[Advertisements⬇️]

Makaranta duniya chapter3 - Bankinhausanovels
Thu. Jun 8th, 2023

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Makaranta duniya

        Chapter3

Dukda bugunda zuciyar tasa tai haka yai qarfin hali yabi su malam saddiq din qofar gidan NASA hango imam din sukai rirriqe DA jama,a yana tirjewa yana sumbatu iri iri waiya zubillahi
Alhaj ya dafe qirjinsa yana fadin allahummah ajirni fil musibati
Bai Iya motsawa daga inda yake tsaye ba malam saddiq ne ya taryesu muddasir ya yaimaka masa sukayo cikin falon alhaj din dasu salatin DA alhaj yaketa kwararowa ita ta jawo hankalin matarsa suwaiba dake can dakinta jiyo hakanne ya tabbatar mata DA ba lafiya a falon Mai gidan Nata don haka cikin sauri ta nufi falon tana tambayan lfy mudassir yace yaya imam ne yaya imam ne mama tace meya sameshi?murya na rawa ya amsa ya haukace ta dau salati ta dire ta matso gabansa sosai inda malam saddiq keta rattafo masa addu,oi
Hawaye suka kubce mata tace imam meyai maka zafi haka?wannan wane irin rash imanine imam yanxu Ina amfanin wannan abun ?
Kan kace kwabo labari yayI tambari qwar gidan alhaj abdurrashid ya cika DA jama,a  wasu Nata bada shawarar a wuce dashi asibitin mahaukata kawai wasu kuma na fadin ai masa ruqiyyah qila shafar aljanune Amman babu wanda akai cikin biyun don shi Alhaj yasan matsalar imam bata shafi aljanuba damuwace kawai haka dai suka kasance har gari ya waye DA abudai yaqici yaqi cinyewane sai kawai washe gari suka yanke shawarar a kaishi babban asibitin dake shika saidai inda matsalar take shine babu kudi kwarama malam saddiq dakeda dubu biyar a aljihunsa Amman Alhaj kuwa
Dubu biyine kacal dashi cikin ikon Allah wani a anguwan nasu yac ga motarsanan ya bada a kaishi ba tare DA bata lokaciba aka cika motar damai sai babban asibiti dake shika  a bangaren masu tabin hankali  likitoci suka basu gado
Daganan takardun bimcike DA magunguna suka biyo baya abindai babu sauqi kudi aqallah suna Neman sama DA dubu chasa’in ne nandanan hankalin Alhaj ya tashi  back tare DA bata lokaciba  yace zaisa tsohon machine dinsa DA yake zuwa gona DA ita  a kasuwa malam Saddiqa ya duba yaga to ai koda ansa mashin din a kasuwa ba zata wuce dubu ashirinba nan take shawara ta fado masa ya Kira shugaban ma,aikatan DA yake aiki yai masa bayanin abinda ke faruwa Allah cikin ikonsa manajan kamfanin ya amince jin cewan yaron harda digirinsa yace koba komai zai amfani alumman nan gaba Alhaj abdurrashid harda hawayen murna lallai  alkhairi gadon barcine idan kayi tabbas kaima baka rasawa
Nandanan aka aiwatar DA dukkana abubuwan DA likitoci suka buqata Cikin gaggawa bincike ya fito DA abin Al,ajabin DA yaba kowa haushi DA takaici
Bincike ya nuna imam bashi Da wata Matsala illa muggan kwayoyin Daya banka sukafi qarfin qaqalwarsa su suka zautar dashi sukasa yabi titi baisan inda yakeba wata qila kuma akwai rashin sabo ma,,ana bai taba shaba wannan shine karonsa na farko  kowa yai turus Al,ajabi ya kamasu Alhaj DA hajiya suwaiba basu taba tunanin imam zai Iya aikata irin wannan rashin hankalinba
Shin wanna wane irin haramtaccen sone  mudasiir yace  Allah ya isa kukan DA nayi kwanana yau uku kenan banyi barciba hajia suwaiba tace ka fadi daidai muda ni kaina badan uwarsa bace  abinda Zan fada kenan
Alhaj ya numfasa gamida cew KO ba,a aunaniba ni nasan jinina yahau  gaba Daya gabobina daqar nake Iya sarrafasu imam yayI rashin tunani Da yawa Amman ba yaddah muka Iya dole muyi haquri mu dubi uzurinsa
Dukda cewa mamaki bazai fita daga zukatanmu ba
Malam Saddiqa shi kadaine yasan musabbabin abinda ke damun imam a anguwan nasu  Amman jama,ar anguwa kowa yasan yaran alhaj abdurrashid
Natsatstsun yarane masu hankali DA sanin ya kamata gamida sanin girman na gaba dasu
Ana wata ga wata kwana shiddah DA kwanciyayar imam a asibity don daman likita yace imam baxai taba komawa daidai ba har sai kwayoyin DA yasha sun gama aiki  a hakane har aka dibi kwana shida a rana ta shiddanne aka kwara ruwa Mai qarfin gaske don haka washe garin ranan DA sassafe mudassir DA Alhaj suka Iso Kaduna Alhaj  yace maza dauko mashin gona zamu idan mukaga komai lfy Alah bishshi gobe saimu koma asibitin yace  to shikenan mudassir dinne ya Goya Alhaj din lafiya lafiya suka isa gona suna hirar abubuwan Daya damesu
Ruwakam yayi qyara a wasu guraren Amman Allah ya tsare gona Alhaj abdurrashid gefe kadanne ruwan ya tafi dadan amfanin gonan
Suna zagayawa tare DA alhinin aikinda ruwan yayi kawai mudassir yaga Alhaj ya yanke jiki ya fadi kamar fadiwar Yan bori DA Saudi ya qaraso wajensa yana subhanallahi baba sannu  Ido ya kura masa kuri ba amsa kamar Wanda ya warke daga ciwon makanta mudassir bai ganeba shima ya tsugunna gabansa ya qura masa Ido baba yaya dai? Bai amsaba kuma nan  take  yaga bakinsa ya Fara karkacewa kai !ya firdo Ido warwaje yace  baba!baba!!gani gawai yai ya tafi luuuuuuuuuuuu

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

Naku hard kullun

Www.Facebook.com/abdullahi.Ismail.salanke

[Advertisements⬇️]

[Continue Reading⬇️]

By AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

[Advertisements⬇️]