Makaranta duniya chapter10

Makaranta duniya

         Chapter10

Ayyukan alkhairin Alhaji ,Abdul-Rasheed kullum dada gaba sukeyi ga kowa, musamman ta bangaren amanar jama’ar gari dake ofishinsa. Ya kawo cigaba sosai a sababbin ma’aikatunsu dake Fambeguwa da lgabi da Dutsen-Wai, karkashin kulawar AlhajiBara’u.
Duk wata cuwa-cuwa da magun magun da akaso
‘ayi. sam-sam! Bashi a Ciki koma duk hanyar da zaibi yaga ya hanata, to zai bita, dun ganin ba a yi .sama da fadi da dukiyartalakawa ba.
dalilin dalilin ‘da yasa kenan sukayi
bannun riga da’mataimakinsa Mr. Bulagun. Shekaru biyu
da rabi .kenan yana matsayin mataimakinsa kuma ya
kosa akawo wanda’zai canjeshi, kamar’yadda aka saba. amma shiru.
Sai. dai zaman naSu bai‘hana Alhajin gudanar da
ayyukan ci-gaba ba, ko a karshen wannan watan, yanasa
. ran isowar‘wani katon Injin bada wutar’ lantarki da za’a
aje a Fambeguwa, don bawa ma’aikatar  wutar‘ lantarkin
~ ‘ Maganar da suka yi kenan su uku a afishinsa, ‘
watau’ shida Mr. ’Bulagun da Alhaji Bara’u. Dukkan-
takardu sun kammala, kowa ya sanya hannu; umarni’ya tabbata’za’a kawo wannan lnji Fambeguwa’
Bayan kammala maganar ofis, sai suka kebe, inda Alhaji Bara’u ke gaya masa‘ -zai kawo Murja makarantar queen amina Amman gidanka Zan Fara kawota kafin na gama mata shirye shirye alhaj din tai murmushi gamida cewa girma dai ba wuya yanxu had murja ta isa shiga makarantar kwana? alhaj barau yace ai kasan girman yaya mata ba wuya yace to Allah e kaimu saika kawota din
Komai a aljihunsa yaka yi, shi kansa Alhaji Bar’a’u yasan Zai bata masa rai ne, muddin ya dunfaroshi da ‘ wasu kudade a matsayin kudin makaranta ko na wani
abu.  Alkhairin Alhaji Abdul-Rasheed ya wuca duk inda
ake tsammani. Domin ba ‘ya’yan AlhajiBara’u kadaike karkashin sa ba, akwai da yawa ’ya’yan garinsu wadanda yake daukar” nauyin karaturnsu a makarantu daban—daban. Wasu ‘yayanma bai taba ganinsu ba, kudin kawai yake ‘ caskewa iyayensu, musamman idan‘ aka ce marayu ne.
Bayankwana bakwai. Aka gamawa Murja shirye- shiryen‘ta. Ranar litinin da safe aka zuba kayanta a boot. Hajiya Suwaiba kamar tayi kuka. Shi kansa Imam da kyar ta amsheshi a hannunta, idanuwanta suka ciko da kwalla A haka ta shiga mota. Alhaji da Mansur suka wuce da ita. Amma sai sun fara a‘ja su Sulaman tukunna.
Hajiya Suwaiba ta wuni jikinta a mace,» saboda‘ kewar Murja. Asheba ita kadai bane. Sulaman ma yana can makaranta tunani ya ishe shi. A hakikanin gaskiya bai san abinda ke damunsaba, harya tsananta masa tunanin Murja cikin ransa. ,
Ya jima yana yawan son kallonta, amma zuwanta a wannan karon,al’amarin ya kara daukar sabon salo, domin tsawon kwanakin .da tayi, kawace rana da ita yake kwana, yake tashi cikin ransa. ‘
Bai dai nunawa kowa ba. Sai dai yau Zuciyarsa na son tAyi masa tonon- asiri Idan har taci-gaba dayi masa sake-saken da yakeji a halin yanzu. Har suka dawo gida. bai gane kansa ba.
‘Suna tacin abinci a falo. Hajiya Suwaiba ta fito janye da hannun Imam. Kai tsaye wajen samarin ya wuca. Mansur ya cafe shi,‘ ya dora bisa cinyoyinsa, yana fadin “Imam Yusuf,,_gaya min loma nawa zakaci?” Yayi dariya, yasa yatsu biyu ya debo kwayar shinkafa ya‘ kai bakinsa. ‘ ’ .
‘ Hajiya Suwaiba ta zauna. Tace “Allah Sarki Murja ana can. Ko wane wainar- ake toyawa?” Mansur. Yace “Kuka‘mana. Ai ‘nasan kukan nan ba yau zata gama shiba”. .
Ta doka tagumi. Tace “Duk tausayinta ya kamani- Wallahi, kamar inje in dawo da ita. Tayi je ka. ka dawo”. “Ta zauna can Mamanmu, sunfi karatu‘, don babu’wasa‘ kuma babu abubuWan da zasu dauke masu hankali”. ‘
Inji Mansur, yana ba‘lmam abinni da cokali, ta dan numfasa. Tace “To, Allah .ya hadata dana kirki. Amma abin akWai ban tausayi, ai Murja ‘yarinya ce, girman jikin kawai”.
, Ji sukayi Suleman ya sauke wawan numfashin, daya‘ dauki hankulansu. ‘kowa ya dubeshi, ‘lokaci guda Maman tasu na tambaya “da akayi me Malam Sule?‘ Wannan ajiyar zuciya haka”. Sadda kai yayi; yaci-gaba’
da tura abincinsa. Sai wanan Ya kalli wannan nancan ya kalli wancan
“SUleman manya. da’ alama yau akwai magana; tunda ka shigogidan nan banji muryarkaba”. Khalid ya amshe “Kuma ya’u ,haka yayita zama shiru, Kin san ba komai yake son‘fadi ba, shiyasa ma ban tambaye shiba”.
Ta tashi tsam! Ta-dawo’gaban tebur din, ta tsaya kusa da‘shi‘-“Me, ya faru Malam Sule?” Ya‘dube ta‘kadan. Yace. “Ba knmai Mamanmu”; “Tace”Da komai Suleman, ka gaya’min kawai. Ko sai munsa labulene?”
.Yayi .dan murmushi kamar yadda Saura ke murmusawar. Ta kara fadin Haba ni na‘san akWai magana. tomu shiga daga cikin inji yadda aka yi”. .
‘ Ya kada kai. Yace “Allah babu -komai Mamanmu’. Tatabe baki. Tace “Shikenan, kuna shaida ko?” “Sosai ma”. Duk suka amsa. ~Shima Imam ya maimaita, abin‘daya sanYasu’ dariya‘kenan; “Yauwa Baba, kaima ka shaida natambaye shi. ko?‘ Idan tayi war’i, 2amuji.ko?” Ya amsa da kai, suna ta dariya.
shi. kuwa Suleman’yana ta ‘faman. juyi. ‘Abin fa kamar yai hauka  yakeji ” to menene Shi? Bai gano’amsanba har gari ya waye,  ya tabbatarma’da idanuwansa; yanason ganin’Murja kuma‘kunnuwansa na’kaunarjin ‘sansanyar muryar ta.
Wandon makaranta ne a jikinsa da farar T. Shirt, lakacin da yayi sallama dakin Hajiya Suwaiba, ta amsa tana kokarin cirewa Imam nafkin, don tashin sa barci kenan. Ya tokare jikin kofar dakin, Yace “Ina kwana Mamanmu?’’
Ta amsa tana saka Imam ’cikin bahon wanka;‘ ruwan dumi ne a cikin butar da take masa tsarki. Jim kadan ta sake dago kai ta dubehis yana nan tokare da kofa. Ta tsananta kallonta gareshi.‘ ”
TaCe “Lafiya Sulaman?” Yayi‘ dan Shiru, sannan . ya kada kai.‘ Yace Babu komai, ,kawai-na shigo gaisheki ne”. Ya juya zai wuce, tasa baki ta kirashi. “Suleman” . . ,
Ya juyu yana amsawa. Ta fidda Imam daga bahon wanka, suka fito tsakar daki. Tace “Zauna Suleman”. zaman rakumi ya yi Watau bisa guiwoyinsa‘ya zauna. Ta kara dubansa da kyau. Tace.
“Shin Suleman kana da wanda, ya wuceni ‘ anan’?”Ya kada kai, ta sakefadin. “To me’yasa kake boyemin _ damuwarka? Ko ka’na zaton bazan iya magance maka ita bane?” Yayi shiru. , . . ~
_ “Tayi jim, tana kallonsa, kafin ta sauke numfashi taci-gaba “Koni bazan iyaba, ina jin Babanka na‘nan da ransa. .
Ban zaton akwai abinda zai gagara shi, sai dai in
Allah bai hore masaba. Amma kake ta zama da damuwa _
tun jiya, ka kasa gaya wa kowa. Kowata rigima‘ka jajibo, bamu sani ba?”
Ya karakada kai “Toka gaya min ,ko manene’ idan ya wuce da sanina. akwai‘na gaba dani”. Tun daga goshinsa ya shafo zuwa keyarsa, ya kuma dawowa da .shafar kan. Tayi dan murmushi. Tace”Wannan shafar kai ko a cikin alwala ta yi Suleman”. –
Shi ma murmushin yayi, ya dan sadda kai jim. ya sake dubanta. Yace “Dama….., Dama ’so nake ,in tambayeki, maganar nan da Baba yayi akan Murj’a, tana nan? Koda gaske wasa yaka yi?”
Ta fahimce shi sarai, kuma dariya ce fal cikinta. amma sai ta boye, ta fara zolayarsa, ta zura masa ido ta ‘ tambayeshi “Wane magana?”
Babanka, ya fadi, fuska yamutse. Yace Kin manta Mamanmu, ba Baha yace yayi min rikonta ba. Mamanmu?” Tace “Rikon wa?” Ya kara shafa kai,_ ya amsa “Auran Murja mana, koba haka Baba yace ba?”
Fuskarta. dauke da dariyar zolaya. Tace “Wannan magana ai ta wasa ce Sulaman, tun yaushe aka barta? Don kace bakaso ba?  ‘
Kamar zai yi kuka. Yace “Ki gane, mana .Mamanmu”. Bakinta sake tace “Me zan gane? Maganar nan bakaso ana yinta, shi yasa kowa‘ ya manta da ita”. ‘cikin hanzari ya ‘bata amsa “Inaso‘Mamanmu. . Wallahi inaso”. Shi kansa bai san lokacin daya jero
wannan bayanin ba. gaba daya suka yi tsam! Da numfashinsu na ‘yan
dakikai, kafin tace “Suleman kenan, yanzu Murja ta zama mutum ko?” Ya sunkuyar dakai. Yace “Ba haka bane, kin ga da ni kaina ban san ke Mamanmu bace, ban ma sa waye ni ba, balle wannan maganar. Sai da hankali yazomin.”
‘ Ta numfasa dauke-da murmushi. Tace “Kafini gaskiya. To .yanzu ka gane ko wayé kai ko?” Ya jawo ‘ hannun Imam yana kadawa. Taci-gaba da fadin. ‘
Ai shi kenan, mu sai shan biki, tunda daman can Babanka ya yi maka riko. Matashiya kawai zai yiwa iyayen ta. Amma banan gizo ke sakar ba, sai an tabbatar da cewa ita ma Mur’jar tana sonka. Saboda haka kayi addu’ar Allah yasa_ta soka”. ‘
Ya hadiyi miyau da kyar. Yace’”Ki tayani addu’a Mamanmu. Sannan ki far’a lallasan min ita, duk ranar da ‘ kika sami ganin’ ta, kinji Mamamnu?” Tace “Karka damu, duk da cewa Murja yarinya ce karama, zanyi iya kukari inga cewa babu wanda ta aje cikin ranta, sai dana Suleman”.
, Ya washe‘baki yana fadin “Na gode Mamanmu. Bari inje na gama shiri”. Tace “Ya kamata”. Harya ‘ kama hanya zai fita, ya sake dawoWa. ‘
Yace “Kin sani wani abu Mamanmu? Don allah karki bari su Mansur su sani yanzu”. ldo waje tace “Ah. gaboda me?” Yace .”Dariya zasuyi min, kuma kinsan” bana son ana min dariyar iya shege, kulewa nake yi”.
Ta jinjina kai. Tace “Taf! In banda abinka, ba’a wajensu za kayi kamun kafa‘. ba? Yaushe 2asu-baka, ita kanafada da yayyinta?” Ya dan numfasa, yasa kai ya fice fuskar nan a yamutse. Ta kada kai. Tace “Suleman manya, wake boye abin‘farin—ciki, banda rigima irin ta Sule?” ‘
Ta dauku wando tana sawa Imam, tana ci-gaha da zancen zucci “Lallai yau Alhaji zai sha mamaki”. Ta jawoshi suka fito ita ta shige kicin, Imam ya shige’ dakin samarin yana kWala kira “Yaya.” Iyakar abinda ya iya‘ kenan, don bai. iya kiran sunayensusu ba. ‘ ‘ ‘
Bayan ta kammala shirya masu abin karin-safe. ‘ dakin Alhajin ta’ nufa da nasa tiran abincin. dumaman’ tuwu ne da ruwan shayi, wani‘lokaci  a dama masa’ (coca oath) yasha da madara. ‘Yanaci, tana maida masa yadda sukayi da Suleman.‘Ya kece da .dariya yana fadin.
“‘yana fadin tsakani da Allah dama’ wasa _nake‘masa. ashe abu zai tabbata.~ ,To Allah ya zaba mana mafi‘ alkhairi”.‘Tace “Amin”
Ya dubeta ,da’kyau. Yace“Kin ,san mafarin farinciki na?” Ta kada kai. -“Saika’fadi”. Yace
“Danqon zumuncinmu da Alhaji Bara’u zai kara dankuwa. kinga zamu dawo zuri’a daya”. ‘
Tace “Gaskiya ne. Allah dai yasa itama Murjar taso shi. don yardar ta, itace yardar kowa”. “Wannan haka yake Mamansu. Ina Baba na, bai tashi bane?”
Ta amsa “Ya shige wajen su Yaya.‘ ga motsin ‘su canma sun’fito‘cin abinci”.falo ina ruwan Babana dan gidan su Yaya”. ‘lnji Alhajin, yana wanke hannu a robar wanke hannu. ‘ ‘
‘ Ya yunkura ya tashi._ Yacef’Bari inje zolaya”.;Ta fara, dariya “Baka da dama Alhaji”. Ya’ wuce ta yana ‘yar dariya. Bisa tebur yasame su, kowa na ba’cikinsa’abinda yakeso. Amma babu Mansur a tare-dasu, sa‘boda inba makaranta zashi ba, bai cika fitowa karyawa da wuri ba.
“Baba har ka fito?” Ya tsaya bayan kujerar .Sulaman ya dafa. Yace “Na dai gama shiri na, ku kawai nake jira”. “Yanzu zamu gama Baba”. ‘
Kafin ya amsa. Imam ya riga shi maimaita kalman .“Baba”. Ya kamo hannunsa ya amsa  dan gidan Baba, anaba ciki ne?” Ya dubi Nasiru.‘ ~Yace “Ashe abokinku ya kusa aure?”
Baki sake yake kallon Alhajin, Yayin da. Suleman yasha ‘ jinin. jikinsa.‘ “Wane abokin Baba?” Yace “Wannan …… ? Kaji, kajika baka gane shi ba?” Suka kalli juna da Khalid. Duk mamaki yarufesu. “Bamu gane  shiba Baba, aibamu’da Wani abokida zaiyi aure’ Yace “Kuna dashi mana anan. wani fari kullum yana gidan nan. Sannan’ai an gaya min ’yar uwarku Murja zai aura”. ,
Alhajin na rufe baki. Suleman ya mike, yana kokarin yabar wajen, saboda tsabar kunya. Su kuwa sauran a kwana Alhajin’ya turasu shiya sa bakunansu suke sagale suna‘kallon‘ juna. Alhaji yayi wuf! Ya riqo

hannun sa_Yace “Dawo mana angu, ina za ka?” Ya dawo dashi kujera‘ya zaunar shiba fushi ba, shi ba murna ha, gashi nan dai fuskahba yabo, ba fallasa. ko kuwa duk kunyar ce?
Hajiya Suwaiba ta fito da tiran kayan .abinci, ta ‘ tintsire da ‘dariya. Tace “Haba Alhaji, ya zakayi masa haka?” Yace dole nai farin ciki mana naSiru” Yace’ “Ban fahimci komai ba Baba wai wa zai yi aure, kuma wa zai au’ra?” Ya dafa kan Suleman ya amsa.
“Malam Suleman ne, zai auri Murja, idan har ta amince”Kansu’ya kara daurewa, suka kura wa ‘Suleman ido, jim kadan kuma suka kece da’dariya‘. Suleman ya ‘ tashi da gudu ya banr wajen’ ‘ ‘
Su Nasiru suka bishi‘dakinsu Jakarsa kawai ya sura, ya yabata bayansa, zai sake ficewa. Suka tare shi, dariya sukeyi suna tambaya “Wai dun Allah da gaske
ne?
Kamar’ ya kule, kamar kuma. yana son yayi dariya- Kai da yaga abin babu dama,, sai ya dake, ya baSU amsa’.’Eh da gaske ne. ya ku kace?” ‘gaaba daya suka kawo masa hannu suka tafa, dauke da ihun daya firgita Mansur. ya tashi zumbur’! Ya zauna ya zubo masu ido “Wane irin .wulakanci ‘ne
‘wannan? Baka da hankali ne?” Suleman yayi waja da sauri. “Labari ya barka Yaya
Ya buga tsaki, yana‘kokarin gyara kwanciya,, Nasiru ya fada bisa’ gadon a gigice, “Kasan’wani abu’ Yaya? Wai Suleman yana son Murja.” Fuska yamutse,ya
tambaya “Wacce Murjar’?”_”Wai.Murjar‘mu Ya kara daure fuska- Yace “l‘nji wa?’ Yanzu
’ Baba ya shaida”mana’. Ya sake jan wani tsaki, ya maida kai bisa’ ” filo Jikin NaSiru yayi dan sanyi, yabiShi  da kallo jimawa kadan. Yace “Kamar ka bata rai Yaya Mansur?“
‘Yace “Kuje School kawai NaSiru”‘.”Jikinsa yé mace, ya dubi inda’ Khalid ke tsaye Shi ma duk yayi lakwas Jin sunyi .shiru, basu motsaba, yasa Mansur.din ya juyo’ ya dubesu. “Ba zaku tafi makaranta bane?
‘Zanso ku dubii agogo da wannan‘zaman; da kukw. Nasiru ya numfasa; Yace “Ai .Baba bai fitoba, da Yayi. ‘horn, amma Yaya me yasa kai bakayi murna ba?;
‘  Ya tabe baki. Ya-e “Nima ban saniba, watakila kuma kawai daliline maybe kafin ku dawo zuciyata zata sanar’ dani, kuma sai kuji ko?” r
Duk suka sauke numfashi tare da hon din motar Babansu. Da hannu ya nuna masu alamar ana jiransu. kowa ya dauki jakarsa yayi ‘waje, jiki babu kwari. Mansur yayi dan guntun Isaki, ya ‘fada a ransa. ‘ .
“Na tSani halin Suleman, me zaisa wannan abu ya tabbata, bayan anjimada manta wasan?” Ya sake jan tsaki. barcin da bai sake komawa ba kenan Baima isa ya koma dinba, tunda Imam ya ziyarce shi; Sai da Mamansu._ ta gama kintsa gida, sannan tazo nemansa, dunyi masa wanka.  _ . ” Abin ba haka yakeba wajen iyayensu, domin dai yau itace‘ magana ta farko da suka fara tattaunawa a’ ofis. Kai! Abin ba karamin farantawa Alhaji Bar’a’u zuciya yayiba, shiyasa yake ta addu’ar Allah ya sa a dace‘, ita ma Murjar ta so shi, idan lokacinda-za’a gaya mata. yayi
Al’amarin Yayanta Mansur’ kuwa yinin nan zungur! Ya. kasa sukuni-cikin ransa, don da gaSke yakeyi ya tsani halayyar Suleman, wadanda ba kowa ke ganesuba sai‘wanda ya zauna tare da shi. ‘
Amma’ abin haushin, bashi da wani abin yi akai, kusan ma yafi koWa rauni a cikin maganar donya tabbatar da shi kadai ne baya son abin. Ina ma ace itama Murja tace bata so? ‘ ., ‘
Wannan‘ tambaya ita ‘- ya gallazawa‘ kansa tunaninta. Wani abinda ke kara masa hauShi da takaici,‘
wai ya san ko addu’a ya yi, ba_zatayi tasiriba, don dai addu’arsa shi kadai, ya_ba zata kada ta dimbin jama’a ba ‘ ‘ Kuma ‘harda iyaye a ciki Yayi tsaki, yafi dubu shi kadai a daki. Ai kuwa kamar wasa,‘duk kowa ya sani, duk wanda ya bUde baki. sai yace Allah ya tabbatar. ‘ Satibiyu bayan tafiyar Murja makaranta. Shima Mansur’ nasa shirin ya kammalu. Haka ya tafi suna wa -juna kallon  hadarin kaji shida ‘Suleman. Kaman ya ’san wani abu
wata Kila kuma Suleman din ya gane Mansur‘ baya farin-ciki da al’amarin  ne, domin shi kadai ne ba‘i ce masa kanzil! Ba akan maganar. Ashe duk haushin. kenan, ai kuwa dole ayi‘kallon hadarin kaji. ‘ Ziyara ta farko da- za’a kaiwa Murja a. makaranta, – dan gogan ne a gaba-gaba wajen‘ siya tarkacen
kayan makaranta na sha’awa, haka kuma shine direban su. .
Zuwa makarantar. Babu wata takura a tattare dashi’, duk da cewa Aliyaa ma tazo ganin‘ Murjar, (In law) take kiransa,‘ yana amshewa bakinsa har kunne lol
Watau surukinta. cikin dan kankanin lokaci suka isamakarantar
Murja ta rugoda gudu ta tarbesu. ta tsunguna ta gaishe dasu‘harda dan‘kukanta. Daka kalleta,’ka zaka fahimci ta rame, ta dan yi duhu. ‘ ,‘ .‘ ‘ ‘ ‘  Suleman ya fara ganin’hakan.‘kuma shi ya fara “ korafi “’gaskiya Murja ta rame Mamanmu, da gani. Wuya‘ . kawai take sha a makarantar nan”.
Kowa ya dubeshi yana dariya, kafin suce wani abu Murja ta cafe “Kamar kuwa ka sani Yaya Sulaman. kawai da asussuba a‘ tada mutane, wanka daruwan . sanyi, ina zan iya?-Kwaskwarima na keyi, in goga mai in buga uniform’mu tafi aji”;
“Shi yasa kikayi bakikkirin‘! Murj  lnji Aliyaa. Khalid ya tushe hanci “‘Hmm …… gaskiya wari ya ishani. ashe bakya wanka?” Duk aka tuntsire da-dariya. ‘
Suleman ya naushe ‘shi “Kai zan… Kai ….. ‘. . dariya sukeyi, yayin da Hajiya Suwaiba kE fadin‘. ‘
“Baka kyauta ba Khalid, a gabansa? .Lallai ka cancanci duka”. ,Ita kuwa‘ shagwabe fuska tayi, ta lankwashe jikin Aliyaa. Suleman ya kam Yar kukar -da yarintar take na shagwaba burgeshi.yake Bayan sun natsa, ta tsinke da labarin makaranta. Suleman baki, har kunne.
Ya duka agurni -yasa mata ido, idan-ta ‘bada‘ dariya, ya kada kai, inta fadi abin tausayi, ransa yayi masa zafi, kamar ya je ya rama mata. Anan suka wuni;
Hajiya Suwaiba ta jawo lrdar kayan Suleman. Tace “Kinga wannan’ledar, duk toshin dana Suleman ne, ina fatan alkawarin yana nan?” “
Tace “Wane alkawari Mamanmu?” cike da fara’a tace “Auren mana, kokin manta ne? Ai muna nan
akan bakanmu”. Dubanta tayi da sauri, tasa hannaye biyu ta rufe fuska tare da kunshewa jikin Mamanta.
gaba daya suka hau dariya, shi kuwa sanyi ne ke kwarara cikin zuciyarsa, ya mike ya bar wajen saboda murna, donya tabbata wannan rufe fuskar, akwai gamsashiyar amsa a cikinta,.duk da cewayasan Murja yarinya ce;
Hajiya Suwaiba’ta shafa kanta. Tace “Yauwa Murjar Baba, dawo nan muyi sirri”. Ta jawota jikinta. “To gaya min alkawarin na nan?” Fuskar‘ ta cike da fara’a, amma ta kasa bude idanuWan ta. “Ki’ bude idanuwanki, ai babu shi anan, kice su’Khalid ma’su tashi?”
Ta amSa da kai. Khalid yace “Baki isaba yarinya, ki tadani …… ” “Ka tashi nace Khalid”. Yana’yar dariya. Yace “Banine abokin angon ba Mamanmu?
Ta fadi kawai, ni kuma inje in isar da sako”. Aliyaa ta mike tana fadin “Tunda nina tashi, dole kaima ka tashi. Tashi marar kunya.
Ya mike yana ‘yan kunkuni. Nasiru kuwa tuni ya . nuf‘i inda Sulelman ke tsaye. Hajiya SUwaiba. Tace”‘To duk sun tashi, bude idonki kiban amsa”.
“Ta dagofuskarta, sai dai bata iya .kallontaba.‘ “Tsakaninki’da Allah, kin yarda?” Ta amsa da kai, cike da murmushi, “.Karfa nan gaba kice bashi ba kuma. Kinyi alkawari?” Tace “Nayi Mamanmu”. _Ta kara jawota jikinta. ta rungume cike da kauna. Tace “Suleman yace in gaya miki yana sonki  kuma yana rikonki a matsayin matar da zai aura da yardar Allah. Kin amince masa?“ Ta kara lafewa ta amsa. “Allah Mamanmu na amince”. Ta dafa kanta.
Tace “Masha-Allah mun gode Murjan Baba. Allah yayi miki albar‘ka Yanzu gaya min dame-dame kikeso in kawo miki, idan zamu sake dawowa?” Murmushinta yaki yankewa, ta amsa. “Babu komai Mamanmu”.
“Akwai mana, ki gaya min akwai”, Tace . “Complex da Geisha”. Tace ,”Ashe‘ Suleman ya san abinda kike so. Kinga kayan bikin ledar nan duk su ne, to babu damuwa, kiyi manejin wadannan, wani watan masu yawa za’a ‘kawo”. Tace, ‘ ‘
“Mamanmu ai wadannan ma masu yawan ne. Kice masa na ,gode”.’Tace “babu ruwana wannan kyakkyawar kalmar baki da baki ya kamata ki gayama’, ta rufe fuska daa hannayenta.
Bata san lokacin da’Suleman din ya iso wajenba, kawai muryarsa taji. “Mamanmu gani”. Ta dubeshi “Zakuyi sallama Yayi ’yar’ dariya.
Bai ce komaiba har’ Maman‘ ta bar wajen Sun jima shiru, bahu wanda ya tanka, inda yake zaune’ma ta kasa kallo. Da kyar ya numfasa.’Yace “Ki rinka kulawa da karatu, kin ji?” ‘
Ta kara kasa dakai. .Tace “To”. Ya zura mata ido yace “‘Mamanmu ta gaya miki sakona’?”‘Ta rufe fuska, ta amsa eh.‘ “Tokin yarda?” ta sake amsawa. . DA eh
Dadi ya kara kwanciya cikin zuciyarsa. Yace “Na gode”. Tace “Nima na gode da wadannan kayan”. Yace “Bawannan ya dameni ba, nidai ki’ rike min alkawari,l don allah” ‘

’ Tace “Zan’ rike”. Muryar’ Khalid sukaji’a kansu “Lokacinda yake  fadin lokakacifa ya tafu  koso_ke ayi mana kurar kare?” Duk , suka dube shi. Suleman yace “Meye haka ko sallama?”-
Yace “Uh, da nayi sallamar, baka jiba, amma dana, ambato lokaci, kun jiku? To a tashi a tashi mu ‘ wuce; Su Mamanmu har sun shiga mita”. Ta mike zumbur’! Tace “Sun tafi?”” ” ~
“zadai su tafi yanzu”. Ta sheka da gudu ta nufi gunsu. Suleman yabita da kallu, yayin da Khalid ke kwasar ‘dariya. nan. suka sameta ta kunshe jikin Aliyaa. Khalid yace .”lnbanda hauka, waya gaya miki ana gudu a ‘ gaban saurayi?” Ta shagwabefuska, saura na mata
dariya. ‘ Tace “Mamakinji shi ko?” Kafin ta amsa, ya riga ta. “Ai gaskiya ne”. Tace “Ba wani, ba kai kace zasu tafi ba?” ‘ ‘ r
Yace “Kunji hauka ko? To waye direban’? Don Aallah a rage hauka, sannan a daure a rinka yin wanka
dom.” “Don Allah Malam ya isa haka. duk ka ishe mu da
surutu. Ya …… Ya …… Ya …… Haba”, Dariya kamarta fasa masu ciki, a haka suka yi
sallama. ganin yadda Murja ta narke kamar zatai kuka. Shiya sanya jikin Suleman yayi la’asar’ sakaliya.
Taqi kawai yake shiru,,ba mai ma‘gana da kowa
har suka iso gida. duk da _yana farin-cikin samun amincewar Mur’ja, tausayin yadda take‘ita kadai kwal! A
makaranta; kwarai shi yake kara kashe masa jiki.Anan
aliya ta kwana..
Washe gari bayan Alhaji Bara’u ‘ya tashi ofis“ ‘
suka rankaya gida tare. Kulum yanajin dadin bayanin da‘tayi masa na yadda Murja ta‘ saki jiki da Suleman, ta amsa rokonsa. Fatansa kawai. Allah ‘yasa a ‘cika wa juna alkawari. Haka al’amura suka cigaba ‘da- cikin’jin dadi da kwanciyar hankali, har Murja ta sami hutu biyu a J.S ,1
kuwanne hutu kuwa kusan anan ‘Kaduna take kammalawa
suna haduwa sosai sa sulaiman domin tana jin dadin
kasancewa atare dashi, koda bazasu cewa jUna komai’ ba
. Kusan haka tadin nasu yake, sai dai yawan murmushi
dasatar kallon juna’HAUKA kenan Inji‘Khalid. , ‘ ,
Shi dariyama take bashi..Takanas yake zuwa, ya
kira ta wajen Suleman, don ya tsokaneta, ta ‘zubada
gudu. Yayin dashi Mansur aka sami akasin hakan cikin
ransa. Dadi ma yaji da Allah yasa bashi a garin. Wani karin abintakaici. ’ .
Ya tabbatar da duk siye-siyen da ake cewa yana yi mata, gaba daya kudin choge ne, domin dai babu aiken‘ da za’ayi Wa Suleman, bai yi cuwa-cuwaba. ldan harna kudi ne. Kalilan ne wanda Alhaji ‘ke dauka da hannunsa ya bashi:
A takaice Mansur baya hangen alheri ‘a‘ cikin wannan abu da akeSo a kulla, wanda manya ke’kallonsa a matsayin dankon zumunci. Suleman yana sane kuma‘ya‘ lura da take-taken Mansur.
” yasan yana da ikon,  ya zuga ‘yar uwarsa.-Dalilin ‘da yasa kenan yake kalonsa a dage, harya masa gida cikin ransa.
“ “Mts …… Banza! Yana cin arszin mutane, yana. masu yankan baya”. Kowannen su yana ganin shi mai gaskiyane Amma ga’ . ido mai kallon-kima da sanin yakamata, ya san cewa Suleman yana da‘babbar matsala. ‘ .
Haka kuma akwai matsala  a‘. dangane da janareton da gwamnati ta ware makudan kudade ta‘ ,shigo ‘dashi domin bawa’ma’aikar gona’ ta Famheguwa wuta. Injin din yayi Wa ma’aikatan girnma sosai. .
Watau ‘karfinsa yafi karfin gidajen daké cikin kwatas din. Saboda hakayake ajiye tun lokacin da aka kawoshi sama da watanni shida‘kenan. ‘ ‘
Akwai‘ shawarwari da dama akan janareton
wanda har yanzu ba’a aje masa matsaya ba. gobe ake sa ran zuwan jami’an bincike watau (oditors) zasu zo daga Lagos. Tun sanyin safiyar’_yau Mr’. Bulagun da‘Alhaji Bara’u keta zaman mitin a cikin ofishin shi Mr; Bulagun din. Allah kadai yasan abinda Suke tattaunawa a kai. ‘ Yayin da shi Alhaji Abdul-Rashead tafiya ta kama shi dole zuwa garinsu’Kauran Juli don ganin yanayin jikin Baba Liman da aka aiko masa yana kwancajikin ‘yayi zafi.
Babu bata,lokaci, babban asibitin ABU na Tudun _ Wada Zariya, nan ya wuce dashi, wanda nan take aka bashi gado. Bincike ya zurfafa akan Baba Liman, ganin yadda yake asa asa yana haki numfashinsa baya sauka kasa. * .
Kafin yamma dole aka garkama masa (oxygen) saboda numfashin baya’tafiya yadda akeso. Hankalin kowa ya kara tashi. musamman na Alhaji. gaba daya ya rasa natsuwarsa, liSsafinsa ya dagule, yanaso ya wuce Kaduna, amma yana ganin kamar yana bada baya. Liman zaicika’. . , . ‘ Saboda haka ya kasa tafiya, har dare yayi, duk da cawar gwaggo nata karfafa masa gwiwa akan ya tafi din. Bai kama hanyar’ Kaduna ba sai karfe shida na’ safiya, ko a lokacin sakamakon da akaima  Baba Liman din bai fitoba tukunna. Yana isa gida, samarin gidan suka tarbe shi, ya zauna falo suka gaisa, sannan Suka tambayi jikin Baban. Ya numfasa. Yace “To, mun gode Allah, amma na barshi da (oxygen), tun jiya aka sa masa” Yana ma asibiti kenan?” .Yana can, nima badon oditors din da Zasuzo yau ba da ban dawoba. Hankalina yana kan’Baba gaskiya”. ”
Suka aje numfaShi, kowa jikinsa yayi sanyi Suka yi masa addu’a. Alhaji ya amsa. kana yace ’ldan; zaku shirya bayan kun taso makaranta. Nasan zuwa. daya na rana lnsha Allahu mun gama da (oditor’s) din..Suka cé – “Allah ya kaimu”. Ya mike ya nufi dakinsa.
Hajiya SuWaiba tabi bayasa Yana  shirin shga bayi, . ta zauna baking gado tace naji ka shiru tun jiya, zuciya ta keta yimin sake-sake a game da jikin‘nasa. ubangiji Allah yasa kaffara ne
Ya nisa yace “Amin. Wallahi Suwaiba gaba daya zuciyata ta karaya, kuma bansan‘ dalilin dayasa gabana yaketa yawan faduwaba. Tasbihi kawai nake wa Allah, lna samun karfinjiki na”.
Tace “Haka ne Alhaji. Amma ltama  ciwo aiba mutuwa,bace, domin rai “a hannun Allah yake ba a hannun ciwoba. Fatan mu Allah’ya gaggauta aiko masa da Manzon ‘sauki”. ‘ Yace “Amin Suwaiba. Bari inyi wanka in wuce  Ina ,fatan gidan kowa lafiya?
.Tace “Lafiya lau. Yauwa kar in manta. Alhaji Bara’u da Mr. Bulagun sun zo nemanka jiya wuraren karfe shida na yamma, nace masu baka dawoba tukunna”. Yace “ok Bari in hanzarta in fito wata kila akwai wata maganane. Ya mike‘ya shiga wanka.
A Karfe takwas da rabi a-kofar ‘ofis tayi masa. Ya iskE ofis shin’ Alhaji Bara’u da na Mr. Bulagun duk a bude, ga kuma bakin mutoci guda uku anyi fakin din su gefe. ‘ ‘
Gabansa ya yanke  ya fadi, don nan take ya ganE yanayin ma’aikatar, kamar tsayawa yai cik
Ko duk‘fargabar zuwan (oditors) dinne ‘Ya tambayi kansa.‘ Ya saba kulum ya iso Alhaji Bara’u zai‘ fito ya tarbeshi, suyi musabaha su gaisa, sannan su rankaya ofishin shi Alhaji Abdul-Ras‘heed din.
Aman’a yau‘shiru baifitoba , don haka ya nufi ofis ‘din tare da gaisawa da jama’ar dake Azazzaune wajen. Su suke gaya masa Alhaji Bara’un yana ofishin Mr. Balngun; Saboda haka yazarce can, ya buga kofa aka amsa masa, ya bude ya Shiga. . ‘
gaba daya suna zazzaune su, bakwai.‘ cikin walwal‘duk’ yabasu hannu suka gaisa, kafin ya ‘dubi bakinsu. Yace “Kuyi hakuri, nazoa makare”. ‘
daya daga cikinsu‘yace “Ba Amatsala, ai an gayamana baka’ kwana gari ba, kanada marar lafiya. ya
mai jikin?” Yace “Da sauki. Muna iya karasawa ofis din nawa ko?” Babban cikinsu yace “A’a, kana iya zama anan
kawai mu kawo karshen magana, tunda baku bamu wahalar bincikeba. Sai dai matsalar, ba mayunwata aka aikoba. Aiki mukazoyi, kuma shi za muyi”.
Alhaji ya gyara ‘zama ya zura masa ido. Yace “Ban fahimce kaba?” Ya-ce “Kudaden da kuka bayar, ba sune a gabanmuba, hayanin yadda akayi aka fitar da janareto. shi muka zaji.” ‘
Fuskar Alhaji Abdul-Rasheed ta. hargitse da mamak‘i, ya dubi Alhaji Bara’u da’ Mr. Bulagun, amma- baiyi nasar’ar hada ida ido da kowannensuba cikin su ba.
.“Yakamata ka fito min a mutum sak In fahimce ka”. ‘Kamar daga’ sama ya ji Mr. Bulagun ya cafe ‘ maganar “Ka dainayi kamar baka’ san komai ba Alhaji. maganar fa ta riga ta ‘lalace, tunda kudaden daka bamu basu, karba ba. Yanzu hanyar da‘ zamu ‘ rufawa juna asiri kadai zamu nema”. ‘
Alhaji Bara’u ya amshe, “Baskiya ne, babu wata hanyar’sulhu-da bamu nemaba, amma sukaki bamu hadin‘kai. Sai dai ban’saniba ko kudadan ne suka yi masu kadan”.
“. Wani abu ya tsirgawa Alhaji tun daga kansa har zuwa yatsun kafarsa. Duhu ya bayyana‘cikin idanuwansa. don haka ya runtse su tamau! Yana fadin.
“lnna-Lillahi’wa-Inna-llaihir-Raju’un!” Dan ya tabbatar da‘bashi da wata mafita a ‘cikin wannan al’amarin da bai k0 fahimce shi ba, sai wannan kalma.
Ko shakka babu an haka .masa wani ‘katon rami har ya rufta ciki, amma yana da imanin wannan kalma daya ambato‘zata fiddoshi daga dukka masifa.
Ya bude Ido, jajawur.yabi Alhaji Bara’u da kallu. Mamakinsa kawai yakeyi. Babban‘ masu binciken. Yace”Alhaji kayi magana, idan kuma babu, ro hukuma ta umarce mu da ka aje takardar waranti, dun kuje gabansu kuyi bayani.
Janarato dai anriga‘ankama motar dake kakarin fita dashi Kwatano’ a karshen makon”jiya. ‘Wannan shine’musabbabin. turo mu bincike. ’
Bayan an gano jenareto daga nan ya fito ga kuma takardu mun kama a hannun Mr. Bulagun ta; yarjejeniyar’ fita. da janeraton mai dauke  dasa hannayenku ku ukun.
Sannan da bankinsa yanzu shi Bulagun din yace tabbas shine .ya jagoranci shirin, ku kuka goya masa baya. don raba kason daidai A‘kwai sauran tambaynyin daya kamata ku amsa. Saboda haka an ‘baku awanni
ashirin da hudu ku kai kanku afishin binciken kayayyakin gwamnati na jiha.
ldan akwai bukatuwarku je hedikwata, to zasu tura manaku can Lagos”.Daya daga cikinsu yamimmika masu dogayan takardu nade, kafin suka mike. Babbansu yace “Mun barku lafiya”. Kai tsaye .suka bar ofishin.
Alhaji Abdul-Rasheed ya sauke wawan numfashi, yayiwa Allah tasbihi har sau uku. Kafin ya karasa. Mr. Bulagun ya tashi ya fice daga ofishin.
Sun jima shiru babu wanda ya tanka, daga bisani sansanyar’ muryar Alhaji Ahd—ul-Rashaed ta gauraye wajan “Ban yi zatoba Alhaji Bara’u! Ko kuma ince laifin ‘me nayi maka dana cancanci wannan sakamakon?
Ashe dama ba zaman amana mukeyi ba? Ashe bada zuciya daya kake kallona ba? Ashe za’a iya hada baki da kai a cimma wani buri a kaina?” ‘
. ‘ Ya kada’kai idanuwansa suka tara kwalla, yaci- gaba da fadin “Na ranse da Sarkin daya kaddara min. wannan masifar ko alama sharrin da kuka kulla min, bai bani mamaki, kamar yadda nake kallan fuskarka da surar’ ka cikin zuciyataba. Me nayi maka Alhaji’ Bara’u? Yaya akayi kayi sakaci shaidan’ yayi wannan mummunar saqra  a cikin zuciyarka?
Yanzu a haka zumuncin namu zai kare? Ban zataba Alhaji Bara’u,,koda a mafarki ban taba hangn ka cikin
lol

mu hadu gobe

www.Facebook.com/abdullahi.Ismail.salanke

About AIS

Check Also

Makaranta duniya chapter 30

Makaranta duniya            Chapter30 masa shishshigi. Wayarsa ya dauka ya kira Mudansir  ya sanar wa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *