zaria ne toh a wace anguwan? Kai a’a da sauri tace a’a mahaifina dan Kano ne domin a can aka haifeshi, tun yana dan shekara Gama sha biyu ya dawo kaduna shida iyayensa har Allah ya musu rasuwa inda mahaifina ya fara buga buga har yakai da yayi aure aka haifemu a garin kaduna, toh Kaga inda aka haifa mutum toh nan ne garinsa. 
Murmushi Yarima Aliyu yayi tare da fad‘in hakane,. Yace Zainab naji dad’i Sosai da naji tariyin ki, babban abunda ya kara burgeni daya kasance princess dita mahaddaciyan 
al’qur’ani ce, Allah yasa ya amfana al‘umma 
Tace Allahumma Ameen Yarima na ….. Shuru tayi dominjin Kalman daya fito daka bakinta…. 
Yarima da sauri ya kalleta domin irin Sunan take kiranshi cikin mafarkin shi,yace Zainab 
plz say it again 
Jin tayi shuru kanta na kasa yasa ya kamo hannunta da take wasa dashi ya ri’ke hannun duka biyu tare da fad’in plz say it again plz. 
Rike mata hannu da yayi yasa komai dakejikinta ya tsaya wannan ne karo na farko da namiji ya taba, taba matajiki taji wani abu, danko mazan da take iskanci dasu bawai tana jin wani abu bane kawai tana dai yine, amma shi Yarima hannunta ya ri‘keyasa tanajin wani abu tun daka tsakiyar kanta Kar kasan kafanta, kokarin Fara Jan hannunta tayi daka nashi, amma ta kasa. 
Murmushi yayi tare da fad’in sai kin fad’a min abunda nace zan sake ki, a hankali tace 
Yarima na, ido ya lumshe cikin jin dad’i tare da wani kara jin Sonta har cikin ranshi. 
Muryanta da yaji tana fad’in plz ka sake min hannu shineya dawo dashi daka duniyar tunanin daya fad‘a, ido ya bud’e tare da d’auko wani Leda, ciro wani karamin kwali yayi anyi raping dinshi, bud’ewa yayi ya d’auko wani diamond ring, saka mata yayi a hannunta das ya shige kaman an gwada,yace this ring is my heart, ina fatan zaki ri’ke min shi dakyau? 
Murmushi tayi tare da saka hannunta a kafanta tana kallon zoban mai shegen kyau Wanda Yarima Aliyu ya kira da zuciyarshi ce. 
Ganin idonta nakan zoban tana kallo kobai kara cewa komai ba yasan ya samu shiga. 
A hankali tace Yarima wannan ringdin bai dace dani ba, hawaye ne ya fara zuban Mata Sosai 
Ganin haka hankalin Yarima Aliyu ya tashi Sosai tare da fad’in Zainab mai yasa kika fad’i haka? 
Cikin kuka mce Yarima ni dakai bamu dace ba baka dace dani ba kafi karfina ba Irina ta dace dakai ba nasan in ….. 
Dakatar da ita yayi tare da fad’in ya isa haka zainab‘ Tissue ya d’auko ya fara gage mata hawayen da takeyi yace kalla yanda kika batamin Fuskanki da hawaye,yana maganan ne yana kallon ta, yace Zainab shi so babu ruwanshi dako Waye mutum, Zainab ina sonki dagaske bada wasa ba, tun Kafin in ganki nake sonki tun cikin mafarki na, bana tunanin akwai abunda zai saka in daina sonki, zainab yau had’uwa na dake da nayi na fuskanci abubuwa da dama, kina da addini kin flto gidan mutunci iya wannan ya isheni, zainab duk irin yanda nake son matarda zan aura ta kasance kina dashi, ina da kishin abunda nake so, ina son mace Mai suturtajikinta Wanda ke gashi ko a cikin mafarki na da hijab kike zuwa har a zahirin ma da hijab na ganki, wannan abubuwan ya isa dukwani namiji yayi burin samunki a matsayin matar auransa kuma Uwar y‘ay‘ansa, I don‘t care ko daka ina kika fito ke nake so bawai wani abuba, inda kin San yanda nakejinki a raina da baki tunanin wani abuba so plz karki kara fad’in ni dake bamu dace ba, d’an matsawa yayi kusa da ita yace kalleni kiga bamu dace ba? Ganin taki d‘ago kai yasa yayi murmushi yace ban taba ganin couple din da suka dace ba kaman ni dake. 
Bata san lokacin da dariya ya sakar mata ba domin maganan shi ya bata dariya. Ganin tayi dariya shima yayi murmushi tare da fad’in yauwa na saki dariya am happy now. 
Murmushi tayi tare da fad’in babu kyau son Kai, ai bakai zaka fad’a ba wani ne zai fad’a yace mun dace ko bamu dace ba. 
Murmushi yayi (are da fad’in Toh Kema ya akayi kika san bamu dace ba? Kanta na kasa tace saboda naga haka dinne. 
shima yace nima na fad’i hakan ne dan Ina ganin mun dace 
Murmushi tayi 
Sunanta ya kira yace Zainab Ina son fad’a miki magana Mai muhimmanci. Gabanta taji ya fad‘i, amma saita daure tace inaji. 
Yace biki na ranan Friday din nan rana ita yau. 
Dam taji gabanta ya fad’i Wanda bata san dalili ba tare da kallonshi da sauri ganin Sun had’a ido domin shima ita yake kallo yasa tayi kasa dakai. 
Yace Zainab iyaye na sun sha bani mata amma naki yarda burina kullum in ganki dan muyi aure sai yasa bana yarda da duk wani zabin iyayena, mahaiflna ya gaii da zama na haka babu mata, musamman daya kasance nine d’ansa namiji guda d‘aya yana bukatan ganin jikansa, sai yasa ya yanke bani auran y’ar sarkin katsina gimbiya zinatu, bayan na amince da auran domin ko ban amince ba dole Ayi tunda mahaifina bada wasa yake ba, kawai sai na ganki keda wancan guy din ya nuna mata habib dake waje yana hararan driver dinshi, Zainab na fad‘a miki wannan maganan ne saboda ina sonki ban son boye miki komai dake tare dani , ina son Kema ki fad‘amin abunda kikeji a game dani. 
Barfki kanta na kasa tunda Yarima ya Mata maganan auranshi rana ita yau, ta shiga damuwa wanda ta rasa dalili, ganin yayi shuru ita yake saurara yasa (ace ina son ka bani lokaci kad‘an inyi tunani akai 
Yace Zainab when no one’s around but you and me. A lokacin zaki iya tunanin mai kikeji a 
Yace Zainab when no one‘s around but you and me. A lokacin zaki iya tunanin mai kikeji a kaina. Kiran sunanta yayi cikin wani irin murya 
d’ago dakai tayi suka had‘a ido da sauri ta sauke idonta ta rasa maiyasa bata iya kallonshi gabanta faduwa yakeyi Sosai,jin hannunshi tayi akan nata ….. 
Yace my princess zan baki lokaci amma fah bamai yawa ba, kwana biyu kawai na baki kiyi tunani akai na Zanzo inji amsa daka gareki. 
Kasa motsi tayi sai gabanta dake faman dukan uku uku, Mai yasa na kasa fad‘a mishi abunda Nayi niya Mai yasa banajinshi kaman sauran mazan da nake hulda dasu? Mai yasa ya banbanta dasu? Ga hannuna a ri’ke da nashi amma na kasa yin abunda nayi niya ido ta 
lumshe domin ta rasa amsan wannan tambayan nata . 
Ganin tayi shuru yasa yace my princess karki manta kwana biyu na baki Zanzo inji daka 
garekijibi kenan, sannan Saturday shine ranan waliman ki koh? Kai ta d’aga alaman eh. 
Yace Allah ya nuna mana ranan,jin kiran sallah la‘asaryasa yace bari muyi sallah sai mu 
kama hanyal 
Tace toh Bari a kawo maka ruwa, bud’e motartayi ta fita cikin gidan ta shiga da sauri habib yabi bayanta.. 
Tana ganin habib tace yauwa Kai ma Yarima ruwa yayi alwala, amsa yayi ya fita tare da 
kaima yarima ruwan 
Sannan ya koma ciki, inda ya sami bariki na sallah itama, zama yayi yanajira ta idar, Bayan ta gama. 
Habib yace ya kukayi? 
(ace Kai bakaje masallacin ba, d’aure fuska yayi tare da fad’in in banda rashin mutunci kin taba ganin mace a masallaci? Gskya banso. 
Bariki tare Allah ya shirya, jin wayanta yayi kara alaman sa’ko ya shigo yasa ta duba taga Yarima ne yayi mata message ’come out my princess” murmushi tayi tare da tashi ta 
d’auko jakarta ta fesa turare sannan ta fita, motar ta bud’e ta shiga inda ta ganshi zaune 
yana waya taji yana fad‘in lil yanzu zan dawo nace kuyi komal’ keda usman Kafin in dawo, kashe wayan yayi sannan ya kalli bariki F 
Yace my princess zan tafi, sai nakeji kaman mu tm tare. 
Murmushi tayi tare da fad’in in lokacin hakan yayi zamu ….. Da sauri tayi shuru dan maganan da taji tana niyan fad‘a 
Ganin tayi shuru yasa Yarima Aliyu yayi murmushitare da fad’in inaji karasa abunda kikai niya. 
Hannunta tasa a fuska alamanjin kunya 
Yarima dariya yayi Sosai abunda bai taba yima wani ko Wata ba sai yau, d’auko wani card yayi ya bata tare da fad’in plz in kin shiga Gida ki turomin Abokina habib 
Tace (oh har zata fita ya kira sunanta waigowa tayi Yace Zainab Waye habib a wajan ki? 
Tace d’an uwana nane yaron kanwarmama nane. Yarima yace ok na gane I love you 
Dariya tayi tare da flta da sauri tayi cikin gida. 
Ko mimi biyu batayi da shiga ba saiga habib yazo, yan’ma wani Leda ya bashi babba (are da 
fad’in kaba ma my princess wannan, wata karaman Leda ya d’auko tare da bama habib yace ga naka. 
Habib amsa yayi yana ta godiya sannan ya fita Su Varima hanya suka kama yana kallon gidan da zainab dinshi take har suka wuce. 
Koda habib ya shiga gida bama bariki sa’kon da Varima ya bata yayi, bud’e nashi yayi yaga agogo Mai shegen tsada da kud‘i dubu d’ari biyu ihu ya saki tare da fad‘in oh wannan koh dan arziki. Ganin bariki tayi shuru kaman mai tunani yasa yace bariki laf‘lya kuwa? 
Bariki tayi firgit tare da kallon habib tace ina son fad‘a mishi gaskiyan koni wacece amma na kasa, mai yasa baiyi min kaman yanda nake ganin sauran maza ba, ya banbanta dasu, 
na rasa gane mai nakeji a kansa, na tsinta kaina da tsoran fad‘a mishi koni wacece, Nasan zai tsaneni ….. 
Habibyace bariki kin kamu da sonshi 
Kai ta girgiza alaman a’a tace ba sonshi nake ba, ina mamakin kasa gaya mishi abunda Nayi niya ne Bayan daka ni sai shi, tunda na fito bariki ban taba had’uwa da mutum Wanda naji ya cika min ido ba sai yau, Indai bazan iya gaya mishi koni wacece ba ya zama dole inyi nesa dashi Kar in kara Bari mu had’u …… 

Advertisements

_____

About Ismail

Check Also

BARIKI NA FITO CHAPTER 45

Advertisements _____ BARIKI NA FITO CHAPTER 45 Mum da sauri ta nufeshi, ganinjini na fita …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *