[Advertisements⬇️]

Makaranta duniya chapter 24 - Bankinhausanovels
Fri. Mar 31st, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Makaranta.  Duniya

         Chapter24

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Gaba daya hankalinsa, ya tashi, lissafinsaya dagule, yayin da ita ma ‘take zaune hawaye suka goce ‘ mata, ita kanta ba ta san me ya sa ta kukan ba, saidai‘ ‘ tunanin ta yana nuna mata bai. kamata ta cabawa  Imam’wadannan maganganun ba. Tabbas ta sanyana sonta, dole kishi ya hana shi sukuni, wata kila abinda ya sa ta zubda hawaye kenan.
Alamar shigowar sako cikin wayarta ta‘sa ‘ hannu ta dauka ta bude ta karanta, “Ki yi hakuri Jamila. Wallah ba na zargin ki da aikata mummunan aiki,son da na ke miki ne yake harZuka kishi‘na har nakasa daurewa, ba laifi na bane. Please Ki yi hakuri!
Ta runtse ‘ ido, tausayinsa ‘ya rufe ta,‘ Wasu hawayen suka kara fitowa, a haka ta ba shi amsa.’Na
‘fahimce ka Yaya Imam, kai ma ka yi hakuri kuma zuciyarka ta sami natsuwa don Allah. Najeeb ya jima da aje ni gida, ba na tare da shi a halin yanzu. Ka yiwa Allah ka kwanta ka yi barki ka huta!
Ya numfasa ido rufe yana kada kai Jimawa kadan ya sake maida sako, “To na gode my love, mu kwana lafiya.” Ta dawo masa da amsa, ‘Amin Yayana.’ sannan fa ya sami ‘yar natsuwa har ya iya yada kafada, bai jima’ba barawo barci ya saCe shi. ”
Haka al’amarin ya rinka tafiya, duk da‘ cewar jamila na matukar kulawa da Imam, babu abinda ya ‘ nema ya rasa, sam hankalin sa ya ki kwanciya, musamman da ya tabbaatar da cewa sosai Sulaiman ya san Najeeb.. ~
Sau biyu kenan suna zuwa Bauchi tare da shi, kasancewar shi Najeeb iyayayen sa na Jos ne, amma
‘yan asalin gombe ne, idan ya sauke su gida sai ya wuce Jos, in ya‘ dawo ya biyo ya dauke su. lmam ya sha mamaki yadda Sulaiman ke rawar jiki da Najeeb, sau da yawa idan ‘suna waya da Jamila. Shi yake fara tambaya, ya kuma ce ta gaida masa shi.
Duk wani goce—gocen da Jamila take yi, sai da
Imam da Najeeb suka gane su kishiyoyin juna ne, sai dai babu wanda ya nuna ma wani cewar sun dago juna. Al’amarin ya dami Imam kwarai da gaske, shi ya sa duk wayar da ya yi gida yake kokarin cusawa su Alhaji la’llai su gaggauta tsaida maganar‘auransa da Jamila.
‘ Haka ma idan ya sami lokaci ya zo Kaduna, maganar kenan guda a bakinsa. Auransa da Jamila shi kadai ya sa gaba, kamar cin kwan makauniya har Allah
’ya kawo karshen zamansa Gombe, babu wani canji, domin Sulaiman ya dage ka’ratu Jamila za ta yi.
Alhj. Abdur rasheed ya ce “Shekara guda kenan da ‘ gama bautar kasar sa, babu bayanin samun aiki
duk iya kokarin da ake yi masa wajen nema masa abin bai nufa ba, ba sai na yi dogon bayani ba, don ka san komai Malam Sadiq a gameda neman aikin Imam, har kai ma ka na daya daga cikin Wadanda suka yi alkawarin taimakawa.
To amma shi Imam ba wannan ya dame shi ba Jamila dai, Jamila dai koda yaushe, gani yake wani zai kwace masa ita, musamman idan ya tuna tana tareda wannan yaro Najeeb, ka ji dalilin daya matsa  kenan akan lallai na je‘Bauchi da kaina in nema masa aure,’
Kamar yadda kowanne uba yake wakiltar dansa na tabbata girma na zai sa Sulaiman ya dauki maganan . Amma me? Ba sai na maimaita ba, domin a gabanka aka yi komai, kuma wannan abu shi ne abu mafi muni da Sulaiman ya yi min, ya zauna cikin zuciya ta, harya haifar min da matsala. ‘ .
Sai dai ina soka sani, kamar yadda na yi afuwa ,ga Alhaji Bara’u, na mance da dukkan abinda Hajiya Aliya ta yi min, na aje géfe na mance da Mr Balogun da bakin sharrin da ya yi min, haka har abada na keso abubuwan da Sulaiman ya yi min su shafe a zuciya ta, su zama tarihi. Wannan shi ne a takaice abinda zan iya ‘ tunawa game da rayuwar mu da Sulaiman.
Malam Sadiq ya yi ajiyar zuciya mai karfin’ gaske, ya jinjina kai ya. ce, ‘Gaskiya Sulaiman yayi butulci Alhaji, idan. ma akwai kalmar da tafi butulci, tabbas Sulaiman ya kamace ta, dole mahaifiyarsa tayi kuka……-
Alhaji ya amshe, ‘Ka ga babbar matsalar kenan, shi ya sa kullum na ke gaya masa ya .kula da Mahaifiyarsa ya nemi albarkarta, amma sam ba yayi  Sulaiman ya ba ni mamaki, k0 alama ban taba zaton
abin duniya zai canza‘ shi ba, ina jiye masa horon duniya, ka yi da kyau ma ya ka kare balle ka bi son‘ . zuciya. Allah ya sa ya gane.’ :
Malam Sadiq ya ce, “Amin, kai kuma Alhaji Allah ya kara maka hakuri, shi ma Imam Allah ya zaba masa mafi alkhairi.’ “Amin Malam Sadiq. Ya kamata “a nufi gida, dare ya yi sosai, sha biyu saura, na tabbata iyali na can suna jimami.’ Yana rufe- baki, kira na shigowa wayar Malam Sadiq, ya yi murmushi yace “Ga ta nan ma ta kira.” ‘Ka ji ba? To tashi maza don Allah.’
Ya mike yana amsa wayar “Hello gani nan zuwa yanzu! Eh lafiya lau! Ya kashe, ya leko cikin gida ya kwala wa Imam kira ya fito, yana .amsawa suka yi sallama, ya tafi. ‘
Imam ya kulle kofa ya koma. Alhaji ya shiga da shi dakinsa, bai gama gyara masa wajen kwanciya ba.,, Mama ta shigo ‘Sai yanzu Alhaji? Lallai yau kun sha hira.” Ya ce, “Ai yau dogon labari muka dauko, babu inda ba’a tabo ba.’ .
Ta ce “Ya yi kyau, sai akwanta a huta.” Imam ya yi masu sai da safe ya juya zai fita. Alhaji ya yi kiransa, ‘ ‘Baba na Ya dawo yana amsawa, “Ka kara hakuri Baba na shi mahakurci babu makawa mawadaci ne. Duk abinda ka ga baka same shi ba, tabbaci hakika ba rabon ka bane, kumashi ne mafi alkhairi a gare ka, ina fatan ka fahimce ni?
Ya ce, “Sosai. na fahimce ka Baba, kuma tuni na mika wuya wajen Allah, ina ganin ma shi ya sa na sami ~sauyi cikin zuciyata.” Ya jinjina kai ya ce, “Allah yayi maka albarka.” Ya amsa, da ‘Amin Baba, sai da safe. Mama mu akwana lafiya.” Duk suka amsa. “Allah ya sa.” Ya wuce ya koma dakin su ya bar Alhaji yana gaya wa Hajiya Suwaiba abinda ya wakana a falonsa.
Haka al’amain. yake wakana tsakanin Malam Sadiq da Asiya a cikin daran nan ya maida mata labarin ‘
butulci mai ban mamaki, ta kuwa sha al’ajabi tana jinjina ma wasu mutane da zukatansu ke mance. alkhairi.
Ya gyara kwanciya ya ce., “Amma kin san wani abu? Ta ce, “A’a.” Ya ce, “Da lmam zai yarda da na share masa hawaye.” Ta ce “Da me? Ya amsa, da “Asma’u. Wallahi tun da na baro falon Alhaji na ke ta Wannan tunanin, saboda gidan Alhaji gida ne, wanda ya cika da tarbiya da sanin ya kamata, zan so ace Asma’u; ta yi ‘dace da irin wannan gidan, ko ya ki ka gani?
“Haka ne, kuma da Allah zai sa abin ya tabbata da na fi kowa farin—ciki.‘ Ya ce “Insha-Allahu zan gWada zamu tattauna da Alhajin, duk yadda ta kaya kyaji.’ Ta ce “Shi kenan. Allah ya sa a dace, dama .taqi tsaida kowa, wata kila abinda Allah ya nufa kenan.” Ya ce, “Ba”, mamaki.’
Washe gari da sassafe wayar Jamila ta farkar da” Imam daga barcin da ya kwace shi, bayan sallar asuba duk da cewar ya goge lambarta a wayarsa, da gani ya gane ,layin ta ne, gabansa kawai ya ji ya fadi, don tunda wannan abu ya faru, ba su nemi juna ba har ya goge lambarta. Ya yi zuru yana kallon wayar, ta tsinke. ‘
Jim kadan ta sake dauka. Mudansir ya bude ido
ya ce “Au ashe ka najin wayar tana ta faman kugi? Ya ce,“Wallahi Jamila ce.” Ya yi wuf Ya tashi zaune,. “Jamila, to ka daga mana.”‘ “Me za ta gaya min kuma, ko ni me zan gaya mata? Ai. ina ‘ganin an kashe zancen, (Game) din ya. kare ko kuwa? Ya yi dan murmushi, “Kuma mun gode Allah, tunda mun yi nasara, nan ba da dadewa ba Allah zai canza maka da wata zukekiyar Bebi
Ya zura masa ido yana murmushi “Me ka ke “ nufi? Ya ce, ‘Komai kuwa, ai rashin Jamila ba zai zama
karshen rayuwar Yayana ba. zaka sha’mamaki dan
uwa, don har na hango maka ita santaleliya mai yawan ibada.” Ya ci-gaba da kallon sa yana ‘yar dariya.
‘Sai kallona ka ke, tukuici Ya kamata ka ba ni, wannan irin kyakkyawan hasashe? Ya ja filo ya maka masa, yayin da wayarsa ke daukar bugu na biyar. “Ka daga mana.” Ya ja dan tsaki ya dauka, ya yi mata sallama ta amsa, “Haba Yaya lmam, wayar tawa ma ba za’a daga ba? Koda yake ka na fushi k0? .
Ya ce, ‘Fushin me? Ta ce, “Sai jiya Dadi ya zo Gombe yake gaya min kun kwanta asibiti kai da Baba, shi ne na ce bari in kira in tambayi jikin naku.’ Ya ce ‘Duk mun ji sauki.” ‘
“To Allah ya kara sauki, jiya ma muna tare da Najeeb, na ke gaya masa, shi ne yace in mun yi waya, na gaishe ka.” Ya ce, “To na ‘gode.’ “Ya labarin aiki ne? Har yanzu ba ka samu ba? Kashe wayarsa kawai ya yi, ya wurga ta gefe ya maida kai bisa filo. ‘
Mudansir ya ci—gaba da kallonsa, da ganin fuskarsa ta shiga damuwa, kwarai ya san Jamila ta shiga ran Yayansa ba kadanba tausayinsa ya lulube-shi. ya shiga tunanin labaran da zai ba shi ya dauke masa hankali. “Yayana? “Me aka yi? Ya ce, “Wai don Allah ni ma budurwar nan ban isa yin ta bane? ‘
Ya,dago ido ya~dube shi, “Kai fa banza ne Ya taso ya dawo kusa da shi ya kifa kai, “Wai me ake ji ne idan ana soyayyar? Ya kamo kunnnan sa, ya ce, “Ka bari sai ‘ka isa yi, ka ji me ake ji Ya fara dariya yana janye kunnansa, “Kenan ni yaro ne?
Ya ce “Na goye ma.” Take nan ya jefa masa kai _a kirji, ya shiga kukan jarirai. Imam nan ya fashe da dariya, ya dada masa duka. “Allah ya shirya ka Muda!
_ ‘ Nan ya dauke hankakalinsa da abubuwan ban dariya har lokacin karyawa ya yi, suka fita falon Mama suka karya. lnna Mairo ta gama shirin komawa gida, suka raka ta tasha; ta shiga mota.
Kowa ya dangana, gidan ya samu natsuwa, harkoki suka ci—gaba kamar yadda suka saba. Malam Sadiq ya iso cin abinci, “A wannan daran Alhaji da wata shawara na zo amma ban sani ba k0 za ta yi wa kowa dadi? Ya dube shi da kyau ya ce, “Ina jin ka Sadiq, fada abinda ke bakin ka.
Ya gyara zama ya ce, “Da ace Imam da ‘yar waje na Asma’u za su daidaita, da na ba shi ita, mu hada zumunci.‘ Cike da fara’a Alhaji Abdul-Rasheed yace Kai! Amma .ka zoda magana mai dadin  saurare Sadiq, zan fi kowa farin—ciki. idan Allah ya tabbatar da wannan, ka na ji ko za mu zauna da lmam din. lnsha-Allahu_zuwa gobe za ka ji amsa.” Yace “Allah ya kai mu lafiya, ya kuma’ zaba mana mafi alkhairi.” “Amin, amin.‘ Farincikin Alhaji ya ki boyuwa, annurin‘ fuskarsa ya
ce.
bayyanar da hakan har suka kare hirarsu Malam Sadiq ‘
ya koma gida. A- falon Mamasuke yanzu su uku har da Imam, Alhaji ya‘ maida maganar da Malam Sadiq ya zo da ita.
Gaban Imam ya fadi, haka kawai yaji.farin-ciki ya kama
shi. “Baba wace ce Asma’u a cikin“ ‘ya‘yan Malam, Sadiq? . Ya ce,‘“Ni kai na ba zan iya cewa ga’ ta ba,” amma ya gaya min ita ce babba kuma tana shekarar karshe a sakandire.” .Ya yi kasake yana hasashenta, bai ‘san me ya sa yake son gano ta ba, “To me ka ce akan maganar?
Yace,”‘Baba ka gaya masa a ba ni lambar wayarta.” Ya tashi da sauri ya bar falon. Mama na dariya ta ce, ‘Ba dai kunya ‘bace ta kore kaba?‘Ya waigo dauke da fara’a, ya dubeta, “Mamanmu kenan Yasa ‘- kai ya fice, suna masa dariya, al’amarin ya masu dadi kwarai da gaske, haka suke ta addu’ar Allah ’ya’sa alkhalri za’a kulla.
Gado kawai ya fada ya yi matashi da hannayen sa Mudansir ya rufe (Hand out) ya bishi da kallo tsawon lokaci kafin ya ce, “Yayana ya amsa, menene? Ya kara matso shi ya ce, “Duk da cewa ni yaro ne na goye ban san me ake nufi da soyayya ba, yanayin ka ya bayyana min ka kamu da jaririyar soyayya.’
Shi ma ya zubo masa ido, “Munafuki duk yadda aka yi ka na jin ta a boye.’ Ya tabe baki yana kada kai “No Ka san Allah ban san wannan ba, sai na kalle ka na ke karanta Love Story.” Ya yi murmushi, ya yunkura ya tashi, “Ka san ‘ya‘yan Malam Sadiq?
Ya ce A fuska na san wasu, amma ban san sunayen su ba.‘kasan Asma’u? Ya yi dan shiru ‘Asma’u….Asma’u…. lna jin ita ce mai yawo da nikabin nan. Me ta yi? Ya numfasa ya ce, “Son ta na ke.‘ ido waje ya ce, “Son ta ka ke yi, kuma ka ke tambayar wace ce ita?. Ya ce “Kai fa banza ne, mai tambayar tsiya, so dai ka ke yi in tona asirin, to Malam din ne ya ce ya ba ni ita.‘
Ya wangame baki har kunne, “Haba don Allah! , Kai amma ka yi sa,a da ’Bebi, _koda ban taba ganin fuskarta ba, da ganin kafafuwanta, za ta yi kyau, kai ba ka taba lura da ita bane? Ya ce, “Kai ni fa da wuka idan. aka tare ni, aka tambaye ni ‘yan mata a unguwan nan? Zan ce babu, tunda ban san su ba. ‘
Amma kai kana nan ka na kallon su, har ka san
kafafuwanta masu kyau ne, to kar in sake ji.’ Ya tuntsire da dariya ya ce, “Yaya kenan, in banda abin ka, ai ni~ na harsaso maka ita, k0 ka manta ne? Ya ce, “Shut up Ya kame-bakinsa ya ce “Na yi!
Shiru Imam’ya yi jim, kafin ya ce ‘Ka san me ke ban mamaki? Ya ce, “Sai ka fadi.” Ya numfasa ya ce “Ana gaya min maganar kawai na ji na zaku in gan ta.’
Ya ce “Kai tsaye ka ce min so ya kama ka.’ “Ka fa raina ni.”
Ya yi dariya “Ba haka bane Yayana, ka san‘shi Allah mai tsananin jin tausayi bawansa ne, shi ya sa ya musanya maka. Ya kuma sanya maka son ta nan take, fatan mu Allah ‘ ya nuna mana ranar da za mu angwance. tare da abin yi. lnsha-Allahu sai mun taimaki Baba.‘ ‘Wannan “shi ne babban- burin mu.” Gaba dayan Su suka daga ido sama. Ya Allah ka cika mana wanna“; burin’ namu kowa yace amin. ‘  qarfe takwas agogo ya nuna, ‘ lokacin da asma’u ta idar da sallar issha, wayar ta ke ta bugawa  gefen’ gado, ta yun_kura_ ta tashi ta duba lambar, take gaban ta ya tsinke’ ya fadi, domin sabuwar lambar da Baban ta ya ba ta ce, ta yi (Saving) cikin wayarta.‘_ Ko’ina jikin ta babu inda baya rawa, da kyar ta danna 0k ta kanga wa kunnan ta “Salamu-alaikuml Tsigar jikinsa-suka mike wani abu yarrrrr.. Ya Watsu cikin jikinsa saboda dadin muryarta da ya ji. A salube ya amsa “Wa-alalkumus-salam- Ki na magana da Imam Yusuf, ina fatan kin game?
Ta numfasa ta zauna gefen gado ta ce “Imam? Na wane- masallacin? Ya yi dan murmushi ya ce, ‘Masallacin Asma’u, idan ba za ta damu ba. Imam zai ziyarci masallacin don ya albarkace shi.” Fuska’ sake tace, “Masallacin Asma’u na maraba da wannan limami mai albarka.’
Farinciki ya lullube shi, cikin doki ya ce, “Ki saurare ni nan da minti goma lnsha-Allahu.’.Ta ce, “Allahumma Ya sha Murmushi ya yinda kuma take ya jibaya so ya kashe wayar saboda dadin muryarta.
Ya mike da sauri ya figi hularsa ya dora, yana kokarin zira takalmi jiki na raWa. Muda ya zura_ masa ido, “Yayana ina zuwa haka? Ya ce, “Matas zan je gani.‘ Ya washe baki ya ce “Oho! .Ai da na ga ka na tsuma, na ‘zaCi dambe za ka.” ‘
Ya doke masa kafada “Ban wuri in wuce kar ka bata min lokaci.” Ya ce, “Bi sannu Yayana, Asma’u taka ce babu mai kwace maka.‘ Ya dube shi tsakar ido ya ce, Ba laifina bane Muda, muryar ta kawai ta gigita ni.” Ya rungume hannayensa ido waje “Ina ga kuma ka ganta ido da ido.” Ya ce, “Ban san me zai faru ba.’ Ya ce, Kawai in biyo ka ni ma kar a ba ni labari.’
Ya ture shi gefe, “Ban _wuri ka na bata min ‘ lokaci.” Dole ya ja ya tsaya, saboda wayarsa da ta hau ruri. Ya zaro ta aljihu ya duba, lambar Jamila ya gani, ya ja tsaki ya wurga ta aljihu, tana ci—gaba da kukanta‘ ‘A‘ dawo lafiya Yayana. Gaisuwa dubu-Dubu a mika wa Antina.‘ Bai waigo ba, ya amsa, “Za ta ji’.
Yana tsaye kofar gidan ya kira ta, ya shaida
mata ya iso, yana kashe wayar, kiran Jamila ya sake shigowa. Haushi ya kara kume shi, ya danna 0k a fusace yace “Wai lafiya? Ta ce “Haba Yayana, magana na ji maras dadi, shi ya sa na Ke ta nemanka.’ ‘ “Da aka yi me? Ta ce, ‘Yau na zo Gombe zan ‘ .kwana, gobe na koma, muna zaune da Umma yanzu take gaya min abinda ya faru, tsakanin Baba da Dadi… Ya katse ta, “Na me kenan? Ta fara ba shi labari…
‘ Ya sake katseta, “Kin ga Jamila wannan magana duk ta riga ta wuce, an dade ‘da rufe wannan caftar, yanzu sabuwa mu ka shiga, har ma ta fi waccan dadi.” Ta ce,- “K0? Ai shi kenan tunda kai ma ka fahimci hakan, sai anjima, ka gaida mutan gidan.‘ Bai amsa ba, ya kashe wayarsa.
‘Lallausar muryar nan ya ji anyi masa sallama, shi ya sa bai tsaya tunanin kalaman Jamila ba balle su sanya shi’takaici, ya juyo a nats‘e ya bi ta da kallo, yana amsawa‘. Tsarki ya tabbata ga Allah mahaliccin wannan ‘ kyakkyawar sura. Numfashin sa ya soma zafi kamar zai dauke, “Sannu da zuwa? Ya kalaci .miyau ya hadiya da kyar ya amsa. ‘
Ta ce ‘Ka na iya shigowa.” Ta juya ya biyo bayan ta salalau~Salalaul Ta tura kofar wani daki da ke cikin turukan gidan, ta sauke labule ta kunna kwan lantarkin dakin ya haske’, gaba daya shafe yake da leda, ka na? aka dora wata ‘yar karamar jar kafet, wacce ta kara wa dakin kyau. . ‘
“Bismillah! Ta ce da shi,.ya shigo ya zauna,yabi—ta da kallo farin leshi ne jikinta wanda aka yi masa‘ ado da zare ruwan gwal, shi ya sa yake ta daukar ido saboda hasken fitila. dakin hijabinta ya karawa fuskarta kyau da kwarjini;
Ta zauna gefe suka gaisa, kafin ta ce, ‘Bari na kawo maka ruwa.’ Ya ce “Ah, kar ki damu.” “Ba zaka sha ba? Me wannan yake nufi? Ya dan kada kai yana murmushi, “Ba yana nufin komai bane Wallahi.’ To “idan kuwa haka ne, ya kamata ka sha ruwa a gidannan.” Ya ce, “Gaskiya‘ ne,’jéki kawo min.”
Ta mike ta fice, ya‘ rakata da kallo zuciyarsa na ‘sambatu. Ba na so ki tashi ne, ‘yan mata kin san sabon kamu.’ Ta yi sallama ta shigo dauke da dan karamin ‘ tire‘ruwa da lemun kwalba ne tare da kofuna biyu.Ta aje gabansa, ta bude ruwan mai sanyin gaske ta zuba masa a kofi, yana ta kallon ta.
Yatsunta zara—zara da’dogayen kumba, farare, “Uhm! Muda ‘ya yi gaskiya da ya ce Asma’u mai kyau ce.” Ya fada a zuciyarsa. Ta miko masa, hankalinsa ba ya‘ jikinsayana can yana sambatu, sai da ta ce “Ga ruwan Ya yi firgégi ya karbi kofin, ta koma gefe ta zauna.sanin kansa ne baya jinkishin ruwa, amma gwanin mamaki ya tada kofin ruWan. ‘
Ya aje’kofin ya numfasa, ya dube ta, “Ruwan akwai sanyi, na’gode.” Ta‘ce, “Saura lemun.”. Ya ce ‘Kar ki damu Shi ma zan sha, to yaya? Ga ki ga Imam.ina fatan kin san dalilin Zuwana? Ta dan‘ sunkuyar dakai
kadan ta ce, “Baba ya yi min bayani har ya tambaye ni “na san Imam?
,Na ce sosai ma, wani bawan Allah ne mai . madaukakiyar kima a cikin al’umma. Wanda matsayinsa baya samuwa face ya cika sharuddan ilimi, kammala, gaskiya‘, amana, kamewa da sanin yakamata. ldan wadannan‘abubuwan sun samu, take nan ake nada masa wannan rawanin.”
Ya ce ‘Asma’u ba limamin masallaci na ke nufi ba.’ “Ni ma ban ce shi na ke nufi ba. sau da yawa- Allah ya kan yi ma Wasu wannan baiwar, sai ka’ga an rada masu sunan tun tasowar su duniya, kuma idan sun girma, ka ga tsaf Sun cika sharuddan‘’
Ya ce “Da alama kin fahimce ni Asma’u. To Insha—Allahu zan ci-gaba da kawo miki ziyara, shi yasa na ke rokon hadin kan ki.” “Me ya sa ka ke rokon hadin kai ‘na. bayan zabin ka ya inganta?
Ya zura mata ido, baya ko kiftawa harda katon taguminsa, zuciyarsa na tambaya, “Ashe dama da irin wadannan ‘yan matan kusa da gida, shi ne na tafi can nesa’ ina wahala? Ya sauke numfashi ya yi kiranta, “Asma’u.” Ta dago idanuwa dara—dara ta dube shi ido cikin ido. , yace

   

Lol naku har kullum A, I, S

www.littafanhausane.com.ng

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]