[Advertisements⬇️]

Makaranta duniya chapter 25 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Makaranta. Duniya

            Chapter25

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

, Ya Ce, “Labarin’duk iri daya ne Asma’u.‘Daga jin ‘sunan. ki kawai zuciya _ta, ta amince min, tabbas kin _ cika dukkanin sharuddan, shi yasa nan take idanuwa suka dokantu da son ganin wannan baiwa daga Allah , Tuni ta aje idonta kasa tana dan murmushi. ‘Asma’u,’ Ya‘sake kiranta, a natse, ta dube shi “Ki na so na Asma’u? Da sauri ta rufe fuska, fara’ar ta ta karu, Ki taimake ni, ki ba ni amsa Asma’u, idan har ki na so, yau in yi barcin da na manta da’ yin kamarsa, kin ji? Don Allah ki taimaka min.” ldanuwanta suka kunshe da hawaye. Me ya sa ka ke magiya? Bayan ya san ta yarda da shi? Take nan
‘ta ji amsar. “Na san kin yarda da ni, amma kalmar kawai. na ke so inji ta fito daga bakinki ta sautin nan nAki, mai tsananin sanyi, ba zan taba mancewa ba Asma’u, koda yaushe sanyin nan ba zai daina taba zuciya ta ba, don Allah ki gaya min Asma’u.” ‘
Ta hade kai da guiwa, shiru sannan ta dago taCe. “To sha lemun.” Ya ce “ldan na sha, za ki gaya min Ta amsa da kai, ya nuna ta’da yatsa, “Kin yi alkawari Ta ce, “Na‘yi  Ya bude lemu da sauri yana fadin, “To shi kenan  Ya tsiyaya cikin kofi, ya sa baki ya kurba, “Na Sha Asma’u.” Ta ce, “Sai ka kara.“ Ya ce, “Wayyo sbd me ? Ta ce “Kai dai ka kara.” _Ya kara kurba, “Na kara.“ “To ka dan kara mana.” Ajiye kofin ya yi’cikin damuwa ya. ce, “Kin cika dukkan sharudda Asma’u, cika alkawari na daya da’ga cikinsu, ban jin tunani na ba zai taba zama gaskiya ba.”
Ta ce “Tabbas haka ne, kuma da ba ka yi gajen hakuri ba, da ka sha mamaki Ya bi ta da kallo, ta yi dan murmushi, ta ce,- “Ka dan kara na ce.” Ya dauka a hankali ya kai ‘ba’kinsa, ya kurba idanuwansa na kallonta, bai cire kofin ba, ya jiyo muryarta. . ,
“Ina son ka, na kuma yarda da kai, na amince da auranka Ta mayar da fuskarta cikin guiwa, ya dire kofi, da farin-ciki mamaye a fuskarsa, ya sauke
numfashi’ ‘mai karfi, sai da ya jawo hankalin ta, ta dago .kai ta’ dube shi.
Ya ce, “Ni ma ina son ki, na yarda da ke, na kuma amince da auranki. Allah ya tabbatar mana.’ Asma’u kai tsaye ta amsa, “Amin Liman—Liman.’ Ya tintsireda dariya “Lallai kin kyauta matar ‘Liman.”’
Cikin nishadi suka sharari hira, ta fahimta. Karfe goma Asma’u ke ta kallon agogo sai kallon agogoki ke yi da alama ki na so ki kore ni kenan? Ta ce, ‘Ni na
isa in kore ka? Sai  ko  lokacinka ya, yi na tafiya.” Ya ce, ‘Gaskiya ne, to sai yaushe?
Ta ce “Nan da sati biyu ko uku.” Ya ware ido, “Amma wasa ki ke yi ko? Taf Lallai za ki tsince ni a asibiti, sati uku? Haba dai! Dariya take ta yi masa. “0k, ‘dariya ma na baki, kenan, zolaya ta ki ‘ke yi, zan rama, bari in lallaba sai mun yi waya k0?
Ta ce, “Ina sauraran ka.” Ya mike, ita ma tsayen ta tashi, “Ki gaida min Mama da kannen nawa‘, sai na sake dawowa, zan shiga in gaida ta.” Ta ce “To, Allah ya ba mu alkhairi.” “Amin.” Ya ficé, ta bi‘ yo bayan sa, suna tsaye, sallamar ta ki karewa. ’ ’
Malam Sadiq ya iso wajan, daga can falon Alhaji yake kamar yadda ya saba “Sannu Baba.” Ya ce, “lmam a waje ku ke? Ya dube ta, “Me ya sa ba ku shiga falo ba? Ya ce, ‘Ah’ah Baba yanzu na fito, zan koma gida ne.”.Ya ce,‘ “Oho, to sai da safe.” Ya wuce ciki. Imam na fadin “Allah ya kai mu.” Yana shiga, ita ma ta sallame shi, ya wuce ta rufe gida, ta dawo ciki.
Yana tafe yana zancen zuci, ji Yake kamar ya juya ya sake komawa, shi kan sa mamakin kansa yake ‘yi, yadda ya ji zuciyarsa gaba daya ta mamaye da sunan Asma’u, ko alama baya jin motsin Jamila. Karatu Muda ke ta yi, ya sadado kusa da shi ya kwanta “Wayyo Allah na Ya bi shi da kallo, “Me ya faru Yayana?
Ya ce, “Babu abin’da bai faru ba, yanzu kai saboda Allah ka san da yarinyar nan, ka kyale ni ina ta bandan-Bandan ka na min wasa da hankali, ana neman kashe ni? Murmushi ya yi “Ai ka san komai lokaci ne, da lokacin ya yi, ba ga shi komai ya sauya ba? ,
‘ Ya lumshe ido ‘ya ce, “Yes? Yarinya mai hankali, ga kalamai Muda, yadda ka san marubuciya mai hikima, gaba daya ta gama sace min zuciya, ba na jin_
motsin kowa sai na ta.” Ya’nuna kansa, “Harda ni? Ya
doke kafadarsa, “Kai fa banza ne, wa ya gaya maka muhallin ku daya? ‘
Ya ce, “Shirme na mana, a‘zatona duka soyayya a Zuciya take. ashe wata na huhu wata na koda, to gaya min. a ina tawa take? Ya daga hannu .ya ce, “A nan take.” Ya kwabe fuska, “Hammata? Oh_ ni, na shiga uku ni Muda a hammata? Yana dariya, ya make masa keya ~ Ya ture shi gefe ni, “Don Allah matsa ban son surutu, inada abin yi.”
Ya zaro waya ya kira lambarta, “Ai mu kuma Yau ba za ayi barci ba.” Ya figi filo ya maka masa, yayin da ita can har ta dauki wayar, saboda haka ya kare fuskarsa da filon, don kar ta jiyo dariyar da Muda ke ta faman yi. Liman ya ce, “Matar Liman, to ya an shiga gida lafiya? Ta ce, “Kalau Ya numfasa ya ce, “Na gode Allah da ya tsare min ke, ina fatan ban takura miki ba? Sai fa _kin yi hakuri,‘ kin san sabon kamu.’ Ta yi ‘yar dariya “Ah’ah Wallahi, dama ni ma yanzu zan kira ka, in tambaye ka ya ka je gida.”
Ya ce “Gani ma a daki, amma zuciya ta na wajen ki, ban jin yau-zan iya barci.” Ta ce, “Don me? Ke ma kin sani matar Liman, banqi mu kwana muna hira _ ba.” Murmushi ta yi “Haba dai, amma ka gaya min yau
‘ za ka yi barcin da ka manta da yin irin sa
Ya ce, “Saboda ina ganin ki ne kusa da ni, shi ya sa na yi zaton zan iya barci, ashe ba haka abin yake ba, yanzu na gane Asma’u,,ban kuma san yadda _zan yi ba, .zuciyata na zugin son ki, idanuwana suna son kara ganin ki.”
Gaba daya ‘ya kashe mata jiki, ba ta san lokacin da take ba shi amsa ba, “So .ba karya bane Imam. .yadda ka keji, haka na tsinci kai na a halin yanzu. Mamaki kawai na ke yi, don ban taba ba wani da namji lokaci na ba, balle in kwatanta son saba, sai ga shi yau ” haka
kawai ka hana ni sukuni, zan iya cewa ni ma yau da kyar idan  zan iyayin  barcin.”
Imam fa ya gigice, fadi yake “Zaki sani, kuma Asma’u don Allah ki gaya min mafita‘? Mudansir ya yi gyaran murya, ya mike ya nufi bayi, yana kunkuni, ‘Lallai ne Yayana, wannan karya har ta sanya ni gudawa.” 
A can bangaren kuma Asma’u ke ba da amsa ‘Hakuri shi ne kadai mafita, ai za ka dawo gobe ko? Ya ce, “Don Allah ki daina tambaya, me zai hanani zuwa? ldan’har ina numfashi. Ki sani fa yanzu na fara son ki, so maras misaltuwa, ashe kuwa kullum  ina bukatar ganin ki, ki min alkawari har abada ba za ki bar ni ba.”
Ta ce, “Allah ya tsare ni cin amanar ka, har abada kai ne zabi na, kai na ke son na aura.” Ya runtse ido ya ce, “Na gode Asma’u! Na gode! Bai ajiye waya ba, sai da kudinsa suka kare, daran nan barci rabi da rabi suka yi shi.
~~~~~~~~~~~~~~~~
wadanda suka hada Su, abin gwanin sha’awa har
shi ma Mudansir ya fara tunanin ko shi ma ya ‘ lallaba wajen Hadiyya ne kanwar Asma’u? Bai dai furta ba, amma koda yaushe ya raka Yayansa, yana gaya wa Asma’un shi ma ya kusa fara zuwa ‘wajen- ta sa budurwar.
‘ Dariya suke masa, suna daukar maganarsa wasa, don sun san shi uban iya shege ne. Allah da ikonsa mutuwa ta riski Akantan kamfanin da Malam Sadiq ke aiki, sakamakon hatsarin mota, nan take aka-zakulo takardun Imam da suka jima a ofishin sakataran daukar ma’aikata. ‘ .
Haka rayuwa take, lokacin da wani ya kwanta, lokacin wani zai tashi, mahakurci, mawadaci, kamar daga sama Imam ya ga takardar shedar daukar aiki,
Kafin wata shida, soyayyarsu ta zarce tunani
bayan tsawon lokacin da ya shafe da yin inta-biyu.‘ kuma ba laifi kamfanin suna biyan albashi daida; gwargwado ba kamar sauran kamfanoni ba, masu zaman kan su.
Kai farin—ciki a wannan rana ba zai misaltu ba‘
Kowa ka gani daga hannu yake yi yana wa Allah godiya,‘
ba kamar mutuniyar tasa, ba watau Asma’u.‘ Ranar litini
da wuri ya je ya samu Malam Sadiq suka tafi tare, ya kama aiki.
Tun daga ranar tare suke zuwa suke dawowa, don haka ne ma Imam bai san matsalar kudin mota ba‘ Gaskiya’babu abinda zai ce ‘wa Malam Sadiq, domin kalmar godiya ta yi kadan, haka kuma dalilin ‘da ya sa kenan kullum son Asma’u ke kara zama zuciyar’ sa daidai da bugun numfashinsa.
Wata na karewa aka cake masa albashinsa dubu talatin da biyar, haka ya rinka ganin su kamar ba na shi ba, gaban Alhaji ya zube su, ya ce ya ba shi shawarar abinda ya kamata, ya ce “Babana ai wannan guminka ne, kai za ka sarrafa abinka, amma ka tabbataka yi wa Malam Sadiq alkhairi.” Ya ce, “Wannan wajibi ne Baba.” Ba su gama magana ba, suka ji tsayuwar mota a kofar gida. ,
Imam ya taso, ya daga labulan taga ya leka. Sulaiman ya hango yana fitowa daga mota, da sauri ya dawo yana fadin’, “Yaya Sulaiman ne.” Cike da mamaki ya ce, “Sulaiman? Ya dauke kudinsa ya sanya aljihu, ya kama hanya zai shige cikin gida. Alhaji ya yi kiransa, “lna- zaka? Ka je ka taro shi mana.” Ya dan tsuke fuska ya ce, “Ai zai shigo Baba ……
. Ya katse shi,‘ “Je ka tarbi dan-uwanka Imam! Ya hadiye miyau da kyar, ya taka’a hankali ya nufi kofa ya . daga labule ya fita. Sulaiman na _tsaye gaban but yana ciro kaya, ya kara tsuke fuska ya isa gunsa, “Sannu da zuwa Yaya Sulaiman.” Ya waigo baki dauke da fara’a.
‘Ah imam‘ya‘ku ke? Ya ce “Lafiya lau.” Ya ce, “zoka shiga da kayan nan, ina Muda? Ya ce, “Yana School bai dawo be.” “OK.” Ya sa hannu ya dauko dan karamin rabin buhun shinkafa, hannu daya ya dauko galan man turkey ya shiga da su ta falon Alhaji, ya wuce cikin gida.
‘ Mama na zaune tana,gyara gyadar miya, ta bi shi da kallo, “Kai Daga ina? Ya ce “Yaya Sulaiman ne.” Take fara’ar ta, ta gintse, ba ta ce komai ba, har ya aje, ya fice ta ‘kofar zaure, sallama sulaiman ya kwarara. Alhaji ya amsa cike da fara’arsa, “Manyan gari, ashe ana jin motsin ku? ‘
. Ya karaso yana dan yake, ko kunya, ya zauna gaban Alhaji “Sannu Baba, ina yini? Ya. ce, “Lafiya lau, ya kuma jikin? Ya ce, “An gode Allah, lafiya ta zauna.” Ya ce, “To madalla.” “Wallahi ina ta son zuwa, kullum sai na. sa rana, sai wani aiki ya fado min, yau dai na‘ce kai duk yadda ake ciki, Zan zo in duba jikin naka.” ‘
Ya ce‘To na gode, amma inaso in gaya maka wata magana Sulaiman, ka ga wannan tafiyar da ka dauko? Ban jin hanyar za ta bulle da kai, domin ka na yinta ne ba tare da albarkar iyaye ba, na sha gaya maka, ko ni ba ka lura da ni ba, wajibin ka ne kula da mahaifiyar ka.
Ba kada wani uzuri da za ka je da shi gaban Ubangiji, muddin ba ka daraja mahaifiyar ka ba. Haba Sulaiman, ka shekara cur! Mahaifiyar ka na’da rai, amma ka gaza zuwa gaishe ta?.Me ka ,ke nema da ya wuce albarkarta? Wallahi tun‘ wuri ka farka barcin da ka ke yi, kafin ka wayi gari babu ita, kuma ta tafi da bacin ranka, ka ji ni?- .
Ya sunkUyar da kai kamar da gaske, yana sauke numfashi “Naji Baba, na gode.” Ya ce  Shi kenan, ni dai
gaskiya na ke gaya maka, kar ka ga na kama ka da
fada ko ruwa ba ka shaba, ah’ah ba komai Baba‘ ‘ na
gode.” “To ya su Jamila da kannenta da Ummansu?
yace, “Duk suna makaranta. Murja kuma “tace a gaishe ku.” “Muna amsawa.” “Mamanmu na ciki? ne“Tana nan, shiga ka sha ruwa.” Ya mike ya shige ciki da  sallama “Mamanmu-.” Yake fadi yanawami‘ wangame bakin rashin gaskiya,‘ta bi shi da kallo. ‘ “Manya-Manya, ai ni da aka ce ka zo, ban ma
Yarda ba, sai da na jiyo’muryarka a falon, anzo lafiya,‘
Ya mutan Bauchi? Ya ce, “Duk suna gaishe ku.” Ta Ce “Muna amsawa.”
Ta mike za ta kawo masa ruwa, ya ce “Ki bar shi Mamanmu, na ci abinci kafin na karaso.” Ta dawo ta zauna, “To ai ya yi kyau.” Ya tashi ya koma falon Alhaji, ya ce masa zai je ya ga wani abokin sa, “To a dawa lafiya.” Ya ce masa ya sa kai ya fice.
Har dare bai sake ganin‘ Imam ba, domin yana fita ya tafi harkokinsa, bai dawo unguwar ba sai bayan lssha, ‘kai tsaye wajen gimbiyar Sa ya wuce. Karfe goman dare ya dawo. Lokacin Sulaiman ya .tafi kwanciya,~inda ya ce ya kama daki. Da sassafe ya yi tafiyarsa ofis, duk da’ cewa ranar sati ce, ba kasafai suke yin aiki ba.
SUlaiman na zaune falon Alhaji, suna sallama zaiwuce kaura daga can zai kama hanyar Bauchi, “Wai ni ina Imam ne, tun da, nazo sau daya na gan shi? Alhaji ya ce, “Ai tun safe ya tafi aiki.” “Au, ya sami aiki ne? Ya ce, “Eh ya’samu a wani kamfani na manyan motoci.’
Ya tabe baki, “Kamfanin ai ba wani albashin kirki a kamfanoni masu zaman kansu kuma babbar illar haka. Mutum zai kare aiki babu fensho balle garatuti.” Alhaji ya ce, “A sa ba ka ai ya fi a rataya kuma guntun gatarinka, ya fi sari ka ba ni, sannu a hankali za’a sami abinda ake nema, idan da rabo.” A salube ya
ce. ‘Gaskiya ne, bari in lallaba.” “Allah ya kiyaye hanya.” Haka suka ce shi da Mama.
Shi kansa ya san ya ga sauyi wajen Hajiya Suwaiba da yaran, amma k0 a jikinsa, tunda ba wannan bane damuwar sa, yana sallama cikin gidan. Inna ta fito ta kare masa kallo, sannan ta koma daki ba tare da ta ce da shi komai ba, dakin ya bi ta ya aje ledar lemu da ayaba gefe, Ya zauna a tabarma.
“Inna ina kwana? Ta watso masa harara, kafin ta ce, “Wai kai ka na so ka gama da duniya lafiya kuwa? Wallahi fushin Alhaji kadai ya isa ya sa duniya ta hora ka, ballantana nawa Sam-Sam- kai ba ka da tunani, ba ka da hankali, kamar Alhaji.
Haka ma bai isa ba, ba kunya ba tunani ka hana Imam auran ‘yar ka, har ma sai da ka .hada da wulakanci da raini? Alhaji ya kwanta asibiti, .ka kasa zuwa gaishe’shi. Bayan cin fuskar da ka yi masa tare da bakonsa To ka sani ni ka yi mawa kuma babu mamaki, don dama can ba ka san daraja ta ba ballema wani….‘..
Ya yi sauri ya katse ta, “Wannan maganar bai kamataki na fadar ta ba Inna, kuma shi kenan ba za’a yi wa Mutum uzuri ba, komai na yi ba’a gani, sai ma a
.raina, wai shin albashin nawa  nawa yake? Sata ake son in rinka yi ina kawowa? Haba don Allah!. –
Ta zuba masa ido, yasa aya kafin ta ce, “ldan ka kare, to ka tashi ka tafi.” Ransa bace ya ce “Ki yi hakuri Inna, dama ba zama na zoyi ba, yaushe Mutum zai ji
‘ dadin zuwa, kullum ya zo sai ran sa ya baci? Shi kenan ai, ga Wannan ki yi siyayyar kayan azumi, wata kila ba zan sami dawowa ba, daga Can zan wuce Umrah.’
Ba ta tanka masa ba, ya aje mata dubu biyar, ya
sake fadin “Ni na wuce, don girman Allah ki yi hakuri Inna.” Ya sa kai ya fiCe rai bace, yana tafe a mota yana
sakar zUci. “Mutane suna ba ni mamaki, daga an gan
ka. an ga kudi? ‘Ka basu dai, ka ba su dai, kamar haqo: kudin ake a rami. Mts ……
Wai har da wani boye min, don Imam ya sami aiki, ba don na tambaya ba, ba za su gaya min ba, daga magana. Baba ya’ hau habaici, kai Mutum bai yi ba Wallahi.’ A guje ya wuce kauyan tsohonsa k0 tunanin ya biya ya gaishe su .bai yi ba, alhalin rabon su da shi ya kusan shekara daya da rabi. kenan
Da yamma likis! Imam ya dawo’da kaya niki niki, buhun shinkafa, kayan. ‘ Tea da kayayya kin masarufi, turame biyu na atamfa, shadda da yadi su ma biyu har da hula kube ya siyo wa Alhaji. Haka gidan Malam Sadiq dubu biyar ya kashe masa. Alhaji da Mamasukayi farin-ciki tare da sa albarka mai tarin yawa. ‘
Mudansir yaci dubu biyu da takalmi. Malam Sadiq kan sa ya yi farin-ciki, sai dai ya shawarce shi da wannan ya zama na karshe, kar ya dami kansa akan sai ya kashe masa wani abu daga cikin albashinsa, fatansa kawai ya zama mai dogaro da kansa kuma ya tallafa wa iyayensa. Wannan huduba kullum da ita yake kwana da ita yake tashi, tare da addu’ar Allah ya sanya masa tausayi da son taimakon.
Watanni biyu tsakanin aka fara azumi. Mai- gidansu ya raba masu kayayyaki kamar yadda ya saba duk azumi. rabin buhun shinkafa, gero da suga ga kuma dubu ashirin kowanne ma’aikaci. Kai su Mama sun sha mamakin wannan bawan Allah, rabon da su yi azumi cikin jin dadi da wadatar abin bude baki, har sun manta.
‘ ‘ Lallai albar‘kar haihuwa ta fara sauka. Abinci har Kauran Juli sun kai wa Inna da‘saUran kayan marmarin buda baki. Ganin sun wadatu da komai na bukatuwar yau da kullum, sai Mama ta shawarci Imam da ya fara tarin kayan aure, kwarai shawarar ta yi masa dadi,‘tashi
guda ya fara aje zannuwan dubu ashirin.
An kammala ibada, an sha shagalin sallah lafiya, kullum girki na musamman Asma’u ke masa ta aiko masa gida. Bayan sati biyu ranar lahadi aka sanya masu ranar aure wata takwas masu zuwa, kowannan’su
farin-ciki baya misaltuwa.
Washe gari ranar litini ya je gidan da safe, don tafiya wajen aiki, ya yi sallamasuka ‘gaisa da kowa, sannan ya fito ya tsaya jingine da mashin dinsa roba~ roba, yana jiran fitowar Malam Sadiq.
Sabuwar wayarsa kirar (SAMSUNG) ta dau ruri, ya fiddo ta daga aljihu ya duba, koda yaushe lambar Jamila ba ta bace masa, ya yi saurin dauka, don ya san dalilin kiran ta, ya yi mata sallama, ta amsa kafin ta ce, “Wani labari na ji mai kama da almara.’
“Na me fa? Ta ce, ‘Wai an sanya maka rana? Shi ne na ji abin wani banbarakwai Ya yi dan murmushi ya ce, ‘Kamar yaya? Ai ba wani wai a ciki, ba kuma abin mamaki bane, domin kin kwana da sanin idan wani ya ki ka, sai wani ya so ka.”
Ta ce, “Ba kishi na keba, naji kamar ka na so ka yi min habaici ne , abinda na ke tunani shi ne, yaushe ka fara aiki da za ka jajibo aure? Ya ce, “Lalura ta ce wannan, ban so ana min baki, kin gane? Don Allah babu
ruwan ki da abinda ya shafe ni! Ya kashe wayarsa, yana sakin tsaki. ‘
Ta bayansa ya ji muryar nan mai sanyi an kira shi, “Liman kenan.’ Ya waigo da sauri ya dubeta, tana tsaye kofar gida kayan makaranta ke jikinta, ta daure ,fuska da nikabinta, ya zubo mata ido, yana dan murmushi, don sosai yake sha’awarta cikin wannan shigar‘, saboda ba karamin kyau take yi ba.
‘Matar Liman, wai dama ki na cikin gidan, ki na . ji na ki ka ki gaisheni? Kin kuwa san matsayina yanzu? ‘ Ta matso kusa da shi ta tsaya da ‘yar dariya, sai dai shi
baya gani, saboda nikabin da ke fuskarta ta ce.
‘Ni kuwa na san matsayin ka. ka kwana lafiya, Ya ce, ‘Kalau matar Liman, ai ko gani sharr Harda kyallin angwanci a goshi na.” Ta juya idanuwa, ta dan kauda fuska “To wa ka fi kyalli?‘ Dariya ta. kwace masa, “Duk wanda ki ka zata kalleni mana ki gani.” Ta juyo ta dube shi, “Ban ga’ komai ba, ya ce, “Ki daga nikabin ne.’ Ta yi ‘yar dariya “Oho‘? Wayonka kenan? To na gane. Dogon tsaki nake taji? “A ina? Ta ce, “Na fito ka na waya, na ji ka na‘ dogon tsaki.” Ya ce “Jamila ce.’ . Ta numfasa ta dube shi; “Au ka ce min Antina Ya nuna ta da sauri “Ba naso, na gaya miki ko? Ta ce Menene ba fushi Allah ya huci zuciyar Liman.‘ Rai bace ya ce “K0 ina ruwanta da zancan aurena Don kankanba, ta wani kira ni, tana gaya min maganar banza! ‘ Jikinta ya yi sanyi a natse ta ce, “Ba laifinta bane nawan, ka san ta so ka da, dole ta ji wani’iri cikin ranta ko.dan yaya ne.” Ya ce “Ya isa haka, ba. na son ji.”Ta ce; “Tuba na ke.” Ya ce, “Ai zan yi maganin abin, ba‘dai layi ke hada mu ba? To zan zare shi; in karya, in sa‘wani ba’ shi kenan be, an kashe case din? Ya ce, ki yaye min nikabinnan. in ga kyallin amarCinnan naki.” . Ta ce, “A nawa? Ya marairaice “Saboda’girman‘ Allah.za ki bude min’, ai na‘ san ba ni da kudin biyan. ganin wannan kyakkyawar fuskar. A taimaka min, tun dazu ki ke ta murmushi, amma idanuwa na ba sa gani, alhali ba su da wani zabi, sai na son ganin ki.” Daga irin ; kallon da-take masa, ya gane kalaman sa sun ‘ ratsa zuciyar ta. Ba ta ‘ce komai ba, ta sa hannu .za ta daga, ya zuba mata ido a hankali ya ce, “Subhanallah Tau’ra’ruwa daban take ko a cikin taurari, ki na da kyau Asma’u.‘ Ta_
sadda kai tana mur‘mushi; Shi kuwa ido ya zuba mata. wani iron shaukin sonta na fizgarsa

Www.littafanhausane.com.ng

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]