[Advertisements⬇️]

Makaranta duniya chapter 22 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Makaranta duniya
             Book3

             Chapter22

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

3
.babu tabbacin zai samu kudaden wajen suleman. amma duk da haka Alh. Abdul. Rasheed ya zura ido washe gari k0
Suleman zai yi ba za ta. Amma har dare shiru Hajiya Suwaiba ta ci-gaba da korafi.
“Ai dama na gaya maka Alhaji, zai yi wuya Suleman ya aiko da kudin nan, don ba su ne a gabansa ba. Yakamata ka daina tagumi, mu fawwala wa Allah. idan ba su yi ba ba na, wata shekarar sai su yi idan muna raye’.
Yace. ‘Haka ne. Allah ya zaba mafi alkhairi. Duk da haka gobe zan sa kiyos din anan a kasuwa. tunda ba wani abin kirki bane a cikinsa’. Tace “To Allah ya sa a dace da mai siyan goben”. Yace ‘Amin’.
Washe gari kuwa haka aka yi. Alhaji ya ba zama neman mai Siyan kiyos, har bayan magariba, ba’a samu mai siye ba. Saboda haka ya dangana ‘ya bar wa’ Allah. Kudin da ke’ hannunsa ya je ya biyawa Mudansir na sa Naira dari uku.
Imam ya ci kuka. kamar manyan idanuwansa za su fado, gaba daya farin su ya dushe. Suka dawo jajur! Su alhaji suka ta sa shi da rarrashi, da kyar hankalinsa ya kwanta.
Shi kansa Muda ya tausayawa Dan— uwansa, da ya ga yana kuka. Shi ma rabewa ya yi gefe ya hau yi. Maganar kenan, haka imam ya
maimaita wata shekarar, kamar yadda suka yi shekarar ba su sake sa Suleman a ido ba, da kuma sakon da yace idan ya samu zai aiko. Shi yasa su kan mance suna da . Sulaima, idan ba maganar sa ta taso ba, ko shi ya yi wa Kaduna zuwan bazata.
Haka  Mudansir ya cigaba da karatu a daddafe, yau da dadi gobe babu. Ba irin halin da Alhaji Abdul-Rasheed bai gani ba na matsin rayuwa, wani lokacin abin ya hade da rashin lafiya ga iyalansa ko shi kan sa.
Amma bai~ taba hangen abinda ‘ke hannun Sulaiman ba, idan ba shi .ya kawo ya ce ga shi ba. To shi ne ya kan karba ya sa albarka, sannan ya yi masa nasiha akan rayuwa da kula da mahaifiyarsa.
A ‘yan tsakanin nan har dan kiyos.din da suke samun na kashe. matsaloli, shi ma ya shiga ribibi. Sulaiman bai taba tambaya ba balle ya ce zai sake zuba wasu kayan, duk da cewa ya san irin taimakon da shagon yake yi a’ gidan, domin shi kansa ya yi masa, amma ya zama kaza ci, share baki. Dan-Adam kenan!
~~~~~~~~~~~~~
Iman ya jima zaune gida bai sami tafiya jaml’a ba, ba .
don wai sakamakon sa bai yi kyau ‘ba ne, ah ah. Sai don babu kudin (Jam) balle ayi maganar Rijistireshon. Al amarin ya dami Alhaji Abdul—Rasheed, da kewa kawai yake yi. ‘
Ana cikin hakan Allah yaturo Sulaiman, da zai koma iman ya ce zai bi shi Bauchi. Alhaji bai so haka ba, cikin ran sa, saboda yana ganin ba Bauchi ya kamata Sulaiman ya tafi da‘iman ba. ‘ ’
Maganar makarantarsa ita ce ma fi muhimmancinsu kuma yana sane, don Inna ta sha yi masa magana, tunda bai nuna zai taimaka ba, shi ma
Alhajin bai bukaci taimakon na sa ba. Amma da ya yi tunanin zumunci, sai ya dauke abin a ransa ya kyale lman ya bi shi.
Shi kuwa kawazucin Jamila yake yi, ta jima ba ta zo hutu Kaduna ba, ga shi idanuwansa sun kosa su gan ta. Haka zalika ita ma, ganin Iman tare da Dadinsu, ba karamin sanya ta farinciki yayi ba. Nan da nan ta baibaye shi da kayan ‘ci da na sha iri- iri. ‘
Da yamma likis! Ta gayya ce shi, da su fita su dan zaga gari sa-boda ita ma shekéran‘jiya ta dawo hutu, ma’ana makarantar‘kwana take yi a Gombe, suka jerO, da ka dube su 2a ka’ gane jinin su daya.
“Wai kai har yanzu ba ‘ka sami (Adimisson) bane? Ya dube ta suka hada ido, yace “Ina zan samu, ni- da banda ‘kudin (Jamb).” Ta ce to me ya sa ba ka yi wa Dadi magana ba? Ya ce “Zai rasa sani ne? Kila baida kudi ne, shi ya sa bai ce komai ba tukun na? ,
‘ Ta tabe baki “Dadin? To in dai ka tsaya wasa zan zo in wuce ka ya yi.” ‘Yar dariya ya yi, ya ce .“Ai babu komai, don mata ta wuce mijinta? Ta dube shi cike da fara’a ta ce “Ka na nan da zancan ka k0 yaya?
Ya ce, “Ai don kar ki mance ne shi-ya sa kullum na ke tuna miki.” Ta dan rufe fuska, “Ni’babu ruwa na, duk ranar da su Dadi suka ji ka,”
Baki hangame’ ya ce “Zancan banza, ba su suka ba ni ke ba, tun ina miki tsarki, ina share maki majina?
Ta watso masa harara, “Ban son Wulakanci Yaya Iman Dariya yake ta yi farinciki fal Zuciyar sa, “Ba ki san wani abu ba?
Anti ta ‘fara cewa ke mata ta ce, ina ganin kuma ta fada. Mala’iku sun amsa, don kullum son ki nake kara yi. shi yasa na tambayi Yaya kun yi hutu ya ce min ya baro, za ki dawo gida. ni ma kawai na ce’a raina.
Insha-Allahu sai nazo .na jima ban ga mata ta
. kar wani‘ya zaga ya yi min kafar angulu.” Ta tabe
baki ‘Umm Kan ka ake ji. Ya ce “Ban son gulma‘ idan kuma keba kya so, ki gaya min inji’? Ta dube shi a kaikaice. shi ma kallon na ta yake yi,- “Ina jin ki! Ta janye idon ta ta ci-gabada murmushi. ‘
Ya kada kai, fara’arsa ta karu, “Gara ma dai su Dama su sani. don kar su bar kowa ya zo gun ki.” A shagwabe ta ce “Allah zan koma gida in har kaci gaba  dariya, yake yana fadin “ba za ki iya barin Yaya imam ba.“ Kallon Sa _take yi, ta tabbata zancen sa dutse
Sati uku hutun su Jamila ya karé; tare da Imam aka maida ta makaranta. lrin siyayyar da ya ga an zabgo mata. Tabbas ya nuna ‘Sulaiman yana da kudi. sai dai. bai  sa komai ba a ransa, face bakin-cikin rabuwa da abin sonsa
A hakikanin gaskiya~yanzu ne ya san yana son Jamila ba kadan ba, sannan kalaman da take gaya Masa sun kara ruruta wutar, sonta cikin. ransa. Shi kansa Sulaiman ya fahimce su, ballantana Murja da take mace. kallonsu kawai take yi kuma sosai abin ya yi
mata dadi a rai
‘ Kwana biyuda komawarta. kadaici ya‘dame shi ma yace komawa yake so. ya yi. Murja ta yi dariya ta ce “Ah’ah kawai ka ce matas ta tafi, kai ma Za ‘ Ra .tsere’ saboda damacan a dalilinta ka Zo” Ya shafa qeyq cike da kunya, yace “Ba haka bane‘Anti, kawai dai… sulaiman ya yi dan guntun tsaki, ya tashi da . Jaridarsa a hannu ya wuce dakinsa. Marja ke dariya. “Ka’wai dai‘me? na gane auran ne zai tabbata….,.. kiran Sulaiman‘taji ta amsa da Sauri taso  ya mike ya wuce masaukinSa,  kamar .bashiba. Zaune ta sami Sulaiman bakin gado. fuska
a daure ta zauna tana dubansa gani! ‘
Ya dubeta cikin fada ya ce “Wai me ya sa ki ke abu kamar wata karamar yarinya ce? gabanta ya fadi ta Ce, ‘Da na yi me? Kin wani zauna da yaro ki na ta wani yake baki, shi kuma sai wani gugar keya yake yi, yana fadin kawai dai’? Kawai dai! Kawai dai-din me? Mts…
Ta saki baki ikon Allah! Baban Jamila, daga maganar wasa, sai ka dauki zafi? …… Ya katse ta da hannunsa, “Dakata min don Allah? Ku mata ba ku da hankali, wa ya gaya miki ana wasa da maganar aure? yana jin dadin zumar da ki ke lasa masa? Ai sai ya dauka da gaske ne? Hannunta a kunci ta ce, “Baban Jamila menene aibun wannan maganar? lna ce abinda ya yi Iman, shi ya yi Jamila? _
Ya kalle ta a fusace ya ce, “Tabbas abinda ya yi ta, shi ya yishi, amma kowace kwarya tana da gurbinta! Tace “Ban fahimce ka ba fa Ya mike tsaye ya nuna ta, ‘Kar ki fahimta! Amma ina gaya miki ba na son wannan wasan. domin ‘babu shi a tsari na Ya fic cikin fushi».
Ta bishi da kallo tana kada kai, “Menene abun zafi? Banda abin Baban Jamila. Shi aureba nufin Allah bane? Ni kuwa zan ga, yadda zai yi, idan har yaran nan suna son junan su!
Da sassafe ya sa lman ya shirya, saboda wai’ yana ‘so ya aje shi tasha kafin ya wuce ofis. Haka kuwa aka yi. Murja. ta ba shi kudi tare da sakon kayayya ki da sabulai ta ce ya kai wa Mama da Inna.
Shi kuwa Sulaiman ya biya maSa kudin mota, sannan ,ya’ba shi dubu daya yace ya sanya aljihu. Bai bada komai ba akaiwa Alhaji ba; don yana ga’nin bai dade da zuwa ba, ya kai masu ‘yan‘ abubuwa. Kai Sulaiman halinsa sai shi.
Haka Iman ya yi ta tunani a mota har Allah ya sauke shi lafiya. Ya karaso gida zuciyarsa fara sol Don ko banza “ya tabbata mafarkinsa zai zama gaskiya. Kowa ya tarbe shi da murna, baran ma Muda da yake
jin kamar ya shekara bai ga Dan-uwansa ba, bayan ya natsa. ya mika wa Mama sakon su. Ta yi godiya mai yawa, haka kudin da ya samo, wanda bai cika masa wani abu ba.
Washe gari suna dakinsu, lman ya sheko Wanka ya sanya Shirt da wando na Jins sababbi, kayan sun bala’in yi masa kyau, shi ya sa Muda ya zura masa ido yana ta kallo; Ya zaro-wani turare yana fesawa. “Ko Yaya na ka’ kure gayum yau fa! Ya dube shi yana murmushi “K0? Mutuniyata ta siya min su, ka ga harda turare kwalba biyu.‘
“Ka na nufin Jamila? “Ina da mutuniyar‘da .ta fita ne? Ya kada kai, amma ba ka nuna wa su Baba kayan ba, “Me ya sa?’Ya zauna gefen gado “Wallahi ni‘ ma ban san me ya sa ba, kuma ka san wani abu? Ni fa da gaske son Jamila na ke yi”;
. Muda ya wangame baki “Ka na ya kyalkyale da dariya har da wuntsulawa daga gado. Imam ya bi shi da kallo’“Meye haka? Hauka ka yi.” Ya zauna kame da ciki yana fadin “Yaya kenan! Daga an siya maka kaya, sai ka ce son ta ka ke yi? Haushi ya kume shi,. ‘
“Ni ka ke gaya ma wannan maganar’? Ina wasa da kai ne? Ya wawuro bell yanufo shi, in ba ka yi ba ni wuri. Imam ya kawo duka. Ki‘ris ya rage ya same shi. .Allah ya taimake shi ya fice a guje, bin sa ya yi har falon Mama, ya bi shi, saboda sosai ransa ya baci.
Mama ta firgita ganin yadda suka’afko mata, ta mike tsaye “Meye haka? Lafiya Mudansir? ya boye a bayan ta. “Wallahi ban masa komai ba Mamanmu! Ta juya ta dube shi karya ka ké yi. haka kawai ba zai biyo ka ba, watau ka raina shi, saboda ka gan shi salihi ‘ko? To ka ci-gaba da kure shi.
“Ina kallo zai ji makaciwo, ba zan hana _shi ba
Ta juya kan Imam da ke tsaye rike da bell, yana huci “Yi hakuri Baban Baba! Ba’a san maza da fushi ba!
Ya watso wa Muda harara, yayin da shi yake masa ‘yar dariya, a dole ya sami mafaka. Dariya ma ka ke yi k0? Ta ce “Au dariya ka ke masa? Waliahi Muda ka kiyaye ni! Ya ce “Wai Mamanmu sai fada ki ke min, ni fa ban masa komai ba, kawai daga ya ce Jamila ce ta ‘ siya masa wadannan kayan, shi kenan fa wai…. Wai… Kawai ya biyo ni…!
Ko kafin- ya gama fadi lman ya juya ya bar falon, ‘Ka dawo Yayana. Wallahi ba zan fadi gaskiya ba ai! Ta zura masa ido, yana ta kwasar dariya, “Kenan ni ku ka raina ma wayau?Ya ce, “Ba haka bane Maman mu.”
‘ Ta ce “Haka ne mana, idan ba haka bane, to gaya min gaskiya.” Ya yi gyaran murya ya ce, “Ki na ji na? Yaya ne dai, Yaya ne dai! Wai ‘daga Jamila ta siya masa kaya, shi ne ya ce’shi Wallahi da gaske sonta yake yi, wai don me zan yi dariya? ‘
Ta nuna shi “Ah’ah Muda, kai da ba ka san yana son ta ba? Ai mu tuni mu ka san yana sonta, ba don ta siya masa kaya bane.” Ya bita da kallo ido waje,
“Auranta kenan zai yi? Ta ce “Muna fatan hakan, idan akwai alkhairi.”
Ya kama hanci ya rangada guda, ya fice da gudu. Mama ta kece da dariya ta Ce, “Wadannan yaran? Ta nemi waje ta zauna ranta fari tas! Saboda hasashensu tuntuni ya tabbata gaskiya.
Yana shigowa. Imam ya watso masa harara, ya ‘ nufo shi yana dariya ya rungume. “Yaya na….! Ya banbaro shi ya ce “Daga ni! Algungumi! Baki har kunne ya ce, “Yaya ban fadi komai ba fa! Ashe su masu Maman mu sun sani tuntuni! Ido waje ya ce “Kai haba! ‘“Gaskiya-na ke gaya maka.” ,
‘ Dadi ya rufe shi, bai san lokacin da ya jawo _kafadar Muda ya manna shi jikinsa ba, idanuwa rufe yake fadin “Allah na gode maka! Daidai saitin kunnansa ya rangada masa guda, ya bude ido, a firgice. Muda ya
keda da dariya, shi kuwa ya murkushe shl bisa gado yana masa dukan wasa. Kowa ya sami labarin wannan al’amari murna yake yi, amma shi dan gogan Sulaiman bai taba zama ya yi maganar da kowa ba, duk da cewar
sau da yawa akan tada zancen a gabansa, musamman Inna Mairo.
~~~~~~~~ §~§~~§~~
watanni tara tsakani. Imam ya rubuta jarabawar share fagen shiga jami’a, ,Alhaji ne ya biya masa, domin ba na amfanin gona ya yi kyau ‘ tamkar yadda sakamakon ya fito yayi kyau. Babu bata lokaci Alhaji ya yi masa rijista da dukkan shirye—shirye.-ya samu gurbin karatu a a b u Zariya karatu a fanni kasuwanci, yayin da son Murja ke kara girma a zuciyarsa.  ita‘ ce mafarkinsa, idanuwansa ba sa ‘ jin dadin rashinta , ga shi ta yi masa nisa, shi ya sa ma idan ya zauna shiru, ya kan ji zuciyarsa  kamar tafashe. ‘ ” akazalika haka zatika Jamilar ke ji cikin ranta kamar Imam ya” birkita tunaninta fiye da yadda take ji can Ta kan tambayi’ kanta, wai son shi take yi da
gaske ko shakuwa ce kawai? Ta kasa gano amsar ‘ ‘ wannan lokacin.
_ ‘ Hutu suka samu na karshen shekararsu na aji daya a babbar sakandire, kwana biyu ‘tsakanin take gaya wa Ummansu Kaduna‘ take son yin hutun ta, gaba
. daya na wata biyu. Cikin jin dadi take gaya wa Sulaiman, nan take ya sauya fuska ya sa ta kira masa ita, a daki ta same shi, ta zauna gefensa ta ce “Gani Dadi.” .
Ya dubeta da kyau ya ce, “Aka ce wai za ki Kaduna hutu? Ta ce “Wallahi kuwa.” .“Saboda me? Ke _Kullum kamar anamintsilinki’ cikin gidan ku, ba kya iya zama   mai yasa su qannen naki basa dokin zuwa kadunan Ta bi_shi da kallo ta tabe baki “Oho! Ni ma ban sani ba
Dadi, wata kila don ba su dandana dadin Kadunar bane shi ya sa.” Ya ce “Au, Kadunar har wani dadi gareta? Ta yi ‘yar dariya ta ce ’Ai kuwa Kaduna akwai dadi Dadi, ga yan tsofaffin nan su yi ta taraiyayar ka…
Ya katseta, “Tarairayarki dai Ta ce, ‘Ai dama hakan na ke nufi.”, Ya ce, “Ke dai ki ce za ki wajen Imam kawai, kin fi so ki je ku yi ta- zama ku na surutan banza kawai, wai ke ba ki san kin girma bane? Ya kamataki fuskanci karatunki kadai, domin ina gaya miki karatu yanzu ki ka fara, a kuduri na, ba zan miki aure ba, sai kin kama aiki
Ta daga kai sosai ta kalle shi, ‘Aiki Dadi? ‘Tambaya ma ki ke yi? To gara ki Gane,a wannan ‘ zamanin ba’a zama wasa. Kowa neman na kansa yake yi, sannan sai kin zama wani abu, za ki sami miji mai na garta wanda za ki huta, ki ji dadin rayuwa, ai kin gane? Ta yi shiru tana tunani, ‘Meye mai na garta? Ya dafa kanta “Kamar ba ki gane ba k0?
Ya yi dan murmushi ‘Koda yake ke yarinya ce, ba ki san me zamani ke ciki ba, amma a sannu zan rinka wamare miki komai, sai dai duk da haka ina so ki sani, ba kowane kwashe—kwashe ake saurara ba, mai aji, sai mai aji dan—uwansa. Shi ya sa ki ka ji na ce ki dage ki yi karatu sosai, ki kama oflshin ki.‘
Ta ce ‘Haka ne, to yaushe zan tafi Kadunan? Ya dube ta da kyau “Kin nace da tafiya Kadunar nan, ki bari karshen sati, sai in kai ku duka mu dawo tare.” Ta dan turo baki, “Ni fa sai hutu ya kare zan dawo gaskiya.‘ Ya kama dariya “To shi kenan a daina turo wannan ‘ bakin kamar na jaba.’ Ta fashe da dariya ita’ma’saboda murna.
Tun yammacin juma’a Imam ya dawo gida, don yin hutun karshen sati. Washe gari kamar daga samasu Jamila suka diro. Wayyo dadi! Imam rasa inda zai sa
– tsumman ransa yayi,babu abinda yake so Ma su dan
kebe su zanta. lta kuwa kamar ja masa rai take yi, sam ta ki yarda tana like da Mama. Yinin nan guda ya kasa cin abincl, saboda zumudi da doki. Bayan sallar lssha, ya same ta zaune lta kadai a falo. Hannun kujerar ya zauna ya bi ta da kallo. “Lafiya? Ta tambaya, ya yi dan murmushi ‘Kalau! ‘To wai nai miki laifi ne? Ta dube shi “Kamar yaya?
“Na ga ki na share ni ne kamar ba kya murna da gani na? Ta ce “Shi ne abinda ya dame ka? Ya ware ido, “Ya ba zai dame ni ba kuwa? Abinda ka ke so, ya ki ya fuskance ka, yaushe za kaji dadi? Ta yi dan murmushi nan mai razana shi, ta ce “soka ke su Maman mu su gane? Kunya ta hana ni zama, bayan na’Ce anan zan yi hutu.”
Ya fara, dariya, “An gaya miki su Maman mu yara ne? Koda yake ki na School ba sani za ki yi ba, amma tun yaushe su Baba suke maganar da Inna.” Ta ware ido, “Don Allah‘da gaske ka ke yi? Ya ce, “Sa Wasa! Ta ce, “Amma Dadi bai sani ba? ’ ‘
Ya gyara zama ya ‘ce, “Tsohon labari.” Ta ce “Shi ne ka zo ka zauna anan? UhUm! Ta yunkura ta tashi ta sauya kujera, ta bar shi yana dariya, “Boye—bOyen me ki ke yi bayan… .
Faduwar Mudansir falon ya sa ya yi shiru‘, ya
dube su ya tuntsire da dariya “Gamo ka yi? lnji Imam, ya’sa hannu aljihu ya ce, “Da masoya ba Mts…. Ta ja dogon tsaki, ta tashi ta yi waje. Imam ya taso ya zungure shi, “Kai dai ba ‘ka yi ba Wallahi, dubi ka ’ korar min ita.” Shi ma’ya fice ya ‘bar shi yana masu‘ dariya.
Can gefen kicin ya same ta bisa kujera ya jawo turmi ya zauna ya ce, “Me na’gaya miki, ‘kowa ya sani, dama kin saki jikinki.” Ta yi dan shiru kafin ta ce “Ka na sha’awar karatu mai zurfi? Ya ce, “Ah sosai ma, ai mu
sai mun ga karshen Mango Park! Ta yi dan murmushi ta “Ba fa kai ba, ni kaina na ke magana
Ya ce “K0 ke din ma menane? ilmi ai yana da kyau Jameela, kuma yadda ‘na ke son ki kamar zan mutu, komai ki ke so ai ban da zabi” Ta sunkuyar da kai tana ‘yar dariya, ya numfasa ya ce, “Ba wasa na ke yi ba Jameela, son ki kamar zai kashe ni na ke ji, amma ke kamar ba ki damu da hakan ban”
Ta duba shi kasa-kasa ta ce, ‘lnji wa‘? Ya kafe ta da ido ya ce,” “To ki ce ki na so na inji? Da sauri ta rufe fuska’, ya bi’ ta da kallo yana ‘yar dariya, har Sulaiman yazo ya kare masu kallo, ya wuce falon ba tare da sun sani ba’. ’ ~
Ya zauna haushi da takaici kamar ya kwarma ihu kai! Ya kasa daurewa ya kwala matakira har cikin hantar ta ta ji kiran, ta amsa, ta taso da sauri, yayin da ita ma Mama kiran’ne ya ankara da ita cewa akwai mutum a falon ta, don haka ta baro sallaya ta fito falan, “Wai daman ka na zaune a nan?
Ya ce ‘Ah’ah yanzu na shigo.” Ta zauna tana fadin “Koda na ji, to bari a kawo abincli  Ina su Maryam da Hafsat? Bai amsa ba. Jamila tashigo, “Gani Dadi.” Shi kansa bai san dalilin kirama ba, dan hakan ya rasa me zai ce? ‘Dama …… .
….Abinci za ki karo min, yunwa na ke ji’.” Mama ta ce ‘Maza kicin na sa yana nan bisa tire ki dauko.” Ta ce to, ta fice ta .iske lman zaune ya’ sunkuyar da kai , kasa, hakan ya ba ta damar kabe hularsa ta fadi kasa.
Ta shige kicin da gudu, ya bita yana ‘yar dariya, kafin ya kada kai yasa hannu ya dauko hularsa ya maida bisa kansa, ta fito da tire ta wuce tana masa dariya,“Ni ko za ki dawo ki same ni.” Ta. waigo’ta yi masa gwalo ta wuce, ya dafe kirji ya lumshe ido ya numfasa, sannan ya ji sanyi ya ransa
Tana aje tire, ta juya za ta fice “Ina za ki kuma? Ku je ku kwanta mana ku huta gajiya.” Ta ce “Ba najin barci Dadi? Ta wuce da saurinta, haushi ya kara kume shi. Ya ja dan guntun tsaki. Mama ta’ ce “Ina ruwan Jamila ai yau babu‘barci, ga ta ga mutumin.” Ya yi shiru
kamar. bai ji ta ba, ya bude samirar tuwo ya yi masa sallama.
“Kai Niba zuwan ba, abincin da Mutum zai ci shi ne matsalar.” Ya fada a_ ransa, ya sa cokali ya cakuli loma biyu, ya rufe ‘Har ka koshi? Ya ce ‘Wallahi kuwa.’ Daga wajé suna jiyo hanayaniyar yaran suna ta tsokanar juna, suna cin abincinsu a tsakar gida.
‘ Mama ta ce ‘Ah! Gida ya yi albarka.” Ya ce ‘Lallai kam! Ta gyara zama ta ce “Wai mu har yanzu ba muji maganar Jamila ba,‘ koda yake maganar ba taka bace, sai abinda muka yanke, muka yanke
Ya kara tsuke fuska ya ce ‘Gaskiya ne, wai ina so ma in tambaya, dama akwai aure a tsakanin su ne? Ta yi dariya’ ta ce .“Ah! Sosai ma, ai Jamila ba ta cikin jerin matan da suka haramta Imam ya aura.’
Ya ce, “0h, ashe shi ya sa suke ta‘shirmensu, yara kenan.’ Ta mike tana fadin “Allah dai ya tabbatar mana da alkhairi.’ Bai ce amin ba, ya wuce yana cewa ‘Bari in je wajen Baba.‘ Ta ce, “To, ni ‘. ma yanzu zan ’kawo masa abinci.’ Ya sa kai ya wuce,
.Washe‘ gari ranar lahadi, suka yi shirin tafiya ‘ Kauran Juli. Sulaiman ya tada hankalin kowa; ya kuma ba kowa mamaki saboda kafewar da ya yi ceWar tare da Jamila za su koma. Jamila .ta fara kukah hankalin Imam ya yi mugun tashi, don shi ma ya saki» Jiki zai shafe kusan wata biyu, duk sati Zai zo ya ga Jamilarsa.
Aihaji ke ta shari’a kusan minti ashirin da suka wuce, ‘Haba Sulaiman, da; ka san ba 2a ka bar taba,
tun farko da ba ka sa mata rai ban, to wai ma me ya sa ka sauya ra’ayi? Ya ce, ‘Tunani na yi Baba akwai
ayyuka da ZaSu hana min zuwa dau’kartane  ni kuma ba na so ta biyo motar haya ita kadai.”
Ya ce ‘Don wannan kuma, ai ko ni sai in dawo da ita.’ Da sauri ya amshe, Ba zai yuwu a wahalar da Kai ba, tunda an zo an kwana, ba an yi zumunci ba? Ya ce ‘Ba shakka an yi zumunci, ke Jamila ki hakura ki’ koma, wani lokacin kya zo, ki yi hutun k0? Yi hakuri, kin ji suruka ta? Ta tashi ta fice cikin kuka ta yi waje.
Suna mota, babu mai magana ,daga ita har imam, shi ma ya biyo su, idan ya gama ziyara a Kauran Juli zai karasa makaranta. A haka suka karaso kurame babu wanda ya san‘ lokacin da suka sulale can bayan wani gida makwaftan su Inna, nan suka boye.
Imam ya yi ta rarrashinta har ta dan saki ranta, suna ta hira, a nan take gaya masa abinda Sulaiman ya ce game da ita. Imam ya yi murmushi ya ce, “Aiki, haba da wasa Yaya yake yi, ina gama makaranta na sami aiki me Za’a jira? Ko ke kin fi son hakan?
Ta ce, “Yin aikin ma ai yana da muhimmanci k0? Ya bi ta da kallo, ‘Yana da shi tabbas, amma bayan mun yi aUre.’ Ta ce, ‘Ka na gani Dadi zai yi magana da wasa, bayan sai da ya zaunar da ni musamman‘? Ya yi dan shiru kafin ya ce.
‘Ke mu fa ba mu da matsala, wuyar abin kawai ba mu ce muna so ba, tunda mun ji, mun gani kuwa, . magana ta kare, yanzu yi maza ki ba ni lambar ki Ta fiddo biro da ‘yar takarda, ta rubuta masa lambar wayarta, kafin ta ce, “insha Allahu zan siya maka‘waya ko karama ce, kai ma ka rike.” Ya ce “Ah – haba? Da gaske? Ta ce “Eh mana ko yanzu da zan sami dubu biyar wajen Dadi, da na latsa shi, akwai dubu biyu ‘ a hannu na, sai in baka, ai za’a’sami ta hannu a dubu bakwai ko?
Ya ware ido, “Sosai ma, amma kar ki damu kan ki, zan rinka kiran ki a ta kudi, sannu a. hankali ni ma zan siya Ta dube shi, ‘Wato ba ka so in siya maka kenan? Ya kada kai, “Ba haka bane, kar ki yi fushi My Baby, ina nufin kar ki takura‘wa Dadi, wata kila bashi da su a halin yanzu, kin gane?
Ta juya ‘fararen idanuwanta, ta dauke kai, zuciyarsa ta kara shiga wani garari na bege, ya kara matso ta, “Look, ‘kin gene? Ban son ki bata ranki, sai ki hana zuciya ta sukuni. To yaushe za ki siya min wayar? Ta juyo a karkace ta dube shi jim,’ ta janye idon ta, ya yi dan murmushi, “Jamy baby, ayi hakuri na ce,please!
Ta sake’ duban sa, zuru suka yi wa juna, a
hankali yake fadin, “Tuba na ke! Ta yi dan murmushi, ya sauke numfashi, amma kafinya ce wani abu, muryar Hafsat ta shigo kunnuwansu, ‘Oh! Dama ‘ku na nan? Duk suka juya suka dubeta, “Watau nan ku ka boye? To ku je Dadi na kiranku
Ta dafe kirji ido waje, “Fada yake ta yi? Ta ce, ‘Oho! Ta wuce abin ta, suka biyo ta. Imam na fadin, “Mun shiga uku! Ta ce, “Kai ka ja min! “Ke dai ki ka ja min! Hafsat ta waigo ta fashe da dariya “Ni kike wa dariya? Za ki sha’wuya, in na kama ki? lnji Jamila imam ma ya hau dariyar ganin yadda ta tada hankalinta, a haka suka karasa gida,
Da Suleiman suka fara karo a kofar gida, ta rage sauri tana ‘yan noke—noke, ko shi Imam din kunya sosai ta rufe shi, har ya rasa me zai ce? Kai tsaye cikin gida take kokarin shiga, “Uban me za ki yi a cikin gidan? Ya daka mata tsawa, take nan gabanta ya yi – mugun faduwa, don ba ta taba jin wannan kalmar ba a bakinsa.
A daburce ta ce,’ “Zan sallami Inna ne! Cikin fushi ya ce, “Don Allah ni shiga mota mu wuce, ki na bata min lokaci! Stupid Ta wuce simi-simi, ta bude mota ta shiga, sai ga Inna da kunshin leda, “An gansu?
Ya ce “Ga ta nan, banzar yarinya kawai! Ya bude mota ya shiga, fuskarsa kamar gobara ko inda Imam yake sototo bai kalla ba.
Inna Mairo ta leka ta taga, ta mika masu leda, “Ke ba ki san sauri yake yi ba, saboda dare? Imam yana nan babu me kwace miki shi, kin ji? Kalaman Inna ya sa ta goce da kuka, yayin da su Ummi da Hafsat dariya ta kwace masu, shi kuwa Sulaiman tsaki ya yi ya ce “Don Allah Inna ki bar maganar nan, bari mu lallaba.”
Ta ce, “To Allah‘ ya tsare, a gaida Marja da kyau.” Za ta ji.‘ Ya tada mota yana ribas, su Ummi na daga wa Imam hannu, babu kuzari a jikinsa, shi ma yake daga na sa hannun, idanuwansa kan Jamil’a da fuskarta ke kunshe da maya fi, tana kuka. Haka suka wuce suka bar shi cikin tashin hankali.
Tsaye yake kikam! Tsawon lokaci. Inna na kallonsa, sai da ta ga abin ba zai kare ba, ta matso ta kamo hannunsa, a firfice ya dube ta, bakin sa na fadin “Jamila ~ki daina kuka.”
‘ Ta zuba masa ido tamkar yadda ya’yi mata zuru, har sai _da ya gane Inna ce gabansa, ya yi sauri ya runtse ido ya kauda kai, ta ‘yi ‘yar dariya ta ce. “Allah’Sarki Baba na, kar ka damu za ta daina kukan, ka ji? Zo mu shiga ciki. Taja shi, duk’ kunya ta rufe shi “Zauna Baba na.” Ya zauna ita ma ta zauna ta dube shi, “Ka kwantar da hankalin ka Baba na…
Da sauri ya katse ta, “Ba kya ganin Yaya ya yi fushi Inna?  za’su tafi yana ta mata fada kin ga ba za ta daina kuka ba Inna.” Ta yi dariya kafin ta ce, “lkon Allah soyayya gamOn jini. Allah dai ya tabbatar mana da wannan‘ abu. ‘Ni dai ka kwantar da hankalin ‘ka, ga abinci nan ka ci, kafin ka karasa makarantar. Ka ji? Bai
tanka ba, ta matso masa da kwanon abincin ta fita yin alwala.

Www.littafanhausane.com.ng

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]