Makaranta duniya chapter 31 Qarshe

Makaranta duniya. Qarshe

             Chapter31

Asha karatu lafiya

Dakin Sulaiman suka dunguma, shi ma barci yake yi saboda bai yi barci da daddare ba sai bayan asuba barcin ya sace shi, don haka ba su tashe shi ba, suka juya Baba da MUrja..suka ra’ka su wajen mota, sai da suka bar wajen, suka dawo. Alhaji ya wuce dakin Sulaiman. Murja ta koma wajen Jamila. Kuka ya ki karewa, wanda ta kasa sanin musabbabinsa.
Ta kasa shan Tin da aka hada mata. Murja ta rasa na yi, haka’ ta tasa ta, ta yi ta fada kamar ta ari baki,~ wanda gaba daya laifinsu take nuna mata a zahiri. Sulaiman bai farka ba sai karfé ta_ra. ‘
Magana ta farko da ya fara yi ita‘ ce, Baba ya ce, “Ka tashi Suleiman? Sannu ya jikin? Ya ce’ “Ina fatan ‘ kun janye maganar nan?. Ya‘ce “Muna nan muna ‘ neman mafita, ka na barCi Likita’ya shigo, na gaya masa har yanzu babu matsaya tukuna…. _ .
“Baba ‘ka daina fadin babu matsaya, ni fa ba za’a maida ni gurgun dole ba.” Alhaji ya yi nuni ga kafar ya‘ce, “Duba ka gani yadda suka shanye gaba daya. Likita ya ce haka za su ci—gaba da kumburi saboda jijiyoyin su
duk sun katse. Sannan kokon kashin guiwowin ya fatattake.
Dan-uwanka ya yi alkawarin siya maku wasu kafafuwan na roba masu kama ’da jikin Mutum. Don glrman Allah ka kwantar da hankalin ka, k0 a samu na_sarar wannan aikin. Da wata wahalar, ai gara wata Sulaiman.”
Ya yi shiru, bakin-ciki kamar ya kashe shi. Can cikin tunaninsa ya ji Alhaji na ci—gaba da fadin “Ka na barci su Imam suka wuce Zariya. Waya D.P.O ya kira wai an kama barayin da suka sace ni, kuma da ikon Allah ku …… –
Zabura ya. yi ya tashi zaune, “What? Me ka ce Baba? Ya zuba masa ido, “Ka ji mamakik0? Ikon Allah kenan. D.P.O ya ce da kudaden aka kama su, ko sisi ba su taba ba, ko kuma sun taba, kadan ne. Sal dai sun isa can za su kira waya‘ mu ji yadda ake ciki”. ‘ ‘ ‘
, Tamke ido ya yi ya runtse SU tam! Ya ce, “Inna-
Lillahi’wa-Inna-IIaihir—Raji’un, shi kenan na gama yawo Kafin Alhaji ya ce wani abu, ya fadi tif Bisa filo, suma yayi? Me ya faru da shi Alhaji bai gane ba. . Sulaiman dai babu‘ magana, babu motsi. Ya debo ruwa da sauri ya yayyafa masa a fuska, sannan ya shafe masa ita, ya yi ajiyar zuciya mai karfin gaske ya bude ido, yana zazzare su tamkar, wanda ya‘ warke makanta. “Sulaiman, kai Sulaiman lafiya? Me ya faru da’ga cewa an kama barayi? ‘
Zuru ya yi Wa Alhaji- “Ka yi magana mana Sulaiman?.” ‘ Hawaye suka fara kwararo masa. “Da gaske… Maganar_sulaiman ta dauke, sai faman juya harshe yake yi. Alhaji ya rude da ya ,lura kamar bakinsa yana komawa gefe. Tashin hankali
Da saurl ya fito ya nufi wajen Murja, ya iske ita ma ta juya wa Jamila baya, saboda ta ‘yi rarrashin ta yi fadan, amma ta ki ta daina kuka, bai bi ‘ta kan kukan
jamila ba, kai tsaye cewa ya yi, “Murja zo ki ga ikon ,allah wajen Suleiman.” Ta mike a firgice “Mutuwa ya yi baba ya ce “Zo dai ki gan shi.” Ya yi waje ta biyo shi da ‘ sauri, suka bar Jamila a tsorace ko kuma mu ce tsoron ‘ taya karu. .
Suna tsaye gaban gadon. “Me ya faru Baban Jamila? Shiru babu amsa, hawaye kawai ke zuba. Ta dubi Alhaji, “Daga tashin sa barci ya fara wannan abin aa ba? Ya ce, “K0 kadan magana ma mu ke yi, ina ba shi labarin an kama barayin da‘suka sace ni, kawai na ga ya tashi zumbur Yana salati, kafin in ce wani abu ya Koma ya fadi a sume, sai da na yafa masa ruwa.” ,
Murja ta yi shiru jim, tana dogon tunani, ba ta iya gano bakin zaren ba, don haka ya ce, “Bari a nemo likita.” Ta fice ta bar su Alhaji na tarai’rayo shi, amma ya kasa daga kansa balle ya dora jikin sa, idanuwansa suka cika da kwalla har suka fara zuba bisa kuncin sa fadi yake, “Allah mun gode da jarabawarka. Allah ka ba mu ikon cinyeta. Ya Ubangiji.” .
Jimawa kadan Murja ta dawo da likitoci har biyu, daya kwararre ne, daya kuwa mai sanin makamar aiki ne, sannan wata Nos ta iso a guje da kayan aiki, nan take suka kama aikin’ su, taba nan, gwada can, a karshe Likita ya dubi Alhaji, sannan ya ce, “Baba bari in gan ka k0? Ya ce to. Suka fito daga bakin kofar suka bar Murja da faduwar gaba. ‘ ,
Likita ya tsaya gab da Alhaji- ya ce, “Baba akwai’ matsala sosai, jinin Sulaiman ya yi mugun hawa, shi ne’ ya haifar masa da wannan lalurar. da alamu gefen jikinsa ya daina’aiki har sautin maganarsaya dauke, ina ganin ya sanya maganar’yanke kafafuwansa cikin ran sa ne. Gaskiya yana bukatar a rinka kwantar masa da hankali ta kowace fuska.”
Alhaji ya numfasa ya ‘ce, “Likita tunani na ya rikirkice, ina ganin Sulaiman addu’a kadai yake bukata.
sauran aikin kuma na ku ne, ku taimaka masa a mu samu biyan bukata. ni kai na, na taba samun irin wannan“ matsalar wasu shekaru da suka wuce, amma da‘ taimakon Allah da taimakon Likita haziki irin ka, gashi na kawo yau ina yawo na. Don Allah Likita ka taimaka masa.”
Likita ya jinjina kai ya ce, “Haka ne, kar ku damu, muna kan bakin kokarin mu, yanzu zai sami  isashshen barci tare da karbar magunguna ta Alhaji ya yi godiya. Likita ya wuce, shi kuma ya koma ciki. Nan suka zauna yana yi wa Murja bayani. Nos da dalibin Likita suna ta yi masa abinda ya dace_ Bayan sun fice, ba’a jima ba barci ya kWashe shi, sannan Murja ta koma wajen Jamila dauke da damuya‘ kamar yadda Alhaji ke‘zaune cikin juyayi
amma a zahiri su Alhaji Imam sune suke cikinsa juyayin, tun isowarsu ofishin D.P.0 aka kawo Oga  da yaransa a gaban su, aka bude kwalayen
kudaden da bakinsu suka fadi miliyan hamsin ne‘babu _. dubu dari biyu. . . A ciki dubu dari biyu kacal Suka taba. Daga nan aka ba oga dama ya yi bayanin da ya ce yana son yayi ‘ a gaban Imam. -Tunda ya kwararo jawabinsa suke ‘ kallon juna, shi da Mudansir kowa baki sake. ‘ Tsananin mamaki yasa kamar kar su yarda, sai dai babu tantama, ga shaida bayyananniya a jikin su Sulaiman, hankiCi Imam ya fiddo yana share zufa saboda al’ajabi, kafin ya ce wa D.P.O “Yanzu Yallabai menene abin yi? Ya ce, “Wannan aikin mu ne, kai kudin ‘ ka kawai za ka dauka, ka bar sauran maganar a hannun mu.” ‘ :. ‘ Sulaiman da Jamila kuma za su ci-gaba da jinya a karkashin (Arrest) din mu. Da zarar sun warke za a” fuskanci shari’a.” Imam ya ce, “Wannan shiri yayi
bana neman wani sulhu, duk abinda shari’a ta tanadar  a zartar kawai, ina rokon ka ba mu ‘yan rakiya mu maida kudaden nan banki.”
Ya ce, “Ba laifi.” Rafa biyu ya aje wa D.P.O, rafa daya kuma ya ce ya raba wa yaransa. Nan da nan aka ba su ‘yan rakiya har banki suka shigar da kudaden. sannan suka bar banki.
“Ina yakamata mu fara zuwa? Imam ya tambaya. Mudansir ya amsa, ‘lnna yakamata a fara sani, in ya so sai mu wuce Kaduna.” Ya numfasa da karfi, “Yaya Sulaiman ya zubar da mutuncin sa, ya ci amanar Baba, meye amfanin hada zuri’a da irin Yaya Sulaiman? Yaya Sulaiman na cike da nuku-nuku da rashin gaskiya, tun dawowar sa gida, hankalina bai kwanta da shi ba.‘
Saboda abubuwan guda biyu; Ban sani ba ko – kai ma ka nazarce Su? Yaya Sulaiman bai taba yi maka godiya akan iya kokarin da ka ke yi a kansa da iyalanSa _ ba, haka kuma ban jin daidai da rana daya‘ Yaya Sulaiman ya taba daukar abubuwan da ya yi baya a matsayin kuskure…
Imam ya katse shi, “Ka daina tantama dan-uwa, ai da ya ,taba tunanin kuskuransa da bai aikata wannan aikin ba. Wannan ya nuna karara za’a iya hada baki’ da Yaya Sulaiman da Jamila a‘ kashe mu.” Ya ce “Me ya rage? Kiris! Ya rage su aikata hakan. Allah ya nuna masu iyakar su Ya kada kai. “Allah abin tsoro, Mutum abin tsoro! ‘
\\\\\\\\\
daidai Kofar‘gidan Inna ya yi fakin, suka fito fuskokinsu dauke .da damuwa, daga sallamar su Inna ta gane akwai matsala. Gabanta .ya fadi, “Lafiya Baba na? Yanzu mu ka gama waya da Hajiya Suwaiba ta ce in, shirya za su biyo da- direba su dauke ni mu tafi Kanon, wani a cikin su ya mutu ne?
Ya kada kai ya ce ‘Babu wanda ya mutu Inna. wata magana ce ta taso.‘ ‘To mu shiga ciki.‘ Suka wuce tana fadin ‘Alhaji ke gaya min an kama barayin da suka sace shi, kuma abin dadi har da kudaden an gani.‘ Suka ce Wallahi kuwa.‘ ‘
‘ , Suka zazzauna. ‘Me zan kawo. maku na ci? Akwai dai fura lafiyayya a firij.’ Imam ya ce, “lnna zauna ki sha mamakin wata magana tukuna.’ Ta kuwa zauna baki sake, sannu a hankali Imam ya warware mata komai, tuni hannunta ke kirji. ldo waje ta mike tsaye, ‘Me? Ta karasa da salati, tana tafa hannu. ‘ ‘
A hankali ta dawo ta zauna, jim, ta yi shiru ta ma . rasa abinda za ta ce. Abubuwan da zuciyarta ke ayyanawa game da ‘Sulaiman ba alheri bane a gare shi,‘ gara ma ,da Allah ya tsuke bakin na ta, ta kasa maganar. .lnna ta yi shiru, ya sa Imam ya ce.
‘ “Dama abinda muka biyo mu gaya’miki kenan lnna, daga nan kuma Kaduna za mu karasa, ga shi kin ce Maman tana tafe.‘ Ta cira kai ta dube shi ido taf Da hawaye ta ce; ‘Ku jira ta a nan ta zo sai mu wuce Kanon tare.‘ Ba zato hawayen ya kubce mata kamar famfo. . ‘ . ‘ Tausayin ta ‘ya lullube su, ‘Don Allah Inna ki daina kuka…… Ta katse shi “ldan ban yi kuka ba, me ka ke so in yi Baba na? In fadi in mutu? Idan hawayen na basu zuba .ba, ina mai tabbatar maku dafin da‘ Sulaiman ya zuba min cikin zuciya ta, za ta iya bugawa in mutu nan take, kamar Sulaiman? Kamar Sulaiman? Ta kada kai ta sa zani ta gage hawaye, ‘Babu komai, ai ga karshen sa nan ya gani, bari in kawo maku fura ku
sha.‘
Ta mike. ba tare da sun iya cewa komai ba, saboda mutuwa da jikinsu ya yi, sabon katon furij din ta kirar (SAMSUNG) da dadewa Imam ya jingine mata shi, tana ta sana’ar kayan’sanyi, shi ta bude ta dauko
Kwanon shan ruwa a rufe ta kawo gabansu ta aje. Ta koma ta kawo kofuna kanana da Iudayai.
Ta motsa fura ta zuba masu,  Imam ya ce, “To sannu Inna.” Furar ita ce abincin farko da suka sanya a .cikin Su, sanyin ta ya sa Sukajidadin shan ta, domin ta samu nono mai kyau, da  kansa daka na furar.
Cikin bayi ta shiga da niyyar wanka, amma sai da ta ci kukan da ya ishe ta. saboda bakin-cikin da take tattare da shi, ji’ take ina ma ace ba ita ta haifi Sulaiman ba. Dole ta yi lstigifari, don ita kanta ta’san zuciyar ta, ta sako mata wani al’amari- mai kama da fushi da yin Ubangiji.
Ba ta gama shiri ba. Mama ta iso da direba da su Ummi tare da Hafsat. Tun daga waje da ta ga motarsu, shi ya sa ta karasa cikin gidan da hanzarin ta, ta yi sallama, duk suka amsa tare da fitowa don tarbar ta. Bayan sun natsa a daki, sun gaisa ta tambayi masu jiki hade’ da yi masu murnar ganin barayi da tsabar kudaden da suka karba.
Nan take ‘Inna Mairo ta ba ta labarin sanadin batar Alhaji, ko kafin , ta karasa kuka ya rufe mata idanuwan ta, ta shiga sharar kwalla, yayin da Mama ke
. ta maida salati. Kai ba ta yarda ba, kara tambaya take yi.
“Sulaiman da Jamila fa ku ka ce? Anya ba sharri suka yi masu ba? Inna Mairo ta goge hawaye da sauri~ ta
‘ ce, ’“Haba Hajiya Suwaiba, wane irin sharri, bayan ga tabbacciyar hujja Da alama kina mamakin wai Sulaiman ne zai aikata wannan aiki? Lallai manta shi ki ka yi, domin Sulaiman ya dade da bayyana mummunan halayensa a zahiri.”
Ta ci—gaba; “Amma babu kamar wannan a iya tunaninki ba’ Ni kuwa a nawa nazarin fiye da haka ma Sulaiman zai ,iya aikatawa, gara ‘Yan Sanda su harbe
mana shi tun kafin ya fara sawa ana bin mu daya bayan daya ana yankawa.” ‘
“DOn, Allah ki ‘daina masa wannan fatan Mairo kin ga kar eana ta yi, ya kamata mu tashi mu kama hanya-” Ta Cc, “A gaskiya ni yanzu ba jikin su Suleiman zanje dUbaWa ba, shawara zan je mu yi da dan~uWana‘ Bai kamata mu rinka wahala da makiyin mu ba, zai fi kyau a damka su hannun hukuma.” Mama ba ta ce komai ba, haka zalika su Imam. ‘ .
Motar su Imam na gaba, direban su Mama na biye, kowa jiki babu kwari, hatta su Ummi zukatan su na cike da mamakin abinda su Jamila suka aikata, ganin sa suke yi tamkar a shirin fim. Lafiya lau suka iso Kano. Suka ‘wuce asibitin’ na Dala, haka suka iske su AIhaji zuciya babu sukuni Gaba daya fuskokinsu. tashin ’ hankali ne bayyané, bayan an yi wa juna barka da zuwa da gaishe—gaishe.
Alhaji Abdul-Ra’sheed ne ya fara bayanin halin da Sulaiman ya tsinci kansa bayan tafiyar su Imam, daga ya gaya masa an kama barayi. Inna Mairo ta yi caf  Ta ‘cafe, “Madalla, saura Jamila, wannan shi ne sakamakon maci Amana, butulu.’
Ya zura mata ido, “Da a‘ka yi me? Ta nuna
Sulaiman’da ke kwance yana ta sharar barcin lalura ta ce, “.Wannan shi ne barawonka, tare da wancan karamar maras kunyar, me ake da ‘haihuwar wannan yaron. Haihuwar asara da…. ‘ ‘ Mairo ya daka mata tsawa, sai da kowa na wurin ya razana, “Kin yi hauka ne ki ke irin wadannan kalaman ga-dan ki? Komai ya yi, ba ki iya hadiye bacin‘ ran ki? Ta Ce, “Ka yafe ni Yaya, amma ba zan iya shiru ba akan butulcin Sulaiman.” Ya gyara zama ya ce, “To wai ma me ya yi ne? Ban fahimci shi ne barawo na ba?. Ita ma ta gyara zama ta ba shi labarin da aka ba ta.
Shi kansa sai da ya dauke wuta, ya kasa cewa Komai. Murja ce ke ta salati, kuka ya kwace mata ta “shi tsam tayi Ta bar dakin ta nufi dakin da Jamila take, “ita ma barcin take ta yi. Ba ta bata lokaci ba, ta shiga “maka mata mari, ta ko’ina, ji ta yi an riko hannunta,
’ yayin da Jamilar ta farka a gigice tana fadin.
‘Menene Umma? Me na yi miki‘? Hajiya Suwaiba
ce rike da hannun Murja ta ce, Menene haka Murja? Wannan abu fa ya riga ya faru, babu yadda za mu yi, sai
dai mu rungumi kaddara, ki tausaya mata halin da take
ciki.’
Ta nemi Wuri ta zauna, ta rike kai hannu biyu tana salati, “Wai me na yi mata ne Maman mu? Jamila ta tambaya, hawaye‘ na ‘zubar mata, duk da cewar ta
san abinda zai‘biyo baya, tunda aka ce an kama barayin Alhaji. Hajiya Suwaiba ta dube ta, “Iskar duniya ta debe ku da yawa Jamila.- Bana mamakin ta ki wautar, saboda mahaifin ki kan sa shi ya jagorance ki.
Tabbas Sulaiman ba uba bane, ko alama bai cancanci matsayin uba ba, domin shi uba wani Mutum ne da‘ ake sa ran zai yi jagoranci bisa tarbiyya ingantacciy‘a. Shi ne Zai sa ido duk wani motsi na lyalinsa. ‘
_, Don ganin ba su kai kan su mummunan matsayin ba. Shi ne zai tsare dukkan hakkokin Ubangiji, don ganin ba’a taka su ba. Sannan shi ne mai kauda duk wata barna, don ganin ba ta yadu ba zuwa dogon zango har ya kai ga wasu al’umma sun gurbata sanadiyyar rashin ingancin iyalinsa.
” Sulaiman duk ya rasa wannan, shi ya sa na Ce shi ba uba bane, kawai dai ya haife ku ne’irin haihuwar’ dabbobi. Ga shi a karshe ya sanya ilahirin iyalansa a nadama tare da dana-sani. K0 ban fadi ba, kin san abinda ku ka aikata Jamila, amma ki sani haryanzu ku
jinin mu ne, ba mu da bolar jefa ku, sai. dai kowane
bawa abinda ya shuka, shi yake girbewa. Wannan kadai
ya ishe ku ishara.’ Jamila kuka take yi tana karawa, kunyar duniya
ta rufe ta, ta rasa lnda za ta sa kanta. lta kuwa Mama daga ido ta yi ta ga dakin cike da jama’a. Ashe tun fara jawabin ta duk suka shigo dakin, kowa ya kara sanyi, hatta Ummi da Hafsat kuka suke yi
Ba karamin razana su al’amarin ya yi ba. Inna Mairo ta fara magana “Zancen ki dutse Hajiya Suwaiba,  ai shi mara gaskiya, koda yaushe dole ya yl wa bakin~ ciki marhabin. . ‘
Dalilin da ya sa kenan suka tsane ni lta da ‘yan~ uwanta. Ko waje na ba sa son zuwa, bai dame ni ba, don na ga shi kansa ‘wanda’na yi wahalar clkinsa, na yi nakudarsa ya fito duniya, na yi dawainiyar goyonsa, bai damu da niba, ina ga wadanda’ uban su kawai na haifa? Idan da gaskiya, menene na kwana hotel? Ina Zariya ina Kauran Juli da ba ‘za su iya karasowa su kwana ba? ’
Wannan kadai-ya isa ya bada shaidar ba’a shuka gaskiya ba, tunda aka gaya min abinda ya same, su, zuciya ta ke cike da tambayoyi masu takaici da bacin rai, amma yanzu damuwa ta ta” kare, amsoshi na sun Samu, babu abinda ya dace. ‘
Sai godiya ga Allah. Muna rokonsa ya kara tsare mu daga sharrin makiyan mu. Roko na shi ne, don girman Allah da son Manzonsa kar wanda ya hana hukuma yin aikin su.’ Ta durkusa gaban Alhaji ‘lna neman wannan alfarmar Yaya Don girman Allah ka cire hannun ka a…
Imam ya yi azama ya dago ta, “Mike Inna Ya maida ta gefe bisa kafet ta zauna. Alhaji ya yi shiru a zaune, gaba daya lissafinsa ya dagule, ba wai abinda
Sulaiman da ‘Jamila suka aikata masa bane ya fi
ba, a’a kukan da lnna Maito ke yi, da kalamanta su suka fi daga masa hankali.
Shekara da shekaru Sulaiman yana shayar da mahalfiyarsa gubar bacin rai. Shi ba yaro karami ba, balle a rufe shl da duka don ya gane ya yi kuskure, amma kamar Sulalman wanda ya ci ace yana da jikoki yanzu, duk da cewar an yi’masa auran wuri ne. kuma ya sami ‘ya‘ya mata, Shekarunsa‘sun kai ya yi hankali ya gene halin da duniya take ciki
Ya kada kai ya dubi Inna ‘Hakika Allah ya jarabce ki Mairo, idan kuma ba ki yarda ba, to laifin
‘daga gare ni ne. Ni ne ban ba Sulaiman tarbiya ba domin a hannu na ya girma.‘ Ta goge hawaye ta ce, ‘Ko
kadan kar ka dora wa kanka wannan laifin. Kowa ya san ka ba shi kulawa da tarbiyya’mai kyau. Ka ba shi dukkan gata.’
Ya ce “ldan kuwa kin yarda da hakan, to ki yarda Allah ne ya jarabe mu da shi, ki yarda babu daya daga cikin mu da zai iya daka‘tar da wannan kaddara, amma .imani da ita shi zai sa Allah yayi mana sauyi kuma ya ba mu ladan yin imanin ‘
Ina son ki maida komai tamkar tafiyar ruwa, idan ya wuce, ya wuce kenan,‘ sai dai a jira sabo, mu yi fatan za su sami kyakkyawar rayuwa nan ‘gaba, ba su
kare rayuwar su-a gidan yari ba Mai‘ro. Hankulan mu ba za su taba kwanciya ba.. ‘
Ba za mu daina bacin rai ba, domin ba za mu » daina tunanln halin da suke ciki ba. Ki sani su jinin mu ne. kamar yadda Hajiya Suwaiba ta fadi, mu yanke su mu jefar, ba ita ce mafitar mu ba, ina ganin ko ba’a hukunta .su ba. Ubangiji ya riga ya saukar masu da wata ishara. ‘ ‘Wacce na tabbata da za’a ba su zabi da gidan yari da ita wane ~za su zaba? Wallahl gidan yari za su
zaba da su rasa wani sashi na jikin su. Mairo ki kwantar da hankalin ki, kibar wa Allah al’amarin sa, kin ji?
Babu wanda kalaman Alhaji bai kashe wa jiki ba. Inna ta share hawaye ta ce, “Ba ni da ja a cikln jawabin ka Yaya, – amma -ko ka san duk tsawon shekarun nan da Sulaiman ya yi yana sheke ayar sa, bai taba cewa Inna yi hakurl ba? Ya ce, ‘Rashin gane kuskuransa ne; kuma da tun lokacin ya saduda, ba zai aikata wannan abin ba. Da yardar Allah wannan zai
zama na karshe, ki yi hakuri Mairo.” ‘ Ta kada kai ta ce “Allah ‘ya sa. Hajiya Suwalba ki yafe masa. Imam ka gafarta wa ‘yan—uwanka.” Ya ce “Kar ki damu Inna, fatan mu kaWai Allah ya sa wannan ya zama na karshe.” Ta ce “Dole, idan ma ya rayu kenan, in kuma ta Allah ta kasance, shi kenan an huta da fargaba.
Sai mu ce Allah ya yi masa afuwa, ke kuma ta rage ta ki, kin dai ga yadda duniya ta mirgina ki, cikin wata irin makaranta, wacce ba ki taba zato ba, ya rage na ki ko ki saurari karatun gaskiya ko karatun shaidan.”
Daga can inda take kwance murya na rawa take magana “Ku yi hakuri, ku yi hakuri don Allah. Ni Wallahi Dadi ne ya zuga ni, tun daga kin auran Yaya Imam har zuwa abubUwan da suka faru yanzu, duk umarnin Dadi
na ke bi. Baba ka yafe min. Yaya lmam.ka yafe min, don Allah kowa ya
gafarta min! Ta ci-gaba. da kuka. Alhaji‘yana fadin, “Komai ya wuce Jamila, muddin kin‘yi tuba sahihi. Allah zai taimake‘ki, ya nisanta ki ga dukkan sabo. Babu abinda yakamata da ke, face ki yi ta Istigifari, kin ji? –
_ Ta ce, “Na ji Baba, na gode. Yaya Imam ka yafe mini-Ya ce “Na yafe Jamila, ina miki fatan alheri tare da addu’ar Allah ya sa tuban ki na gaskiya ne.” Ta ce
“Ban taba. sanin haka duniya take ba, sai yanZu. Ashe haka take ba ta da tabbas?
K0 sau daya Dadi bai taba’gaya min ba. Umma
Kadai ke gaya min in bi a hankali, sai dai ba na damuwa da maganarta, saboda na fi son- zugar Dadi. Zancensa yafi min zaki da dandano mai dadin saurare. Kaico na bani da. wata riba a rayuwa ta, ta duniya.“ .
Wani kUlulu ya tsaya wa Imam a wuya, yana jin tausayin ta, amma bakin halinta ya sa idanuwansa ‘ke ganin duhun fuskarta, don haka ya mike ya bar dakin, Alhaji ya ce, ki daina fadin haka Jamila,~in har kin yi tuba na gaskiya rayuwar da za ki yin nan gaba ita ce za ta zama riba a gare ki. ‘
Mudansir ya mike ya biyo Imam yana fitowa wata nos na isowa a sikwane, ku 20 patient din ku ya farka‘. Mudassr ya leka dakin ya-gayawa saura duk suka
fito suka koma wajen sa. Likita na tsaye gefensa yana gudanar da aikinta. .
Suka tsaya cirko cirko har ya kare, ka na ya ce jinin ya dan saUka, idan akwai abinda zai iya ci a ba shi nan da rabin awa zai sake komawa barcin, duk suka amsa da to dakta, mun gode.
Bayan ya fita suka zagaye shi ya rinka kallon su daya bayan daya. Alhaji da Mama kadai ke masa sannu. Ganin Zai fara hawaye ya sa Alhaji ya ce kowa ya je ya sami waje ya zauna. Imam da Mudansir masu ficewa suka yi daga dakin, Mama ta hada masa shayi’ta yi ta yi ya sha amma ya ki, kwararar kwalla kawai yake yi, cikin wannan halin‘barci ya sake dauke shi.
Har ya yi barcin babu wanda ya yi masa magana saboda Alhaji ya hana kowa ya kara daga masa hankali don a samu jinin na sa ya ci-gaba da sauka, amma shi cikin zuciyarsa ya san asirin su ya gama tonuwa, tunda . aka kama-barayin, shi ‘ya sa ya kasa sukuni yake ta zubda hawaye, kamar karamin yaro
‘A wannan yammacin su Imam suka koma Kaduna da Mama. Haka Asma’u da Hamdiyya suka
kwana’al’ajabin wannan al’amari mai kama da almara‘ Lallai duniya ta gangaro karshe, abubuwan da ke faruwa cikinta kadai sun isa misali ga mai hankali Kowa ya ji abinda su Sulaiman suka aikata.
Sai ya yi tir! Da halinsu, ‘musamman ‘yan uwansa, watau Raliya da Asabe. Can dangin mahaifin sa kuwa,‘ har ma sun manta da shi, sai da wannan maganar ta bullo ne, sannan suka tuno shi, kuma suka bi shi, da shaidar banza. (Ina amfanin wannan rayuwa. Kowa ya cemaka tir?).’. ‘
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
BAYAN WATANNI HUDU
sati biyu da sallamo su Sulaiman daga asibiti. “ Babu kafafuwa, babu baki kuma gefen jiki a ‘ shagube. Haka ita ma Jamila ke zaune da kafa daya. Gaba dayansu Imam ne ya siya masu tsadaddun kekunan guragu masu rimot a jikinsu.
Karfe bakwai na safiyar ranar litini a yau. Jamila ce kadai idon ta biyu a cikin gidan, zaune take cikin kekenta tana rubutu a .wata ‘yar takarda, bayan ta kare ta ninke ta dora bisa madubin su. ~
Sannan ta latsa rimot din keken ta ya gara ta
zuwa kicin kai tsaye galan din ka nanzir ta dauko ta bude, ta yi jim, shiru tana sharar kwalla ka na ta rufe ido, ta daga galan din ta sha iya shan ta, ta aje galan din gefe. . Ta garo keken falo da kyar, ko kafin ta karasa dakin su ta tiko kasa, tana wani irin kakari da tari mai tsananin gaske. Karajin ta ya farkar_‘da Umman su. Ta tashi firgigi tayo waje don ganin wake kakarin mutuwa kuma a cikin gidan?
Jamila ta gani warwas! Tana asa—asa. Da karfi ta kwala mata kira, sai da kowa ya farka daga barci.
“Baban Jamila zo ka gani. Jamila ta kashe kan ta  “Inna—
Liilahi’wa-Inna-Ilaihir-Raji’un! Su Ummi suka yo waje su ma suka fasa kuka da kururuwa.
Hakan ya kara gigita Sulaiman ya yi ta kokarin yadda zai dora kansa bisa’ kekensa, abin ya faskara
sab0da gefensa na dama baya aiki, ga. babu baki bale
ya kwala kira, shi ma a. zo a taimake shi Bakin-ciki
kamar ya kashe shi. Take nan ya fasa kuka.
Cikin rudani Murja’ ta koma ‘ dakin tana sallallami, “Shi kenan Jamila ta hallaka kan ta, ta sha Ka nanzir Baban Jamila ya za mu yi akai ta asibiti? Ya zuro mata ido, yana nuni da daya hannunsa alamun ta Kira waya. Sannan fa tunanin ya zo mata.
. Da sauri ta suri waya kai tsaye Mama ta kira cikin kuka take gaya ‘mata abinda ke faruwa. Mama ta rude ta  kira Alhaji. Nan’da nan suka kwashi direba sai gidan. Tana kwance kumfa kawai ke hauhawa bisa bakinta. Mama ta fasa kuka, “Me ya kawo wannan masifar kuma ni Suwaiba? Jamila nada hankali kuwa?
Haka take ta fadi har asibiti aka bata gado, ka ‘na Alhaji ya kira su Imam misalin karfe tara saura. Imam ya tallafe goshi. ya ce a ‘ransa, “Kai jama’a‘
‘ wannan wace irin rayuwa ce? Shi ma Mudansir haka ya fada al’amarin ma ya koma ya ba su’haushi. Haka nan suka rankayo asibitin tare da matayensu.
Kowa tambaya yake menene dalilin kashen kanta. Kamar wata maras imani? Babu wanda ya san amsar cikin su. Shi ya sa abin ke ci-gaba da bata masu rai, shi kansa Sulaiman da‘ke gidan bakin-ciki ya kusa hallaka shi. Likitoci na ta iya kokarn su ‘wajen kashe mata gubar data kwankwada.
‘ Can Kauran Juli kuwa. Inna cewa ta yi “Iskanci ne kawai don kar su bar mutane su huta. Shi-ya sa ta ki tada hankalin ta.” Ta yi zamanta ta ci—‘gaba da sabgoginta. “lta ta sani, idan ta mutu, ta mutu kafira, ta
je can ta yi wa ma haliccinta bayani. Al’amarin ba haka .yake ba a can Kaduna.
Sakamakon takardar‘ da Hafsat ta gani bisa madubinsu, sunan Imam ~ne bisa takardar, don haka shi ta mika wa takardar da yamma likis, bayan sun dawo ofis _suka biyo su duba jikinta. Har yanzu numfashin ta a sama yake.
Ya dubi Hafsat ya ce, “Ta ‘mece ce Hafsat? Ta ce “Akan madubin mu na ganta.’.’ Ya warware. ya fara karantawa. “Na tabbata-hukuncin’ dana yankewa kai na  . ba zaiyi wa kowa dadiba, musamman kai Yaya Imam.
Na .‘san ka na so na mai yawa. . ‘
Bakin halin da Dadi ya cusa‘ min, shl ya sa ka tsane ni, ban ga ’laifin ka ba, domin nl ma na tsani kai na a yau, tsananin kunya da nadama sun sa ba zan iya . ci-gaba da rayuwa a cikin ku ba. ‘
Ba na son kowa ya ganni ya ji gabansa ya fadi Saboda mummunan alkin da muka aikata. Ba na son fuska “ta ta zama wani littafi mai dauke da tarihi, da zara’r an ganni. Ba na son ka’ci—gaba da kashe miliyoyin kudin ka a kaina ‘Yaya Imam. Kafafuwan da ka ke so ka siyo mana ba su da wani amfani a gare ni, ka gama min komai Yaya Imam, tunda ka so ni lokacin da na ke ganin na fi karfinka.
Sannan ka taimake ni Iokacin da duniya ta koya min hankali, ka sani zan mutu da bakincikin rashin ka, domin tun ranar da ka ce ba za ,ka‘ aure ni ba, na tabbatar da ‘cewa ba zan taba samun mijin aure ba, saboda kai kadai ne ka nuna min soyayyar da babu wanda ya taba nuna min irin ta.
Yaya Imam ka yi hakuri ka yafe min, na san nayi zunubi mai ‘girma, wannan hanya da na dauka ta kashe kaina da kaina. Wallahl ba ni da zabi ne, alhalin ina son in nisanta kai na da kowa. Musamman ma kal, ka yI min alkawari kullum za. ka roka min Allah ya yi min
rahamarsa. ka sani shi mai gafara ne. kuma maijin kai. sannan ka roki kowa ya yafe min kuskure na, na barka da alhéri Yayanal.‘
Idanuwansa suka kada jawur! Hawaye ya cika su taf Ya dubi Mudansir ya ce. “Mu je gida Muda.” ~Ya matso shi’sosai ya ce, ‘Menene Yayana? Ya mika masa takarda, ya karba ya karanta. Shi ma shiru ya yi tsaWon lokaci, kafin ya ce‘Me ya sa Jamila ta zabi ta kashe kanta’? Gani take ba’a yafe mata bane?
‘ A kasale ya ce,» “Oho, ni Wallahi na- ma rasa abi‘nda zan ce. Mu je gida kawai hankalina kara tashi yake yi, idan ina ganin ta.” Ya mike suka sallami Murja suka bar asibitln.
Tun _ shigoWar sa Asma’u ta gane yana’ cikin damuwa, tana tambaya, ya mika mata takardar Jamila,
. ta karanta ita kanta sai da ta nemi wuri ta zauna shiru tsawon lokaci kafin ta ce, “Sam—Sam bai kamata Jamila ta yan’ke wa~kanta wannan hukuncin ba. Kuma tun farko sai da na gaya maka, idan ka aure ta, ba‘karamin taimakon ta za ka yi ba.”
‘Ta numfasa tana kada kai, “Haka Allah ya so, kuma .Shi zai duba mana wannan al’amari, fatan mu ta samu kubuta kar wannan guba ta zama sanadiyyar rasa ranta.” Ya ce. “lnsha—Allahu Jamila ba za ta‘ mufltu ba; ta wannan hanyar.” Ta ce “Allah ya amsa.”
Kwana Uku babu fashi dare da rana addu’a yake, yana rokon Allah ya kubutar da Jamila daga kangin kuskuran da” ta tafka. Har cikin dare baya runtsawa,
_ .face ya yi nafila ya mika kukansa ga Allah.
A rana ta hudu cikin ikon Allah Jamila ta farfado, sai dai idanuwan ta ne kadai a bude ba; Ta iya motsa ko’ina a ‘jikinta, sannan ba ta iya furta komai farin-ciki ya lullube kowa. ‘
Musamman Imam. Ana gaya masa ya aje ayyukansa ya nufo asibitin ya ja kujera gabanta.‘ ya
zauna. ya zuba mata ido. kafin ya kira ta a hankali, ta jima ba ta bude ido ba. jawur Suke kamar garwashi, su kadai ya isa Mutum ya tausaya mata.
_ Nan da nan hawaye suka ‘goce mata, ya mika hannu ya yago tishu ya share mata, “Ban ji dadin abinda ki ka aikata ba Jamila, duk abinda ki ke ji cikin zuciyar ki game da abinda ya faru, ai ba zai taba kai azabar Allah ba, don‘ me za ki mutu kafira, bayan kin ce kin tuba, kuma an yafe miki? ‘ ‘
Wa ya gaya miki ba mu yarda da ke ba? Kuma wa ya gaya miki kowa ya tsaneki ba haka rayuwa take ba Jamila, duk wanda ya yi tuba tsakani da Allah, baya kokarin sake aikata‘wani laifin, ki na son ki nuna min ba sahihin tuba kika yi ba kenan? lye? Ban amsa.
Ta kada kai hawaye na kwarara, “To ki tubaki sake komawa ga Ubangijinki. sannan ki yi masa godiya da ‘bai dauki ranki ta hanyar gubar da ki. ka sha ba. lallai Allah yana son ki da rahma, saboda haka ki daura dammarar tuba daga yanzu har zuwa karshen rayuwar ki. Haka ne kadai zai sa ki dace da babban rabo.
Bayan kin karasa’rayuwa mai’ amfani. Sabanin abinda ki ke zato ki na ganin rayuwarki ba ta da amfani, wannan babban kuskure ne, kar ki sake, kin ji? Ta runtse ido hawaye suka ci-gaba da tsiyaya. Ya sa tishu ya share, “Ya isa haka kuma ina miki albishir da cewa har yanzu ina son ki Jamila ……
Da-sauri ta bude idan‘uwanta ta bi shi da kallo, ya yi dan murmushi ya lumshe ido kadan ya bude, kafin ya sake fadin, “Kowa ya san ke matar Imam Ce, tun ina miki tsarki ina share miki majina. Wani irin dadi ya kwarara‘cikin zuciyarta, ta fara murmushi, a lokaci guda kuma wasu sababbin hawaye-suka tsinke mata.
Na ce “Ya isa k0? Ki daina kuka, yanzu gaya min ina ke miki ciwo? Ta ta’ba cikinta ya ce, cikin ki? Ta amsa da ka, ya ce “Sannu, kar ki damu likitoci nata
Insha—Allahu za ki tashi. aiki na son zama dani . k0 ba kya so? Ta yi murmushi tana kallon sa. “Yakamata ki yi” min magana in ji?‘Ta saukar da ido ba ta San me ya “hana ta magana ba, itama kuma tana so ta ce wani abu, amma ta kasa. Ya, jima‘tare da ita yana kwantar mata da hankali. . A wannan ranar kowa sai da ya zo duba‘ta. kuma sai ta roki gafara, hatta Sulaiman sai .da ya sa aka kawo shi ya duba ta, suka yi ta kuka Suna sa mutane yi |nna ce kadai ba ta zoba, don haka imam ya kirata a waya. Ya roke ta da ta zo ta duba jikin ta. . Washe gari kuwa ba ta yi kasa a guiwa ba, da sassafe ta iso Suka yafijuna. Al’amarin dai gwanin dadi. , Jamila na ta Istigifari cikin zuciyarta. Da zarar lokacin sallah ya yi za’a yi mata alwala ta yi sallar ta a kwance. Tsaw0n kwana biyu bayan farfadowarta, cikin ya fara kunbura kO dama yana mata tsannanin ciwo. Nan da nan Likita ya sa aka kara yi matawasu (Scaming) din. * Abin da Likita ya gani. shi kansa ya yi shakkar gaya wa ‘yan-uwanta, don hakaya yi shiru ya kara mata
wasu magunguna, sannan ya rage wasu. Amma ya ‘,
‘tabbata Jamila lokaci kawai: take jira, domin ilahirin kayan cikinta sun sami matsala har wasu sassa na hanjinta sun huhhuje, ga hanta ta kunbura.
‘ lta, kan ta Jamilar zuciyar ta na gaya mata mutuwa 2a ta yi. shi ya sa take kara azama wajen ,lstigifari kamar yadda Imam ya ke gaya ‘mata, duk iokacin‘ da ya 20 duba ta. abinda ke kara faranta mata .rai. Baya rabuwa’da ita. face ya gaya mata yana son ta, kuma ita matarsarce tun ‘yana’mata tsarki yana share mata majina.
A wannan daran Jamila ba, ta kwana ba. Kafe ukun dare ta ce ga garin ku. Ummanta ta.ga abin
alaJabi abin ,fa’rin-ciki. domin har Jamila ta daina
numfashi bakinta na fadin Astagfurullah, tare da Salatin Manzon rahma ($.A.W). Kafin takwas na safiya an kai ta kushewar ta‘
wannan mutuwa ta daki zukata ba kadan ba, sai dai kowa godiya yake wa Allah da‘ ya sa Jamila ta ‘yi kyakkyawar cikawa, saboda haka suka yi ta bin ta da addu’ar fatan samun dacewa.
mutuwar Jamila ‘_ta kara jaddada -imanin Sulaiman, ya zamana( babu komai cikin zuciyarsa face nadama da tunanin yadda zai bi
ya karasa rayuwarsa, cikin ’kwanciyar hankali. Da kansa
ya ‘tara sauran yaranSa da mahaifiyarsa, ga Alhaji da,
iyalansa a zaune. Ya mika doguwar takardar da ya rubuta ga Imam, ya sa hannu ya warware -ta ya fara karantawa kowa na ji. . ‘ ,
“Bayan sallama irin ta ‘addinin musulunci, ina » mika godiya ta ga kowa da~ku ka amsa kira na, na tara ku ne don na ga ya cancanta’ in yi hakan, sabo’da wasu dalilai’maSu karfi. _’ ‘
Da farko don in bayyana kurakuran da na aikata can baya, wadanda suka nuna zahiri ni ba kowa, bane face butulu. ‘Na zama kaza ci‘ share ‘baki, akan dawainiyar da Baba ya sha da ni. ‘
Tun ina yaro karami, ni kaina idan na zauna ina‘
tunani a halin yanzu, ni kan tsinci kai na cikin mamakin ‘yadda aka yi na aikata wadannan munanan halaye. alhalin Baba ya ba ni dukka nin tarbiya ta-gari ya ilmantar da ni karatun addini da bako, sannan ya nuna min ‘hanyoyi masu kyau ta nasiha da hannun ka mai sanda. Baba ka yafe min ka yo min afuwa. hakika na tsinci kaina cikin ribatar shaidan.
Na biyu gare ki zan waiwayo Inna. ban san me zance ba, domin laifuka na bayyanannu ne gare ki, shi ya sa idan na tuna girnan su, ni kan ji kamar in aikata
abinda Jamila ta alkata.,Amma Allah’ya taimakeni ta ‘ “kuubutar da ita mutuwar kafirci.
Sal ina ganin Kamar da sauran fushi na a clkin zuciyara ki Inna. Shi ya sa Allah ya sake jarabta ’ta da tashin hankalin abinda Jamila ta aikata, don Allah Inna ki taimake ni, ki wanke ko’ina na zuciyar kl, ko na sami sukunin rayuwa. ‘
Na karkato gare ka Imam, sai dai ban san ta’ ina zan fara ba, saboda ban san radadin karya zuciya ba akan soyaWa,misali kawai na gani a kan ka, kiris! Ya rage
‘ rayuwar ka‘ ta rushe ta Ialace, amma da yake ba‘ ku da hakki na, sai Allah ya taimake ka, ka zama Mutum kuma tamkar dubu, duk da haka ban kyale ka ba, na ci—gaba da cin dunduniyar ka, alhali gaba daya nida iyalina da kai muka jingina. ‘ ‘
Na rasa wanda zan sa aci zarafin sa, sai mutumin, da ya yi min komai, na rasa wanda zan damfara, sai mutumin da ya karbe mu bayan duniya ta hore mu. Kai! Da wane ido zan rinka kallon ka Imam? ldan ba ka yafe min ba, lallai zan rasa rabon lahira kuma Allah ba zai daina jarabta ta da masifa ba anan duniya, kafin in koma gare shi. – ‘
Murja ta shakl bakin-cikin taurin kai na da rashin
‘ daukar shawarada takaicin rashin tarbiyyar ‘ya‘yanmu, ina rokon ki ki yafe min. umml da Hafsat ku‘yafe min, ni na rushe fayuwarku, ni na hana ku aure, duk abinda ya sami‘ ‘yar-uwarku nine sila. ‘
A yanzu kam ina takaicin wannan rayuwa da na yi. Rokon da na ke gare ku, shi ne ku ji tsoron Allah ku aje duk abubuwan da ku ka koya, ku natsu ku taumaki kan ku da addu’ar Allah ya kawo ma ku mazajen kwarai, ku aura. . A karshe ina yi ma ku Wasiyya da ku daukl Imam . a matsayin uban a gare ku, duk wacCe ta tsallake umarninsa, ku san ban yafe mata ba, wannan shi ne dalilin
tara ku, ku yafe min Ku yafe mini Ku yafe_ min!!!
Imam ya dubi Alhaji idanuwar jajur! Ya ce ‘Ka ji abinda ke ckin takardar Baba.‘ Alhaji ya numfasa. yayin da su Mama ‘da Inna da ,sauran matan wajen ke share  ya taso ya dawo kusa da Sulaiman ya zauna, kafin ya yace
“Ban taba zaton ka na tunanin ba’mu yafe maka ba Sulaiman, me zai sa mu rike ka a zuciya, bayan mun sanillar yin hakan?-Wannan magana ta wuce har abada. ba na so ka sake tada ta. Mun yafe maka Mun yafe maka!! Mun yafe maka!!! .Amma ban sani ba k0 lnnar ka “na’da abin cewa?
‘Ta kada kai ta, ce .‘Ka gama magana Alhaji, bani da abin karawa sai dai in ce Allah ya yi masu albarka, ya ‘ inganta rayuwar su‘ ta nan gaba.” Ko’wa ya ce ‘Amin Summa Amin’. Imam da Mudansir suka taso suka rungume shi tsawon lokaci, ka na suka dago suka dube shi. ‘ Imam ya goge masa hawaye ya ce, ‘Nan da sati biyu. kafafuwanka- za su iso. lnsha—Allahu; Za ka yi tafiya kamar da, na tabbata zai rage maka radadin rashin wani ’sashi na jikin ‘ka, hair abada mu kannenka ne, dole mu kira ka Yaya! Ya sa hannunsa mai lafiya ya sake jawo su ya . ,rungume, hawaye ya’cigaba da digar masa.
Bayan an natsa. Alhaji ya ce, “Alhamdulillahi, zama ya yi kyau, sai dai ba za’a tashi ba sai na yi tunsarwa akan matsalolin mu a yau, daga cikin Su shi ne son kan mu da ya yi mana yawa a zuciya, a ha‘kan shi ya haifi hadama da babakere, kowa kokari yake ya tara ta kowa ne hali. Daga nan ne cin’rashawa da hanci suka saki ras’san su, suke ta  gurgurar zukatanmu har suka yada furanni masu yawa.
A karshe ‘ya‘yan rashinAmana ~suka yi dandazo cikin ayyukan . mu, gwanin takaici babu inda zaka .kyankyasa ka ji sanyi, sai ka‘yi dogon zango. Anya? ina za mu je da rashin tsoron Allah? Bayan ya zo a Hadisai da Ayoyin Al’qur’ani ce’wa rashin Amana yana daya daga cikin alamomin tashin kiyama.
Wata rana Manzon Allah (SAW) yana bisa munbari, wani cikin Sahabbai ya yi masa tambaya yace .ya Rasulallah, yaushe ne tashin kiyama? Manzon rahma, ya yi shiru bai amsa ba. ‘
Wasu suka ce. Bai ji tambayar bane, wasu suka ce ya ji tambayar ce bata yi masa dadi ba, sai da ya kare wa’azi, sannan mai girma da daukaka ya ce, “Wanene ya tambayi tsayuwar kiyama’ Sahabin nan ya mike ya Ce, “ni ne ya Rasulallah.” Manzo rahma ya ce, “Duk lokacin da – aka nemi Amana aka rasa a ‘tsakanin al’Umma, to ku
‘saurari kiyama ta kusa tsayawa
Allahu Akbar To yanzu ina Amana take? Dan-uwa da Dan—uwa babu amana, miji da mata babu amana, kasuwanni babu amana, kotuna babu amana, ma’aikata babu amana, shugabanni babu amana, talakawa babu amana. Babu amana Babu amana Babu amana!!! Duk‘ wannan zubar da‘jinin da ‘ake yi rashin amana ne ya jawo shi, da akwai amana ba za’a hada baki da musulmi Dan— uwanka a kashe ka ba.
Da akwai amana da ba za’a hada baki da kabilarka a kasheka ba. Da akwai amana Wallahi ba za’a kafa wata kungiya da sunan addini a rinka ta’addanci ba, me muke so mu zama ne jama’a? Yakamata mu gane Allah daya ne.
Kuma zai hore mu a bisa abubuwan da muka aikata tun a nan duniya. Saboda haka ina mai jawo hankalinku da’ku zama masu rikon Amana a duk inda ku ka tsinci kan ku. Daidai da kwayar zarra ‘karka ha’inci wani. Allah ba zai kyale ba, ina fatan kowa ya ji-ni da kunnen
‘ basira.”
Babu wanda bai share hawaye ba, gaba daya jikin su ya mutu, musamman Suleiman. Kowa ya tofa albarkacin bakinsa, aka rufe taron da addu’a. Gida su lmam suka aje su Alhaji, sannan suka wuce ofis, tun daga ranar ‘Ummi da Hafsat suka shiga lslamiyya, natsuwa sosai ta zomasu tamkar-ba su ba. Al’amarin ya yiwa
kowa dadi. Alhaji Imam kuwa ya kara dammarar inganta rayuwarsu.
~~~~~~~~~~~~~~~~
bayan wata uku Hafsat suka daidaita da Jibo direban Alhaji, abin…kamar wasa sai ya tabbata gaskiya. ,. ‘ Imam ya ce al ba’ayl haka ba Hafsat ta tafi ta bar Umml, ‘alhalin ita‘ ce babba, don haka ya. turo mata Auwal daya daga cikin Akantocin sa ne. Ba-ta yi musu ba, nan take suka fahimcir juna, ba’a hade watanni hudu ba, sai da suka angwance. ‘
‘ Alhaji Imam ya kashe masu kudi ba na’wasa ba sannan ya ba kowanne Ango gida da mota. Hankalin kowa ya kwanta. Amare‘ suka yi‘ zaman su lafiya kuma ba su daina zuwa lslamiyya ba, shi ya sa-zaman su gwanin dadi tare da ma_2ajen su
Al’amarin yana yi wa Alhaji Imam dadi, idan ya _ duba ya ga duk wata baraka an dinke ta. Zumuncin su yana ta tafiya yadda ya‘kamata, tun daga gida Kaduna har Kankiya. Ya’kan ‘daga hannu ya ce‘;
“Allah mun gode maka da rahamarka. Ya Allah ka kara wa Baba da Maman mu tsawon kwanan masu, albarka! Alhaji Imam kenan wanda jama’a kewa kirari, mai asin da asin har ma da gyalen yafawa. , , ‘
. Lallai babu babbar makaranta kamar duniya. Mun ga misalai da dama a cikin wannan hikaya. Saura abinda ya rage mana kawai, mu yi koyi da kyakkyawa,‘ da yardar Allah za mu sake haduwa‘ a Wani sbn book din

masu buqatar jin maimaicin book din saisu biyoni WhatsApp

@08035453572

naku har kullum

www.littafanhausane.com.ng

About AIS

Check Also

Makaranta duniya chapter 28

Makaranta duniya               Chapter28 sati biyu murja tayi a kankiya ta dawo hankalintatashe, saboda halin …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *