Makaranta duniya chapter16

makaranta duniya

               Chapter16

Fuskar‘ta daure da mamaki ta tambaya “Motarka Alhaji?” Suka kura wa juna ido “Ban shawarceki ba ko? Ki yi hakuri, tunani na ne ya kare na ga ba ni da wata hanyar samun kudi, face in sayar da kaddara ta.
Wadanda ba su wuce gidan nan ba, ka gonaki na biyu, ko kuma akwalar’ motata. Sai na duba na ga ‘ gidan da gonakin sun fi motar muhimmanci a guna. domin sai in kwashe sati biyu ban fita da ita ba, saboda babu kudin man da zan zuba mata. lna fatan za kidubi uzurina.” . ‘ ‘ ‘
Ta aje numfashi mai karfi, cikin sanyin jiki tace. “Haka ne, tabbas dalilinka mai karfi ne. Fatana kawai Allah ya mayar maka da alkhairi. Ubangiji Allah yasa kai ma _ka’samu wanda zai ‘yi hidima da kai kamar yadda ka ke bakin kokarinka da mu”.
cike da fara’a yace, “To amin Suwaiba. Yanzu Saiki shirya yadda za ku yi siyayyar. Ko tare da dan gogan za ku, ya zabi kalar kayayyakin da yake so?” Tace “Ya zama dole, domin shi zai tambaya mana lambar takalminta da sauran su”. “Haka ne
Imam ne ya afko falon da gudu, har’ yana faduwa, yai azama ya mike ya nufi Alhaji ya fada jikinsa. “Baba Yace “Kai da wa ka ke faduwa haka?” ‘
Idanuwansa suka yi kwalkwai! “Yaya ne ya biyoni!” Ya fara dariya. “Kai dai da Yayan nan naka?” Hajiya Suwaiba tace, “Wai har an taso lslamiyyarne?”
‘ Suleman neya ba ta amsa, “An taso mana, yana can ya ta sa kwata yana wasa da ita”. Alhaji yace “Ashe ba ka da gaskiya Baba na. Kai kazami ne?” Suleman ya amsa, yayin da yake ‘zama kusa da su.
“Babban kazami kuwa”. Hajiya,Suwaiba tace, “Babu
dai ruwanka, kai din wanene? Ai ba’a tonawa indai kazanta ce”. ‘
Yace “Ko? To ai a Wurinsa na gado”. Suka tuntsire da dariya, tana fadin, “Tunda haka ne, ba ka yiwa tsoho biyayyaba ba zaka ji albishir’ din nan ba”. Ya yi sukuti kafin yace “Albishir din me?” “nan! Ya marairaice yana ‘yan dube-dube. ,
“Mane ne Mamanmu? Don Allah ki gaya min?” Karaf! ldanuwansa suka kai kan akwatuna. gaba daya ya dauke wuta. yana zare ido Baki sake ya mike, ya nufi wajan ya tsuguna, ya rungume katon akwatin
yace, “Mamanmu! Akwatin wanene?”tace na ‘ imam ne
Ya kyalkYale da’ dari‘ya, har‘” yana’ faduwa dabas A zaune, “Me zance wa Baba na yau?” Ya tallaba goshi, tsananin farin-ciki yake neman sanya zuciyarsa bugawa, domin ji yake tamkar za ta tsage kirjinsa ta yo waje Daga dariya al’amarin ya rikide. ya zame masa kuka. Hajiya Suwaiba ta kece da dariya tace .
“‘Ah‘! Kuka? Lallai yau imam zai ‘fanshe tsiyar ‘da ka ke masa, matso ka gan shi Imam. Yayanka ma kUka yake yi saboda shagwaba'”. “To meya na kuka~?_ Alhaji ‘ ya tambaya. Ta amsa. “dama so nake ‘Imam yayi masa’dariya zoka gan shi nace”. “ Ya taso ya tsaya gabansa, yana kallon  fuskarsa”Yaya! yaya kuka ka ke yi?” Ganin hawaye yasa shi ma ya ‘fashe da kukan Alhaji yace, “Ai shi kenan. ga ka’ninka nan yana taya ka”.- Ya jaWo Imam ya zaunarbisa jikinsa, ya”shiga share ma’sa‘ hawayen, murya shake yana fadin. ka Daina kuka Imam” “Alhaji ya gyara zama yace Ka ga kai ma ka share hawayenka . Kaje :kaci abinci’ ka ‘natsa . sannan ku zauna da Mamanku ku yi shawarai’ siYayyar da za a’yi. ga kudaden nan Allah ya kai mu’gobe‘ ko jibi aSabar kujetare ku siyo”.  Wasu hawayan dadin suka kara’tsunke masa
‘ yayin ‘da Hajiya Suwaiba ke fadin “Dama lahadince ranan bisitin ko?” Ya amsa‘ da kai. To Sai‘ ka gama shiryawa”. gaba daya jikinsa ya mutu; ya zura mata ido ya kasa motsi. Taci gaba da murmushi. “Ya naga ka yi tsaye’? Mu tafi mana. Mu sallami Alhajin yana can falon baki da Imam. Ka san‘ bada Shi za mu ba, saboda wahalar’ kasuwa”. ,
Ya gyara tsayuwa tare da aje numfashi ,mai kar’fi, yace “Ai ban sani ba Mamanmu, na‘ yi zaton tana‘gareji, don na san wani lukacin ta kan yi sati baba bai fito da ita ba. Amma’me ya sa…” ‘ ‘
Ta katSe shi “‘Sulaman .mu tafi kawai! Tambayar’ da ka ke so’ka yi, Iokacin ta ya wuce'”. Ta rataya jaka ta wuce tana yafa mayafinta. ‘
‘ Can ya same ta falon baki tana rarrashin Imam. Ya shigo ya zauna ‘kamar, maraya. Alhaji ya‘ dube shi. “Mane ne na ganka a salube?” Hajiya ‘ Suwaiba ta kar‘be tambayar.
“‘Wai daga na gaya masa motarka ka siyar saboda lefen nan, shi ne yake yi kamar‘ mai ciwo”.. ’Ya ce “Wa ya aikeki Suwaiba?” Tace “Shi ya tambayeni makulli, tunda an saba fita da ita”. Alhaji ya dan nisa yace, “Ina ganin ya kamata ku wuce kafin rana ta ‘ daga”. ‘ Tace “To sai mun daWo”. “A dawo lafiya”. Ta mike ta yi gaba, ya taso ya biyota’ba tare daya‘ ce wani abu ba. Imam ne ke ta fadin, “Ki siyo min jirgi Mamanmu!” Tace “Allah ya ban iko”. ‘
Ba su shigo gida ba sai gab da la’asar. Kaya jaka-jaka suka zube‘ a‘falon  Sallah‘suka fara ‘yi‘
suka ci abinci. ka na suka zauna suna shirya, su cikin akwatuna. Daga atamfofi zuwa leshi da shadda, sun zuba kala ashirin da biyar. Sannan dogayen riguna guda uku. Haka akwatinan kayan suka cika makill
mayafai da (Under wears) masu kyau hade da jakunkuna. Takalma ne kawai ba su siyoba, saboda basu da lambar qafarta Tunda bai samu tambayar Murja  lambar‘ kafartanba
Da karamin kit kuma ~an zuba masa kayan karas. ‘na  yayi masu kyau. Alhaji da _kansa ya yabawa‘ siyayyar Hajiya Suwaiba, don ta yo zabe masu’ kyau. cikin zuciyan Suleman  ko ba’a tonaba, shi kadai ya San yadda yake ji cikin ransa. duk ya kusa gari ya ‘ waye ya je ya labarta Wa Gimbiyar ta sa.
Imam kuwa tunda ya samu jirginsa ya tattaro sauran kayan wasansa yake ta yi ba ji, ba ‘gani. ‘
Washe gari yana makarantar su Murja. Sun sha hirar’jin dadi da kara kaunar’ junansu har’ zuwa azahar. Ya yi mata sallama ya ba ta‘kayayyakin daya kawo mata, ita ma ta ba Shi lambar’ takalminta. .
Ya tafi, ya bar ta cike dafarin-ciki jin cewar za’ayi mata aure da zarar sun kammala jarabawarsu ta koma gida, sam bai bata mata‘ rai ba, sai ma kara ‘ son abin da kaunar masoyinta.‘
Saboda ita ma tana matukar’ fargabar kar ta Allah ta ka sance ga Abbansu kafin ta kammala makaranta, su koma su karya wasiyyar da Abban ya yi. Domin take-taken Umman nata yana ba ta tsoro kwarai‘ da gaske Ko hutu aka yi. ta .kanji zaman gidan ya” ‘ gundure ta. ‘
Dalilin tsangwamar da mahaifiyarta ke nuna ’ mata, don ‘ta nace Suleman take so. Haka Yaya Mansu ba sa ga‘maciji, rabon daya kawo mata ziyara makaranta, tun ranar dayaxo suka hadu da Suleman.
A hakikanin gaskiya wannan daddadan labari ya kara mata karfi da azama a jarabawar da suke yi.
can bangaren Suleman ma haka abin yake, domin da karfin sa ya koma gida. Yana gama cin abinci. suka bazama siyo takalma. Akwatuna kam Sun cika, duk hassadar mutum, dole ya’dagawa kayan nan kafa. Washe gari Alhaji ya yi Shatan mota.‘
‘ Hajiya Suwaiba ta kwaShi kaya, ta fara sauke wa Dutsen Abba, don dangin Ubansa su sa albarka. Sai dai maimakon hakan, nan take yayyin ubansa’ suka shiga yada magana. ‘
. – Yaya za’ace auren Suleman zai ‘taso, ba’a
‘ gaya masu ba,‘ sai kaya kawai za’a kawo masu Su gani daga sama? Saboda an raina su. Saboda basu da kudi ko, kuma gasu ‘yan kauye ko?
. Tun Hajiya Suwaiba na ba su hakuri tana bayyana masu uzurin Alhaji, cewa maganar ceta taso
daga sama, babu wanda ya zata, har’ abin ya Fara bata
haushi. Ta kwashe akwatuna. Kauran Juli. Sallamar ta kawai Gwaggo.ta ji, yara na shigowa da akwatuna, “Ah! Maraba da manyan baqi ‘ lale!” “Sannu gwaggo. “Yauwa Suwaiba, sannu da zuwa. Ke kadai ce? Ina Malam?” Tace “Ni ‘kadai ce Gwaggo, Malam. yana makaranta”.. Tace “To, madalla”. Bayan sun gaisa, tace “Akwatuna nake -gani reras?”
Tayi murmushi tace, “LEfenkine gwaggo inji Suleman. yace a kawo miki”. Ta kama‘baki tace
tace Maxa mu qarasa ciki Allah! Abin godia  Kai a gaida Alhaji da
kokari! Wai! Wa zai ga min farin-ciki wajen Mairo yau’? gaba-daya ta tada hankalinta akan maganar nan. Shekaran jiya har kukan maraicin Sule tayi anan dakin.
Tace tasan Yayanta .ne kadai zai iya yi masa komai kamar mahaifinsa to shima yanxu babu shawara ta gama yankewa akan tafia kaduna ta umurci sule da ya haqura da murja inhar ita ta haifesa  Ashe yana can yana fadi tashi bawan Allah! Ubanglji Allah ya biya shi”.
Tace “Amin Gwaggo  dama cewa ya yi in kawo a kira kowa ya gani, asa albarka, zuwa jibi ko gata za mu kai can Kankiyan”; Tace “Ya yi kyau, amma ya kamata a kai Dutsen Abba, Suma Susa albarka”; Nan take ta kwashe yadda suka yi a Dutsen  Abban. ta gaya mata.
gwaggo kuwa ta bude wuta. “To sai me idan .ba su sa albarkar ba? Ai mai zuciya ake gayawa biki. Me suka tsinana  masa tun mutuwar ubansa?” Tace “Ai su kuma kuka sukeyi da Suleman din, baya zuwa gaishe su”.
Tace “Ashe kuwa za su mutu, idan gaisuwar Sule ce  da. Ko uwarsa, sai ya shafe: watanni bai zo garin nan ba saboda ita. Amma duk abinda za ka yi, ai sai kayi don Allah, tunda aka ce ai masa uzurin dalilin da ya saba su sani ba da wuri, ya kamata su karbi uzurin, su dubi zumunci”. ‘
“Ni ma bayanin da na yi masu kenan gwaggo. basu ma saurareni ba”.
Tace “Kar su saurara, mu za mu karbar masa auren, ni. bari in ~kawo miki ruwa ‘ki jika makoshi.da abinci Hajiya Suwaiba ta yi-wuf! Ta mike “Bar shi gwaggo, zan je in ‘dauko. Kamar wata bakuwa?”_Ta wuce tana murmushi. gwaggo tace. ,
“To .ki zubo isashshe, don Allah. Akwai naman ‘toro na daya kasa nasa aka yanka min shi, ki debo mai isarki kin ji?” Ta amsa “To gwaggo”. Ta fita ta barta, tana ta shafa a‘kwatuna. tana sawa Alhaji albarka.‘
. Saboda murna da kanta ta yafa gyale ta tafi wajan Inna Mairo, kafin Hajiya Suwain ta”idar da .sallah, har sun dawo tare. Tsaye ta yi sabe da haba tana kallon jarin akwatuna. Kawai zama tayi ta rushe’ da kUka saboda farin-clki.gwaggo tace “Lallai  kuka kuma Mairo. Wannan abin dadi?” . ,
Hajiya Suwaiba ta idar da sallah, ta juyo ta _ dUbeta “Mairo! Me ya kawo kuka ana zaune kalau? Dan Allah ki daina-zubda hawayen nan,Ta dan goge .fuska tace “Kin dauki al’amarin da .wasa-Hajiya Suwaiba. ldan ban yi,kuka ba, me ki ke son in yi’?
Kalmar godiya‘ dai ta yi kadan,.in fadeta ga ‘. Yaya. Kai Allah ya saka maku da alkhairi, domin har da gudunmuwar ki, Yaya ya samu dukkan nasarorin daya samu wajen raya zumuncin mu, .
‘ ‘ A hakikanin gaskiya duk inda kika ga”yan uwan miji ‘suna samun kulawa ta musamman daga gare shi; to akasari dace ya yi da matar kwarai, mai tsoron Allah. Wannan gagarumin aiki a ina za ki same , shi a wannan zamanin? Ai sai an tona”. ’
Hajiya Suwaiba tace, “Ban yi musu ba, sai dai” ina so in‘tabbatar‘miki ‘Yayanki mai zuciyar yine tun  aSalinsa, illa iyaka ya shawarceni, wani lakacin ma sai bayan ya zartar ya kan gaya min”. . ’
Tace “Yauwa, kin ‘gani inda ake ‘samun miskilar’ da kanki. Ai da zaran an shawarce ta, wata anan za ta baje kolinta. Kota hana gaba daya, ko kuma ta’ san yadda‘za ta rage alherin”. . Hajiya SuWaiba, mu dai mu gode ma Allah daya ba
mu keda Dan-uwa mai kaunar- mu. kuma ya hada shi da abokiyar zama ta—gari. Ubangiji Allah ya saka masa da alkhairi mafifici”. duk suka amsa “Amin”.
Nan da nan Hajiya Suwaiba ta bude akwatuna. gwaggo na taya ta.fiddo kaya, suna zuba santi, Inna Mairo dai tagumi ta zabga. ba baka, sai ido  cikin zuciyarta albarka kwando-kwando take sanya wa Dan-uwanta. ‘ ‘
Nan suka wuni cike da farin-ciki. duk Wanda ya kamata ya sani ‘yan-uwa da abokan arziki an gayu masu, suna ta shigowa suna gani, ‘suna sa albarka. Bayan sallar la’asar Hajiya Suwaiba-tayi shirin ,komawa gida, har’ bakin titi inna Mairo ta rakota. ta shiga mota.  Amma Hajiya Suwaiba ba ta gaya wa kowa yadda aka yi aka samu kudinba. Inna Mairo da gwaggo’ suka ci-gaba da gayyato jama’arsu, suna ta zuwa
suna ganin kaya.
              ‘******’****
Kwanaki hudu tsakani,’ kamar yadda suka aje cewa
za’a kai kayan Kankiya, kuma tuni Alhajin ya aika da sako ta hannun Wani Direba cewa a gaya masu za’a kawo lefen Murja ranar asabar’.
Wata mota ya sake yin shata ta kwaso su suka bar Suleman jiran gida. Sun iske mata uku na jiran su. ‘
gwaggo itace ta hudu. Ta sha adonta kamar ranar sallah.‘ Alhaji da kansa yake tsokanarta, “‘Wannan kwalliya gwaggo kamar ke za’a kawowa akwatin? Kenan ba kya kishi?”
Tace “Kishin me zan .yi? In don. Wannan makwadaicin mijin ne, na bar mata”. Ana ta dariya. Hajiya Suwaiba na tarewa Suleman. “gwaggo ki gode Allah, babu abinda Sule ya rage miki, ko wannan kayan’ ma na jikinki, ai duk shi ya dinko miki’
Tace “Haka na ji, dokin mai baki, ai gudu gare shi. Ni me zance’ tunda iyayensa sun’hayayyako?” Cikin wannan rahar aka‘fita da kaya aka sanya a mota, suka rankaya.
Har‘ suka iso Kankiya. tambaya daya ke zuciyar Gwaggo, sai dai ba ta furta ba, saboda ba, a lokaci guda ta  ba kanta amsa.
~ “Me yasa Alhaji bai zoda motarsa ba,‘ ya dauko _ ta haya?” Take kuma ta amsa tambayar, Wata kila yana zaton ko ba za ta ishesu bane”. Shi yasa ta yi shiru ba ta furta ba. ‘
Sun iso lafiya. Direba yaja birki kofar gidan. kowa ya yi hamdala ga Allah daya kawosu lafiya, tare da fatan ya maida su lafiya. Babu yara a wajen, dole su ne suka yi dakon akwatunan, ita ma Gwaggo ba’a bar ta baya ba wajen daukar dan karamin (Kit) din. Da farko dai cirko-cirko suka yi tsakar wuri. suna ta sallama ba’a amsa ba.
Sai da Alhaji ya shiga, ya jagorance su zuwa sasan Baba Sallau saboda kara. Daga kofar zaure ya tsaya, yace “Ku shiga nan, bari inje in shaida masu.” Gwaggo tace “A’a ko ba su’ san da zuwan mu bane?” Yace”sun sani, ai na aiko’kusan kwana uku da suka wuce, kuma dan aiken ya tabbatar min cewar ya isar ’ da sakon”.
Tace “To”. Tana rufe baki, wani saurayi ya sako kai cikin zauran daga cikin gida. Dane ga Malam . Sallau. “Sannunku da zuwa”. Suka amsa, ka na Alhaji ya tambaya, “Malam na ciki kuwa?”
Ya amsa “Eh yana ciki”. alhaji yace “Ku bi shi ya shiga da ku, daga nan ka yi min iso gunsa, kace ina wajen Alh. Bara’u”.
Ya amsa da “To”. Tare da amsar katon kwatin daga hannun kawar Inna Mairo. Yana gaba suna biya da shi, shi ma cikin zuciyarsa tambaya yake. “Shin wannan kayan waye haka?” ,
Nan take aHajiya Suwaiba suka zama abin kallo, Daga ganin fuskokin, mutanen gidan. akwai
alamun‘ tambaya, duk cike’ suke da’ mamaki sukace marabanku Suka amsa’gaba daya, suka shiga dakin da aka Jagorance su. Aka kawo masu :tabarma suka zazzauna‘ Shi kuma saurayin ya Wuce turakar Malam Sallau, Bayan yan gaishe-gaishe, daya daga cikin matan gidan ta: tambaya, “Baki daga ina?” Hajiya ’Suwaiba tace  daga Zariya, ai kayan Murja ne muka kawo”. gwaggo ta amshe “Kamar’ baku da labarin ‘ ‘zuwan mu?” daya daga ciki tace gaskia kam shi yasa abin ya bamu mama ki yannzu ‘lefan Murja ne wannan?” Tana rufe baki’Malam Sallau’ya shigo a sukwane’; ina bakin suké? Uh! ikon Allah! ‘ Sannun ku da zuwa”. ‘Duk suka amsa  yace “Wallahi bamu da‘labari, ashé Alhaji ya aiko yau kwana’uku kenan. Aliyaa ba ta fada ba Wallahi. Don’Allah ku yi hakur’i.”  Gwaggo taCE, Babu komai; ga kaya dai mun ” ‘kawo .Yacé ’~”To”Masha-Allah. Ke saude zo ki ji”. Ta taso suka fice, don shirya wa bakin abin abinci Kafin wani lokaci, sun damo masu lafiyayyar ‘ fura’ gefe guda kuma an kawo masu abinci harda kaji :biyu Malam‘ Salllau ya yanke, aké gyaré su ‘nanda nan. ” .Bayan sun sha ruwa,‘ sun ‘kora fura suka Fara baje  kaYan .lefen Kaya kam gwanin sha’awa kowa ya bude baki‘ fadi Yake “Masha-Allah,Murja tayi’” sa’a. Allah ya sa gidan ta ne
Suna kammalawa. Agogo na nuna biyu saura, kwata Kai tsaye ruwa aka zuba masu a butoci suka yo! alwala, dun sauka farali. Suna idar’wa. Gwaggo tace su je sasan Hajiya Allyaa’ su gaida mai jiki. ‘ ‘ ~
gaba ‘dayansu suka dunguma sasan; Ba suji’ motsin Aliyarba, sai Alhaji ya leko, yace su shigo ‘ cikin dakin. Kai! kowa ya kalli Alh. bara’u take’nan‘  zaiji kwalla sun taru cikin idunsa. ‘
gwaggo kam nata har sun zubu, ta’ share tana wa Allah tasbihi. “Sannu Alh. Bara’u.  Allah ya. ‘ sa kaffara ce” Yace “Amin Gwraggo. Don Allah ayi mana afuwa, la’ifukan da muka yi bisa kuskure a yafe mana. ‘- Hajiya Suwaiba, a yafe mana a taya ‘mu addu’a”. Hawaye suka kubce mata tace Haba Baban Mansur, duk wanda ya dube ka bai ji tausayi cikin ransa ba tabbas yana da karancin imani. Allah ya yafe mana baki daya, ya takaita wahala”.
anan ya amsa da “Amin”. gwaggo ta zarce da fadin. “Ba kai min laifi ba Alh. Bara’u, hasalima ka faranta‘min rai, tunda ka tsaya tsayin’ daka ka cikawa Sulaman ‘alkawari. Mun gode kwarai da gaske. Allah ya nuna mana ranan lafiya”, ‘
Yace “Amin gWaggo‘ Kuma ni tsakanina da Allah banisan da maganar kawo lefe ba, dunfa ‘ni’ ban bukataba. Sadaki ne wajibi shi nace a kawo saboda haka nace’ba za’a karbi, lefan ba, don innuna wa Aliyaa ba ta isa ta dora abinda ban umurceta tayiba
alhaj abdurRasheed yace a’a. A amsa . ba ta gamsar da ni ba. dole a koma da kayan nan”. ; ‘
Gwaggo ta kara matsowa, tace “Ko ni ban goyi bayan a koma da su ba. Ai al’ada ce, ko Aliyaa tace a kawo ko ba ta-ceba, idan da hali dole mu yiwa amaryarmu suturu. Saboda hausawa sun ce yaba kyauta. tukuici. Don haka na ke so ka karbi lefan nan a matsayin tukuicin kyautar Murja da ka yi mana”.
Ya yi shiru na dan lakaci, kafin yace “Shi kenan Gwaggo. Allah ya yi masu alharka”. Duk suka ‘ amsa da “Amin”. Yace”Tunda ga shi har’ sadaki Alhaij ya kawo. kuma muna sa ran dawowar ita Murjar ‘ gida, nan da’sati biyu. – ‘
To insha-Allahu nan da sati’ uku za’a daura auren su”. Farin-ciki ya bayyana bisa fuskukinsu. gwaggo da Hajiya Suwaiba suka hada baki. “Ba shakka. Allah ya_nuna mana lafiya. Kai kuma Allah ya’ kara sauki, ya sa kaffara ce. ‘
Saura suka ce “Amin”. ‘Hajiya Suwaiba ta zarce da tambaya, “Wai ina Hajiya Aliyaar ne?” Yace “lta ta‘san inda ta tafi’, ni dai na gaya mata ta bi a‘ hankali. idan ba haka ba, za ta ji kunya. _
Na gaya mata na sake maimaitawa kuma ba zan daina gaya mata ba, har sai. na mutu”. Kowa-ya yi shiru. masu sauke numfashi na saukewa. ‘ , ‘
Cikin shirun ne, wasu mata suka yi sallama aka
amsa. Suka shigo da kayan abinci’ suka aja, suna ta yi masu barka da aiki. Nan da nan suka zuzzuba abinci.
Alhaji ya dauki na direbansu ya kai masa, sannan ya dawo ya iske su gwaggo sun baje a falo, suna ta; burush da naman kaji. Ya wuce daki, suka ci tare da’
Alh. Bara’u.
‘ Yana ba shi a baki. su kuwa su Gwaggo cike da mamakin Hajiya Aliyaa suke. Watau saboda zuwansu. ya sa ta dauki gyalenta ta bar gidan, don kar su gaisa lta kuwa me ya” yi mata zafi haka?-Wannan wane irin gaba‘ ce ta jahilci’? ‘
Ai kuwa ba ta dawo ba, har suka yi shirin tafiya, bayan sallar la’asar. Har’ sun gama sallama, za su fice. Hajiya Suwaiba ta dawo tace, “Don Allah idan Mansur yazo ace ina gaishe shi”. Alh. Bara’u yace “Da yardar‘ Allah zai ji, na yi Zaton ma yau zai zo, don Yace ba dadewa zai yi ba a Katsinar'”
Tace Katsina yaje?” Yace “Eh,”ya tafi neman kudin makaranta, idan an samu ya idan ba’a samu ba kuma nace ya hakura da karatun kawai, ya nemi ‘yar sana’a ya kama”. Ta kada kai cike da tausayi tace. ‘
“Allah Sarki, to Allah ya shige mana gaba”. Ta wuce ta bar Alhaji suna kara sallama, ya fito ransa babu dadi ko alama, saboda ‘yana so ya taimaka wa Mansur, ya” koma makaratan, amma babu hali. Hidimomi sun masa yawa. ’ ‘
Duk iya kokarin da’ ya yi, don ganin ya bada wani abu, hakan bai yiwu ba, domin kudaden baza’Su’ ishe shi ba. Bayan su gwaggo sun shiga cikin gida sun
sallame su. suma rakiya suka yo masu har’ zaure, Can suka iska Alhajin shi ma suna ganawa da Malam Sallau. . _ gaba daya suka yiwa juna fatan alhari, suka dauki hanya. Kai tsaya mutan gida suka kwaso kaya suka kawo wa Alh. Bara’u ya gani. ya sa albarka, duk da cewar ransa bai so aka dorawa Alh. Abdul-
Rashed wannan babban nauyi ba. alhalin auren ya zo : babu shiri
bangare guda kuma dauke yake dafushin Aliyaa. A yadda yake ji game da ita yau, ba don Alh. Abdul-Rashaed yace bai yafe masa ba, daya bayyana mata duk abubuwan da suka faru.‘
Domin ta gane burgar banza take yi kaf! Abin kun’yar yana tare da su. Yana cike da tsananin fushinta ya tsinkayi shigowar ta, ta sawo kai dakin, ba tace da shi kala ba, harta nemi wuri gafe ta zauna.
Tana wa akwatunan kallon banza. cikin bacin rai ya fara magana. “Da izinin wa ki ka sa kafa ki ka bar gidan nan?” Ta daure fuska, cikin rashin kulawa tace “Ka yi hakuri Baban Mansur‘. na san ban gaya maka zan fita ba. Amma ina da hujjar- yin hakan…”
Ya katse ta “Hujjar banza, hujjar wofi! Hujjar da ba za ta daura miki zani ba duk ranar da asiri ya tonu! Hujjar’ da ki ka hango cikin duhu? Hujjar da ba za tai miki rana ba, ina amfanin ta?” Ta tsura masa ido. baki sake tace
“Ban fahimce ka ba Baban Mansur’? Ka na nufin don na hana idanuwana tozali da maciya amana. ba hujja bane a wajan ka? Ban san me ya sa koda yaushe ka ke gwasileni kan Alh. Abdul-Rashed da iyalin sa ba? Ni kuma ina nan akan bakana har abada babu yafiya tsakanina da su”. ’ ‘ ”
. Kai tsaye ya ba ta amsa. “Ai kuWa kin shiga uku, kin lalace. Ina mai tabbatar miki rayuwarki za ta kare cikin nadama da cizon yatsa. Ki na ‘yar’ musulma? Amma zuciyarki ta kasa gane kuskure daya daga cikin kurakuran da ki ke aikatawa? Tir
Da wannan zuciya ta banza mai manta alkhairi. wacce ba taitunanin kowa, yanayin kuskure kuma yana bukatar yafiyaba Kibi a hankali, kullum ina gaya miki wannan kalmar, amma ba kya ji. To Wallahi kin fara kureni, muddin ba za ki bi umarnina ba, zan sallamaki ki kama gabanki, ba dola bane, ki yi min takaba”.ba
Ta zura maSa ido taf! Da’kwalla‘isawon’ lokaci ‘kafin tace “Da bakinka ka ke fadar wannan maganar Baban Mansur? Ka na nufin babu rawar da zan taka don nuna kishin iyalina? gaskiya ne, to ina son in gaya maka, kai ma za ka yi kuskura. ‘
Domin furucin ka, yana alamta cewa sauran
kiris ka ba Alh. Abdul-Rashed damar daya dade yana nema daga gareni! Ko don ina kauda kai ina- kokarin
rufewa, saboda a zauna lafiya ?
Cikin bacin rai ya katse ta. “idan ki kikaci gaba da boye min, ban yafe ba Aliyaa”. Kanta tsaye
ta bashi amsa. tace_ Sau uku yana min tayin soyayyarsa
Hmmmmmm lol

Ku biyoni donjin yaddah zataci gaba DA kayawa

naku har kullun
THE.( O I C ) of littafan Hausa zallah

About AIS

Check Also

Makaranta duniya chapter 30

Makaranta duniya            Chapter30 masa shishshigi. Wayarsa ya dauka ya kira Mudansir  ya sanar wa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *