[Advertisements⬇️]

Makaranta duniya chapter8 - Bankinhausanovels
Sun. Mar 26th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Makaranta duniya

             Chapter8

Ya runtse idu. YaCe “Subhanallahll Yanzu meye‘ abin yi?” Tace “Dama taimakon farkn zan masa yanzu. sai a kai shi asibitin. hakora”. Yace “Toyi sauri”. Ta
‘ wuce kicin ta barshi. yana cewa.
“Wasu iyaye akwai sakaci. wai ace gari ya waye ba za’a kula da bakin yaro ba? Ai mu ma kauyen mu ka tashi. amma kullum safiya sai an goga mana gawayi da
dan gishiri ace mu wanke baki. Wani lakacin ma gwaggo da kanta take dirje mana. Tace bama wanke wa da kyau. Mts
Yaja dugun tsaki. Hajiya Suwaiba ta fito da ruwan dumi a kofi da wadataccen gishiri’a cikinsa. Hannunta daya kuma wani katon timatir neta taho dashi bayin inda Suleman ke tsayuwar jiranta. 3,
‘ Alhajin ma _ya biyo bayanta. Ta kama shi ta dirje bakin NASA  da timatir din nan. Tun yana daurewa har ya fara kuka.
Tace “Hakuri zakayi Suleman, ‘idan ba haka ba yau, sai dai ka kalli abinci, tunda ka fama gyambon sabada Allah dubi hakura har gansa kuka suke yi. Mts …… ”
Alhaji yace “Dirje shi da kyau, haka zakaje  makarantar da yalolan hakora, suna azabar wari?” Yana tsaye, ta gama, ta zuba masa ruwan dumin nan, yayita kuskurewa har ya kare, sannan Alhaji ya bar wajen. Ta zuha masa ruwan wanka, ta cuda shi da kyau, kafin ta
‘ fito, ta kyale shi ya karasa.
Yana fitowa, ta gage shi da tawul. Ta dauko ‘wani maganin cututtukan fata (Sulphur 8), ta shafe masa jiki gaba daya, sannan ta goga masa basilin a,kafafuwansa da fuska. Ta gyara shi tas! sannan ta zabo masa kananna kaya,. ta fesa
masa turare. Tace “To maza falo, gani nan zuwa, da abin karyawa”. .
Yace “to. Ya fita ya iske Alhaji a tsakar’ falon, shima fitowarsa kenan. YabiShi da kallo kafin ‘yace “Malam Sule kenan. to zauna mana, kaga yadda ka yi kyau?” Yana murmushi ya karasa gunsa,‘ ya rike hannunsa Mun kuwa gaisa?
au na manta  aahe Mamanka ta dirje bakin  babu halin gaisuwa ko?” Ya sunkuyar da‘» kai yana ta murmushi. Yace~,”|na kwana?” “Lafiya kalau. Mu karasa tebur’ mu jira abinci”.
Yana rufe ‘baki, ta fito tana cewa, “Ayi min hakuri, ku’ nata jira ko? Nadan ~gyara Wajenne. Bissimillah!” Alhaji ya jashi, yana fadin “Mu dai mun kosa, cikin mu nata kiran ciroma”.
Tana dariya ta shige kicin, su kuma suka karasa tebur. ‘Zauna anan”. lnji Alhaji yana nuna masa yadda zai zauna. Jimawa kadan tayi ta fito da abincin karin safe, ta zubaWa kowa. Suleman ya shiga’jan gaya.
Alhaji ya dube ta. Yace “Wai  yanzun wane Aji ma za’a sa Suleman. gotai-gotai dashi?” Tana ‘yar daria ta amsa “Aishine, idan aka sa shi ajin kananan
yara dariya zasuyi masa. Baban aji kuma bA iya karatunsu zaiyiba  Yace.
“Haka nan za’a sa shi aji daya, idan Allah ya‘ taimakeshi ya maida hankali, sai kiga ya mike, ya kuwa bama kowa mamaki”. Tace “Haka muke fata. Allah ya sa a dace”. Ya amsa da “Amin”. Suna gamawa. Direba ya yaxo suka wuce office.
da daddare kamar kullum. tare suke cin abinci da Alhaji Bara’u. Shine gidansa ke manna da na Alhaji Abdul-Rasheed kuma shine mataimakinsa a ofice
Abincin gidajen biyu na kam bisa dardumar da aka shimfida a ‘koridon gidan Alhaji Abdul-Rashead. Kowannen su ya tankwashe qafa. suna aika abinda ya samu. ‘ Alhaji Bara’u ya dubeshi. Yace “Yallabai. wai da gaske ne maganar tiransfa ta?” Yayi dan murmushi Yace “Tama kusa nanda wata ukune 
._ Yace “yane ka kosa ne? Nida naketa addu’ar’ kada Allah yasa tazo”. Ya dubeshi da kyau “SBD me? Ni Ina ta murnan cigaba yazo maka, kaifa zaka rinka kula da Fambeguwa; Dutsan’Wai da igabi. Sai
dai ko in zaman kauyen ne bakaso ya  kada kai. “Ko kadan Yallabai.
dadin zama dakai gida da ofis. shiya sanya ni tsanar
tiransifar.
cike da fara’a. Yace“’Gasl<iya ne, yanzu haka yaron yana nan a cikin gida?” Yana ciki. bari in kirashi, kaganshi, dan wajen kanwata ne ina son ya sami karatu susai shi yasa na daukoshi”. “Wallahi ka kyauta Yallabai. ka ga gobe in Allah ya kaimu, sai ya shirya in tafi dashi inyi masa rijista da kaina”.
Fara’arsa ta karu “Da kanka?” “Eh mana, danka, ba dana bane?” Yace “Gaskiya ne, kuma ka tallafa wa maraya, kai ma Allah yabaka lada”. Yace “Maraya ne? Allah ya taya ka riko”. Yace “Amin”.
‘ Ya mike ya kwala wa Suleman kira, ya amsa ya fito. Ya sugunna gabansu,‘ ya gaida mutumin daya gansu tare, sannan Alhajin. Yace “Wannan shima Bahanka ne. in Allah .ya kaimu gobe zai kai ku makaranta tare da ‘ yaran‘gidansa. Ka sami abokai ko?”
Yana murmushi ya amsa “To tashi ka ’ kuma cikin gida, sai Allah ya’ nuna mana guban”. Ya tashi ya koma ciki Alhaji Bara’u yace. ‘ . .
‘ “Yaro kyakkyawa dashi”, Yayi ‘yar dariya, sukaci—gaba da hirarrakin duniya har’zuwa tara na dare. Suka yi sallama kamar yadda suka’ saba, kowa ya koma gida, don jin labaran karfe tara watau (N.T.A News).
‘ ‘ Babu kowa‘ a falon, ya nufi tabur ya aje kayan abincin, sannan ya wuce daki ya same su cikin bayi, tana
wanke maSa baki. “Ka shigo Alhaji?”
Yace “Na shigo Anata wankin bakin ne?” Ta amsa “wlh” “Lallai an kawo miki aiki”. Tace “Ai na jima ina marmarin irin wannan aikin. Allah ne bai nufaba, shiyasa na hakura. Kaga kuwa mai neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki”. ‘
Ya gyara tsayuwa cikin taushin murya. Yace “Bai manta da muba Suwaiba, kullum fatana Allah yasa jinkirin ya zama alkhairi‘. Farin-ciki na koda yaushe. yadda hakuri ya zama linzamin ki. ‘Shiyasa nake ganin ke kadai ki ka dace dani. koda laifin daga garakine, balle-
ba daya kanwar biyu”.
Ta juyo ta dubeshi sasai. Tace “Nina fi cancanta da in fadi haka Yallabai. don kai ma laifin ba daga wajenka bane. Sannan bazan yi butulci ba, kowa ya bani goyon baya babu matsi ba tsangwama.ina Godiya ga Allah wanda komai nasa ni’ima ce ga bayinsa”.
Ya numfasa. Yace “Kinyi gaskiya. Kinma san wani abu? Gobe Alhaji Bara’u zai tafi dashi makarantar yaransa, kuma shi zai dauki nauyin yi masa rijista”.
Tace “Ah! To madalla, Allah ya saka ‘masa da alkhairl”. “Amin”. Ya amsa tare da juyawa ya koma falo
donyin abinda ya dawo daShi cikin gidan.  lta kuwa bayan ta gama wanke masa bakin. suka‘ dawo daki, tabashi magungunan da aka bashi a asibiti.
Ta sake shafe shi da maganin fata. ta zura masa kayan
‘barcinsa. ya haye gado yayi kwanciyarsa. Ta duko kusa da fuskarsa.
Tace “Ka dai kashi sosai ko?” Ya amsa yana murmushi. “Eh”; Ta shafa kansa. “Toshi kenan, Allah ya tashemu lfy
Yace “gobe da gaske za’a kaini makarantar’?” Tace “Eh mana,‘ bakaji Babanka yana fadi ba? Shiyasa nace ka yi barci da wuri. saboda ka tashi da wuri, ba,a barci a Mankaranta
‘ cike da murna. Yace “To Ya runtse idonsa, ta  ,fito tana murmushi, tana fadin “‘Sulemén kenan. anata doki,
********W* “
Watanni uku ‘kenan da zuwan Suleman gidan kawunsa. Ya yi’bulbul! Ya kara haske, fatarsa data dafe da kirci, duk ta waShe ta dawo subul! Kamar yadda Mairo  haifoshi sutura kam ya cire wannan yasa wancan safe da yamma daban. Makaranta  kuwa, ya dage qarai da gaske  ganin cewar sauran yaran duk sun tsere masa, musamman ta. yadda ’suke juya harshe..zuwa turanci,
hakan yasa ya dage wajen ganin shima ya iya Shi yasa yake ‘kwaba abinsa. koda za’ayi masa dariya ne. Haka kuma lnnarsa Hajiya Suwaiba ta sa ido sasai akan karatun nasa, sosai take masa darasi a gida. sannan ta kanyi masa‘turanci Wajen magana, kobashi umarnin yin wani abu, donta lura yana son juya harshe ‘ kwarai da gaske. ‘
Shi kansa Aihajin yana jin dadin hakan, dalilin da yasa kenan komai ya gani na sha’awa kona wasan yara,. sai ya siyo wa Suleman, sabuda ya kara masa kwarin gwiwa ‘tare da faranta masa rai, donya kara sakin
jikinsa dasu. _ duk inda ka duba cikin gidan tarkacen Suleman ne  sauran ‘yan-uwansa, kuwa ko alama ba za’a kwatanta suba.don Shi kansa idan Alhajin ya kaishi dutsen Abba, ji yake tamkar bai taba rayuwa cikinsu ba. ‘
Sai ya zama tamkar farin wata a cikin duhun
dare, ya zama abin kallo da sha’awa ga kowa, musamman ‘yan—uwansa yaran da suka taso tare. Kwarai rayuwa ta sauyawa Suleman, shida kansa da yake yaro ya sanhakan; Inna Mairo kuwa; farin-ciki ta baya. misaltuwa’, shiyasa koda yaushe sallolinta biyar bata sauke hannu ba tare data sanya Yayanta cikin addu’ointa ba. ‘ Karshen watan nan, tiransifar Alhaji Bara’u ta shigo hannunsa. A hakikanin gaskiya ransa bai soba”
shi kan yafi son zaman Kaduna, kodon sabuda karatun ya’yansa. Tsananin damuwa ta sa ya baYyana wa Alhaj
Abdul-Rasheed matsalar sa dangane da karatun  yaransa. Take nan Alhajin. Yace “ldan zaka iya Alhj Bara’u. ka barsu mana a wajena, suci-gaba da karatunsu anan?” ‘
Ya tsame hannu daga kwanun abincin, ya dubeshi da kyau. Yace “‘Ya’ya uku Yallabai. ai na bar maka hidima. Sunyi yawa Alhaji, haka nan zan hakura, su koma can suyi karatun”. Alhaji ya kada, kai. ‘
Yace “Banji dadin lafuzanka ba Alhaji Bar’a’u,
kana nufin ’yayanka, ba nawa bane?” Da sauri ya kada. kai “Ba haka nake nufiba Alhaji
“To me zaisa ka gaya min ka kawa min hidima?” Ya ajiye kai kasa, ya numfasa jim, kafin ya dago ya dubeshi “Yi hakuri Yallabai, zan barsu wajenka, ina shiga cikin gida zan yiwa Mamansu magana”.
Yace “Yanzu na tabbatar da cewa ka daukeni tamkar dan uwanka kamar yadda abin yaka cikin
zuciyata”. Yayi kayataccan‘ murmushi. Yace”Alhaji Allah ya bar mana zumuncin mu, na gode. Allah ya saka da alkllairi”. ‘ Yace “muci abinci Alhaji Bara’u. zaiyi sanYl’~ sul<a maida hankali kan abinci. “gobe in Allah ya Yarda
nakeson tafiya can Kankiya. don sanar wa tsuhuwa tasa albarka”. Yace “Wannan shawara ta yi kyau. Allah ya kai mu goban lafiya’. Yace “Amin”. Zuciyarsa cike da farin- cikin samun makwabci na gari irin Alhaji Abdul-Rashaad. Ana gayawa yaran. anan za su zauna gidan Alhaji ” Abdul-Rasheed. yara suka hau tsalla da murna. Wai dama su basu son komawa kauye. Abbansu ya saki baki yana kallnnsu kafin yace. ; ‘ ‘
“Karyar banza kukeylli  marasa kunya. in gaya maku asalin ubanku kauyene, saboda haka kuma kauyawan ne’. Duk suka hau ihu, “Ah, Abba mu ba ‘yan kauye bane. A Kaduna aka haife mu”. , _
Ya zaro ido “Eh lallai ne. toku sauraraneni da kyau ku jini ga Kankiya. inda Gwaggo take? Can muka fito nida uwarku, kuma can ne makomarmu, duk ranar da bukatar hakan‘ ta taso. Kun fahimceni? Kuke wani bangara baki, wai an haife ku a Kaduna. shi kenan kun zama ‘yan birni”. Suka hau dariya. suna kallon juna,
Hajiya Aliya ta fito da tsuhon cikin ta wata bakwai. ta zauna taci—gaba da tsokanar yaran tare da kara jaddada masu asalin tushen su.
gidan Alhaji Abdul-Rasheed ya kasance cike da yara maza har hudu. kowa ya san an hada kinji. Surutu sam baya damun Hajiya Suwaiha. kula take yi da su susai
tsakaninta da Allah. Shi kuwa Alhaji bai gazaba wajen tattalinsu da biya masu bukatunsu daidai kar‘fin sa. ‘ Kullum karfe bakwai da rabi direbansa ke kwashe su, ya ‘aje makaranta, sannan ya dawo ya dauki alhajin ya kaisa ofis. Karfe hudu ya koma ya kwaso su. ya sake, wuceWa ofis zuwa karfe biyar’ ya dauko Ubangidansa.
Al’amura gwanin dadi daban sha’awa. Sukaci gaba da tafiya, ba kasafai Alhaji Bara’u yake zuwa ganin yaran
ba, duk da cewar kusan kullum yake zuwa Kadunan saboda anan babban ofishinsu yake
Watau anan yake tafiyar da ayyukan da suka shafi ofishinsa har zuwa lokacin da Hajiya Aliyaa ta haihu. Kuma akayi sa’a, ranar asabar ta haihu. Murna kawai yaran sukeyi da dokin son _zuwa su ga ‘yar qanwarsu. Amma Alhaji‘yace sai suna’za’a tafi gaba daya. ‘ .
Kafin ranar. juma’a shiri ya gama kankama, suna dawowa makaranta sha biyun rana suka sake Sheqa wanka, sukayi shirin masallaci, karfe daya daidai direba ya iso da Alhaji.
Ya shige gida. Magaji na .binsa .da ledoji a hannunsa. Yaran suka tarbe shi da murna, ya amsa cike da farin-ciki kamar yadda yake ji kullum cikin zuciyarsa tamkar’ ‘ya ‘yansa.
Hajiya Suwaiba na zaune gefe tayi masa sannu da zuwa, ya amsa, sannan ya zarce da fadin “Bamu da
lsasshen lokaci. ga kayan cin suna nan an karbo daga dinki. Ku gani da sauri mu wuce masallaci, muna dawowa. Insha-allahu zamu wuce Fambeguwa”.
“Yara Duk suka hau ihu yayin da Hajiya Suwaiba ke fadin “lye! Babu shakka. Toni ina nawa?” ‘ ; ‘
Yace Baki bukata Maman yara”. Tace “Gaskia ne”. Lafiyayyar shadda ce mai tsada aka danqara masu aiki, ga kuma yadin kaftan,_ shima ya aikatu da sirfanin hannu.
Kaya sun yi kyau. shiyasa farin-cikin yaran ya kara karuwa, kokari suke yi su sanya a jikinsu. alhaji ya
‘hana. Ya kada su suka wuce masallaci don sallatar juma’a‘.
Karfe hudu daidai motar Alhaji na shiga rukunin gidajen hukumar bunkasa kogin Niger da raya karkara reshen Fambeguwa. Katon wuri ne mai kunshe da sababbin gine-gine masu kyau da tsari, tamkar yadda- gwamnatin take da kyakkyawan tsari wajen yin ayyukanta dake zuwa ga talakan kasa. Motar na tsayawa, gaba daya yaran sukayo waje.
Suleman ne kan gaba, don yafi kowa kosawa a kawo garin. Hannu biyu ya kame kugu ya gantsare, yana kalle-kalle har’ su Mansir da Nasiru suka wuceshi. Khaild
yabi bayan su. Hajia Suwaiba ta iza keyarsa.
Shi kuwa Alhaji Abdul-Rasheed karfe shida ya yi niyyar komawa Kaduna. don haka yayi sallama da kowa. ya juya abinsa Washe gari shagalin yaci-gaba da gudana. yarinya taci suna Murjanatu. Su kuwa su Suleman tunda cikin su ya dauka. .
Suka bazama yawo cikin kwatas din, kasancewar sa babban wuri dajin Allah. Debi da kanka. Sun sha adonsu da sababhin kayansu. Ko dama Alhaji Bara’u ya dinka masu na cin suna din har da Sulaman.
, ganin suda sababbin kaya. ya sanya shi farin- ciki tare dayiwa Alhaji Abdul-Rasheed addu’ar’ fatan alhairi.
A washe gari lahadi, suka sake gwangwajewa da kaftan. karfe sha biyu, ya kwashesu ya maida gida Kaduna. Yayin -da jama’ar Kankiya sai ranar litinin suka
koma. aka bar Mai-jago taci-gaba da’ rainan bebinta. watau Mur’janatu.
‘3 BAYAN SHEKARU TAKWAS!

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

shekaru ne da Alhaji Abdul-Rasheed ya . matsaloli a ma’aikatarsa. Tun dauke. Alhaji Bara u a
matsayin mataimakinsa. Allah baisa ya samu na kwarai ba. ‘
Duk bayan shekaru biyu. gwamnatin tarayya ke; masa canjin mataimaki, amma duk wanda yazo, yakan zo da tasa matsalar.
Mr. Santos, dan kasar Filifins ne kadai Alhaii Abdul-RasHeed yaji’dadin aiki da shi kuma yake kan jin dadin zaman dashi. domin shine mataimakinsa a halin yanzu.
Amma’kash! A ‘yan tsakanin ‘nan ne yake shirye- shiran komawa kasarsa,-shiyasa gwamnatin taryya ta sake turo Mr. Bulogun yazo ya karbi kujerar, Mr. Santos.
Tun daga ganawar farko da sukayi, hankalin
Alhaji Abdul-Rasheed bai kwanta dashi ba. Harya iso gida a yammacin’yau, zuciyarsa na tunanin Mr. Bulagun, ’kuma bai san dalilin da yasa hakan ba.
Motarsa tayi fakin kofar gida; Suleman ya fito da saurinsa ya tarbi Alhajin “Sannu da zuwa Baba!” Yana far‘a’a ya amsa Dogo da hankali’dacene  ina sauran ‘yan- uwanka?” ‘
idanuwanta runtse sabuda jiri daya “sata ganin duhu, kafin ta tashi ta shiga kicin ta dauko masa abincinsa, ta, same shi dakinsa, ya rage kayan jikinsa yana kashingide yana hutawa. Ta nufi inda wata darduma ke shimfide ta aje. ‘
A can ya sameta shima ya zauna, ta zuba masa – kuskus da miyar kayan lambu. Yace “Kina fama da kanki. kike wannan wahalar?” Tace “A’a Wallahi, nima irin miyar na ke sha’awa kenab, shiyasa na daure nayishi yai murmushi.
Yace “Ai laifinki ne. kin hana a samu mai tayaki ‘
aiki. gashi ke ’yayan duk maza ne, babu mai iya kauda miki kara, sai dai masu karo miki”. ‘
Tace “Ba wannan matsalar ta, dameni ba Alhaji …… ” Ya kai abinci baki, Sannan Yace “Menene matsalarki Hajiya ta?” Ta gyara zama ta jingina da ~ bango sosai. Tace “Alhaji, a. kullum tunani na yawan shekarun mu dake kara shudewa, a koda yaushe.
‘ ldan na fadi daidai ina ganin a yanzu kaba shekaru hamsin da shida baya, yayin dani kuma nake shirin kama arba’in da biyu. Abinda nakeso ka fahimta
anan. Alhaji da gani har kai mun fara kama shekarun gangara.
Sai fatan’ gamawa da kalmar. shahada. Amma
kai nan Alhaji ya kamata’ ka gane cewa Magaji yana da  muhimmanci a kowane al’umma kuma nasan su gwaggo
zasuso suga ‘kwanka, kasancewar, ka Da namiji tilo. wanda suke gani suna jin dadi.
Hausawa kuwa na cewa abin cikin kwai. ya fi kwan dadi. ldan kuwa hakane, tabbas su Gwaggo sunyi hakuri, ya kamata mu san halin da muke ciki”.
Ya aje cokalin dake hannunsa  yayi mata zuru. “Ban fahimcekiba Suwaiba? Wata magana ki‘ka ji daga wajensu?” Ta girqiza kai “Ko kadan, amma zai zama rashin adalcina, idan nasa ido wannan zaman namu yaci-gaba a haka. alhalin kullum zuciyata tana ban shawarar inbaka dama ka qara aure, wata kila rabon ba a jikina yake ba …… ” ‘
Baki bude yaké kallonta; “Wannan wane irin zuciyace taba ki shawarar nan Suwaiba?” Tace “Mai sona da adalci Alhaji, ina ganin kuma tayi daidai.
‘ Tunda an kusa gama gininka na Tudun Wada, toka sami ko bazawarace ka aura. Wata qila ka sami rabonka Alhaji. Wallahi da gaske’nake maka maganar nan,
Ya numfasa yana kada kai, kafin. Yace’ “Naji jawabinki, amma kibani dan lokaci nima in shawarci tawa zuciyar. Ni yanzu damuwa ta maleriyar nan data kici, taki cinyewa. Shi yasa nace muje babban asibiti, tunda magungunan kilinik din nan basu yiba”. Tace
“Shikenan, amma ldon Allah, Alhaji kar kace min a’a”.
Yace “Don me zance miki a’a. idan har eh din ne hakikanin abinda ya dace? Ki kwantar da‘hankalinki insha-Allahu zamu sami magada masu albarka.
idan kuma Allah bai nufa ba, aigasu Suleman nan. su ma ‘yayanmu ne. Allah kadai yasan dalilin da yasa muka jawosu jikin mu. Wata kila sune zasu rikemu’ idan karfinmu ya kare. Ni Wallahi danaji kin ca akwai magana, na zaci akan kin zuwan Suleman laburari ne”:
Tayi dan murmushi tace “Aini Suleman ya girmeni tunda ya kereni tsawo, idanuwansa na‘ hango tsakiyar-kaina.
’ Yace “Duk ranar’ da ki ka gaya masa abu baiyi ba, ki taka kujera, ki tsinka masa mari, zai tabbatar da cewa
ke kika haifeshi, dale yabi maganar ki. kuma na gaya masa kar ya kuskura. in sake dawowa in tarar an tafi
an barshi”; Tayi’yar dariya. Tace “Alhaji kenan, in taka
kujéra fa kace?  daga nan axo anamin dariya ko?” Shi kansa dariyar yakeyi. Tace. ‘
“Uhn’, dama zugani kakeyi. don ayimin dariya?” Yace “Dama kullum sai nayi duk in kina  cikinsu, zabga-‘zabga dasu, a raina nake fadin girman Da, babu wuya wurin Allah”.
Suna cikin’ dariya  samarin duk suka  sanyo  kai cikin falon “Mamanmu, Ina babanmu?”.
ya amsa, “gani nan. kun dawo?” Sukayi sallama dakin “Mun, dawo. Baba sannu da zuwa7 Ya amsa yana duban su, Har sun juya zasu fita. ya kirasu. ‘
_”Kai kuxo nan”. Suka dawo gabanSa suka zube. “Meyasa inzaku tafi laburari, bakwa tasa Suleman kuje tare?” Mansir. Yace’ “Baba kasan halin Suleman. idan yace bayayin abu, babu .wanda ya isa ya sashi …… ,
Ya katse shi “Nina isa, so duk lokacinda yace bazaiyi abinda ya kamataba ka tabbatar da ka sanar dani”. Yace “To Baba Dama kuwa ina son gaya maka;
Suleman ya daina zama ayi karatun asuba dashi.‘ Da zar’ar an ,idar da sallah, yake tserewa gida”. “Shi Suleman din?” Hajiya Suwaiba ta café. ‘
– “Kaji ko? Nima ban san yana hakan ba Wallahi.‘ Shiyasa tuntuni bakaji na fada makaba. Kuma koda na sanin, koda na ‘gaya maka cewa zaiyi  karya ce nayi masa gulma ne, kuma baya yin hakan; sai yaga baka nan kayi tafiya’
Yacé “Kyale dan butar kasa. .ku kiramin shi Khalid”. Ya tashi‘da sauri ya fice, yayin da Alhaji keci- gaba da fada “me  Sule keso ya zama ne? Yayi
tsawon kafa ko? Ko kuma yana bin wasu lalatattun yarane  a School?”
Ya tambaya yana kallon Mansir. Ya kada kai. Yace “A’a Baba, duk abokansa ne nada bai sauya wasu ba”
Shigowarsu ceta dauki hankalinsu zuwa garesu “Dawo nan kusa dani, ka tsugunna. idan ta kaiga kasha duka ne; basai nai wahalar kamoka ba”.
Ya fara raba ido yana ‘kallonsu Mansir. Ya tsugunna gefan Alhajin‘yace me nayi Baba?” Yace
Dame-dame ka sani cikin boko da Muhammadiyya DA  har ka fara zukewa a neman ilimi?” Yayi shiru. kai sunkuye. “Watau kai har kayi , ‘ girman da zaka fara gudun karatun asuba? To ‘koni ina zama inyi, idan har na sami lokacin yin hakan balle kai da yanzu ka tsoma yatsa. To saurareni, ina son wannan ya zama na farku kuma na karshe. Banason in sake jin “ magana makamanciyar wannan, ai kajini?”
Ya_yi shiru, fuska kunbure “Duk inda ‘yan uwanka zasu neman ilimi, ka tabbatar da kana cikinsu, kamar yadda nagaya maka dazu. Ina son dukkanku ku sani. ilimin nan ne kadai zamu baku, ya zama gata a garaku duniya da lahira. muddin kukayi amfani dashi yadda ya kamata. Ina fatan Suleman yajini?”
Yace “Naji Baba, ka yi hakuri”. Yace “Nayi. shi kenan ku tashi. Allah ya yi maku albar’ka”. duk suka amsa da”Amin”. Banda Suleman, haushi ya hanashi amsawa. Su Mansur sun yi masa gulma. Suka bar dakin. su ukun suka shige dakinsu, shi kuwa Suleman waje ya
fita, haushi kamar ya kashe shi.

Www.Facebook.com/abdullahi.ismail.salanke

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]