[Advertisements⬇️]

Makaranta duniya chapter17 - Bankinhausanovels
Thu. Mar 30th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Makaranta duniya

               Chapter17

ta amsa..”Sau uku yana min tayin suyayyarsa gareni, yana nuna min tsawon lokacin da nayi babu miji kusa, alhalin ban wuce hakan ba…”Ya katse ta ~”Ya; .isa haka‘Aliyaa Ya isa!” Haushi ya-‘hana shi» kara cewa komai, ,sai hakin bakin-ciki da yake . yi kamar wanda Asma ke neman kama shi.ta share hawaye, tace; , ‘ _ “Ba dole bane ka yarda dani amma ina‘mai tabbatar- maka ina. da hujjata, ‘kan tsanar Alh. Abdul-Rasheed, kuma idanuwana ba zasu daina kallonsa a matsayin maci amana.ba Murja kuma ‘yarka ce, duk yadda ka ga-dama, ka yi da ita”. Ta yunkura ta tashi ta bar dakin, tana shashshekar kuka. _ Alh. Bara’u ya. shiga rudu mai tsanani, domin zuciyarsa ,ta rikice, da tunani ,kala-kala, sai dai kwakwalwarsa ta ki amsar sakon. Kafin wani lokaci  jikinsa ya rikice, ba tare da Hajiya Aliyaa ta sani ba. .tana can dakinta‘tana nazarin matakan da za ta bi, na ganin ta.yiwa mijinta katanga da Alhaj Abdul- RaSheed tana cikin tunaninne ta jiyo muryar mansur yana kiranta a waje ummah tana daga ciki ta amsa ya shiga ya sameta gamida fadin lafiya?
‘Tace “Auren Murja da Suleman zai tabbata Mansur. Na rasa yadda zan yi in hana zuri’ata hada jini da zuri’ar Alh. Abdul-Rasheed”. Yace “Sun kawo kayan ne?” _
Tace “Ga su can dakin Babanku, akwatunane. saiti guda. Koda ban budesu ba, na san babu abinda za’a kushe a ciki!” Yace “Umma ki kWantar,‘;da ’ hankalinki akan maganar nan, kar ki lika wa kanki ‘ ciwan zuciya. Ki sa masu ido, suje‘su ‘yi abinda suke
so.. .Tace”.Kash! Kai yaro ne‘ Mansur. ba zaka gane halin da nake ciki ba da‘alhaj Abdul-Rasheed, wanda ya sa na kara tsanarsa’, na kara tsanar hada zuri’a‘ da shi”. Ya gyara zama, yace “Na sani Umma, duk kuncin da’ muke ciki, shine sila. ni kaina marurun ya tsiro cikin zuciyata daurewa kawai na keyi, saboda ina tuna .abubuwan daya yi mana a baya”.’Ta bi shi da kallo tana kada kai “Ba duka ka sani ba Mansur, akwai abinda na boyeko Babanku bai sani ba, sai yau da qura ta kai bango
. Dauke da mamaki yace “Mane ne shi Umma?” TaCE-“Ba maganarka bane Mansur. Meka yi kokari ka samu a Katsinar’?” Yace “Dari takwas na samu Umma,_kin ga ana neman dubu uku da dari biyu”.Ta dafe goshi tace. ‘
“Ka san shawarar’ da zan ba ka ’Mansur?” Ya kada kai. Tace “Ka hakura da karatun nan. Kar ka
wahalar da kanka akan abinda Allah bai shirya maka ba. ldan ka na‘da rabo, nan gaba sai ka ga ka samu, ka ji?” ldanuwansa suka tsatso kwalla. _
_ Ya sauke numfashi mai karfi, ya sunkuyar da kai. Tausa’yin sa ya rufeta, ta sanyaya, murya tace “Mansur’ dubeni nan!” Ya dago ido ya dubeta, hawaye suka tsunké masa. ”
‘ Ta’ dafa kansa tace, “Ka kwantar da .hankalinka nace, share hawayenka. Ka yi kokari ka zama mai’ juriya. Wannan dari takwas din ka nemi wata ‘yar’ sana’a ka fara, idan Allah yasa ‘ maka albarka, sosai za ka sha mamaki. Kar ka damu kaji?” Ya goge kwalla yace, “Shi kenan Umma, na karbi shawararki, ka na ina son ki gaya min abinda yasa kika kara tsanar Alh. Abdul-Rashede domin ni ma yanzu na kara samun hujja”. ’
Ta yi jim shiru, kamar ba za ta tanka ba. sannan ta sauke numfashi tace “Ba maganarka bane Mansur. don tana da nauyin da ba za ka iya dauka’ba. ~ Amma tunda ka nace, zan gaya maka. Ka ga wannan tabarmar’? Nan Alh. Abdul-Rasheed ya zauna sau uku yana gaya min, bai kamata in rinka zama ba miji ba…”
“Ban gane ba Umma?” Tace “Shi ya sa nace maganar ba ta’ ka bace, amma wanda ya kamata ya sani, yau na gaya masa ya rage nasa, ya gane da ‘ wanda yake tare. Ko ya dauki mataki kokar ya dauka. ni AliYa ba zan sauke ba, ina’ nan kan bakana, sai naga bayan maci amana”; ‘
Take nan ya gane inda ta dosa, hankalinsa ya yi mummunan tashi. Fuskarsa ta dawo tamkar gobara, yace,, ba don ke ki ka gaya min maganar nan ba DA bazan taba yardaba Wai dama haka mutane suke? A fuska  Musa, zuciya Fir’auna?
Alh. Abdul-Rashed yaban mamaki, don ban
taba jera shi Cikin sahun-fasikai ba”. Tace “Natsu
Mansur, ai ka bar mutum kawai. Allah daya zai gaya’
maka ka yarda..
Yace’,’To Wallahi dole ya bar gidan nan‘, tunda ba mu hada komai da shi ba. ina zuwa”. Ya yi waje, tana kira bai dawo ba. don haka ta taso ta biyoshi. Dakin Babansa ya‘ nufa, ita ma can tabi shi. Duk iya fushin daya kunso. tilas ya watsar- da shi, domin arba ya yi da Baban sa babu rai babu dalilinsa.
Ya tunkare shi da sauri, ya tarairayoshi yana.
kira “Abba! Abbal!” Ido waje‘ya’dubi Hajiya Aliyaa, “Umma taba shi ki ji, bai mutu ba ko?” Jikintaya dauki rawa,-ta fara kuka mai karfin gaska ta yi waje da gudu. Da Malam Sallau ta ci karo yana kokarin shigoWa sasan sa. “Ko lafiya?” ’ ‘ “ Ya‘tambaya a firgice, domin tuni gabansa ya tsitstsinke ya fadi. Ba ta iya magana ba, sai data zube
guiwa biyu kafin, tace “Baban Mansur ne..” Ta sarke ’
cikin kuka, ta kara narkewa kasa.
Ganin haka ya sa Malam Sallau ya kwasa da gudu ya_fada dakin. Mansur ya gani da ruwa yana ta shafa masa, ‘yana kira. “Abba! Abba
Malam Sallau ya durkusa yana salati, shi ma
ya tarairayo shi yana fadin. “Allahu-Akharl” Ya dubi Mansur. “Daina zuba
masa ruwa haka, ka kwantar da hankalinka, .ka yi masa addu’a”. Mansur bai yarda‘ ba, sai da ya kara watsa masa ruwan. Allah da ikon sa’ kuwa, ya sauke numfashi mai karfi tare .da dan .tari mai’tabbatar da cewa daman can doguwar suma ya yi.
” .Gaba _daya hamdala suke yi, jikinsu na rawa. kamar mazari, ba ma kamar Mansur da yake jinshi ma kiris Ya rage a zare masa ranba. Daidai lokacin zugar _ matan gidan suka fado da sallallami da koke~ koke. Malam Sallau’ya dubi Mansur. “Je ka‘gaya masu ya farfado”. ‘
Ya mike da sauri ya fito falon Ummansa. na kife, kukanta ya qaru. ya nufeta yana fadin. ‘”Ya farfado Umma, dogon suma ya yi”. Ta yi zumbur! Ta tashi zaune. “Ya farfado?” Ya amsa da ka, hawaye na bin kuncinsa. Kowa ya dauki hamdala. duk Suka duru‘ cikin dakin, Kai! Raida dadi yake. Allah ka ba mu rayuwa mai amfani.
‘ cukun-cukun tafiya da ‘shi asibiti suke ta ‘faman yi, sai dai babu ko kudin da za’a dauko shatar motar da zata kai su face wadanda Mansur ya samu. kuma yake shawarar fara sana’a. Sai kuma sadakin ; Murja dubu biyar da kudin dinkin da aka zubamata a
lafe dubu daya da dari biyar.
Amma lafiya ta fi gaban komai, sannan ba su da ‘wani zabi, dole da wadannan kudade suka yi
amfani, ko dama suna hannun Malam Sallau. Alh.‘
Bar‘a’u yaba shi yace a siya mata duk abindaya dace’ na daki. watau kayan daki. ‘
‘ Tuni Malam Sallau ya manta da wannan shirin, yanzu neman lafiyarsa suka yi. Kwance kawai yake sharkaf Bisa gadon asibiti a Katsina yana amsar- taimakon Likita. ‘
” ” ‘ Mansur ya ra’sa inda zai tsoma tsumman ransa yaji sanyi har garin Allah ya waye haka shi ma Alh. Bara’u bai cewa da kowa komai duk da idanuwansa bude suke, yana kallon mutane.
Bakin-ciki kamar ya kashe Mansur, karfe
takwas na safiya’ko karyawa bai iya yi ba, yace wa ‘Ummansa zai je gida ya dawo. -Yana barin asibiti, tashar mota ya nufa, ya fada matar Kaduna. ga su nan ga su nan har Kaduna daidai shigowar azahar.
cikin wani masallaci ya shiga, ya bada farali, sannan ya nemi mota da ta karasa da shi kwanar ‘chanchangi. Kawai sallama Hajiya Suwaiba ta ji.
Ta fito tana‘amsawa. Yaron dake tsaye yace
“”Wai ana sallama da mai gidan’”. Tace “Kace yana
zuwa . Yaron’ya fice, ita kuma ta nufi falon bakinsa,
’yana kishingide, dawowarsa masallaci kenan  tace
“Sallama ake da kai a waje”. Ya mike yana fadin. “To Baki aka yi?” Ya bude kofar’ data fidda shi Waje.“
Take gabansa ya fadi, saboda ganin Mansur. Babu abinda ya zo ransa. face Alh. Bara’u ya rigamu gidan gaskiya. “Mansur Ya zaka tsaya waje ka na sallama kamar bako?”
Ya zura masa ido fuska murtuke, amma kash Kwar-jinin da Alhaji ke masa koda yaushe ya hana ya ci masa fuska, kamar’ yadda ya yi niyya, domin ganinsa yake tamkar’ mahaifinsa. Idanuwansa suka cika da hawaye. Alhaji ya kara matso shi yace
“Ina fatan lafiya Mansur? Don Allah kar‘ ka ce min babu aboki na’?” .Jikinsa ya kara narkewa, kuka ya
goce masa. Ganin haka yasa Alhajin ya janyo shi yana fadin. “Shigo ciki Mansur”.
Haka ya bi shi kamar rakumi da akala har falonsa. “Zaune!” Ya zaunar’ da shi, ya wuce ya kwala ‘wa Hajiya Suwaiba kira. Ta shigo ta same shi zaune ‘kusa da Mansur.
Ta tsura masa ido, kafin .tace “Wai dama Mansur ke sallama? Ina fatan dai lafiya?” Yace “Babu alamar hakan, sai dai bai yi magana ba tukuna”.
Ta zauna a hankali tana masa kallan tausayi. don Mansur ya canza kwarai da gaska. Ya yi baki, ya rame‘kamar ba shi ba. Jim suka yi shiru, kafin Alhajin ,ya sa hannu ya goge masa hawaye, yace
“Ka yi hakuri Mansur,‘muddin ina numfashi, ba zaka taba yin maraiciba”. Ya kara goge hawayensa yace, “Kullum na kalleka, ka na min kwarjini da yawa a ido na, saboda yadda na taso cikin gidan ka,  na shaku da kai fiye da ‘mahaifina. ‘ . ’ Shi yasa duk tsawon lokacin nan na kasa maida maka martani akan abubuwan da ke faruwa. Dalilin da yasa kenan na gwammace in bar wajen, da zarar na ganka, don baki na ba’ zai iya furta mummunan kalma a gareka ba. Amma yau kura ta kai bango, ‘na kasa hakuri, ‘dole na zo ka fassara min abinda ka ke nufi da kalamanka. cewar bai kamata .umma taci gaba da
zama babu miji ba?” ‘  Gaba daya, sai da gabansu ya fadi, don hannun
‘Hajiya Suwaiba ma har yanzu bisa kirjinta yake. Shi ,kuwa Alh. Abdul-Rashed tasbiHi~yaketa faman yi. Sosai kansa ya daure, ‘har ya kasa magana, babu
abinda yake. tunawa,-sai gargadin’ da Hajiya Aliyaa ta ‘
yi masa. Ya numfasa yaCe.‘
Tabbas shaidanci ya shiga cikin …… ” Mansur yai zumbur! Ya mike, “Ban zata. ba. Wallahi ban taba “zatan ka na cikin jerin irin Wadannan mutanan ba. ‘baba nacan yana kokarin mutuwa,’saboda tashin hankalin
maganar nan.
‘Tun jiya yake gadon asibiti, kuma Wallahi’idan ‘ ya mutu, kai ka kashe shi“ domin gaba daya matsalolin daka janyo masa ce ta sauya rayuwarsa!  ‘ Me muka yi maka Alhaji?” Ya zube bisa gwiwa, ‘hawaye na bin fuskarsa, Don Allah, don son Annabi ka bar mu 
mu huta haka Ka kwace masa komai. Umma kadai ta rage
masa,~don Allah ka kyale masa ita, ya rinka ganinta
kusa da shi yana jin sanyi a ransa”. Kafin su’ ankara, ya yi azama ya fice daga falon yana share hawaya.
,Tsananin kasala ya hana Alhaji koda mutsi,
’saboda a rayuwar‘sa bai taba jin maganar da ta gigita
shi irin ta Mansur ba. Kafin Hajiya Suwaiba ta San me
zatayi, hawaye sun tsunke bisa fuskar’sa;
.lnna-Lillahi’wa lnna-llaihir-Rajl’un! Hankalinta ya yi tashin gwauron zabi. Ta matsa gare shi da sauri tana fadin “.Alhaji kar ka bar’shi ya tafi  ba tare da yaji bayanin bakin ka ba” ‘ ,
‘ ya gage fuska, yace, “Mezan gaya masa Suwaiba?’ Ai duk laifina ne, domin Aliyaa ta gargade ni babu iyaka, amma banji ba”. Tazauna a
natse tace, “To wai dole ne-abotan nan Alhaji?”
Yace “Wallahi ina yi ne saboda Suleman‘ da kuma amincin dake a tsakani’na.da mijinta”. Ta kada kai_ “tace “Ba wannan bane babban laifinkaba.» Hana Alh. “Bara’u ya fadi gaskiyarshi ne laifin’ka”
‘ Yace “Na sani.amma‘ ban yi zaton abin zai kai
ga haka ba. Saboda haka gobe da yardar‘ Allah zan tafi
asibitin, muddin Alh; Bara’u ya amince da kalaman matarsa‘ ni kumazan fasa kwan
‘ . Tace “Hakan _ shi ya kamata. Aliyaa .ta ban  mamaki kuma na jima ina tunanin wautar ta. da wane
‘ idon za ta kalleka, idan gaskiyar tayi halinta?
Tana nufin ba za ta taba yafe mana ba kenan. da ace mu ne muka yi mata laifin? Duk zaman da muka yi a baya‘ya wuce har abada, ba zai dawo ba? Aliyaa ba ta cika mutum ba, tunda ba zata kwatanta yafiya ba, ko don ta samu yardar Ubangiji”.
Ya sauke numfashi yace “Ki manta da wannan amganar Suwaiba, ni zan nemi mafita, lnsha- Allahu ba za’a sake maimaitawa ba”. Tace  “Allah shi kyauta”.Yace’ Amin
Washa gari Sulaman’bai san-halin da ake ciki ba, illa iyaka ya ga Alhaji yana Shirin tafiya. Daya tambaya, aka gaya masa Katsina zai je dubo jikin Alhaj Bar’a’u ance yana asibiti. cikin tausayi ya bada sakon gaisuwar sa. Alh. Abdul-Rasheed ya sauka Katsina lafiya, ‘kuma da- wuri, don ma ya tsaya Kankiya. ya tambayi ainihin asibitin da aka kaishi ne.
Ya kuwa yi sa’a bai samu kowa tare da shi ba. Ya matsa gaban gadon a hankali ya matso da kujera ya zauna.‘ Mutsinsa ya sa ya bude ido’, ashe ba barci yake yi‘ba. ‘ _
Ya matsa masa da kallo cikin ikon  Allah, tunda aka kawoshi sai yanzu ya yi magana ta farko”Alh. Abdul-Rashed! Yaushe ka zo?” Yace”zuwata kenan Alh. Bara’u..Ya jikin?” ,.
. Yace “Mun gode Allah. Ya aka yi ka san ina asihiti?” Yace “Jiya Mansur’ ya je ya gaya min tare , da wata magana mai daga’hankali. Ban iya barci ba
‘alhaj Bara’u, saboda tashin hankalin da na tsinci kaina a ciki.
‘ ya daga masa hannu, alamun ya’dakata,.kafin
yace “Ban ga laifin kowa ba sai naka. Ban ga sakacin
kawa ba, sai naka. Ban ga wautar’ kowa ba sai naka
Alh. Abdul-Rasheed. ‘
‘ Duk kai ka jawo mana baraka, ‘har’ Aliyaa.take so ta ratso tsakiyar mu da shaidancinta. Me yasaba ka bari in gaya mata shirme take yi cikin’duhu ba gashi harta fara tura yara a ciki!” ‘ ”alhaj Abdul-’Rasheed ya runtse ido, ya Sauke . numfashi mai ‘karfin gaske Ya yiwa Allah godiya A Zuciyarsa, sannan yace. ‘Ba sakaci bane, ba kuma wauta bace‘alhaj Barau Ina ganin amsar ta fito fili a yau, .amincewa da na yi maka, ita ta karfafa zuciyar ka ‘Wajen cire maka zar’gi na daga abinda Aliyaa ta ‘kawo maka.‘Ashe kuwa na ga alkhairin aminci da ~sadaukar dakai ‘da zuciya daya Saboda haka kar ka samu damuwa karka jefa‘; kanka yanayin da bai kamata ba.,Ni kai na tUnanin’ abin‘ ‘
‘ da za kaji a zuciyarka, shi ya hana‘min barci. Amma : yanzu na‘samu natsuwa, abinda ya rage mu yiwa‘ Aliyaa adu’ar’ samun natsuwa, ita ma cikin‘ cikin zuciyarta ba‘taré da’ta san komai ba, a tsakanin mu”. . ;. Ya miko masa hannnu,-ya ‘kama‘yace alhaj Abdur-Rashed ban taba ganin mutum irin‘ ka ba
Tabbas na amince maka kuma ban yarda ka daina zuwa wajena ba, saboda tsaron kaidin mace”. Ba
Ya yi dan murmushi yace “Muddin dayan mu na numfashi, ba za mu daina zumunci ba. Addu’ata kullum Allah ya ba ka-lafiya, ya kankare maka wannan
wahala”. . ‘ Yace “Amin Alhj. Abdul-Rasheed’Suka ci-
gaba da labarin su har Nos mai bada magani ta shigo.~ “Baba har ka na hira yau? Lallai sauki ya fara
samuwa”. Yace”Naga aminina. dole inji sauki”. Ta dubi Alh. Abdul-Rasheed, yayin da take’ bincika magungunan sa, tace “Ba shakka .wannan
abota ta yi zanzan! Sannu da zuwa aminin‘ Baba.” cikin fara’a ya amsa. “Sannu yarinya, ya aiki?” Tace”Mun gode Allah”. ‘ ’ Ta mika masa magani a baki. .Alhj. Abdul- Rasheed ya taimaka ya kora masa da ruwa. “Tona bar ku lafiya, aminan juna”. gaba daya’ murmushi ‘suke yi “An gaisheki‘yarinya”. lnji Alh. AbdulRashed.
‘Yan mintoci da tafiyar’ ta. Alh. Abdul-Rasheed ya numfasa kafin yace “Ina ganin zan lallaba gida Alh. Bara’u,’kar yamma ta yi. Ina fatan za, ka kwantar da hankalinka, saboda yanayin jikinka”. -Yace “Babu kamai, sai’ Allah ya kai mu ranar ‘daurin auren. Na gode. Allah ya saka da alkhairi”.
.  Ya amsa da ‘Amin”; Ya mike ya yi masa addu’u’i, ya tufa masa, sannan suka yi sallama. Alhaji  ya fito daga dakin. Ashe Hajiya Aliyaa ke kwance bisa
tabarma tana barci a koridon. Bai lura itace ba,sai a yanzu daya dawo cikin hayyacinsa, sannan ya gane ta Bai saurara ba, ya .yi gaba abinsa yana yiwa Allah godiya cikin ransa.
Daidai gate zai fice, shi kuma Mansur zai shigo
dauke da bakar’ leda da’ ‘yar kula cikin ta. Kai tsaye Alhajin ya yi masa sallama. Da kyar’ Mansur‘ ya amsa‘ Yana kakarin wucewa. Alhaji ya tare shi. “Zan soka dan tsaya ka saurari ‘yan kalamai‘na ,Mansur”:“
‘ ‘- Suka ‘bi juna da kallo  kafin Alhajin ya ci-gaba’ “Zan kasance mai farin-ciki idah har- kaci-gaba da kallona a matsayin uba a gareka, kamar yaddaka shaida min jiya. ‘ ‘
A dalilin haka zan yi~ maka ‘yar nasiha da
‘ . cewa, idan za ka so mutum,_ kasoshi don Allah, haka
’ lnza ka‘ki shi: ka ki shi dan Allah. ‘Haka idan za kayi fushi kar ka‘ Zur’fafa, gudun ‘kar’ gaba .ta ‘ sarke
“tsakaninka‘da Dan-uWan’ka‘musulmi.
Koda yake zan tayaka da addu,a donka gane ka dawo  bisa hanya madaidaiciya. Ubangiji ya karemu da lafiya baki daya”. Ya sa kai ya fice daga harabar’ kofar aSibitin, ya bar Mansur‘ tsayajiki babu kwari
, ’Ya kwa’she “yan”dakikai‘ yana‘ kallon ‘bayan Alhaji ba tare daya san me yake’tunani ba. hakaya juyu ya karasa ‘cikin, asibitin, zuciyarsa cike da tunanin kalaman Alh.‘Abdul-Rasheed. ‘
Masu taushi da ratsa jiki. haka kalamansa suke koda yaushe. shi ya sa ya kara tunawa Mansur irin ingantacciyar rayuwar da suka yi shi da ‘yan-uwansa.
Jikinsa ya yi mugun sanyi har ya jefa masa kokwanto akan maganganun mahaifiyarsa.‘Barci sosai take har’ ya ajiye kular abincin, ya wuce ba ta sani ba-
Wajen Abbansa ya Shiga, ya same shi ido rufe. kamar shi ma barcin yake yi. Kujerar da Alhajin ya tashi, ita ya maye. Motsin zaman sa, yasa Abban nasa ya bude ido ya dubi mai zaman. “Sannu ’Abba‘! Ya jikin?”
Kallonsa kawai yake‘ yi, bai tanka ba; Ya kara matso shi, cikin taushin murya yace. “Abba me yasa ba za ka yi’ magana ba? Ni na‘tabbata ka yi magana. ‘ tunda Alhaji yazo Ya kara zuba masa‘ ido kafin yace “Dole in yi magana tunda na ga masoyina…”
“Mu ba masoyanka bane Abba?”- Yace “Ban sani ba’tukunna”. Fuska yamutse ya tambaya. “Mayasa haka Abba?” Ya amsa, “Saboda ban isa in bada umarni abi ba. Na kuma tabbata tunda ka iya yiwa Alh’. Abdul-Rasheed tattaki, ni ma za ka iyayi min
Da sauri-’yace, “A’a Abba! Ban je wajen Alhaji, domin yi masa rashin kunya ba, sai don in tambayeshi ya kyalemu tare da Umma, don ita kadai ta rage mana”. Yace. ’
“Kar ka zama jahili kamar yadda uwarka ta zama. Kar ka ‘zama kaza, ci share baki. tamkar mahaifiyarka. Haka kuma kar ka zama mai tsananta zargi. kamar Aliyaa. in kuwa ka ki karshenka na tare‘ da jin kunya maras misaltuwa”.
Mansur ya yi shiru, kai sunkuye cikin kwakwalwarsa cunkushe da tunani. “Yanzu ina Aliyaar take?”‘Ya dube shi firgigi,“ya amsa, “Tana waje tana barci”. ‘ , Yace “da ace za ta wuce lahira daga barcin nan, da ta tababtar da cewa ta .yi barcin asara, saboda tayiwa bawan Allah sharri  shiyasa nake gargadinka da ka ‘nisanci hudubar mahaifiyarka”.
Ya numfasa a raunane-yace. Abba me ya sa baka ganin laifin Alhaji?” Kai tsaya ya ba‘ shi amsa,
“Saboda ya yi min alkhairin da har in mutu ba zan ‘taba mantawa dashiba”‘Amma Abba Da sauri ya daga‘ masa ‘, ‘ hannu kafin yace, “Ban sonji, muddin ba‘zaka‘fadi alkhairi ba. zaifi maka kyau ka koma daga waje, ka kyaleni na sarara”. ‘
Mansur yayi” shiru tsawon lokaci, ka na ya numfasa yace, “Allah ya huci zuciyarka Abba”; Ya . tashi ya fito inda Hajiya Aliyaa ke kwance, ya zauna tare da zabga uban tagumin takaici. ‘
Motsinsa ya sa ta farka ta yi ‘zuru da ido tana kallonsa. Jimawa’kadan, ta’tashi zaune tace. “Wai
har ka dawo ne?”
Ya dubeta firgigi, ya amsa.. “Na dawo tun dazu. ki na barci”. Tace “Naganine Mansur, ni kaina-da za’a bincikeni, tabbas za’a ba ni gadon. Ka leka Abban ne?” Ya amsa, “Na shiga”. “Ya yi magana? Ko shi ma barcin ‘yake yi’?” Yace “Mun yi magana‘ da shi. ‘ bakinsa ya bude da ya ga Alhajin Kaduna”. ‘
‘ Ta kara wartsakewa a razane, tace “Ban gane ba Kana’nufin Alh. Abdul-R‘ashed ya zonan?” Yace “Har ma ya tafi…” “Abbanka ya ci mutuncinsa’
‘hakanan. shi ya Sa ya tafi,  don na’ tabbatar da har yanxu yana nan .
Ya dubeta ‘da. kyau’yace. “Duk da ban san me suka tattauna ba, domin ni ma a bakin get muka hadu zai tafi. Kalaman Abba sun tabbatar min yana goyon ‘ bayan Alhajin ne. Ni kaina bayanan da Abban ya yi.min yanzu sun jefa min shakku Umma…”
Ta zabura, “Shakku! Ka na nufin kai ma baka amince da‘ niba?” “Umma…” Ta daga‘masa hannu.
dakata mansu  ban Hmmmm

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

mu hadu a next chapter

naku har kullun

The  (O I C)@littafan Hausa zallah page

www.Facebook.com/abdullahi.Ismail.salanke

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]