[Advertisements⬇️]

Makaranta duniya chaptwr14 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Makaranta. Duniya

         Chapter14

Alhaji yace “Ka daina fadar haka Magaji. Ni ban yiwa dayansu Allah ya isa ba, tsakanin Alhaji Bara’u da Mr. Bulagun. sai dai na ‘mika al’amari na wajan Allah ta hanyar yin imani da kaddarar da ya saukar min. ‘
Tsautsayi na kan kowa. Allah ya sani zuciya ta na cike da alhini da tausayin Alhaji Bara’u da iyalansa Nasiru da Khalid. Rasuwarsu jinta na ke, tamkar yadda na ji rasuwar mahaifina. idan kuwa har hakan shi ne ya jawo wannan abu. da sai ince me ya sa na yi?” ”
Magaji ya murza makullin mota, ta tashi, yana fada cikin ransa. “Ni ban san irin zuciyar Alhaji ba. Baya damuwa da kansa, sai damuwar da ta shafi wani”. Ya yi ribas ya bar harabar wajen, ba tare da sun kara cewa juna komai ba.
Sun ci zangon tafiya mai nisa dunkum! Kamar kurame, kamar daga sama Alhaji ya ji kira “Baba!” Ya juyo ya dube shi. “Mene ne Suleman?” Ya yi dan jim shiru kafin. Yace “Shi kenan an bar maganar Murja?” Ya runtse ido, ya bude.
Yace”Suleman. yanzu ba wannan maganar bace a gaban muBa baka ganin abinda ya same sune’? Fatan mu Allah ya ba Alhaji Bara’u lafiya. Na gaya maka Murja yarinya ce, haka . kai ma, akwai sauran lokaci mai tsawo kafin a fara maganar aurenku. Muna addu’ar kafin zuwan wannan lokacin, komai zai daidaita da yardar Allah. Kar ka sawa ranka damuwa tun yanzu. . Ka rushe abinda ya. kamace ka, watau karatu. Ka sani, shi kadai ne ribar’ ka a rayuwar, kuma gata na karshe
da kowane da yake fatan samu. idan har ina da rai. da
karfina da dan abinda na mallaka. Sai ka samu ilimi tamkar yadda zan tsaya, sai ka samu Murja, in lokacin ya yi da karfin Allah. Saboda haka ka
kwantar da hankalinka, sannan kullum ka yi sallah ka roki Allah alkhairi. Ka ji ni?”
. Yace, “Na ji Baba, sai dai ina so ka yi min alkawari ba za‘ka manta da maganar ba har zuwa lokacin?” Ya zuba masa ido. yai murmushi tare da kada kai, ka na yace “Murja . , ta zauna a zuciyar dana. yaya za ayi in manta da abinda dana keso alhali ni ma ina matukar so da kaunarsa?” ‘  Ya sunkuyar da kai. yana dan murmushi. “Na gode Baba, shi kuma Abba Allah ya ba shilafiya”. Ya amsa. “Amin, ,Suleman”. a Kauran Juli suka yada zango, shi Sulaiman barci ma kawai yake yi,.bai san lokacin da suka wuce .cikin garin Zariya ba. Mota na tsayawa, ya bude ido yana dube-dube, “Har mun kawo ne Magaji?”
Yace. “.Mun kawo mana”. Alhaji yace ina zai san an kawo yana can yana mafarkin Murja?’ Ya bude kofar da sauri. yana fadin “Baba …… ” Magaji ke masa dariya’. “Ashe Kaura muka zo  gaskiya naga  munyi sauri. yanxu goggo zata hadomu DA tuwannan Nata Mai daddawar tsiya
“Shi ka ci. ka girma yaro” lnji Magaji.‘ Alhaji yace “gaya ‘masa dai Magaji”. Suleman din ne ya saba lmam, don shi ma barcin ya tashi,, kuma ga gajiya. Magaji kuwa but ya bude, ya dauko leda mai kunshe da abarba da aya hade da
lemu suka wuce gidan. Ba zato. Gwaggon ta ji sallamar su tsakar gida. Ta tarbesu. “Kai! Daga ina haka da yammaci?”
Suleman ya aje mata Imam bisa jikinta. Yace “Daga Saudiya muke ‘yan mata”. Ya zauna gefenta bisa tabarma. Tace “Masha-Allah, to i’na tsaraba?” Ya nuna ledar‘da Magaji ya aje. “gasu nan!” Alhaji yace.
“Sannu gwaggo”. Tace “Sannunku da zuwa, daga ina?” Yace “Daga Kankiya …… ” Raliya ta katse shi “Sannu Baba!” Ya dube ta, “Raliya! Ana nan wajen Gwaggo ko?” Tace”Eh, ina yini?”
Ya amsa. “Lafiya Iau”. “Ya Mamanku’?” Tace “Kalau ‘ take”. Ta gaida‘ Yayanta, ta tashi-‘ta koma kicin. “Me kajeyi Kankiya?” Yace. “Labarin ba dadin ji Gwaggo. Nan take’ ya bata Iabarin iya abinda ya sani. ‘
Ta dora hannu aka tana salati. “Sun yi me Su Nasirun? “lnna-Lllahi’wa-Inna-IIahir-Raji’un!” Su Alhaji suka tsaya ta gama Salatin. Ta sada kai kasa tana girgizawa. ’Allah ya jikansu!” “Amin”. Raliya ta kawo masu ruwa.‘ “Gwaggi waya rasu?”
Tace “Nasiru da Khalid” ldo waje tace. “Su ‘ Nasirun ka Baba?” Ya-ce. “Su fa Raliya’. Ta yi salati ta sanar da Ubangiji. “Garin yaya?” Ya bata amsa. “Hadarin mota. shi ma Abban na su yana asibiti kwance”. Ta yi shiru tana ganin samarin a idonta. tausayi ya rufe ta, ta-ce “Allah ya
jikainsu”. . ‘ Kuwa ya amsa da amin. Ta jawo Imam ta zuba masa ruwa ya sha. Alhaji ya dubi Gwaggo ya-ce “gwaggo bari mu
yi harama, dama munbiyo mu duba jikin naki. ne KO  kinji sauki?” ,tace “Ah! Alhamdullllahi, ciwan kan .yayi sauki”. “yace Allah kara’lafiya, ga wannan, babu Yawa”. Tace, “Kar ka rinka matsa wa’ kanka don kaga yanzu ba kamar da bane. Allah ya‘ yi albarka”; “Amin”,
Kowa ya samu labar’in abinda ya faru, sai ya girgiza. Haka al amarin ya kwancewa Hajiya Suwaiba Kai. Ta jima shiru ba tare da ta yi koda matsi ba. Kai wannan rayuwa da
‘ ban tsoro take, ashe dama ba’a‘ bakin komai take ba? ‘
_ Yaushe zamu hankaltu mu gane lal‘lai rayuwaba ta da ’tabbas? Tunanin .da Alhaji ya tashi tsakar’dare yana yi kenan.’ Hajiya Suwaiba ta farka, ta hangoshi za‘une bisa kujera. Ta taso ta zauna gabansa
_ Tace. “Me ya sameka Alhaji? Dama ba ka yi barci ba?” Ya sauke numfashi. Yace “Na kasa yi Suwaiba, tunanin ‘Alhaji Bara’u ya hana min harci. Da zarar na runtse ido, shi na ke gani”. ‘
Tace “‘Hakika Alhaji .Bara’u da iyalansa abin tausayi ne Sai dai su suka dauki abin da zafi Alhajl. Yaya za’ayi hakki ya bar su? Ai bai kamata ba abinda Aliyaa ta yi koda, kai:ne ka yi wa mijinta laifi Sai a zauna abinciko inda matsalar take, a sasanta, idan har akWai zama na amana;
Ka ga abinda ta yi‘ta ma, ya nuna ba tsakani’da Allah suke tare da mu ba. Saboda haka kai ma ka Watsar da
alamarin su,’ ka kama kanka Alhaji, don ba zai yiwu Aliyaa ta rinka ci maka fuska ba. tabbas ni ma wata rana zan nuna
mata ba najin tsoron ta. Ina ganin zai fi kyau ku  nisanci juna. tun kafin hakan ta faru
Ya zuba mata ido harta kare.‘ sannan yace “gaba daya maganganunki gaskiya ne Suwaiba. Amma abinda’na ke tunani, shi ne, me ya sa ban yafe wa Alhaji Bara’u ba a cikin zuciyata?”
Da sauri ta ba shi amSa. “Ya nemi afuwarka ne? ’Ko’ ka na ganin bai fika sanin akwai tarin hakkinka bisa kansa. ba ne?” Ya girgiza ‘kai’. Yace “Ko bai nema ba, ya kamata na ‘ yafe masa…’…” «_ ‘
“Ai’ ka yafe, tunda ba ka kullace shi ba.  Haba Alhaji! Ko makiyinka ya san ka‘yi iya yin ka”
Yace “Suwaiba, daga Allah sai mu biyu cikin dakin nan a tsakiyar “dare: Zuciyata ta kaunaci Alhaji Bara’u da iyalansa tsakani da Allah, shine dafi na farko da yasa ba na son gaba ta zama‘sakamakon zumuncin mu. dalili na biyu, kin ga Suleman’ ya kwallafa ransa akan Marja, idan ban nemi zaman lafiya ba. ya ki ke so in yi?” Ta zuba maSa ido .
Tace. “Ka na da aiki kuwa’ gagarumi.‘Sai dai in ce ~ Allah ya bada sa’a, amma ni Suwaiba banyi alkawarin‘zan sa kaina a’ciki ba,  Alhaji”. Yace. “Ba ki yi laifi ba, don kin cé’haka, addu’ar ma ta wadatar. Allah ya » karba”. Tace “Amin. Ka taso ka kwanta, dan na tabbata akwai gajiya a tare da kai”;
Yace. “Ina son yin raka’o’i guda biyu ne  . Ta zuba masa ido cike da damuwa. tace Ina fatan Allah ya amshi addu’o’inka”. Fuska sake ya amsa. “Amin Suwaiba”. Ya mike, ya shiga bayi ya dauru alwala, ya
fito ya hau sallaya. Ta sa katon mayafinta, ta zauna gefen sa. .                                
                ********
gaban gadonsa suka ja birki. idanuwansa na rufe. Ba za ka taba shaida shi ba, saboda ya sauya gaba daya. Wata shida a kwance, ba wasa ba. Ya yi wani fari na musamman. kafafuwansa duk sun kumbure suna saba. ‘ ‘
Abin gwanin tausayi, sai wanda ya ganii- Alhaji ya ‘ zauna a hankali ya zuba masa ido, yana yi Wa Allah tasbihi. Ya, jima yana kallon sa, sannan ya dubiMalam .Sallau.Yace. “Ana ganin sau’ki kuwa?” ‘ ‘
Yace “To gamu nan dai , tunda wuya ya tsaya, kuma ” yana magana, ya fadi abinda yaka so. Amma kai ma ka sani,_ komai sai an yi masa. Bayansa da nan gefen kafadarsa duk sun salube. saboda ‘kwanciya, Shine aka so a siya masa keke_ a rinka dan jingina shi, ko dan yaya ne, yana zama; Dalilin ‘da ya sa kenan ita Aliyaa ta je gida a samu wasu kayayYaki a siyar, a hada kudin”.
Hawaye suka wanke fuskarsa, bai’gama gogewa ba. Alhaji Bara’u ya bude ido. Kai tsaye idanuWan nasa cikin na Alhaji Abdul-Rasheed suka shige. Ya yi tsam’! Da su. .kamar bai. yarda idanuwan nasa‘gaskiya suke ‘nuna masa ba. Ya ‘hadiye miyau da kyar‘. Yace “Da gaskr Alhaji Abdul-Rasheed na ke gani?” ‘ ‘ ‘
. . Ya kara matsoda kujera, ya kama hannun sa ya amsa. “Ni ne Alhaji Bara’u…….”‘;Ya katse shi “Haba “Alhaji Abdul-Rasheed, sai yau zaka zo gaishe ni? Da na’ mutu ban ganka ba fa?”‘gaba daya ‘kuncin sa ya wanke da hawaye, ya kara runtsehannun ‘Sa; Yace‘. ‘”Ba haka bane Alhaji Bara’u, wannaa shi ne. karo na shida da na zo duba ka, amma’ Allah
bai’sa na ganka ba sai yau. Ya jikin? Ya kuma muka ji DA   hakurin su Nasir?”
Shi ma idanuwan nasa taf Suke da hawaye, ya amsa‘ “Mun gude Allah Alhaji Abdul-Rasheed. Sai dai ba’a taba gaya min ka zoba?” Ya dubi Malam Sallau. Yace “Malam don Allah idan ba za ka damu ba, ka dan ba mu wuri minti‘ biyi Ya-ce‘ “Babu laifi”. Ya juya ya fice
Sannan Alhaji Abdul-Ra’sheed ya dubi Alhaji Bara’u.
Yace ‘”Tunda wannan abu ya faru, daidai da rana daya’ tunaninka bai taba ,gushawa a cikin zuciyata ba. Kamar yadda na gaya maka, wannan shi ne karo na shida da na zo amma Hajin Aliyaa ke hana min ganinka, saboda tana ganin girman laifin da na aikata gare ka. Ban ga laifin’ta ba, dun kishin mijinta take yi.
da sauri ya katse shi._ “Bari fadi Alhaji Abdul- Rasheedl Don Allah ka daina ‘fadi, kar’ ka sa Allah ya gaggauta daukar raina, ba tare da na nemi’gafararka ba! Na yi kuskure, na yi kuskure ba karami ba. Alhaji Abdul- Rasheed, da ace na mutu, kai tsaye a hadarin nan, da ban san iya bakin-cikin da zan tarar ba.
Na san shaidan ya yaudareni, kuma nayi wa ,iyalina karya, don in tsira da girmana da mutunci na a wajansu. Ban san hakki zai kama ni da tsanani haka ba. Ban san tarkon ama‘na yana da radadi haka ba!
Amma duk da haka ina yi wa Allah godiya da bai sa ‘ na yi tazarce ba, ga shi har ya nuna min kai, don in roke ka
gafara. Ka yafe min Alhaji Abdul-Rasheed, ka yafe min don girman Allah”. ‘
Yace “Tuntuni na yafe maka Alhaji Bara’u, sannan ina so ka yi min alkaWarin ba za ka taba gaya Wa Hajiya Aliyah cewar laifin ba nawa bane, koka gayama wani “saboda me?” ‘ ‘ ‘
’ “Saboda ‘girmanka da mutuncin ka ya ci;gabada zama cikin idanuwanta’. idan kuwa har ka gaya mata, to ban yafe ba duniya da lahira”. ‘Kwalla suka zubo masa. Yace. “Don me za ka daure ni da jijiyoyin jiki na?
– Me ya sa zan ci-gaba‘da lullube laifina, in bari ana ganin bakin ka‘ a duniya? Bai kamata ka fadi hakaba‘Alhaji Abdul‘-Rasheed.saidai in kana so tunanin maganar nan‘ya ‘ zama ajalina ne
‘ Ya kada kai. Yace. “Ba zai zama ba, da yardar Allah za ka tashi ka yi rayuWa ‘kamar kowa. Kar kuma ka dauka da wasa na ke’ yi, ba na son inji maganar nan a bakin kowa, shi yasa tun’farko nace Malam ya ba mu wuri”. ‘ “
Hawaye ke ta kwarara‘ bisa kuncinsa. “Kai! Lallai ! Na yi asara ba karama ba da na bari Mr. Bulagun ya ingiza ni‘ramin hallaka. Na bata’watanni hudu ina koyon sa hannun’ka. domin shi yayi, yayi ya kasa ‘ ‘
cikin dan’kankanin lokaci ya rusa zumuncin shakara da shekaru. Alhaji, na ‘san yanzu Suleman ya daina son Murja, ya tsane ta, ba za‘i iya aur‘enta’ba. Shi kenan idan“ hakan ta faru zumuncin mu ya kare’ ‘kenan?”
Ya yi dan murmushi. Yace. “Sulaman‘bai ‘daina son”: Marja ba, ‘hasali ma kullum sai ya yi maganar ta. Idan har za ka ba shi, shi ma yana nan akan bakansa”. Dadi ya lullube shi. Yace, “Me zai hana?
Alhajl Abdul-Rasheed ya sauke numfashi Ya-ce. “Da yardar Allah kai zaka daura masu sure. Ai ba don Kakan Suleman ya, rasu ba‘da tare zaka ganmu”.
Yace; “Ayya! Allah ya jikansa”. “Amin summa amin. ai mutuwa. sai su Nasiru , anyi mutuwar kuruciya. Allah ya karbi aikinsu kuma yajikansu
Yace “Amin. Sannan yace ka san wani abu Wallahi har zuwa lokacin da hadarin nan zai faru, fada suke yi da mahaifiyar su, saboda sun ki yarda a dora maka laifi. ” Sun kasance cikin’ damuwa da takaicin abinda ya faru.  “Allahu-akharl Allah dai ya jikansu”. hira. Alhajl Bara’u ke ba shi labarin yadda Mr. Bolagun ya yi ta masa shisshigi da dadin baki tare da yi masa alkhairai masu yawa, har ya yi galaba a akansa Sannan ya : shiga aljihun sa da zarar ya bada hadin kai. Shaidan . ya yi ta yi masa sarewa, yana jin dadin sabuwar hanyar da ‘ ya dauka. Rabon da Alhaji Bara’u ya yi hira irin wannan har .ya manta.
Bayan sallar la’asar karfe biyar na yamma motar alhaj ta iso sannan suka yi sallama Alhaji Abdul-Rasheed ya bar asibiti. dauke- da alkawarin taimakawa rayuwan Alhaji Bara’u ta~ kawace fuska. idan har yana’da ikon yin hakan Yau kam da farin-ciki ya dawo gida. Tun kafin ma ya yi bayani. Hajiya Suwaiba ta gane hakan. Yana cin abinci, yana warware mata abinda Ya faru a a-sibiti. , ‘
Ta jinjina kai. Tace “A gaida manya. lnji kanana! Yanzu ka yarda .a‘lullube laifin wani, a bude naka? Alhaji manya. To. Allah ya tabbatar mana da alkhairi”. . .
” Yace. “lya abinda ya kamata ki fada kenan  Yau kam ina cikin farin-ciki, don bukatuna dukka biyu Allah ya biya min”. ‘ Tayi murmushi tace “Haka ake so, to Allah ya biya mana dukkan bukatun mu. Sauran Abinda ke‘ raina shline. a sanya Imam makaranta. tunda ya shekara uku. kuma bakinsa .-
‘Ya gyara zama. Yace. “Kamar ki na raina. lnsha— Allhu zan duba makaranta mai saukin kudi. nan kusa a sanya
~ shi”
Tace “Allah ya yarda. Uh ni Alhaji. Magaji‘shi: ba ko labari; tunda ya tafi?” Ya-ce. “Ai dama Magaji da wuya ya dawo tunda ya kwashe iyalinsa. Wata kila. kuma__ wata rana ki gan shi, kin saN nijar‘ ba nan da Zariya bace’ Tace. – ‘ ‘ ‘ ‘ – gaskia ya So zama da kai. kaqi .yarda  da bai tafi ba”; Yace. “Na so hakan. amma baihalasta a. ‘
sulaiman ne Ya yi kasake, duk kawai Murja ta ‘ishe shi. idanuwansa basu son ganin kowa, sai ita. ‘ Washe gari da sassafe suka dunguma Dutsan Abba aka yi addu’ar‘ uku da su. Ba su jima ‘ba. gwaggo da Inna Mairo suka iso Sai da suka’yi sallar azahar; Alhaji ya kwasosu ya aje gida, sanan ya_sake dawowa suka koma.Kaduna. Sati biyu tsakani. Alhaji Abdul-Rasheed ya raba ‘yan raguwar kudadensa dubu ashir‘in dake banki, gida biyu. ya dauki hanyar‘ bai zame ko ina .ba, sai asibiti a Zariya.‘Yana isa ya tarar ba sanan,’ ya tambaya akace masa sun‘karbi sallama sun koma gida. Alhaji Bai bata lokaciba. kai tsaye ya dauki hanyar Katsina. Kafin azahar yana Kankiya, cikin. yardar Allah. ‘ ‘ ‘ ‘ Ya jima yana doka‘sallama a kofar gida, kafin wani dan matashin saurayi ya fito. Bayan sun gaisa. Alhajin ya ‘ tambaya. “Malam Sallau yana ciki?” Yace “A’a ya yi ‘dan – tafiya zuwa kauye”. Yace “Ay’ya To don Allah .jeka yi min iso wajan Alhaji Bar’a’u, kace Alhaji Abdul-RaSheed ne ya zo gaishe shi
“matashin”. Ya juya ya koma ci‘kin gida. Yana’ nan tsaye’yana jira Dan saurayin ya dawo. Yace yace zaka Iya shigowa cikin murna ya bi bayan saurayin, ya’yi masa jagora Sashin alhaj barau shashin yafi ko wanne kyau ’ Anyi masa siminti tare da fenti ruwan~ madara. sallama, sukayi gamida shiga har dakin barcin Alhaji‘
Bara’u. Katifa aka aje masa a kasa, aka tara masa filulluka saboda jingina.
Amma a halin yanzu kwance ,yake ta gefen damansa ‘ yana lazimi, don kammala sallar azahar dinsa kenan. Yana sallama ya amsa cike da murna. “Alhaji Abdul-Rasheed! Me zai sa ka tsaya a waje‘ ka na naman iso kamar nan ba. gidan ka bane?” ,
. _Ya zauna kusa da shi yana dan murmushi. Yace “‘Haka ne, sai dai ka, san neman izini kafin ka shiga gidan wani, wannan wajibi ne,,kaima ka san hakan tun asali ba ma. fadawa gidaje kai tsaye babu izini”. ‘
Ya miko masa hannu a hankali, yana fadin. “Alhaji Abdul-Rasheed kenan. To daga yau na ba ka _izini ka rinka shigowa kanka tsaye’. Ya kada kai yace “Ai ba dokar ka ; bane, umarnin Ubangiji ne. Yace kar mu shiga gidajen da ba ‘ namu ba; sai da izini”.
‘ Yace “Ka fi-ni gaskiya. Toya iyali?”‘”Lafiya kalau. ‘
suna gaishe ka Yace “Ina amsawa”. “Ina Madam?” Yace “Ta shiga wanka yanzu” Yace. “Madalla, dama cewa na’yi bari in zo duba jikin ka. Asibiti na fara zuwa, aka ce an ba ka sallama”;  Yace. “Ya’zama dole a Sallame _ni Alhaji Abdul- Rasheed, domin ba warkewa zan yi ba. Sun dai yi iya yinsu. kuma sun ,ba ni magunguna da shawariwari masu dama. Sannan koda matsala ko babu, duk wata zan je kilinik”. Ya nisa cike da tausayi yace. .”Allah ya baka   ka lafiya Alhaji’Bara’u”. Yace “Amin summa amin. Ina suruki na’?” Ya yi murmushi, ya amsa. “Sulaman ?
gida. na baro shi zai tafi duba sunan sa anan Poly, ance sunayen sun fito’ za’a fara raba (Admission)”.
Yace”Ya yi kyau. Allah ya bada sa’a”. “Amin. Nima na jima ban ga Mansur ba”. Yace “Duk sati yake zuwa. lokacin ina asibiti kuwa kullum yake zuwa. Ai koda yaushe ina gaya masa ya rinka-zuwa yana gaishe ka. koda ba‘zai zauna a Kaduna ba.
Kuma kaqi  bari na in gaya masu gaskiya, shi ya
’ janyo har yanzu Suke jin haushinka”. Ya gyada kai. Yace “Ni dai ban yarda ka fada ba, hakan ya fiyé min~da ace ka zama makaryaci wajen iyalan ka. Ka ga, ga dubu goma na kawo ma ‘yar gudummuwa ta, ko cafane ayi”.
‘ ‘ Hawaye suka .cika idanuwansa, suka Fara bin kuncinsa . “Bai kamata ba Alhaji Ba’ra’u…’…” Ya katse shi”Me zai sa ba zan yi kuka ba? Kai ma ka san ba zan iya hana haWayen nan fitowa ba,‘ don sun cancanci su kwarara” . idan da akwai jini ma, duk ‘ya dace ya zuba. Alhaji Abdul?” RasheEd.
Na yi.kuskure Alhaji. ka yafe min! Don girman Allah ka yi min izini, in gaya wa iyalina, ba ka da laifi cikin abinda ya faru: Sharrina ne kawai” Yace. “Ya isa haka Alhaji Bara’u! , ‘ -.
Kuma ina kara jaddada maka ban lamunceba. ban yafe ba, idan har wéni ya san wannan magana. Allah ya ga zukantan  mu gaba daya mun yafewa juna, ,don haka ka kwantar da-hankalin ka. A shirye nake in taimaka maka; ta
kowacce fuska,idan har ina da ikon yin hakan”.
Alhaji bara’u ya matse hannunsa tamau! Yana fadin, “Na gode Alhaji Abdul-Rashaed; Kuma yau agaban kowa zan fadi kudurina akan auren Suleman da Murja, ‘ Saboda .har yanzu Aliyaa tana kawo korafe-korafe akan maganar da na yi mata. Bara in tara Shaidu su sani. tuni kafin na mutu. Aliyaa ta ‘sauya min Magana”.‘Yace‘. “Babu laifi,‘ idan ka yi hakan.” Tsulum! Hajiya Aliyaa ta fado dakin Ta yi tsaye kame da kugu tana kallan Alhaji Abdul-Rasheed. “Ah! ‘Hajiya Aliyaa!” Ta kauda fuska gefetana yamutsa fuska a. Can cikin makoshi. Tace “Sannu da zuwa
Cikin fara’a‘ya amsa. “Yauwa! Ai na’ jima da shigowa
.Alhajin ke gaya  kin shiga wanka. Toya mai jikin?” Ta tabe baki. Tace, “ga shi nan a kwance kana ‘ganin sa. Ai zakaran da Allah ya nufa da cara, ~ko ana mazuru ana‘shaho. sai ya ‘yi”. Ta wuce kusa da mijinta ta zauna, yayin da Alhaji Abdul- Rasheed ke ba ta amsa “gaskiya ne Allah ya ba ki ladar jinya. Allah yasa kaffara ce
_ Watso masa harara,tayi Alhaji Barau yace. “Banji kin amsa ba  Nafa gaya miki maganar nan ta Mu Ta wuce Aliyaa Idan kina kullatar mutane cikin ‘ranki. Wallahi lokaci zai zo wanda zaki ji kunya. Wannan ‘al’amari’tsakanina da Alhaji ne,-kuma mun fuskanci juna, mun yafe tare da korar shaidanin da ya shiga tsakaninmu
Bai kamata ki zauna ki na daukar duniya da zafii haka ba. Ki sani koba ki yafe ba. Allah zai ‘yafe, balle ke ba’a
ma yi miki komai ba. saboda haka ina mai ba ki shawara da .ki
hankaltu, don kar wata rana ki zama cikin‘ masu dana-sani
irina. Ki tashi ki kawo masa ruwa da abinci. tun dazu ya zo yana zaune baburuwa, ba kumai”.
Fuska yamutse ta tashi. don bin umarnin mijinta kawai. Ta debi ruwan a wulakance cikin kofi, kamar’ za ta ba almajiri, ta’zo gabansa ta dangwarar da kofin har yana dan zubewa. kafin tace. “Babu dafafffen abinci Baban Mansur. sai dai ya sha fura”. Yace. “Ki dora masa mana. Ko babu ‘abincin ne?” . ‘
Alhaji Abdul-Rasheed ya café. “Don me? Ai furar ma ta wadatar, kai ma ka san mutuniya tace”.Yace “To’ ki“ yi sauri ki dama masa, yunwa ta ci ta cinye?” Wani dan guntun tsaki ta yi, ta wuce. Falo ta zauna ta dama furar, ta kanbado gishiri ta antaya mata, ta jujjuya ta rufe ‘murfin kwanon shan, ta dura ludayi, ta dauko ta shigo tasame su suna ta hirA
Ta aje‘ gabansa tace; “Ga. ta nan”. Yace an gaida uwargida”. Alhaji Bara’u Yace “Ga dubu goma nan Alhajin ya  kawo‘ min, ki yi masa godiya”. Ta kwabe baki tace. “An gode”. Tasa kai ta fice abin ta.
Alhaji ya bude fura, ya sa ludayi ya motsa, ya kanbadu ya kai bakinsa Da kyar ya hadiye wacce ya zuba wa ‘bakinsa, saboda tsabar gishiri. Ya suri kofin ruwa ya sha. Amma saboda baya son Alhaji Bara’u ya gane, sai ya yi ta motsa ludayin. yana’ kai. Wa hakinsa kamar’ da .gasken sha yake yi. Jim kadan ya dauki murfin ya rufe, yana fadin. “To Alhamdulillahi!” , ‘
“Ba dai. har ka koshi ba?” Yace”Ai na sha, na
gode”. Yana rufe baki. Malam sallau ya yi sallama, ya shigo
suna amsawa. “Ah! Alhaji Abdul-Rasheed! Saukar yaushe?”
Yace Ban wani dade sosai ba”. nan suka gaisa”. Alhaji Bara’u yace. “Na ji dadin dawowar ka yanzu domin» akwai wata magana da na ke so in kaddamar a yau kaje ka tara min maza da mata manyan gidan nan su zo su yi
shaidar abinda zan fadi”. gaban Malam Sallau ya fadi. Babu abinda ‘yazo a
ransa, ’face ko mutuwa Alhaji Bara’u zai a salube ‘ya fita, -‘
jim kadan ya dawo tare da mutanen da ya zazzaba’ a cikin
gida. Sannan ya sa aka kira ‘masa Hajiya Aliyaa, ta Shigo
ciki, kamar‘ za ta fashe saboda haushi.
Bayan duk sun natsa. Alhaji Bara’u ya farada cewa,
“Na sa a tara min kune, don ,ku zama shaida a maganar’ da zan
yi. ‘Ba wata mai tsawo bane, amma muhimmancinta yasa’ . dole ayi mata taran dangi. Akwai alkawarin aure da na yi
tsakanin Murja da dan aminina, watau Alhaji Abdul-Rasheed da ku ke gani halin yanzu.
To shi ne na keso kowa ya zama shaida, ko bayan raina. wani ya tada maganar nan, ban yafe masa ba, koda ita
,kanta Murjar ce. sai dai in shi Suleman din ne yace baya yi,
Amma baya ga’wannan dalili, ban lamunce wa kowa  ba;ina  fatan kowa anan zai zama shaida, ban yafe ba! Ban yafe ba
Ban yafawa dUk wanda ya sauya min magana naba
Ya yi shiru. Malam Sallau ya dauka. “Mun ji bayanin ka
ciwo‘kuwa ba mutuwa bane . Alhaji Abdul—Rashaed yace
to Alhaji Bara’u Allah ya ba mu ~ikon daukan wannan babban. . kaya. Sai dai kar ka manta. Allah kadai ya san gawar fari.
“Wannan magana haka take Malam. Muna sa ran kai da kanka. za ka kaddamar da wannan al’amari.
Saboda haka za mu ci-gaba da rokon Allah sauki da rahmar sa gare ka. A .karshe ina mika godiya ta. tare da dimbin farin-ciki game da wannan albishir. Mun gode. mun gode. Allah ya sa wannan lalura ta zama kaffara”.
kowa ya_amsa, .”Amin; amin”. Amma banda Hajiya Aliyaa, wanda da ka dubi fuskar‘ta, ka san tana cikin kunci da bacin rai. Kowa ya yi fatan alkhairi, ya kama gabansa dauke da alhinin jawabin Alhaji Bara’u.
Kwarai jikin koWa ya ‘mutu, domin suna kallonsa ,a matsayin wasiyya. lta ma Hajiya Aliyaa ba ta yi kasa a guiwa ba wajan‘tashi ta bar masu dakin. Alhaji Bar’a’u yace “Me ya sa Aliyaa take so ta yi min taurin kai?”
” Ya kada- kai yace; “Kar ka dubi wannan Alhaji Bar’a’u. balle ka aje shi cikin ranka ya dame ka. Aika gama magana. saidai mu zuba ido. Allah ya nuna mana lokacin.
Yanzu abu na gaba da nake so in nemi alfarma shi ne, ka ba Suleman‘ Umarni _ya ‘ rinka kai mata ziyara ‘ . makaranta, kamar yadda yakeyi ,da. ‘Wallahi rashin ganinta ya dame shi…..’.” ‘ .
“Ba Sai‘ka rantse ba Alhaji. Tabbas na san Aliyaa ita- ta hana shi zuwa, amma dawo da wannan magana, ta dawo da duk wata halastacciyar mu’amala a tsakaninsu, don su shaku ‘da juna- su kuma-fahimci junansu. Saboda haka Suleman na da damar zuwa wajenta har anan gida, idan sun yi hutu. Ka fahimce ni?” ~ ‘ ’
Yana fara’a ya amsa. “Kwarai da gaske kuma farin. ciki na ya karu”. Ya miko masa hannu. Alhaji Abdul-Rasheed ya kama suka yi ta hira. har aka kira la’asar. Alhajin ya fita masallaci, ya bar‘ Alhaji Bara’u na yin ta sa a kwance
Yana dawowa, yafara haramar komawa‘gida Alhaji
Bara’u ya damke hannunsa kamar ba zai bar shi ya tafinba. da kyar ya samu ya salube hannunsa ya wuce,‘ dauke da alkawarin zai sake dawowa sati biYu masu zuwa. Har ya bar dakin, .yana jin muryar Alhaji Bara’u yana fadin ya gode Allah. Ya saka da alkhairi. ‘ ‘ –
Bai ga Hajiya Aliyaa a falo ba, bai jinkirta ba, ya yi waje, duk da cewar ya so ya yi mata sallama. Tsakar gida ya ~sameta tsaye,‘ ta harde kamar an sauko mata da ciwon ciki. “Ashe ki na nan? To na yi harama, sai wani lokaci”.
Ta gyara tsayuwa tace. “Alhaji’AbdulRasheed! Ina jin kunyar ka, ina ganin girmanka! Amma na lura ka na so ka kai ni bango. Wai shin dole ne mu hada zuri’a da ku? Maye a zuri’ar taku da za’ayi sha’aWarta? Zalunci?
.cin amana? Ko kuWa ha’inci da son ruf da ciki akan dukiyar mutane? Ka gaya min daya na zaba a cikin abinda na lissafa!”
, Tayi shiru tana‘kallonsa. Ya yi dan murmushi yace “ai wannan maganar a taron daya gabata ya kamata ki
kawota, don kowa ya gane aibun mu. Wata kila su soke‘
maganar‘ da Alhaji Bara’u ya yi. Yanzu ,kam kin makara, _sai dai ki yi hakuri ki’bar wa Allah zabinsa”. , Ta watsa masa harara. Tace “To Wallahi
sai ka yi.
nadama, zaka yi dana sanin haduwa da Aliyaa. don zan nuna ~ _ maka kowace ce ni! zaka gane kai ba ka san~ komai ba a cikin shika-shikan sharrina da ba su da adadiba
Saboda haka idan ka na son kanka da arziki, ka na so ‘ ka tsira da sauran mutuncinka! To kar ka sake tako kafar ka
cikin gidan nan! inba haka ba kuwa,’na rantse da Allah, sai ka dora hannu akai ka na rusa “ihu
cikin zafin rai ta shige “, ta bar shi tsayé saboda

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

plz zakuyi haquri post din yau sai a hankali
page 29’30’36’37’38
duk sunyi damage nayi Iya bakin qoqarina Amman abin yaci tura hakan yasa kawai na kyalesu dalilin DA yasa banyima post DA wuriba kena

www.Facebook.com/abdullahi.Ismail.salanke

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]