[Advertisements⬇️]

Makaranta duniya chapter12 - Bankinhausanovels
Tue. Mar 21st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Makaranta duniya

           Chapter12

Ta tafa hannayenta tana . “Fadi da qarfi in don rikon yaran da ku kayi mana ne, ya saiki gaya mana butulu. Allah na gani, hakan bazai sa in kyakuba, ina ganin zalunci kiri-kiri. saboda haka duk sunan da kikeso ki kira mu dashi, ba wai butulu kadai ba”.
, Ta juya kan yaran da suke tsaya baki sake, cikin matsanancin mamakin wannan rana mai kama da ganinta a cikin mafarki. “Kuzo mu wuce. ba zama ya kawoni ba”.
Nasiru ya matsa gareta idanuwansa taf da
kwalla. Yace”Ma’zan gani haka mama? Manene ya faru da zafi haka?” ‘
Tace “Ubanka ne. kaji abinda nace’? Khalid wuce ka sawo riga mu wuce, idan shi yanada tambayoyin da:
yake jiran amsoshinSu! Zan ji idan nan gidan ubansa ‘ne’” Hawaye shar-shar! Suka wanke masa fuska, ya yi zuru yana kallon Hajiya Suwaiba. “Mamanmu meke faruwa?” Tace “Ba zakaji komai a baki .na ba Nasiru, bukatata kawai itace kabi umarnin’mahaifiyarka”.. Hajiya Aliyaa ta café, “Ai dama baki da bakin da zaki gaya masawata magana Umarni na kuwa, koba kiceba,‘ dole subi don nina haifesu”. ‘ » Ta juya kan Nasiru. “Katon janerato Alhaji Abdul- Rasheed yasa aka dauke a Famhaguwa, da yaga asiri ya tonu, sai yace dasa hannun Babanku, saboda yaga
komai a Fambeguwa karkashin
sa yake
Babanku suke. Su Alhajin an kamasu tun jiya. sannan kuma akabi Babanku har Kankiya aka kamoshi. saboda haka ba zan yarda kuci-gaba da zama gidan azzalumai ba. dama rikon ba saboda Allah aka yishi ba.
duk kuwa abinda aka yi ba saboda Allah ba, to dole wata‘rana ya rushe! ‘Kar ka bata min lokaci,-kuzo mu wuce, bance ku dauki ko hankiciba. daga cikin tarkacensu. donma karku tafi tsirarane da nace ku sire har kayan jikin ku! Maza kuyi ku fito,- ina jiran ku”.
‘turkashi Fadan da yafi karfinka,hausawa suka ce maidashi wasa. Ita Hajiya Suwaiha ba wasa ta maida fadanba, gagarumin tashin hankali ya haifar mata, da jiri, ta lalubi kujera ta zauna, batasan lokacin da hawaye suka goce mataba, fadi take. ‘
“Dama haka mutum yake? Ashe sakamakon alkhairi ya kan zama sharri wata rana? Tabbas DUNIYA. MAKARANTA CE! Yau mun shiga tsaka mai wuya”. Hajiya AliYaa ta kama kugu.’Tace “Kanki akeji”. Suleman dake tsaye bakin’ kofar’ su, ya karasa tsakar falon murya dishe ya tambaya.
“Wai meke faruwa ne haka Mamanmu? Ina fatan dai ba fadabane?” Duk suka kyaleshi; ita Hajiya Aliyaa baima isheta‘ kallo ba. Su kuwa sauran takaici ne ya hanasu bashi ‘amsa. Nasiru ya fara’ wucewa daki. Khalid ya biyo bayansa.
Sallamar Mansur tare da daga labule. ita ta dauke hankulansu tare da hana Suleman sake yin wata magana. Banjin akwai wanda ya amsa masa sallamar.
Ya shigo a natse shima yana mamakin ganinsu cirko—cirko. “Umma! Mamanmu! Dama kun sami labarin rasuwar ne?” Hajiya Suwiba ta mike zumbur, ilahirin jikinta ya dauki rawa. ‘ ‘
“Rasuwa? Waya rasu Mansur‘?” Yace “Baba ~; Liman ya rasu Mamanmu tunsha biyun rana. ganin Baba baizoba. gwaggo tace inzo in gaya maku. Mundaiyi.. kokari mun amshi gawar yanzu haka yana gida”.
Ta koma dabas! .Ta zauna. haka shima Suleman.. zaman yayi. suna wa Allah tasbihi. Mansur ya kada kai, hawaye suka tsirgu masa. Yace. ’ .
“Tun safe yake ta kiran Baba, shi kadai yake ta son ya gani, bamu san abinda ya hanashi zuwaba. Hakuri kawai Gwaggo keta faman bashi, har ajalin ya, : sauka. gwanin sha’awa Mamanmu. Baba Liman ya cika da ‘ ,kalmomin shahada a bakinsa”. ‘
.Kuka sosai ya gucewa Hajiya Suwaiba. wanda ya kara ‘kashe jikin Nasiru da Khalid dake tsaye, suna sauraron bayanin Mansur. Don haka, yana shiru, suka tambaya. ‘ Baba Liman ya rasu ne’?” Ya amsa da kai, yana gage kwalla. Suka yi shiru na ‘yan dakikai kafin Hajiya‘
Aliyaa ta .katse shirun. ‘
“Tokun gama jimamin?” Duk yaran suka bita da “ido. musamman Mansur da baisan abinda ke faruwa ba. ta sake fadin.
“Kun” gama jimamin?, muna iya tafiya.” Ya kada kai. yace “Ban fahimce kiba Umma? ‘Kauran Juli zamu wuce? Aiya kamata mu jira Baba. Ni zanje ofis in ‘ gaya masa”. Kai tsaye ta bashi amsa. ”
“Sai dai kaje ofishin ‘Yan Sanda ka gaya masa. daga nan ka gaida Babanka, kayi masa jaje. “‘Yan  Sanda? Jajen me? Wai meke faruWane ake rufe min? Mamanmu meya faru .da Baban?” Hajiya Aliyaa ta café.
“Ni zaka tambaya, ba itaba! Sai dai a yanzu ba
lokacin karin bayanibane. idan ka biyoni, zakaji kome ke faruwa, domin daman can nayi niyyar tafia dasu Nasiru. ne
Ina fatan kowa ya fara ganin sakamakon zalunci ko? Yana rufe ga Babansaya mutu’, ba’aje ko inaba ma kenan. Toda saura ma! Saboda haka a cikinku duk – wanda ya tabbatar da na isa dashi, kuma nina haifeshi nonona yasha, toya biyoni mu tafi”. Tasa kai ta fice daga falon.
Hajiya suwaiba ta goge hawaye. Mansur zai‘ yi magana, tayi wuf! Ta daga. masa hannu ta ,dakatar dashi, kafin tace “Karka tofa komai Mansur, ku tashi kubi mahaifiyar ku
Sun kwasha dakikai uku kafin su kammala ficewa
daga falon, suna share kwalla tare da waigen Hajiya‘
Suwaiba, musamman Mansur dake cikin duhu. Suleman kuwa dum’Yake kamar gunki. donya
rasa duniyar da yake. Bayan ficewar su. Hajiya‘ Suwaiba ta kara gage hawayen ta. Tace”Allah mun gude maka da wannan jarabawa taka.‘ Uhangiji Allah ka jikan Baba, Allah kayi masa rahama Allah ka dubi wannan magana! kafitarwa mai hakkidahakkinsa!Sulemanl”
Ya dago kai ya dubeta. Tace“duk kaga yadda
abubuwansuka kasance. Yanzu maye abin yi?” Yace “Ni .
abinda ban ganeba Mamanmu, wai me ya faru’da su Bahan?” Nan take ta mayar’ masada yadda al’amarin yake. ‘ _
Yayi shiru jim, ~kafin yace “Shine Umma take gayon bayan Baban Fambaguwa?” Tace “Toba abinda ya gaya mata shi zata dauka ba?” Yace “Aikema abinda Baba ya gaya miki, shi kika dauka. Kenan dukkan su suna‘ da laifi”.
Ta zuba masa IDo  a fusace. Tace “Wane irin magana kakeyi Sulaman? Kasan abinda kake fadi’ kuwa?” Yace “Bazaki tantance ba Mamanmu, tunda ance kuwannensu akwai Sa hannunsa acikin takardar
“Kana. nufin ka goyi ,bayan Aliyaa? Lallai
Sulaman, har’ kamance tsawon shakarun da Babanka ya ‘
‘yi yana aiki, ba’a taba kamashi da laifi ba? Har wasu
bare sun yabeshi. su goya masa baya. amma kaika kasa
sulaman?- Sabuda me? Saboda kana son ‘.yarsu Murja?” ‘ ‘ ; .
Tayi shiru tana gyada kai. Ya sanyaya murya yace “Kiyi hakuri- Mamanmu. ‘ba haka nake .nufi ba. Amma Wanna“ Shari,ar: mu barwa Allah ya yita a tsakaninsu”- ‘tace  tuni_na_ ,“mikawa Allah lamarin. ‘
Yanzu tashin hankalina. yadda za’a kaiwa Alhaji labarin rasuwar kada Tashin hankalin yayi yawa Sulaman”.Ya dafa goshi,’yayi‘shiru. _ . .
Tsayuwar mota suka ji Sulaman ya mike da sauri .sukayi kicibis da Magaji. ina Baban, Magaji?” “Yana nan Sulaman”
“Yasan komai Magaji. ka gaya masa, yana- (hedikwata kawai”.‘lnji Hajiya Suwalba‘ tana tsaye a bakin kofa. “Baba ya rasu- Magaji.’-Take nan ya dauke wuta ya shiga salati. ‘ _
‘ “Tunaninta yadda‘ za’a gayama alhaj wannan  tashin hankalin zaiyi masa‘yawa”. Yace hakanan za,a daure a gaya masa domin  Alhaji jarumi ne, yanada karfin’ imani. na tabbata zai iya ‘dauka duka,‘kuma ya jure yayiwa Allah godoya. Ko yanzuma turoni yayi na gaya miki ki shirya in‘kaiki asibiti. ki sake dubu Baban.
Sannan ki rarrashi gwaggo gamida gaya mata  gaskiyar lamarin abinda ke faruwar tunda abin ya canza salo ba kamar yadda ake zatoba. Saboda haka zan koma
in gaya masa don ya sani, yayiwa mahaifinsa addu’a”.
ta share kwalla. Tace “Shi kenan, na gode Magaji”. Suleman yace “Bari in cire-kayanmakaranta inxo mu tafi tare”
Ya juya da gudu cikin gida, ya sauya kaya suka’ – tafi . Hajiya Suwaiba ta dawo falonta ta zauna’ shiru tsawon lokaci. kafin ta ‘koma daki ta‘fara shirya kayan ima ajaka. ‘ ’a Awani daki na musamman Suke ajiye su uku. ‘ Anan kowannensu yake tsatstsaye bayanin. Yawan zuwan da Magaji yakéyi wajen, .yasa jami’an ‘tsaron suka taresu, tun kafin ya nemi alfarmar ganin Alhaji. ‘ _ ‘ “Sintirin ka yayi yawa a harabar nan, bamu son mu sake ganinka- daga yanzu!” Jami’an. tsaron suka gargadeshi. YaCE “Kuyi hakuri, babban ‘sako nake dauke daShi, wanda ya tilastamin dawowa”. Daya’daga cikinsu ya zaburu…yayi maSa tsawa. kai Ba zaka gan shiba Malam! Ka koma da sakon
ka!” Babbansu yace Kyaleshi. ya fadi_Sakon a gaya masa.”. Yace “Mahaifinsa ne ya rasu yanzu a asibiti”. ” Jikin jami,an yayi sanyi; domin shine wanda Alhajin ya ’yiwa magiya yanaso yaje yaga yanayin jikin  mahaifinsa a asibiti a ‘safiyar yau. ‘
Har yace asa jami an tsaro su raka shi Ko kallon.Alhajin baiyiba. balle ya bashi amsa. Yayi Jim, yana kallon Magaji kafin yace “Dan jira.
ina zuwa”-
Ya juya ya shige ofishin ogansu, ya zayyana masa abinda yake tafe da shi.  Yace “Ka tabbatar?” yace “Kwarai, Sir! Don ya gaya min Babansa na kwance a asibiti har ya nemi ayi masa rakiya yaje ya ganshi”.
Yayi dan shiru. sannan’ yace “ba komai  ka gaya masa, sai a raka shi yaje jana’izarsa. amma asa ido sosai”.’Yace “Yes, Sir!” Ya-sara masa. ,kana ya fita. dakin da aka ajesu Alhajin can ofisan ya nufa, ya bude dakin ya shiga.
Duk suna zaune. Alhajin na yiwa Alhaji Bara’u nasiha akan abinda ya aikata da kin kawo kansa kamar yadda aka umarcesu. gashi ya jawo wa kansa. jamia’an sun kwankwashi kaurinsa ‘da girman sa da komai. Jami’in ya tsaya .gaban Alhaji yace.
“Bako yazo cewa mahaifinka ya rasu, so na nemi izinin wajen oga kuma ya bada umarnin a raka ka jana’iza”. Zuru Alhajin yayi .na ’yan dakikai, kafin kwakwalwarsa ta dawo aiki.
“lnna-Lillahi’wa-lnna—IIaihi-Raji’un!” Ya maimaita sau uku. idanuwan sa’ suka kada, ya sake fadin “Allaha- Akbar! Allah” ka jikansa. ka yafe kurakuransa”. Ya dubi
jami’in. Yace ” yanxu zamu tafi?” Yace “ldan ka shirya”.’Ya mike. Yace “Muje_ Har ya kai kofa. Alhaji Bara’u yace “Allah ya jikansa”, Ya Waigo yace “Amin”. Ya fice. ofisa ya maida kofa ya rufe. Mr. Bulagun ya kece da dariya. Alhaji Bara’u ya bi shi da kallo har ya natsa. “Me ya baka ‘dariya?’
Yace “Babu abinda bai ba ni dariya ba. Na dade ina jin haushin “mutumin nan, saboda toshe mana hanyoyin alheri da yake yi. Ni fa wannan halin da na ke ciki, bai dame ni ba, tunda bukata ta, ta biya.
. ‘ Wannan mugun-mutumin yabar kujerarsa, dama burina kenan, ‘kuma na dade ina kallon takunsa’, ina tunanin ta inda zan bullo masa. Amma kai duk ka wani gigice idan ka rasa wannan kujerar, ai ‘zaka  samu a can gaba”. ‘  Alhaji Bara’u ya zura masa‘ido. Yace “Ni dai ban ji dadin wannan abuba‘, bai kamata tashin farko mu rikito kasa warwas! Haka ba. Ba mu ga tsuntsu, ba mu ga tarko? Shi fa dama Alhaji ba wai gajiyar abin zai ciba’a. a. Ya kalle shi a dage. Yace “Kai daman kana tunanin shirin ya yi maka kama waddah za’aci gajiyar wani abune?” “Ban’gane ba?’.’ Yace “Ai damaduk inda ta fadi sha nE. shi yasa‘tun farko na gaya maka, ana tauyemu a ma’aikatar nan. ‘ ga sauran ma‘aikatu nan ana ta hada-hadar arziki, kowa
yana yagar rabonsa.
mu zauna mutum daya ya danne mu. shi baiciba, sannan kuma ya danne na kasa dashi wannan ai mugunta kenan. kaga gwara duk ta kwabe, kowa ya manta dashi  shi kansa zai dauki darasi. A! an wuce wannan zamanin da zakaqi tara arzikl Duk ka tsufa a gwamnati, ayi maka ritaya ka tafi a tsiya ce”,
Alhajl Bara’u ya kada kai. Yace “To yanzu ina ribar take, ta bakin ‘Alhaji Abdul-Rasheed din?” Yace “NinA gaya’maka ni burina ya cika”. _
Ya ja tsaki. Yace”dana san haka ne. Wallahi da ban biye makaba, nayi asarar lokacina a banza. wata hudu Ina koyon sa hannun Alhaji. ‘
Yanzu ga shi girmana da mutuncina sun zube a idonsa. Dan ma nayi wa mata ta karya naca shine ya jefani ciki. ai da kunyar tafi haka. gaskiya ni wannan abu bai tsinana min komai ba, sai masifa. Haka kawai muna
zaman mu lafiya ‘da mutum. kazo ka shirya min gadar
zare YayI dan murmushi. Yace “Ka kwantar da
hankalinka. Kai dai ka yi addu’ar Allah ya fitar da mu nan. akwai inda nake sa ran samun wani aikin. Kai ma zan taimaka maka”. Alhaji Bara’u ya yi shiru. duk takaici ya damashi. _
Fitar su Alhaji Abdul-Rashead da jami’an farin’ kaya guda biyu da Magaji ya kwashesu, bai zame-ku ina
ba, sai gida. Suna zawa shi Magaji ya shiga ya kira Hajiya suwaiba‘ta “fito cikin hanzari. ‘
Magaji ya dauko mata jaka,‘ ya riko hannun Imam ‘ Bayan ta kulle kofar ta’samesu cikin mota,‘ sai dai dole ta zauna gidan’ gaba domin Alhaji da Suleman suna tsakiyar jami’an’ tsaro. Imam nata murna yaga‘ Baba yana zauna bisa cinyoyin Hajiya’Suwaiba. ~
‘ , ,Ta juyo‘ta’dube shi. Tace “Sannu Alhaji”. Yace
“An gaisheki Suwaiba. ya mukaji‘ da alhini?” Tace “Mun goda Allah”. Yace “Allah ya gafartawa Baba”. Ta amsa. “Amin summa amin”. Yace “Yanzu Suleman ke gaya min abinda ya faru tsakaninki da Hajiya Allyaa”.
Tace “Hmm’…… Ai naga abin mamaki Alhaji, wai Aliyaa na tsaye. .Mansur, ya zoda ‘sakon mutuwar nan; amma ta’tarkata ‘ya‘yanta suka wuce, bata ko ce Allah ‘yajikansa‘ba. Wannan abu ya daure min kai, har yanzu sarawa yakeyi. ‘ Alhaji ya numfasa. Yace “Bar komai Suwaiba. Aimu saboda Allah muka rikE yaran, kuma ya Sani, tun’da shi Ubangiji da zuciya yake hisabi;
“Saboda haka ki‘kwantar da hankalinki, komai zai wuce da yardar Allah. Wannan duk ba wani abu bane. kawai darasi ne daga MAKARANTAR DUNIYAl Tace “Allah
yabamu lkon cinye jarabawar”. Ya amsa da “Amin”.
Suka yi dan shiru, kafin tace “Yau za ku dawo?” yace “Ya zama dale Suwaiba, na ma gode ‘da aka bar ni inje in sallace shi”. Ta dafe goshi. _
Tace “Tonon asiri ni Suwaiba! wane irin fahimta jama’a zasu yi wa‘wannan abu? Ace ‘babu kai a zaman makokin‘Baba? Kuka biyu,‘ ya kamamu Alhaji. ban san yadda ‘Gwaggo zataji ba yau?” Hawaye suka goce mata. Kowa a matar sai da jikinSa ya mutu. –
Alhaji Ahdul-Rasheed ya yi karfin hali. Yace “Ki yi hakuri Suwaiba. Na gaya miki -komai ya yi zafi.’ maganinsa Allah. Ki daina tunanin‘kallon da mutané za suyi min, idan ba haka ba, zaki sawa kanki wani ciwo”. Ta yi shiru tana share kwalla. Kowa ma a motar shiru ya yi. sai Imam dake ‘yan‘ surutansa.
Sun iso la’asar_ ta ‘dan bada baya kadan. Gidan
dankareyakeda Bil-Ada’ma wasu nata koke-koke. Yana ~ fitowa jama’a suka tarbe shi, ana ta yi masa gaisuwa. . ‘ Ya kutsa kai cikin gida tare” da iyalansa, sabon kuka ya barke a dakin gwaggo shi da kansa Alhajin yake ba mutane hakuri. Daga nan ya shiga dakin Baba Liman inda gawarSa take. Ya zauna ya rungumi kansa, yayi masa addu’o’i masu yawa. ‘ ‘
Babu bata lakaci aka fito da shi, don dama can a shirye take gawar. Tuni gwaggo ta yi masa wanka, ta shirya shi cikin’ likafaninsa, daman Alhajin kawai ake jira.
Don haka ba’a bata lokaci ba, daruruwan jama’ar Kauran Juli suka sallace shi, suka kuma rakashi masaukinsa. Hankalin Alhaji bai gama tashi ba, sai da ya maida kasa ya rufe shi.
Hawaye shar-shar! Suka wanke masa fuska. A
haka ya ‘tsugunna, yana masa addu’a. Sun bar._ ma’kabarta; yake‘ gaya wa jami’an .tsaron yanaso  ya’koma
gida. ya:bar wa mahaifiyarsa sako. Ba musu, nan take suka rankaya gida.
Yana shiga, ya iske har’ Hajiya Suwaiba ta kebe da gwaggo da Inna Mairo tashaida masu dalilin rashin ganin Alhajin tun shekaranjiya. Shiya sa kukansu ya . karu, Suke ta yin sa gwanin tausayi. ‘
Saboda haka suna zama. gwaggo ta fara da cewa “Allah zai yi maka sakayya Alhaji, tunda Alhaji Barra’u ya ci amanar ka. Da yardar Allah bazaka tozarta ‘ba.
Kai dai kaci-gaba da tsayawa akan gaskiyarka.
kuma ina mai tabbatar maka har Malam ya cika, yana. ‘ sanya maka alharka  Don haka baza ka wulakanta ba _
Abdul-Rasheed, koda babu wannan mukamin a hannun ka”..
Tayi shiru tana gage kwalla. Alhaji ya numfasa. Yace “Na’gode gwaggo,.ke ma abinda nake so dake.‘ shi ne ki kwantar’ da hankalin ki.
Na san dole abin ya dame ki, kasancewar ni kadai yafi cancanta da zama’ bisa shimfidar makokin Baba.
Amma babu yadda muka iya, ya zama wajibi mu duka mu dauki dangana’da hakuri. Ke ma Mairo kiyi hakuri, ni da Baba bama bukatar’ kuka. Addu’a mukafi bukata, kin ji? don Allah komai ya wuce”.
Tace “Na ji Yaya, amma duk da haka sai, nace Allah ya isa tsakaninmu da Alhaji Bara’u da dukkan wanda yake da hannu wajen kulla maka sharri”. ‘Hajiya Suwaiba ta café.
“gaskiyane Mairo, .tabbas zasu gani nan bada dadewa ba”. Alhaji ya numfasa. Yace “Shi kenan ya isa‘. gwaggo ina fatan akwai Wadataccen abinci?-ldan babu, mu koma tare da Suleman su kwasu, duk kayan abincin dake can gida”. ‘
tace “Kar ka damu, akwai abinci”. Hajiya Suwaiba tace “Nan wajena ma ‘akwai‘ kudade za su kai dubu biyar, na san zasu isa cefane da sauran su”. ‘
Yace “To madalla, ni zan koma, sai yadda hali yayi. Allah ya jikan Baba”. duk suka amsa da “Amin”. Ganin ya mike kuma duk sai hawaye ya ciko  A idanuwansu.‘ Ba zasu iya hadiye su ba, shi kuwa da sauri ya fice.
Yayi sallama cikin .jama’a, hankalin kowa ya dawo gareshi, suna amsawa.‘ Ya dubi Ladan yaci-gaba da fadin “Baba wadannan da kuke ‘gani jami’an tsaro ne daga hedkwata kuma suna bakin aikinsu ne, na binciken
wata matsala da ta taso a ofishina. 
Saboda haka yanzu za mu koma ne da su, dumin daman dan lokaci aka ba ni inzo in samu jana’iza. Ina fatan kowa anan zai taimaka min da addu’a, tare da yi min kyakkyawan zato a wannan jawabi nawa”. Ladan da Malam Lado da sauran dattijan gari kam har ma da mata sai suka dauka da salallami, ‘
’ Ladan Yace “Subhanallahi Alhaji wannan al’amari. sai mu ce jar’abawa’ ce don ba ganin ido ba mu mun yi imanin kai da ne na halas wanda muke alfahari da shi. Saboda haka da yardar Allah za ka fita daga ko wane irin zargi ake maka.” . ‘
Malam Lado ya karba, “Tabbas haka yake. ‘InSha- Allahu ka na nan tare. da albahkar iyaye, babu abinda 2ai sameka, sai alkhairi Alhaji Abdul-Rasheed.”.‘Farin-ciki‘ya lulluba shi, ya daga hannu. yace
“Mu yiwa Baba addu’a!” Bayan sun‘kammala yayi musabaha da kuwa, ya wace mata DA maza. Jama’a suka yo caa! kowa na fadar albarkacin bakinsa na fatan alkhairi.
Haka suka wuca, suka bar kowa‘zaune Suna jimami tare da alhinin wannan al’amari,‘ duk da. ba su san ko menene ba. Amma kunsan tashin hankalin mutumin karkara, idan aka ce magana ta hada da hukuma’
‘ Suna tafe. Alhaji baya ganin komai sai fuskar mahaifinsa. Baya jin komai face kalaman da aka .gaya masa a matsayin’sakon sa zuwa gare shi. Nan da nan hawaye suka tsinka masa,’yasa  gefen rigarsa yana
sharewa. su kansu jami’an tsarun nan jikinsu ya yi la’asar, don ba su taba ganin mutUm mai kwarjini wajen jama’arsa ba, irin Alhaji Abdul-Rasheed.
Tabbas babu abinda zai kawo hakan, face aikata alkhairi. Magaji ya ajesu hedikwata, hai bata lokaciba ya’ wuce unguwan Shanu, don isar da sakon rasuwar kamar yadda Hajiya Suwaiba ta umarce shi. ,
Washe gari‘ jama’a nata tururuwa Kauran Juli, don’ yin gaisuwa ga iyalan Liman Malam Yusuf daga kuina, amma ba sa‘ ganin Alhaji Abdul—Rasheed, kowa kuwa tambaya yaker yi.’ Babu hoye boye kai tsaye ake. gaya masu matsalar data same shi. –
Kowa ya yi masa addu’a kuma ya tausaya‘masa gameda. Wannan al’amari s gwaggo ta lika cikin ranta ya yayi mata karan tsaye Cikin zuciya, shi yasa hawayen ta keyawan zuba, sai dai bata gaza ba wajen tashi cikin dare tana gaya ‘wa Allah damuwarta. ‘
Haka’ Hajiya Suwaiba ta tsaya tsayin daka kiyamul-laili, don kai kukanta wajen Ubangiji. Inna Mairo’ tana nata bakin kokarin sallolin nan hiyar, hannunta na sama, don rokan, gudummuwar Sarkin da- baya gyangyandi
Can wajen maza a waje, duk sallah sai an sanya liman da Alhaji Abdul-Rasheed cikin addu’a. Abinci kuwa
tun ranar da Baba Liman ya rasu, ba’a daura tukunya ba.
saboda abincin sadaka ya wadatar har fita akeyi dashi ana rabawa almajirai. ldan ka ga tukunya akan wuta, to ba zai wuce
ruwan zafin wanka ba. Ko dama gwaggp da Hajiya Suwaiba, ba wani kula abincin‘suke yi ba.
A kwana biyu. gwaggo ta wuni da matsanancin ciwon kai. Har’ washe garin ranar uku. Magunguna kawai Hajiya Suwaiba take bata tana sha. Akayi addu’ar‘ uku. Jama’a suka ragu. ‘ –
Amma duk ‘da haka akwai maza a waje. Suleman na .cikinsu, sai dai shi zaman da’yayi shiru, ba wai yana jimamin tashin hankalin biyu bane. Matsalarsa, ina za’a . jingina zancen aurensa da Murja? ga wannan gagarumin
,fada ya taso? ‘ ‘
Tun ranar, da abin ya faru, gabansa yake ta faduwa, kuma tamhayar ke hanasa barci, domin‘yana bukatar‘amsarta.
,Zaune kawai yake ana ‘kallon gangar jikinsa, amma ‘zuciyarsa nacan yana lissafin, yau lahadin karshen wata, ranan da za’a kaiwa su Murjar’ ziyara makaranta.. Siyayyarsa na can kulle a daki, ji yake kamar yayi tsuntsu yaje ya dauka, ya wuce. ‘
‘ Ya runtSe ido, ya ‘sauke wawan -ajiyar ‘zuciya., Malam Ladan dake kusa dashi, ya kafaa masa ido jim, kafin ya dafa shi. Yace “Hakuri zaka yi Sule,~ zafin nan kowa
kowa yana jinsa, amma daurewa ake yi. Da yardar Allah Babanka ba zai wahala ba. Allah zai kubutar da shi.
Ya dubeshl, yayin dan yace”Allah ya amshi rokon mu”
Ya amsa da “Amin”. Kai zuwa karfe goma ya ga ba zai iya jurewa ba. tashi ya yi’tsaml Ya shiga cikin gida ya kra Mamansu gefe ‘
Yace”Mamanmu ldan akwai kudi a wajan ki.’don Allah kiba ni in tafi Kaduna .in dauko kayana. TUn da muka zo  riga daya na ke ta fama,DA ita sai dai Inyi wanka in maida ta.har Ta fara wari Wallahi”
Tace “dama ba ‘ka dauko kaya ba?” Yace”Ina ma na tuna da wani dauku kaya”. Tace “Ina zuwa”.- Ta juya da sauri tana fadin. “Ai dole suyi wari, kwana uku ‘ waSa ne” . ~ ‘
Yana tsaye ta dawu da kudi da makullan gidan ’ta mika masa. Tace “Idan ka ga da sarari, don Allah ka leka mana Alhaji”. yace “Shi ma Magaji tun shekaranjiya bai zoba”. Tace “qila  ya zauna gunsane, tunda babu kowa kusa da shi, koda wani Abu ya faru  sai ya hanzarta zuwa ya sanar mana”. –
Yace “To sai na dawo”. “A sauka lafiya”. Yace”Amin”; Ya yi waje..Yace ,wa su Malam Ladan an aikeshi.  Kai tsaye ya nufi bakin titi, bai dade ba ya
samu motar Kaduna suka cilla.
Yana isa gida, ya sheka wanka ya sha ado da gogaggiyar shadda, ya dora. hula ya daura agogo ya zura takalmansa ya Suri kayan tsaraharsa ya fito. ya kullé gida ya kama hanyar makaranta a Tasin ,da ya’yi shata. Kusan Murjar ita kadai ce ba’a’ zo mata ba, shi yasa tana ganinsa, ta kidime da murna.
‘ Nan da nan ta nemar masu wajen zamasuka- kebe. Kanta sunkuye ta gaishe shi. “Yaya Suleman ina yini?”
Ya amsa cike da fara’a. “Lafiya lau, ina fatan‘ . gimbiya ta ma kalau take?” Ta amsa da kai; ba tare data kalle shi ba. ‘Karatu ya yi zafi ko?” Tace “Sosai ma. Kai . kadai ne yau’?” Yace “Ni din ma satar jiki na yi na ‘gudu nan Wallahi Baba Liman ne ya rasu, duk suna can”.
Karonta na farkoda ta dubesh‘i sosai, dafe da kirji. Tace “Ya yi me? Allah Sarki Baba’Liman. ‘yaushe ya rasu?” Yace “Yau kwana uku”. .‘ .
Ta kada kai cike da’ alhini, idanuwanta taf! ’Da kwalla. Tace “ Allah ya jikansa”. Ya amsa da “Amin”. Suka dan yi shiru. ‘Murja‘na ta jimamin mutUWa,_kafin ya katse shirun.
“Kin san abinda ya hana in daurewa’har na tasu na ta’ho?” Ta gyada kai. “A’a”. Yace_”Matsala ce babbaa ‘ta taso Murja kuma~ na tabbatar za’ ta iya shafar soyayyarmu.
yace a takaice dai su baba da abbanku suna hannun ‘Yan-Sanda” Ta dago kai ido waje.’Tace da
karfi “Ma?” Yace “Natsu ki kwantar da hankalinki, in warware miki yadda maganar take”.
Ya kama ‘hanya tiryan-tiryan har ya kai ta inda yakeso ta sani. Take nan ta .goce da kuka, tana fadin. “Na shiga uku! Na shiga uku!!” Yace _”Ba maganar shiga uku bane Murja, ni na kasa gane‘ gaskiyar lamarin. Baha yace bai san komai ba akan maganar.
Abban ki ne da Mr; Bulagun suka kulla masa sharri. Shi kuma Abbanki yace Baba ne. Wannan magana  akwai rikitarwa a ciki, yanzu gashi
Zumunci ya rushe lokaci daya. Damuwata kawai. kar maganar nan ta shafi auren mu. Kinji matsalar da ta hananisukuni ‘ ‘
Ta yi shiru sai sharar hawaye take yi, saboda ba ta san abinda za ta ceba, domin sheka’runta kalilan ‘ne. Bata da cikakken hankalin da zata yiwa maganar alkalanci. Ya kara-matso ta sosai. Yace.
“Mé ya sa ki ka yi shiru; Murja? Kin fi so’. a raba mu ne? Shi kenan mu daina ganin juna kwata-kwata? Kin san Allah  muddin aka raha mu, mutuwa zanyi’nima a binne ni, tamkar yadda aka rufa Baba Liman, Ki‘na son hakan ta faru’ dani ni?”
yarinta yasa ta girgiza kai DA sauri
don har
cikin zuciyarta ta amince Suleman zai iya mutuwa, idan aka raba su.
YaCe. “To ki yi magana mana, ki gaya min kalaman da zasu‘tabbatar min baza l<i yarda arabamu ba?” Tace “Me zai sa su raba mu? Ai basu fada za su raba muba ko? Ko sun fada ne?” Kamar ya dora hannu ya kwurma ihu. .
_ “Baki gane yarena bane Murja? Sai sun fadi, sannan za mu gane hakan? Bayan ‘na gaya miki Umman ta zo ta tafi da su Khalid! Don Allah ki daina maida kanki yariya’ ‘yar karama mana
Ya kamata ‘ki’ gane’cewa wannan rigimar za ta ‘ ‘iya rushe alkawarin da aka yi min ‘na auren ki. Amma idan na sami goyon baya daga gareki, dole su kyale mu, muyi aurenmu. Kin ji?” 1
Tace “Naji Yaya Suleman,.kuma-na amince. Na ‘ ma san kafin lokacin sun manta’da rikicin, wata kila ma su shirYa; ‘ tunda akwai sauran lokaci”. ‘Ya sauke numfashi.
Yace “Yanzu ki ka .yi magana  Murja, to ki share hawayenki, ki daina’kuka rai na ya daina baci. Kin
ga, ga tsarabar l<i duk’ abinda ki keso akwai a ciki. Kin ji?” ta share hawaye taja katuwar. ledar ta leka. Tace. Na gode”. Ta dan dube shi ta sake fadin. “To yaushe za’a saki su Baban?” Yace “Allah kadai ya sani.
, kiyi masu ‘addu a . Tace “Allah ya sa kar su dade ‘ Yace “Insha-Allahu ba za su dade ba. Ki kwantar da hankalin ki, kin ji?” Ta amsa da kai. Ya sake fadin “To ni bari in zo in koma. kar Mamanmu taga na dade kwara na tafi ko
Ta kara kasa da’kai. Ya yi murmushi. Yace “Murja ta kenan, Sarkin kunya. To ki yi murmushi mana in gani ko na ji sanyi a rai na”; Murmushin ta yi, ‘amma kunya sosai ta kara lullube ta. Ya mike tsaye, ita ma ta yunkura ta tashi. “Zan tafi,‘ba ki gaya min wata kalmar‘ da zan rinka tunawa da itaba?” ‘
Ta dan. rufe fuska. tace “Ka gaida Mamanmu”. Yace “Kin kinsan ba zan fada ba, tunda ba da izinin’ta na_zo ba. Kawai ki ce Yaya Suleman ina sonka, in tafi da farin- ciki har kauyen mu, ba zan daina dariya ba.
Ba don ma Baba Liman ya yarasu ba,kuma ba’a dariya gidan mutuwaba, ai da har cikin gidan zan shiga ‘ina kyakyatawa.” Ko? “To gaya min’in tafi?”
Tadan juya gefa, tana murmushi tare da ‘yar rausawar kunya “Ko ba kya sona ne?” Take nan yai mata dahara ta amsa. “Ina‘sonka mana”. Ta yi kasa da kai ta rufe fuska. Bakinsa har kunne. ‘
Yace “Na gode gimbiyata. Sai wani lokacin ko?”
To“Allah ya kiyaye hanya”. “Amin””- YaWUce
taka masa har zuwa inda ya kamata ta juya. sakai sallama, ya wuce.
Ta dawo inda suka zauna, ta sake zama ta yi shiru tana tunanin Abbanta, a lokaci daya tana mamakin yadda wanann al’aamrin ya faru haka. Allah da ikonsa, wucewar minti ashirin kana Da tafiyar Suleman.
Sai ga Mansur ya bullu, shi ma dauke da leda mai giwa a hannunsa. Ya tambaya akanuna masa ita inda take zaune, rungume da kunci. Kawai ji tayi an dauke hannun  daga‘kuncin. ‘ –
Ta dube shi da sauri a .firgine, har da ’yan kwallarta suna bin fuska “Yaya Mansur!” Ya zauna inda Suleman ya tashi. ‘yana munmushi.
‘ Yace “Kukan me ki ke yi? Ba‘ki ga kuwa ha ko? Wallahi mutar dana shigo ce, ta lalace a hanya da tuntuni na iso”. Ta gage kwalla. Tace “Sannu da zuwa”. Ya amsa. ‘ Ya karatu?” Tace “Lafiya lau”. “Ina fatan ana yin karatun?” Tace “Sosai ma. Ya su Yaya Nasiru da Umma?” “Kalau suke”. Ya jawo ledar gaban ta. Yace “Maye anan’?” Kafin ma ta ba shi- amsa tuni idanuwansa suka gane masa.
“Wa ya kawo miki?” Kai tsaye ta amsa “Yaya Suleman ne ya kawo min, bai jima da tafiyaba  hala kunma hadu. Shi yake gaya min abu’buwan ‘da suka faru. Yayi
Mansur don Allah da gaske ne?”
Ya murtuke fuska. Yace “Da gaske ne, kuma
gara da Allah yasa ba mu hadu ba, da ya ga wulakanci. Shi in banda shi dabba ne har ya yi tunanin zai sami
auren ki’?”
Murja ta firgita sosai, sai a lokacin kalaman Suleman suka tabbata gaskiya a gareta. ldo waje ta dube shi, Tace “Yaya Mansur‘ maganar nan ta yi zafi sosai ne?” A fusace yace “Ta yi har ta zarce yadda ki ke zato
d Umma tace kar in gaya miki, don kar a daga miki hankali a makaranta. Amma tunda wancan mahaukacin ya zo ya fadi, zan iya ce miki yadda ki ka san rikakken barawo, ‘haka ‘Yan—Sanda Suka watsawa Abba ankwa, suka tura mntar su. Kuma ya yi rantsuwa bai san komai akai ba. ‘
Baba ya kyauta kenan? Ai idan za ka yi abinka, sai ka yi can abinka kai kadai, bawai ka jawo wanda bai ji ba, bai gani ba ka ce har .da shi! Ai da ba ta tashi ba shi kadai zai ci kudinsa! Amma don zalunci.
Yace da hannun Abba, saboda ya san komai yana karkashinsa. in dai na Fambeguwa ne. Sabodahaka ki kama kanki, idan har ki na kishin mahaifinki!
Ki yi masa addu’a. Allah ya kubutar da shi. Ni dama Suleman ba kaunarki na ke yi da shi ba, saboda bai
da tunani da sanin me ya dace a rayuwa mai kyau? Kin ji abinda na’fada?”
1 Ta gage kwalla. ba ta amsa ba. “Na ji kin kyale ne. me Sualman din Ya gaya miki?” Tace“Ba komai” Yace. “Karya kike yaxo, yana zuga ki ko? Ki na sonki gaya min wai ke har yanzu ki na sonsane To karya ki ke don ubanki! Kwaya nawa ki ke? Ke bari ma in tambayeki, nan ina nE?”
Baki tura, ta amsa “Makaranta”. “Me aka ‘yi ‘ cikinta?” Ta amsa “Karatu”. Yace “To shi za ki yi, zan ga shegen da ,zai zo. ya gurbata miki kwakwalwa da . . soyaYyah ‘Ba. ki isa yin ta ba, ku’ma ba za ki yi ba! Kin jini’ ai?” Tace “Ka yi hakuri Yaya Mansur, ni Wallahi duk kun ruda ni, na rasa inda zan fuskanta”. ‘ ‘
’ Ya nuna kansa. Yace “Ni, ni nan za ki fuskanta, har yanzu shekarun kurucciya gare ki, saboda’haka ragamar- tarbiyar ki tana hannun mu. Kin ji abinda nace? Zan kuma gaya wa Umma ta san .matakin da-za ta dauka; tun kafin abin naki yayi  nisa Ungn nan, Umman ce tace in kawu miki.
Da tace‘ kar in gaya miki, tunda kin sani, sai‘ki nasu ki taya mu addu’a kar’ kuma ki sa damuwar daza ta hana ki karatu. Komai zai’wuce Insha-Allahu. Suleman ne kawai na ke so ki cire shi daga wannan ‘yar’ jaririyar zuciyar‘ ta ki, «lokacin da za ta fara soyayya bai yi ba, kin ji ai?” ‘ ’
Ta amsa da kai tana share, fuska. “To shi kenan. ki daina kuka autar ‘Umma. Ni zan wuce Zariya
makaranta. kar ki manta da yi wa Abba addu a . Tace “Tona gode”. Ya kama hanya. ya wuce tana kallon sa.
Tasa tagumi, ta shiga sakar‘ zucci “Ni Wallahi duksun dagula min lissafil In banda abin Yaya Mansur menene na wannan masifan? Ya ma’ manta da makarantar‘. < da yake rawar jiki zai koma. Baban ne ya sama mashi  Mun riga mun zama daya, ya kamata a shirya,‘ ba don wai Suleman na sona ba. Allah ka yaye mana bala’i!”
Ta yi ajiyar zuciya, ta sake fadin. “Kai! Yayaq Mansur ya iya masifa”. Ta kada kai “Kenan maganan Yaya Suleman zata tabbata gaskiya? Kai. zama su shirya kafin lokacin‘ insha-allahu”.’_ ‘ ”
Ta gage fuska ta hada ledojinta, ta koma ’(HostEl) . dakin kwana .su. Haka ta kasance cikin damuwa, dakda ma ba ta da wayau kwarai al’amarin ya .jefa ta cikin ‘ tunani ’
tan tsananin .tausayin iyayen nasu biyu..Ta jima barci bai dauketa ba a wannan daran Sabanin shi Suleman, hankalin sa kwance yake_ tun – fituwar’sa makarantar. har ya koma gida, ya debi ‘yan kayayyakinsa a jaka ya koma. Bai tashi tuna Alhaji ba.
Sai da motar su ta shigu Marabar Jos. Yaja dan tsaki. Yace a ranSa. “Koma naje ma wahalar banza zan yi,. tunda ba bari suke yi a ganshi ba; Kawai zan yi, tunda ai bani nace yaje yasa kansa cikin matsalarba ya qara Jan tsaki haka kawai naje wani qaton banzan yaxo ya dinga jeromin tambayoyi karya kawai zanyi musu idan name nace naje Amman ankibarina na ganshi

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

my hadu a book2 in Allah ya kaimu donjin yaddah wannan taqaddamar zata kasance meye ra,ayinku shin shin shin shin lol mudai hadu Ina fatan kuna karantar darussah masu damage

naku bar kullun
WhatsApp.   @08035453572

www.Facebook.com/abdullahi.Ismail.salanke

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]